WAJABCIN AIKI DA SUNNAR ANNBIN ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA KAFIRCIN WANDA YA MUSANTA HAKAN
3
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin TalikaiKuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu jin tsoron AllahKuma tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Bawansa kuma manzonsa Annabi Muhammad wanda aka turo shi ya zamo rahama ga dukkannin halittu ,ya kuma zamo hujja ga Daukacin bayin Allah baki daya.Kuma da Iyalansa da kuma Sahabbansa wadanda suka riki littafin Ubanngijin su da sunnar Annabinsu tsira da aminci su kara tabbata a gare shi har zuwa ga wadan da suka zo a bayansu da amana da cikakkiyar kiyayewa ga ma’anoni da laffuza yardar Allah ta qara tabbata a garesu Allah ya sanya mu daga cikin wadanda zasu biyo bayansu da kyautatawa
Bayan haka
To hakika Malamai Ra'ayinsu ya zo daya na da da na yanzu kan cewa Ginshikin abubuwan da ake lura da su wajen tabbatar da Hukunci, da kuma bayanin Halal da Haram cikin littafin Allah Mabuwayi wanda Barna bata iya shiga cikin sa ta gaba ko ta bayansa.san nan sunnar Manzon Allah tsira da aminci su qara tabbata a gare shi Wanda baya Magana akan son zuciya sai kadai abinda aka yi masa wahayin shi.San nan abin da manyan Maiamai suka hadu akan shi akwai kuma wasu tushen da Malamai suka yi sabani akan su mafi muhimmanci shi ne kiyasi amma mafi yawan su sun tafi akan cewa hujjane idan ya cika dukkanin sharudan da suka kamataKuma dalilai akan haka suna da yawa yawan da ba za su Kididdugu ba mafi shahara daga cikin su su ne
Tushen da suke bayani kan tabbatar da hukunce hukunce
Tushe na farko: shine littafin Allah mabuwayi
Amma tushen farko: shine littafin Allah mabuwayi
kuma hakika zancen Ubangiji ya nuna a wurare da yawa na littafin Allah kan wajabcin bin wannan littafin da kuma riko da shi da tsayuwa akan dokokinsa.
4
Allah Madaukaki ya ce
Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
kuma Allah Madaukaki ya ce
Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
kuma Allah Madaukaki ya ce
Haqiqa Manzon Mu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah.
Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
kuma Allah Madaukaki ya ce
Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.
arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.
kuma Allah Madaukaki ya ce
’An yi min wahayin Wannan Alqur’anin dan na gargade ku dashi wa ye ya isar
kuma Allah Madaukaki ya ce
Wannan Sako ne ga Mutane kuma don ayi musu gargadi da shi
Ayoyin da suka zo da wadannan ma’anonin suna da yawa Hadisai ingantattu sun zo daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da suke umarni da riko da Alqur’ani da tsare shi
5
suna nuni da cewa wanda duk yayi riko da shi to hakika yana kan shiriya wanda duk ya bar shi kuma haqiqa yana kan bata
Daga wannan da wani abinda ya tabbata daga Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shi, yana cewa a cikin Hudubarsa ta Bankwana :
’Hakika na bar muku abinda in kun rike shi ba zaku Bata ba ku yi riko da Littafin Allah
Muslim ya rawaito shi a cikin Sahih din sa
Acikin Sahih Muslim ya rawaito kuma cewa Zaidu dan Arqam Allah ya qara yarda da shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa:
Lallai na bar muku abubuwa biyu Littafin Allah cikinsa akwai shiriya da kuma Haske to ku riki littafin Allah kuma kuyi riko da shi.
Ya kwadaitar a kan Littafin Allah san nan yace:
Ahali na Ina tunasar da ku Allah akan Ahalina Ina tunasar da ku Allah kan Ahali na
Awani lafazin yana cewa a cikin Alqur’ani:
Shi Igiyar Allah ne duk wanda yayi riko da ita to ya kasance a kan shiriya kuma duk wanda ya barta to ya kasance kan Bata.
Hadisai da suka zo da wannan ma’anar suna da yawaAcikin abinda Ma’abota ilimi da kuma Imani daga cikin Sahabbai da kuma wadanda suka zo a b ayan su kan wajabcin riqo da Littafin Allah da yin hukunci da shi tare da sunnar Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shiba zai is aba ba kuma zai warkar ba wajen tsawaita ambaton dalilai da suka zo kan hakan .
Asali na biyu: Abinda ya inganta daga Manzon Allah tsira da aminncin Allah su kara tabbata a gare shi da Sahabban sa da Wadanda suka zo bayansu daga Ma’abota Ilimi da Imani
6
Amma Asali na biyu: daga cikin gishikai uku wadan da aka hadu akansu shi ne abinda ya inganta daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata da kuma Sahabban Annabi da kuma wadanda suka biyo bayansu daga cikinsu na Ma'abotan Ilimi da Imani sunyi Imani da wannan ginshiki mai tushe kuma suke kafa Dalili da shi kuma suka koyar da shi ga Al'umma.sun wallafa Litattafai da yawa kan hakanSun bayyana haka a cikin Littattafan Usulul Fiqihu da MusdalahuDalilai kan hakan ba zasu kirgu baDaga cikin su abinda ya zo a cikin Littafin Allah Mabuwayi na daga umarni da bin abinda yazo da shi da kuma biyayya gare shiWannan ya gabatar da shi zuwa ga mutanen zamanin sa da wadanda za su zo a baayansu saobda shi Manzon Allah ne zuwa ga Mutane baki dayaAn umarce su da su bi su kuma yi biyayya a gare shi har ya zuwa ranar tashin AlqiyamaDomin cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi shi mai fassara Littafin Allah kuma mai bayyana mafi kyawun abinda ke cikin sa ta hanyar aiyukansa da maganganunsa da kuma abin da aka aikata a gabansa bai hana bakuma ba don Sunnar Annabi ba da Musulmi basu san yawan Raka'o'in Salloli ba da kuma Sifofinsu da kuma abinda ya wajaba a cikinsu.Kuma da ba zasu san banbance-banbance ban a hukunce hukuncen Azumi da Zakkah da Hajji da Jihadi da kuma umarni da mai kyau da kuma hani da mummuna,kuma da ba za su san banbancin hukunce hukuncen mu’amala da abubuwan da aka haramta da abinda Allah ya wajabta akansu na daga iyakoki da uqubobi.
Daga Ayoyin da suka sauka kan haka
Ayoyin da suka sauka kan haka sune fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratu Aali Imran :
Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da Manzon Sa, tsammaninku a yi muku rahama.
Da kuma fadinsa Madaukakin Sarki cikin Suratun Nisa'i
Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan
7
kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
Da kuma fadinsa Madaukakin Sarki cikin Suratun Nisa'i kuma dai.
Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu.
Ta yaya biyayya a gare shi za ta yuwu da kuma raddin abinda mutane suke riyawa akan Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah idan Sunnar ta shi ta kasance ba’a da buqatarta ko ta kasance ba’a kiyaye ta ba.kan wannan zancen sai ya zamo Allah ya dora bayinsa kan abinda ba za’a same shi baWannan yana daga vatacciyar vata kuma mafi girman kafirci ga Allah da kuma munana Masa zato
Allah Madaukakin Sarki yana cewa a cikin Surat Annahl
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni.
Ya kuma fada a wata Ayar acikinta
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
Ta yaya Allah Madaukakin Sarki zai qyale Manzonsa ya na bayyana matsayinsa da Sunnarsa cewa basu da wani wuri ko ba wata hujja a cikinta ?
Misalin haka shine fadar sa acikin Suratun Nur:
Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna."
Allah Madaukakin Sarki yana cewa acikin wannan Surar dai :
8
Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama.
Yana kuma fada a cikin Suratul A’raf:
Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."
Acikin wadannan Ayoyin dalilai ne bayyanannu da suke yin nuni akan cewa akwai shiriya da rahama acikin bin Annabi sallallahu alaihi wa sallam ,to ta yaya hakan zata kasance ba tare da aiki da Sunnar shi ba ko kuma fadin cewa bata da wani inganci ko kuma kar a dogara da ita ?
Allah Madaukakin Sarki ya na cewa a cikin Suratu Nour
To wadanda suka saba Umarninsa su kiyayi kansu kada Musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma Azaba mai radadi ta same su
Yana kuma fada a cikin Suratul Alhashr:
kuma duk abinda Manzo ya baku shi to ku karbeshi kuma duk abinda ya haneku ga barinsa to ku hanu ga barinsa.
kuma Ayoyi a cikin wannan Ma'ana masu yawa kuma dukkansu suna nuna wajabcin biyayya ga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma bin abinda yazo da shi, kamar yadda ya gabata a dalilan wajabcin bin littafin Allah da riko da shi da kuma bin umarninsa da hanuwa da haninsa.Tushe ne guda biyu ababan lazimta wanda duk ya lazimci daya to ya lazimci dayan wanda kuma ya qaryata su ya kafirta ya fada cikin fada ya fita daga da’irar Musulunci a gabaki dayan haduwar Malamai
Daga abinda aka rawaito daga Hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi
9
Hadisan Manzon Allah tsira da aminci su qara tabbata a gare shi sun zo kan wajabcin biyayya agare shi tare da bin abinda ya zo da shi da haramta sava masa kuma wannan haka yake ga wadanda suka zo a zamaninsa da kuma wadanda suka biyo bayansu har ya zuwa ranar tashin Alqiyama ,Daga cikin abinda aka tabbatar acikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim daga Hadisin Abi Huraira yardarm Allah ta qara tabbata a gare shi ,cewa Annabi tsira da aminci su qara tabbata agare shi yana cewa:
Duk wanda ya bini to hakika ya bi Allah kuma duk wanda ya saba mun to hakika ya sabawa Allah.
Acikin Sahih Muslim ya rawaito kuma cewa Zaidu Dan Arqam Allah ya Kara yarda da shi cewa Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa.
Kowanne daga cikin Al'ummata zai shiga Aljannah sai wanda yaki to waye ma zai ki ya Ma’aikin Allah ?Sai yace wanda duk ya yi min biyayya zai shiga Aljannah wanda kuma ya sava min haqiqa ya qi’’
Kuma Ahmad ya fitar cewa da kuma Abu Daud da kuma Hakim da Isnadi Ingantacce, daga Mikdam bin Mu'addi Karib daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi cewa ya ce:
‘’Ku saurara haqiqa an bani Littafi da kuma kwatankwacinsa a tare da shi shin ba za ku yi shakkar mutum ya koshi yana kishigide kan Karaga yana cewa da ku kan wannan Alqur’anin abin da kawai kuka samu cikin sa na halal ku halarta shi kuma duk abin da kuka samu na haram a cikin sa ku haramta shi
Abu Dawud da Ibn Majah sun fitar da shi da Isnadi ingantacce :An karvo daga Abi Rafi’ daga baban shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:
’Zai yuwu Daya daga cikin ku yana kishingide akan shimfida umarni nay a zo mishi na yi umarni daaikatawa ko wani hani daga gare ni na yi hani da aikatawa sai ya ce ban san shi bad an ban gani ba a cikin littafin Allah da na bi shi
10
An karbo daga Al Hasan Bn Jabir yace naji Miqdam Bn Ma’di Karb Allah ya qara yarda da shi yana cewa:
‘’Manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata a gare shi ranar yaqin Kaibara ya haramta wadansu abubuwa sa’annan ya ce shin dayan ku ba zai yi shakka ba ya qarya ta ni ya ji hadisi na sannan yace atsakanin mu akwai Littafin Allah abinda kawai muka samu na halal daga cikinsa shi zamu halarta wanda kuma muka samu na haramun daga cikin shi shi zamu haramta haqiqa duk abinda Manzon Allah ya haramta dai dai ya ke da abinda Allah ya haramta.
Hakim da Turmizi Ibn Majah sun fitar da shi da isnadi ingantacce
Hadisan Manzon allah tsira da aminci su qara tabbata a gare shi sun zo cewa Annabi ya yiwa Sahabban sa wasiyya a hudubar cewa wanda ya ke nan ya isarwa wanda bayanan yana cewa da su Ubangiji mai isarwa ne ga wanda ya ji
Ya zo a cikin ingantattu guda biyu akan wannan cewa Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shi loqacin da yayi hudubar ban kwana ga mutane ranar Arfa da kuma ranar yanka yana cewa da su
Wanda duk ya ji ya isar ga wanda baya nan
To ba don cewa Sunna Hujja ce ga wanda ya ji ta da kuma wanda aka gayawa kuma ba don cewa ita wanzazziya ce har zuwa ranar Alkiyama bai umarcesu da isar da ita ba sai yasani cewa lallai Hujjar Sunna tana tsaye akan wanda yaji ta daga bakin Annabi Amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma wanda ya karbo ta izuwa gare shi ta hanayar Sanadanta ingantattu.
Hakika Sahabban Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shi sun kiyaye Sunnar sa wacce ya yi ta Magana da ta aikace sun isar da ita ga wadanda suka zo bayansuHaka yardaddun Malamai suka isar da ita Al’ummah bayan Al’ummah ,karni bayan qarniSuka tare su a cikin litattafansu kuma suka bayyana ingantattunsu daga raunanan su.suka sanya qa’idoji da dokoki wanda da su ne za’a gane ingantacciyar Sunnah da mai raunikuma hakika Ma'abota Ilimi sun yi maganar litattafan Sunnan na daga Bukhari da Muslim da wasunsu
11
kuma sun haddace su cikakkiyar haddacewa kamar yadda ya kamata kamar yadda ya kare shi daga wasan masu wasa da kuma batattun masu bata, da batawar masu barna, don tabbatar da Dalili yake nunawa akansa fadin Allah Madaukaki.
Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
Babu shakka cewa Sunnar Manzon Allah tsira da aminci su qara tabbata a gare shi wahayi ne saukakke.Hakika Allah ya tsare Sunnar Annabinsa kamar yadda ya tsare Littafinsa ya sanya mata Malamai suna shafe mata Batancin masu vata da fassarar Jahilai suna goge mata duk wani abinda jahilai da maqaryata suke shafa mata.Saboda Allah Madaukakin Sarki ya sanya ta fassara ce ga Littafinsa mai girma kuma bayanin da zai kyautata hukunce hukunce wasu kuma hukuncin Alqur’ani bai kawo su ba sai a Sunnar za’a same su kamar rabe raben hukuncin shayarwa da kuma wani sashe na hukunce hukuncen rabon gado da haramta hada Mace gwaggonta ko kuma Innar ta da wasu daga cikin hukunce hukuncen da Sunna ingantacciya ta zo da shi wadanda Alqur’ani bai ambace su ba.
Daga abinda ya zo daga Sahabbai da Tabi’ai da wadanda suka zo a bayan su ma’abota Ilimi
ya kawo abinda aka samo daga Sahabbai da Tabi’ai da wadanda suka zo bayansu wajen girmama Sunnah da aiki da ita
Ya zo a cikin Buhari da Muslim daga Abi Huraira yardarm Allah ta qara tabbata a gare shi yana cewa:
’Yayin da Manzon Allah tsira da Aminci su qara tabbata a gare ya rasu wadanda suka yi ridda daga Larabawa suka yi ridda sai Abubakar Allah ya kara masa yarda yace:
‘’Na rantse da Allah sai na yaki duk wanda ya raba tsakanin Sallah da Zakkah‘’
Sai Umar Allah ya qara masa yarda yace:
12
Ta yaya zaka yaqe su bayan Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa?
‘’An umarceni da in yaki mutane har sai sun ce La’ilaha illallah idan suka fadeta jininsu ya kuvuta daga gare ni d dukiyoyinsu sai dai kan hakkinta ’’
Sai Abubakar Siddiq yace:
’Shin Zakkah bata daga cikin hakkinta na rantse da Allah da zasu hanani Alhalin sun kasance suna bayar da ita ga Manzon Allah sai na yaqe su kan hana ta .
Sai Umar Allah ya kara masa yarda yace:‘’Daga nan na san cewa Allah ne ya bude kirjin Abubakar da yin wannan yaqin na gane hakika akan gaskiya yake,Sahabbai yardar Allah ta karu a gare su sun bi shi kan haka sun yaki Masu ridda har sai da suka dawo da su kan Musulunci suka kuma kasha wadanda suka cigaba da yin riddar,Cikin wannan kissar dalilai sun bayyana girmama sunnah da wajabcin aiki da itaWata Kaka ta zo wajen Abubakar Allah ya qara yarda agare shi tana tambayarsa gadonta sai yace da ita’Baki da wani abu a cikin littafin Allah,ban kuma ga Annabi tsira da aminci su kara tabbata a gare shi hukunta miki wani abu ba amma zan tambayi mutane’’ sai ya tambayi Sahabbai sai wani sashe ya shaida cewa Annabi ya bawa kaka daya bisa shida sai yayi mata hukunci da haka,Umar yardar Allah ta tabbata a gare shi ya kasance yana yiwa Ma’aikatansa wasiyya da su yi hukunci tsakanin mutane da Littafin Allah,idan bas u samu acikin shi basu yi hukunci da Sunnar Annabi tsira da aminci su kara tabbata a gare shiyayin da aka tambaye shi hukuncin macen da tayi Bari saboda ta’addancin da wani yayi mata sai ya tambayi Sahabbai Allah ya qara yarda dasu akan haka sai Muhammad Bn Muslamata da Mughira Bn Shu’uba Allah ya yarda dasu suka ce Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya yi hukuncin akan Bawa ne kowata Baiwa sai shima Allah ya kara yarda da shi yayi hukuncinda wannan
Lokacin da aka zo wa Usman Allah ya kara yarda da shi kan hukuncin takabar mace a gidan mijinta bayan mutuwar mijinta sai aka bashi labara cewa Riy’a yar Maik Dan Sinan yar uwar Abi Sa’id Allah ya
13
yarda da shi cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya umarce ta da ta zauna a gidan mijinta har sai ta cika wa’adinta sai sayyidina Usman yayi hukunci da haka
Haka yayi hukunci da Sunnah wajen tsayar da haddin shan giya akan Walid Bn Uqba.Lokacin da labari ya isarwa Ali allah ya yarda da shi cewa Usman ya hana yin tamattu’i sai Ali Allah ya qara yarda da shi ya yi niyyar hada Hajji da Umra gaba dayaKuma ya ce: Ba zan bar sunnnar Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ba sabida fadin wani Mutum daga cikin Mutane,kuma yayin da kafa Dalili da wasu Mutane akan Ibnu Abbas Allah ya yarda da su wajen Mutu'ar Hajji da fadin Abubakar da Umar -Allah ya yarada da su- a cikin kwadaitarwa da yin Ifradi a aikin Hajji Ibn Abbas ya ce:ya kusanta a saukar muku da Dutse daga sama, ina cewa Annabi ya ce ku kuma kuna cewa Abubakar da Umar sun ce:To idan ya kasance duk wanda ya sabawa Sunnar Annabi don fadin Abubakar da Umar ana jiye masa tsoron Ukuba, to yaya wanda ya saba masa da waninsu daban sabida kawai don ra'ayinsa ko Ijtihadinsa.Loqacin da wasu Mutane suka yi jayayya da Abdullahi Bn Umar Allah ya qara musu yarda akan wata Sunnah sai Abdullahi Bn Umar yace da su Shin an umarcemu ne da mu bi Umar ko kuma an umarcemu ne da mu bi Sunnah?
Yayin da wani Mutum yacewa Imran Bn Husain Allah ya qara musu yarda muna tattaunawa kan Littafin Allah shi kuma yana yi muku Magana akan Sunnah sai Allah ya yarda dashi yayi fushi sannan yace :Haqiqa Sunnah fassarar Littafin Allah ce ba don Sunnah ba da bamu san cewa Azahar raka’a hudu ce ba Magariba uku Asuba biyu da bamu san rabe raben hukunce hukuncen Zakkah ba da wasun su da Sunnah ce ta zo da sun a daga rabe raben hukunce hukunce.
Abinda aka samu daga Sahabbai yardar Allah ta tabbata a gare su kan girmama Sunnar Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare su da wajabcin aiki da ita da tsoratarwa ga duk wanda ya saba mata suna da yawa matuka.Kuma daga wanca nan ka kuma cewa Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda da su- yayin da ya zantar da fadin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.’Kada ku hana bayin Allah mata zuwa Masallaci’’Wasu daga cikin Yayansa suka ce: Mun rantse da Allah sai mun hana shi sai ya yi fushi da Abdullahi
14
kuma ya ya zage shi zagi mai tsanani kuma ya ce: ina cewa Manzon Allah ya ce kai kuma kana cewa na rantse da Allah sai na hana su.Lokacin da Abdullahi Bn Mughaffal Al Muzani Allah ya kara yarda da shi yace shi ya kasance daga cikin Sahabban Manzon Allah wasu da cikin makusantansaKuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:Ya hana harbi da Gwafa (bada niyyar farauta ba) kuma ya ce lallai cewa shi baya farautar abin farauta kuma baya yiwa abokan gaba Azaba sai dai cewa shi yana karya Hakori ne da kuma kwakule Idanuwa kawai.San nan ya sake ganinsa yana harbi da Gwafa sai yace da shi wallahi ba zan sake yi maka Magana ba tunda nace maka Manzon Allah ya hana amma ka koma ?
Baihaqi ya fitar daga Ayyubu Al-iktiyani Tabi’I ne mai girma ya ce::
Idan aka yiwa mutum Magana akan Sunnah sai yace kyale mu da wannan ,ka bamu Labari akan Alqur’ani to ka sani wannan Batacce ne,
Al-Auza’I Allah ya kiara yarda da shi yana cewa Sunnah itace mai hukunci akan Littafin Allah ko yin qaidi kan abinda aka bar shi a sake kohukunce – hukuncen da ba’a ambata ba acikin Alqur’ani kamar cikin fadar Allah Madaukakin Sarki:
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni.
Fadar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ta gabata
‘’Ku saurara Ni an bani Littafi da kwatankwacin sa tare da shi
Baihaqi ya fitar da shi daga Aamir Assha’abi Allah yayi masa rahama yana cewa da wasu mutane:Hakika kun halaku tun lokacin da kuka rabu abin da Annabi yagadar mukuYana nufi da wannan ingantatun HadisaiBaihaqi ya kuma fitar da shi daga Al Auza’I Allah yayi musu rahama yana cewa: yana fadawa wasu daga cikin abokansa idan an zo muku da da wata Magana an ce daga Manzon allah na hane ku
15
da kuce ba itaba wanin ta domin cewa shima Manzon Allah daga wajen Allah Madaukakin Sarki ya zo da shi
Baihaqi ya kuma fitar da shi daga Al Auza’I Allah yayi musu rahama yana cewa: yana fadawa wasu daga cikin abokansa idan an zo muku da da wata Magana an ce daga Manzon allah na hane ku da kuce ba itaba wanin ta domin cewa shima Manzon Allah daga wajen Allah Madaukakin Sarki ya zo da shi
Baiqi ya fitar daga babban Malami Sufyanus SauriyAllah ya yarda da shi yana cewa ilimi gaba dayansa yana cikin abinda da annabi ya bari.
Malik yana cewa duk wani abu da ya zo daga gare mu abin mayarwa ne sai abinda ya zo daga Ma’abocin wannan qabarin sai yayi nuni da kabarin Manzon Allah tsira da aminci su qara tabbata agare shi.
Abu Hanifa Allah ya yarda da shi yana cewa:
‘’Idan Hadisi ya zo maka daga wajen Ma’aikin Allah to yana kai da kuma ido
Shafi’I Allah ya qara yarda da shi ya ce:
Duk lokacin da naga Hadisi ingantacce daga manzon Allah tsira da Aminci su kara tabbata a gare shi ban kuma dauke shi ba hakika ina mai shaida muku sai hankalina ya gushe
kuma wata fadar yana cewa:
Idan na fadi wata Magana sai Hadisi yazo daga Manzon Allah sabanin abin da na fada ku buga zance na jikin bango.
Imam Ahmad Bn Hanbal Allah ya yarda da shi yana cewa wasu daga cikin Sahabbansa:
‘’Kada ku kwaikwaye ni ko ku kwaikwayi wani Mai mulki ko Shafi’I ku dauka kawai daga inda muka dauko.
kuma wata fadar yana cewa: Allah yayi masa rahama
16
‘’Ina mamakin wasu Mutane sun san isnadi sun ingancinsa daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare amma suna tafiya wajen Sufyan alhalin Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
To wadanda suka saba Umarninsa su kiyayi kansu kada Musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma Azaba mai radadi ta same su
?kuma ya ce: Ko ka san maye Fitina
Fitina ita ce Shirka watakila idan akai watsi da wasu daga cikin maganganun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam cewa wani abu ya fada cikin zuciyar wani na bata sai ya hallaka
Kuma Baihaqi ya fitar daga Mujahid Jubair tabi’I ne mai girma yana cewa kan fadin Allah Madaukakin Sarki:
To idan kukayi Jayayya cikin wani abu to kumaida Hukuncinsa zuwa ga Allah da Manzonsa.
Ya ce: komawa zuwa ga Allah da littafinsa da komawa zuwa ga Manzon Allah komawa zuwa ga Sunna ne.
Kuma Baihaqi ya fitar daga Zahariy Allah ya yarda da shi yana cewa
‘’Wadan da suka gabata daga Malaman mu suna cewa riko da Sunnah tsira ne"
Kuma Muwafiquddin Bn Qudama Allah ya yarda da shi a cikin Littafin Raudhatun Nadhir fiy Bayani Usulul Ahkam abinda yake cewa:
Tushe na biyu daga dalilan Sunnah fadin mnzon Allah tsira da amincin Allah su qara tambaya a gare shi hujja da ta ke shiryarwa kan mu’ujiza tana kan gaskiyarsa sai Allah yayi umarni da ayi masa biyayya ya kuma tsoratar kan sava masa.
Manufar ta kare.
Hafiz Ibn Kasir Allah yayi masa rahama yana cewa a cikin tafsirin fadin Allah Madaukakin Sarki
to wadanda suka saba Umarninsa su kiyayi kansu kada Musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma Azaba mai radadi ta same su
17
Ai umarnin Manzon Allah tsira da amincin Allah su Kara tabbata a gare shi shi ne hanyar da ya bi da shari’arsa da Sunnarsa a auna maganganu da aiyuka da maganganunsa da aiyukansa wanda yayi dai dai da wannan sai a karbe shi wanda ya sava masu sai a mayar da shi ga wanda ya fade ta Makaryaci ne ko waye shi
Kamar yadda ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim da wasun su daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Duk wanda yayi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abun mayar masa ne
Ai lallai wadanda suke sabawa Shari’ar Manzon Allah a zahiri da badini su ji tsorosu kuma fadaku
kar wata fitina ta shafe su
Ma’ana a zuciyoyinsu na daga kafirci da munafurci ko kuma daga Bidi’a
Ko azaba mai radadi ta shafe su
Anan duniya kamar kisa ko haddi ko a tsare su da makamantan haka
Kamar yadda imam Ahmad ya rawaito yace Abdur Raziq ya bamu labari daga shi kuma Mu’ammar ya basu labara daga Hammam Bn Manbah yana cewa:
Wannan ne abinda Abu Huraira y aba mu labari:
Thauban Baron Annabi - Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi
Misalina da misalinku kamar misalign mutumin da ya kunna wuta ne a lokacin da ta haske zagayen da take sai ya sanya shimfida da abin hawan da yake kai a cikin wutar su fada cikinta sai kuma yazo yana son ya kubutar dasu sais u ringaye shi sai ya fada cikinta sai yace haka shi ne kwatankwaci na da ku Ni ina son na kuvutar da ku daga wuta ina kiranku daga gare ta ku kuma kuna sai ku fada cikinta
Suyudi Allah yayi masa rahama yana cewa a cikin wasikarsa da ya sanya mata suna:Miftahul Jannah Fil Ihtijaj Bis Sunnah.ga Nassin:
18
Suyudi Allah yayi masa rahama yana cewa a cikin wasiqarsa da ya sanya mata suna: Miftahul Jannah Fil Ihtijaj Bis Sunnah.ga Nassin:
Ku sani Allah yayi muku rahama cewa duk wanda ya qaryata kasancewar Hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasance wani aikinsa ne ko Maganar sa da sharadi sananne daga tushe ya kafurta ya fita daga da’irar Musulunci za’a tashe shi tare da Yahudawa da Nasara ko tare da wadanda Allah ya so daga wadan da suka kafirta.
Manufar ta qare.
Abinda aka samu daga Sahabbai yardar Allah ta tabbata a gare su kan girmama Sunnar Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare su da wajabcin aiki da ita da tsoratarwa ga duk wanda ya saba mata suna da yawa matuka.
Ina fatan abinda muka ambata daga Ayoyi da Hadisai sun wadatar kuma zasu ja hankalin mai neman gaskiya
Muna roqon Allah gare mu da kuma daukacin musulmai dacewa da abinda Allah ya yarda da shi da kuma kuvuta daga abinda zai sa shi fushiYa kuma shiryar damu gaba daya hanyarsa madaidaiciya hakika Allah Mai ji ne kuma Makusanci
Ya kuma shiryar damu gaba daya hanyarsa madaidaiciya hakika Allah Mai ji ne kuma Makusanci
Tsira da amincin Allah su Kara tabbata ga bawansa kuma Manzonsa Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da Mabiyansa da kyautatawa.
AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz
Allah ya yi masa Rahama
19
WAJABCIN AIKI DA SUNNAR ANNBIN ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA KAFIRCIN WANDA YA MUSANTA HAKAN 1
Gabatarwa ................................................................................................. 3
Tushen da suke bayani kan tabbatar da hukunce hukunce ...................... 3