Labarai

DALILAN ANNABTA(1)


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa, kuma muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da kuma miyagun ayukkanmu. Duk wanda Allah ya shiryar dashi babu mai ɓatar dashi, kuma duk wanda Ya ɓatar babu mai shiryar dashi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawata da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, Allah yayi daɗin tsira a gare shi da iyalansa da sahabbansa, kuma yayi daɗin aminci, aminci mai yawa.


Bayan haka:


Kuji tsoron Allah -yã ku bayin Allah- Haƙiƙanin jin tsoro, kuma ku zama a faɗake dashi cikin ɓoyenku da gãnawarku.


Yãku musulmai:


Allah ya aiko manzanni domin shiryar da halittu, suna kammala Fiɗira [tsarin da Allah ya halicci bayinSa akai na yarda daShi da kaɗaitaShi] da abinda ke tare dasu na hasken wahayi, Suna ƙira zuwa ga bautar Allah, da kuma kyawawan ayukka da hãlaye na gari, kuma bukãtar bayi zuwa ga manzanni itace mafi girma sama da bukãtar su ga abinci da abin sha da numfashi; domin babu hanyar samun kwanciyar hankali da rabauta da samun yardar Allah kwata-kwata sai ta hanyarsu.


Kuma Allah Madaukaki ya kadaitu da cikyakkiyar wadata, da ĩko kammalalle, da ilmi kewayayye, su kuma Manzanni aminci ya tabbata a gare su mutane ne bã sã makallakar wani abu cikin


(1) An gabatar da wannan huɗubar ranar juma`a ashirin da ɗaya ga watan Rabiul Akhir shekara ta dubu ɗaya da ɗari hudu da arba'in da uku bayan hijra, a masallacin Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.


2 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


wadancan ukun [cikyakkiyar wadata, da ĩko, da ilmi kewayayye] sai gwargwadon abinda Allah ya bãsu, Allah Madaukaki Ya cema AnnabinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:





«Ka ce; bance maku a wurina taskokin Allah suke ba, kuma bansan gaibu ba, kuma bana ce maku ni malã'ika ne» [Suratul An’am aya ta: 50]. sai Allah Ya keɓancesu da ãyoyi masu ban mamaki daga cikin ikonSa, da ilminSa, da mulkinSa, domin Ya bayyana wa bayin Allah cewa su Manzannin Allah ne kuma masu gaskiya ne cikin abinda suke bãda lãbãrinsa. Wanda Tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi yãce: «Bãbu wani Annabi cikin Annabawa face an bashi abinda mutane suke ina domin irinsa» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Annabi Salihu -aminci ya tabbata a gareshi- yãzo wa mutãnensa da tãguwa mai girma wacce ta fito daga cikin dutse.


Kuma aka jefa Annabi Ibrahim -aminci ya tabbata a gareshi- a wuta mai girma, amma bata cũtar da shi ba.


Kuma aka baiwa Annabi Musa -aminci ya tabbata a gare shi- ãyoyi tara bayyanannu, kuma ya bugi teku da sanda; sai ya tsãge, kowanne tsãgi ya kasance tamkar dutse mai girma, kuma ya jefa sandarshi sai ta zama kumurci [maciji] mai girman halitta.


Kuma an sanar da Annabi Dawuda da Annabi Sulaimana -aminci ya tabbata a gare su- maganar tsuntsãye, kuma aka bãsu daga cikin kowane abu.


Kuma Annabi Isa -aminci ya tabbata a gare shi- yã kasance yana warkar da makaho, da zabiya, kuma yana rãyar da matattu da izinin Allah, kuma yayi Magana yana cikin zanin goyansa, sai


DALILAN ANNABTA 3


a-alqasim.com


ya kubutar da mahaifiyarsa kuma ya kadaita Ubangijinsa.


Kuma yana daga cikin ayoyin da ke bada shaida game da gaskiyarsu: Abinda aka sani tattare dasu na kyãwun tarihin rãyuwarsu, da saituwar hãlãyensu, da kuma abinda Allah yayi gare su da kuma mabiyansu na bayar da nasara da kuma kyakkyawan ƙarshe, da yanda ya hallakar kuma ya azabtar da masu ƙaryatasu da saɓa masu.


Kuma Allah ya tattara wa Annabinmu Muhammad -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- mafi yawa kuma mafi girman abinda Annabawa -aminci ya tabbata a garesu- suka zo dashi na ayoyi, Shehun musulunci [Ibni Taimiyya] -Allah ya jikan sa- ya ce: «Kuma mu`ujizozinsa sunfi mu`ujiza dubu, kuma a dũniya babu wani ilimi da ake nemansa ta hanyar labarai mutawatirai [ma'ana: ta hanyoyi masu yawa da suke yanke shakku) fãce ilmin ãyoyin Manzo Allah, da shari'o'in addininsa sun fisu fitowa fili, Allah mai tsarki yace:





«shine ya aiko ManzonShi da gaskiya da shiriya domin ya ɗaukakashi akan addinai dukkansu, kuma Yã isa Mai shaida». [Suratul fatahi aya ta: 28].


Yana daga cikin ãyoyin annabtarsa: Bishãra da Annabawa sukayi game da zuwan sa tun kafin yazo, Annabi Ibrahim da Annabi Ismãil -aminci ya tabbata a gare su- suka ce:





4 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


«Ya Ubangijinmu Ka tayar da wani manzo daga cikinsu, da zai karanta masu ayoyinKa kuma ya koyar dasu littafi da hikima kuma ya tsarkake su» [Suratul Baƙara aya ta: 129]. kuma Annabi Isa -aminci ya tabbata a gare shi- ya ce:





«Kuma ina mai bishãra da wani manzo da zai zo a bayana sunanshi Ahmadu», [Suratus Saffi aya ta: 6].


kuma wani mala`ika ya sauka zuwa gare shi yana karamin yaro ya tsãga ƙirjinsa ya cire abinda ke jikinsa na rabon Shaidan.


Kuma kafin Annabta Allah Ya kãreshi daga ayukkan jãhiliyya da dauɗarta, ba'a taba ganin tsaraicinsa ba, kuma bai taba shafar wani gunki da hannunsa ba, kuma bai taɓa shan giya ba, kuma bai taɓa cinikayya da wani, da abu na haram ba.


Kuma an ƙara tsaro ga sama da yũla [taurãri masu haske da wuta] waɗanda ake jifan shaidanu dasu, domin kiyaye sakonsa, aljanu suka ce:





«Kuma lallai mu mun nufi kaiwa sama, sai muka tarar da ita, an cika ta da masu tsaro ƙarfãfa da kuma yũloli» [Suratul Jinni aya ta: 8].


Daga cikin ayoyin akwai waɗanda suka kasance lokacin rayuwarsa kuma suka wanzu zuwa yau kamar Alƙur'ãni mai girma, da ilimi da imani wadda mabiyansa suka ɗauka.


Daga cikinsu akwai abubuwan da ya bãda lãbari daga cikin abinda Allah ya tsinkayar dashi na abubuwa masu yawa da suka faru da suka gabãta, da kuma abubuwan gaibi wanɗanda zãsu fãru a gaba, labari dalla-dalla, wanda ba wanda zai iya sani sai


DALILAN ANNABTA 5


a-alqasim.com


dai idan Allah mabuwayi da ɗaukaka ya sanar dashi, Allah Mai tsarki yace:





«Waɗancan na daga cikin lãbãran gaibi da muke yi maka wahayinsu, kai baka kasance ka sansu ba hakanan mutanenka kafin haka». [Suratu Hudu aya ta: 8].


Ya bãmu lãbari daga abinda ya wuce: Lãbarin Ãdamu da sujjadar malã`iku gare shi, da kuma Iblis da girman kansa, da bayanai daki daki masu yawa da ban mãmãki daga cikin kissoshin Annabãwa, da abubuwan da al`ummomi kafin mu suka yi sãɓãni acikinsu, da lãbarin mutanen kogo, da ma`abota giwaye.


Kuma Allah Ya ƙãlũbalanci halittu da cewa su zo da sũra daya kwatankwacin ta Alƙur'ãni; sai ya bada labarin cewa bazasu iya haka ba har zuwa tashin ƙiyama, sai gãshi ba wanda ya iya yin hakan, kuma ya faɗi game da kafirai -lokacin da yake cikin rashin karfi a Makkah-:





«Da sannu za`a rusa rundunar kuma zasu koma da baya» [Suratul ƙamari aya ta: 45], sai gaskiyar haka ta bayyana bayan shekaru mãsu tsawo, sai musulmai sukaga mamatar manyan kuraishawa kafin ranar yaƙin badar, sai ya ce: «Nan ne wajen mutuwar wane, Anas -Allah ya yarda dashi ya ce-: kuma yana sanya hannunsa -wato: Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- nan da can, babu daya cikinsu daya gusa daga wurin hannun Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare


6 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


shi-» (Muslim ya ruwaito shi), kuma ya fita zuwa Khaibar sai yayi kabbara yace: «Khaibar ta rushe!» sai Allah ya bude ta gare shi.


Kuma ya aika sahabbansa zuwa Mu`utah domin yakar Rũmãwa, kuma ya shelar mutuwar shahidan cikinsu kafin isowar lãbarinsu (Bukhari ya ruwaito shi).


Kuma ya ambata cewa Fãrisãwa zãsuyi galaba akan Rũmãwa a lokacin rayuwarshi, sa`annan lokacin da dan sakon kisra yazo da wasika daga wurinsa sai ya ce masa: «Lallai Ubangijina ya kashe ubangijinka -wato: mai gidanka- a wannan daren» (Ahmad ya ruwaito shi).


Kuma a hanyarsa ta zuwa Tabuka ya ce: «A wannan dare wata iska mai karfi zata taso maku, kada wani cikin ku ya tashi acikinta» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Kuma ya bãda labarin kusantowar ajalinsa da komawarsa zuwa ga abokan zama maɗukaka, kuma ya zauna minbari sai yace: «Wani bawa Allah yã bãshi zãɓi tsakanin bashi ƙyaleƙyalen dũniya, ko kuma abinda ke wajenSa, sai ya zaɓi abinda ke wajenSa! Sai Abubakar yayi kuka ya kara yin kuka, sannan ya ce: Munyi Fansarka da iyayenmu maza da kuma iyayenmu mata!» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi), bai yi kwanaki da yawa ba, sai da yabar duniya, kuma yace: lallai bayan shekara ɗari babu wanda zai rage a doron kasa cikin sahabbansa (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi), kuma duka wadannan suka kasance kamar yadda ya fadi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.


Kuma ya bada lãbarin cewa za`a buɗe masallacin ƙudus, sannan wata annoba zata biyo bayansa wacce zata ƙarar da musulmai, sannan bayansa dukiya zata kwarara har a rasa mai


DALILAN ANNABTA 7


a-alqasim.com


karɓanta, sai abinda ya bada labara ya kasance; sai gashi an bude masallacin ƙudus, kuma annobar ta auku a Sham, dukkan su a lokacin khalifancin Umar -Allah ya yarda da shi-, sannan dukiya ta kwarãra a lokacin khalifancin Usman dan Affan -Allah ya yarda dashi- har ya kasance za`a ba mutum dinari ɗari, sai ya ɓata rai da ita.


Kuma ya bada labarin cewa za'a bude birane, sai mutanen Madinah su rika fita zuwa gare su domin neman jin daɗi da yalwa, kuma yace «kuma Madinah tãfi alkhairi a gare su inda su sun sani» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi), da kuma cewa Kisra da Qaisar zasu hallaka kuma za'a rabar da taskokinsu a bisa hanyar Allah, da kuma cewa za`a bude duniya ga al`ummarsa, sai suyi gãsa cikinta kamar gãsar wadanda suka gabacesu, da kuma cewa al`ummarsa zasuyi kamanceceniya da al`ummomin da suka gabace ta, kuma zasu bi tafarkinsu koda ramin damo suka shiga to suma da sun shigeshi. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Kuma ya bayyana alamomin tashin ƙiyama wadanda zasu faru kafinta: Kamar ƙarancin ilimi, da yawaitar jahilci, da bayyanar fitintinu, da yawan kashe-kashe, da gasar mutane wajen gina gidaje masu tsawo; kuma ya mike a cikin sahabbanshi ya basu labarin abubuwan da zasu faru har zuwa tashin ƙiyama, Huzaifah -Allah ya yarda dashi yace: «Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tsaya a cikin mu wata irin tsayuwa, bai bar wani abu ba acikin wannan tsayuwar tasa da zai faru zuwa tashin ƙiyama sai da ya bada labarinsa, wanda ya haddace ya haddace, wanda ya manta ya manta» (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Kuma ya basu labarin abubuwan da ya gani a sama, Allah ya tafiyar da ruhinsa da jikinsa cikin dare daga Makkah zuwa


8 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


masallacin ƙudus, sannan aka hau dashi sama har ya isa zuwa ga itacen magaryar tuƙewa, sannan ya dawo Makkah a wannan dare nasa, kuma ya basu labarin abinda ya gani na daga Aljannah da Wuta da mazauna cikinsu da kuma iccen magaryar tuƙewa, da kuma abinda yaji na ƙarar alƙalumman gudanar da duniya.


Kuma ya ƙarfafa shi da ayoyinsa na sararin duniya wadanda idanu ke iya gani: Allah ya tsaga Wata har ya zama gida biyu aya a gare shi, mutane sun gansu [yanki biyun na wata] a Makkah da wasu wuraren.


Kuma Alamomin annabtarSa har cikin mutane sun bayyana kuma du: Domin a cikin huɗubar bankwana Allah ya buɗe masa kunnuwan mutane har suka ji shi gaba ɗaya, kuma sun kasance fiye da dubu ɗari, (Abu Dawuda ya ruwaito shi).


Kuma yayi addua ga Anas -Allah ya yarda da shi- Allah ya yawaitar dukiya da `ya`ya, Har ya zamto da ransa sai da ya binne sama da mutum ɗari da ashirin daga tsatsansa (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Kuma yayi addua ga Abu Hurairah da mahaifiyarsa -Allah ya yarda da dasu- cewa Allah ya sanya ƙaunarsu a zuciyar muminai, Abu Hurairah -Allah ya yarda da shi yace: «sai ya zama babu wani mai imani da aka halitta da zai ji labari na kuma bai gani na face sai yã so ni» (Muslim ya ruwaito shi).


Kuma yayi addu`a ga Urwatu Al-bariƙi -Allah ya yarda dashi- ta neman albarka cikin kasuwancinsa, sai ya kasance ko turɓaya ya siyar sai yaci rĩba a cikin sa (Bukhari ya ruwaito shi).


Kuma an karya ƙafar Abdullahi dan Ateek -Allah ya yarda da shi- sai ya shafeta; sai ta warke (Bukhari ya ruwaito shi).


Kuma yayi tofi ga idon Aliyyu -Allah ya yarda dashi- saboda ciwon ido da ke tare dashi, sai ya warke kamar bai kasance cikin


DALILAN ANNABTA 9


a-alqasim.com


ciwon ba (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


Kuma Har a cikin dabbobi ma alamomin annabtarsa sun bayya: Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wata rana ya shiga wani shinge na wasu mutanen Madinah wanda akwai ra ƙumi a cikinsa, da raƙumin yaga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai yayi kuka, sai manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya shafa samansa sai yayi shiru, sai yace wa mai raƙumin: «Shin baza ka ji tsoron Allah ba cikin al`amarin wannan dabbar da Allah ya mallaka maka ita? Ya kawo min kõken kana yunwatar dashi kuma kana ladabtar dashi -wato: kana gajiyar dashi-» (Abu Dawuda ya ruwaito shi).


Kuma Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: «Iyãlan gidan Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sun kasance sunada wata dabbar daji, idan Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya fita sai yayi wasa yayi gudu yayi ta kai komo, idan yaji Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya shiga gida, sai ya kwanta, baya


motsa bakin shi -watau baya motsi ko fitar da wani sauti- muddun Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cikin gida, domin kyamar kar ya cutar dashi» (Ahmad ya ruwaito shi).


Yana daga cikin mu`jizozinshi: Abinda aka bashi na yawaitar abinci da abin sha, a Hudaibiya ya kasance a tare da shi akwai sahabbai dubu ɗaya da ɗari biyar, Jabir -Allah ya yarda dashi- yace: «Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya sa hannu a cikin rikwah -wato: karamar ƙwarya-; sai ruwa ya riƙa tasowa -wato: ya rika ɓuɓɓugowa da ƙarfi- a tsakankãnin yãtsunsa tamkar idanun ruwa, sai muka sha muka yi alwala, aka tambayeshi ku nawane a lokacin? Yace: da mun kai dubu ɗari da


10 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


zai wadatar damu, mun kasance ɗari goma sha biyar -wato: dubu ɗaya da ɗari biyar-» (Bukhari ya ruwaito shi).


A yãƙin Zãtur Riƙã`i ya tara ruwa kadan a cikin kwano -wato: kwanon abinci- sai dukkan mayãƙa suka cika ƙõren su daga cikinta.


A Khaibar kuwa abinci yayi ƙaranci; sai -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya basu umurni suka tara abinda suke da shi, sai yasa albarka a cikinsa -wato: yayi masu addu`ar samun albarka a cikin sa-, sai suka ci har dukkan rundunar suka ƙõshi, kuma sun kasance dubu ɗaya da ɗari biyar.


A Tabuka ya kasance a tare da shi akwai kwatankwacin mutum dubu talatin suna neman ruwa, sai yayi alwala a wata idaniyar ruwa, sai ta fitar da ruwa mai kwarara dayawa har suka sha dukkan su (Muslim ya ruwaito shi).


Kuma Samurata dan Jundub -Allah ya yarda dashi- ya ce: «Mun kasance tare da manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- muna karɓa-karɓar wata akushi -wato: kwano kewayayye mai fadi na cin abinci- tun safe har dare, mutum goma su taso mutum goma su zauna, sai muka ce: shin bai kasance ana masa ƙari ba kuwa? Yace: me kake mamaki? Bai kasance ana masa ƙarashi ba saidai ta can, sai yayi nuni zuwa sama» (Turmizi ya ruwaito shi).


Kuma Allah yãhore masa itãce da duwãtsu matsayin alamar annabtarsa: Yã sauka a wani kwari tare da sahabbansa sai ya riƙo bishiya biyu sai suka taho tare dashi, suka haɗu a gare shi -wato: suka haɗu da juna- da umurninshi (Muslim ya ruwaito shi).


Aljannu sun taru a wurinsa suna sauraren Alƙur'ãni daga gareshi a lokacin yana makkah; sai wata bishi kusa da shi ta sanar da shi suna wurin (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).


DALILAN ANNABTA 11


a-alqasim.com


Kuma ya kasance yana huɗuba a kan wani kututturen dabino acikin masallacinsa, sai aka yi masa minbari, yayinda yayi huɗuba akansa sai kututturen ya rãki yayi kuka irin na kananan yara, har -tsira da amincin Allah su tabbata a gare- shi ya dora hannu akansa; sannan yayi shiru (Bukhari ya ruwaito shi).


Kuma yace: «Lallai nasan wani dutse a Makkah da yake gaisheni kafin a aiko ni, lallai na san shi yanzu haka» (muslim ya ruwaito shi).


Kuma ya hau dutsen Uhud tare da wasu kadan cikin sahabbansa, sai ya girgiza dasu, sai ya buge shi yace: «Ka tabbata kai Uhud» sai ya tabbata (Bukhari ya ruwaito shi).


kuma Allah ya ƙarfafa shi da Mala`ikunsa ƙarfafawar dabai taɓa yima wani ba kafinsa don nuna alamar annabtarsa; a Makkah Mala`ikan duwãtsu ya nemi izininsa akan ya kifa wa kafirata al-akhshabãn -sune: wasu duwatsu biyu na Makkah- sai ya nemi ya jinkirta musu.


A lokacin hijra Allah ya ce:





«Yanã na biyun mutne biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a yayin da yake cẽwa abokinsa: Kada ka yi baƙin ciki, lallai ne Allah Yanã tãre da mu, Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa gare shi, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, da ba ku gansu ba». [Suratut taubah aya ta: 40]


A Badar kuma mafi darajar Malãiku sunyi yaƙi tare da shi, a Uhudu kuma an ga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- tsakanin Mala`ika Jibrilu da Mika`ilu suna kare shi mafi


12 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


tsananin kãriya (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi), kuma Jibril -aminci ya tabbata a gare shi- ya tafi tare da shi daga khandaq [gãnuwa] zuwa unguwar bani Quraiza (Bukhari ya ruwaito shi).


Yana daga cikin alamomin annabtarsa: Kariyar da Allah yayi masa daga maƙiyansa, sai ya ce:





«Kuma Allah zai tsare ka daga mutane» [Suratul mã'idah aya ta: 67] sai suka kasa isa zuwa gareshi, har yayi nasara akansu, duk da yawansu da ƙarfinsu.


Kuma wasu daga cikin yahũdawa sun yi mashi sihiri; sai Allah ya tsinkayar dashi kan sihirin nasu. sai ya warware shi,


kuma suka sa masa guba cikin tunkiya; sai Allah ya sanar da shi.


Yana daga cikin alamomin annabtarsa: hãlãyensa tsarkaka da ɗabi`unsa cikakku.


Duk da bayyanan al`amarinsa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, da biyayyar halitta gareshi, da fifita shi da suke akan rayukansu da dukiyoyinsu, ya mutu bai bar dirhami ko dinare ba, bai bar tunkiya ko raƙumi ba, sai dai alfadarinsa, da takwobinsa, da sulkensa, kuma ya kasance yayi jinginarsa a wurin wani bayahũde, kan sa`i talatin na sha`ir wanda ya siya domin iyalansa.


Bayan Haka, ya ku Musulmai:


Duk wanda yayi tunani acikin tarihin annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- daga haihuwarsa zuwa mutuwarsa; zai gane cewa shi Manzon Allah ne na gaskiya, yazo da zancen da `yan farko da `yan baya basu taɓa jin irinsa ba, kuma yã


DALILAN ANNABTA 13


a-alqasim.com


kasance koda yaushe yana umaurtar al`ummarsa da tauhidi -kaɗaita Allah-, kuma yana nunar dasu zuwa ga dukkan alkhairai, kuma yana hana su daga dukkan sharri, kuma Allah yana bayyana masa ayoyi masu ban mamaki.


Ya zo da mafi cikar addini, ya tattaro kyawawan abubuwa da dukkan al`ummomi suke kai, sai al`ummarsa ta zamo mafi cikar al-ummu kan dukkan wata falala, kuma dashi ta sami waɗannan falalolin, kuma a wurinshi suka kõye su, kuma shi ya umurcesu da su, sai suka zama mafiya ilimi da addini da cikan adalci da falala a doron ƙasa


Ina neman tsarin Allah daga shaidan jefaffe


Ka ce:





«Nĩ, mutum ne kaɗai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lallai ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinshi, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinshi» [Suratul kahafi aya ta: 110]


Allah yayi albarka a gare mu ni da ku cikin Alƙur'ãni mai girma…


14 DALILAN ANNABTA


a-alqasim.com


HUƊUBA TA BIYU


yabo da jinjina sun tabbata ga Allah akan kyautatawarsa, kuma godiya ta tabbata gare shi bisa datarwasa da kuma Ni'imominsa, Kuma ina shaidawa babu abin bautawata da gaskiya sai Allah shi kaɗai bashi da abokin tarayya don girmama al`amarinsa, kuma ina shaidawa Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa, Allah yayi yabo a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci mai yawa.


Ya ku Musulmai:


Yin nazari acikin ayoyin Annabinmu Muhammad -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da hujjojin gaskiyarsa, yana ƙara Imani, kuma daraja tana ƙaruwa ta hanyar yawan dubi cikin kyawawan abubuwansa masu ban sha`awa da shariarsa tsarkakakkiya, kuma bamu dawata hanyar sanin Allah sai ta hanyar Manzonsa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.


Wanda yaso yasan gaskiyar manzanci, da bayyanar hujjojin ta to yayi riko da Alƙur'ãni mai girma.


Yayin da ya kasance buƙatar mutane na gaskata Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yafi tsananta sama da bukatuwarsu zuwa ga komai; to sai Allah ya sauƙaƙe dalilan da ake sanin gaskiyar Annabawa da su, ya sanya su masu yawa da bayyana da fitowa fili ta yanda babu wanda zai ƙi Imani dasu, sai mai taurin kai, kuma babu wanda zai yi kokwanton gaskata su, sai mai gimankai.


Kuma dukkan alkhairi yana cikin tabbatuwa kan gaskata Annabta, da yi masa biyayya.


Sannan ku sani cewa Allah yã umurce ku da yin salãti da sallama ga Annabinsa...



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH