Kayatarwa cikin cikar Shari'a da kuma da kuma hadarin Bidi'a
3
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.ma
Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa kuma muna neman gafararsa kuma muna tuba a gareshi, kuma muna neman tsari daga Allah daga Sharrin kawunan mu da kuma munana nan Ayyukanmu, kuma duk wanda Allah ya shiryar to babu mai iya batar da shi haka kuma duk wanda ya batar to babu mai iya shiryar da shi.
kuma na shaida cewa babu wani Ubangiji sai shi kadai, kuma na shaida cewa Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzon sa, Allah ya turo shi da Shiriya da kuma Addinin gaskiya to ya isar da sakon kuma ya bada Amanar, kuma yayiwa Al'umma Nasiha kuma yayi Jahadi a tafarkin Allah Mayukar iyawarwarsa har wafati ya riske shi.
kuma ya bar Al'ummarsa akan Hanya fara wadda darenta kamar tanarta yake kuma babu wanda ai kauce mata sai Hallakakke, kuma yayi bayani acikinta duk abinda Al'umma take bukata a cikin baki dayan Al'amuranta har Abu Zarrin - Allah ya yarda da shi yake cewa:Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi bai bar wani tsuntsu da yake yawo da fukafukansa a sama ba har sai da ya fada mana Ilimi game da shiWani Mutum daga cikin Mushirikai yace da Salman Al'farisi -Allah ya yarda da shi- Annabinku ya sanar
4
da ku har ladaban biyan bukata, yace:Ey, Hakika ya hanamu mu fuskanci Al'kibla da Bayan gida ko Fitsari ko muyi tsarki da kasa da Duwatsu Uku, ko Muyi tsarki da Hannun Dama ko kuma Muyi tsarki da Turoso ko kashi.Kuma kai Wallahi zakaga wannan Al'kurani Maigirma ya bayyana a cikinsa ginshikan Addini da kuma Rassansa kuma yayi bayanin Tauhidi da baki dayan bangarorinsa, kuma yayi bayanin ladaban wuraren zama da yadda akeyin Sallama Allah Madaukakin Sarki yace:
"Ya ku wadanda kukayi Imani idan aka ce da ku: ku buda a cikin wurin zama to ku buda din kuma sai Allah ya buda muku"
(Suratu Almujadalah 11)kuma Allah Madaukaki ya ce
"ya ku wadanda kukayi Imani kada ku kuskura ku shiga gida da ba naku ba ne har sai kun nemi Izini kuma kunyi Sallama ga Masu gidan wancananka sune mafi Alkairi gareku ko kwa wa'azantu, to idan baku samu kowa a gidan ba to kada ku shiga har sai an muku Izini kuma idan akace ku koma to ku koma shi ne Mafi tsarki a gareku kuma Allah Masani ne da abinda kuke aikatawa"
(Suratu Annur 27-28)Har ladaban sanya Tufafi sai da aka yi bayaninsu, Allah Madaukaki ya ce:kuma tsofaffi daga cikin Mata wadanda basu da sha'awar Saduwa to babu laifi a garesu idan suka cire lullubinsu amma ba tare da sunyi kwalliya ba suna masu nuna tsiraici.(Surat Annur 60)
5
Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtanka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, kuma Mai Jin ƙai.
(Surat Al'ahzab 59)"kuma kada su rika buga kafafuwansu domin asan abinda suka boye na Adonsu"(Surat Annur 31)kuma baya daga cikin bin Allah cewa ku shiga gidaje ta bayan katanga sai dai Bin Allah shi ne jin tsoransa kuma ku shiga gidaje ta kofofinsu"(Surat Albakara189)Zuwa wasu Ayoyin masu yawa wadanda suke bayanin cewa wannan Addini ya game komai kuma cikakke ne kuma baya bukatar wani kari a cikinsa kamar yadda yake cewa bai halatta a tauye komai daga cikinsa ba, kuma wannan shi ne abinda Allah yake cewa yana mai sifanta Alkur'ani"kuma mun saukar maka da littafin wanda yake bayani baki dayan komai"Surat Annahl 89To babu wani abu da Mutane suke bukata a Duniyarsu da lahirasu sai da Allah yayi bayaninsa a cikin littafinsa kodai Nassan ko kuma yana mai nuni da ishara kodai baro baro kuma a kirdadance.Ya ku "yan Uwa: Lallai wasu daga cikin Mutane suna fassara fadin Allah Madaukaki da cewa:"Kuma babu wata Dabba a bayan Kasa ko kuma wani Tsuntsu da yake tashi da fuka fukansa sai suma sun zamanto wata Al'umma ce kamar ku kuma bamu yi sakacin bayanin wani abu acikin littafin mu ba.(Surat Al'an'am 38)Yana fassara Fadin Allah :"Bamu takaita bayanin wani abu
6
acikin littafin mu ba"Kan cewa lallai littafin shi ne Alkur'ani, abinda yake daidai shi ne cewa littafin anan shi ne Allon Kudura, kuma Alkur'ani Allah ya sifanta shi da cewa shi ne mafi mafi cika daga korewa kuma shi ne fadinsa:"kuma mun saukar maka da littafin wanda yake bayani baki dayan komai"To wannan shi ne mafi isa kuma mafi bayani daga fadin AllahBamu yi sakacin bayanin wani abu acikin littafin mu ba sannan kuma zuwa garemu za'a tashe su"
kuma watakila wani ya ce to a ina zamu samu yawan Salloli biyar a cikin Alkur'ani?
Da kuma yawan Adadin kowace Sallah cikin Al'kur'ani?
kuma ta yaya cewa mu ba zamu samu a cikin Al'kur'ani ba bayanin Adadin Raka'o'in kowace Sallah kuma Allah yana cewa:"kuma mun saukar maka da littafin wanda yake bayani baki dayan komai"kuma amsa kan hakan ita ce cewa Allah Madaukaki yana mana bayani a cikin littafinsa cewa yana daga cikin Wajibi akanmu da muyi riko da abinda Annabi ya fada mana da kuma abinda ya nuna manaWanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma" wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu"(Surat Annisa 80)Kuma duk abinda Manzo yazo muku da shi to ku karba kuma duk abinda ya haneku ga barinsa ku hanu kuma kuji tsoron Allah cewa lallai Allah Mai tsananin Ukuba ne"(Surat Al'hashr 7)To duk abinda Annabi yayi bayaninsa a cikin Al'kurani to hakika daya daga cikin bangarori biyu na wahayi (Kur'ani da Hadisi) ya nuna shi wanda ya saukar da shi ga Manzonsa kuma Manzon ya sanar da mu shi kamar yadda Allah Madaukaki ya fada:"kuma Allah ya saukar da
7
littafi da kuma da kuma fassarar littafin kuma ya sanar da kai abinda baka sani ba kuma falalar Allah akanka tana da girma"(Surat Annisa 113)kuma kan haka ne to duk abinda ya zo a cikin Hadisi to hakika yazo a cikin littafin Allah maigirma da Daukaka
Ya ku "yan Uwa: Idan wannan ya tabbata a gareku shin Annabi yayi Wafati kuma da ragowar wani abu na Addini wanda zai kusanta mu da Allah bai bayyana shi ba?
Har Abada to Annabi Amincin Allah a gareshi yayi bayanin komai na Addini kodai ta fadinsa ko ta aikinsa ko ta ikirarinsa ko da haka kawai ko kuma amsar wata tambaya,kuma wani lokacin yakan turo Balaraben kauye daga kurgumin kauye don yazowa Annabi ya tambaye shi wani abu na Addini wanda Sahabbai da suke tare da shi ko yaushe bazasu iya tambayarsa ba sabida haka suke farin ciki da zuwan Balaraben Kauye ko yaushe ya zo tambayar Annabi wasu abubuwan Addini.kuma wannan yana nuna cewa Annabi baibar komai ba da Mutane suke bukata a Ibadar su ko Mu'amalarsu ko rayuwarsu face yayi bayaninsa kuma fadin Allah ya nuna hakan:"Kuma yaune muka cika muku Addininku kuma muka cika muku ni'amarku kuma muka yarje muku Musulun a Matsayin Addini"(Surat Al'maa'ida 3)To idan hakan ya tabbata a gareka kai Dan Uwa Musulmi to ka sani lallai cewa Kowace duk wanda ya kirkiro wata Bidi'a a Addinin Allah kuma koda kyakkyawar niyya ce to wannan Bidia ce kuma wannan ya hadar da kasancewarta Bata kuma wannan Suka ce ka Addinin Allah Madaukaki don tana karyata Allah Madaukaki cikin Fadinsa:"Yau ne na cika muku Addininku"
8
Domin wannan Mai Bidi'a wanda ya kirkiri wata Shari'a daban a cikin Addinin Allah kai ka ce yana cewa a harshen sa yana nufin cewa Addinin Allah bai cika ba cewa akwai ragowar wani abu na Sharia da ya kirkiro shi don ya kusanci Allah da shi.
kuma yana daga cikin abin mamaki cewa Mutum ya kirkiri wata Bidi'a wacce take da Alaka da Zatin Allah ko sunayensa ko kuma Sifofinsa sannan kuma ya ce wai shi yana girmama Ubangijinsa, cewa kuma lallai Allah ya tsarkaka ga barin hakan, lallai kuma cewa shi cikin hakan yana kwatanta fadin Allah ne Madaukaki inda yake cewa:"Kada ku kuskura kusanya kishiya ga Allah kishiya alhalin kunsan haramcin hakan""Surat Albakara 22"kuma yana daga cikin abin zakayi Mamaki daga wannan cewa wannan Mutum ya kirkiri wannan Bidi'a a cikin Addinin Allah ne wacce take danfare da Zatin Allah wacce kuma Magabatan Al'umma ko Jagororinta, sannan kuma ya ce shi yana tsarkake Allah ne kuma wai yana girmama Allah kuma cewa shi mai kokarin kwatanta fadin Allah Madaukaki ne inda yake cewa:"Kada ku kuskura kusanya kishiya ga"kuma duk wanda ya saba hakan to shi mai kamanta Allah ne da halittunsa ko mai kama da hakan da dai wasu sifofi mumana
Kamar yadda cewa kai zaka yi mamakin wasu mutane da suke kirkirar wani abu cikin addinin Allah wanda baya daga cikin sa wanda ya danganci Annabi sallallahu alaihi wa sallam suna da’awa da shi cewa su din masoyan Annabi ne sallallahu alaihi wa sallam sannan masu girmama shi ne kuma duk wanda baya bin dai dai Da abinda suke kai na Bidi’a to shi Makiyi ne ga Annabi sallallahu alaihi wa sallam da sauran munanan lakubba wadanda suke yi wa
9
wadanda bas u bin bidi’arsu kan abinda ya danganci manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam.
yana da ga cikin abin mamaki yadda wadannan mutane n suke cewa su sune ma su girmama Allah da manzon sa ,alhalin su ne wadanda suka farar bidi’o’I a cikin addinin Allah da shari’ar da annabi sallallahu alaihi wa sallam ya zo da ita suka sanya abinda babu a cikin ta.Hakika ko shakka babu sun gabatar da wani abu gabanin Allah da manzon sa kamar yadda ALLAH madaukakin sarki yake cewa :Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.(suratul Hujurat 1).
Ya ku yan uwa :Ina tambayar ku ina kuma hadaku da Allah ina son amsar ta kasance daga zukatan ku ba da ga abin da ku ka karkata gare shi ba ,daga hukuncin addinin ku ba dag aba daga abubuwan al’adunku ba.Me zaku ce kan wadanda suke kago Bidi’a cikin addinin Allah suke kawo abinda baya cikin Addini na daga abinda ya ta’allaka da Zatin Allah da sifofin sa da sunayensa ,ko kuma kan abinda danganci annabi sallallahu alihi wa sallam ,sa’annan su ce sune ma su girmama Allah da Manzonsa ,Shin wadannan sune suka fi cancanta su kasance masu girmama Allah da Manzon sa?
ko wadancan suke basa sabawa shari’ar Allah ko kadan, suna fadar abinda yazo a cikin shari’arsuna masu Imani da bada gaskiya kan abinda aka ba mu labarin sa mun ji kuma mun yi biyayya kan duk
10
abinda aka yi mana umarni da shi ko aka hana mu ,suna kuma fadi kan abinda shari’a bata zo da shi ba an hane mu bay a yuwuwa mu rigayi Allah da manzon sa ba zamu fadi wani abinda babu shi acikin addinnin Allah ba .Wane ne daga cikin su ya fi cancanta ya zamo masoyin Allah da Manzon sa kuma yake girmama su
Ba shakka wadanda suka ce sun yi Imani sun bada gaskiya da abinda aka basu labari sun kuma yi biyayya ,suka kuma ce mun hanu kan duk wani abu da ba’a umarcemu da shi ba suna kuma cewa mu ba mu isa mu sanyawa shari’ar allah abinda babu acikin ta ko mu yi Bidi’a cikin addinin Allah; ba shakka wadannan su su ka san matsayin su ,suka san matsayin sabawar su ,Wadannan su ne suke girmama Allah Ta’ala da Manzon sa kuma suka bayyana gaskiyar soyayyar su ga Allah da Manzon sa.
Ba wadanda suke yin Bidi’a a cikin addinin Allah suna kawo abinda bay a daga cikin sa a cikin Aqida ko Magana ko wani aiki ba ,z aka yi mamaki kan mutanen da sun san maganar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam:“Na hane ku da fararrun Al'amura ,domin cewa dukkan fararen abu Bidi’a ne ,kuma dukkanin Bidi’a Bata ce ,kuma kowacce Bata tana cikin Wuta.Kuma suna sane cewa lallai fadinsa:Kowace Bidi'aGamewa ce ta baki daya wacce akayiwa kawanya da mafi karfin alamun gamewa da tattarewa.KowaceWanda ya yi Magana da wannan gamewar tsira da aminci su kara tabbata a gare shi ya san abinda wannan lafazin
11
yak e shiryarwa ,shine mafi fashar dukkannin Halitta kuma mafi nasihar halitta ga Halittu ,bay a furta wani lafazi face yana nufin ma’anar sa ,dan haka lokacin da Annabi sallallahu alaihi wa sallam yak e cewaKowace Bidi'a Bata neHakika ya san abinda yake fada,Ya kuma san ma’anar abinda ya ke fada,wannan ta tabbatar da cikin nasihar sa ga Al’umma.Kuma Idan zance ya cika wadannan al’amuran uku cikar nasiha da kuma fata ,da cika wajen bayani da fasaha ,da cika ta ilimi da kuma sani ,wannan ya na shiryarwa da cewa zancen yana nufin ma’anarsa ,shin bayan wannan gamewar ya inganta a raba Bidi’a zuwa kasha uku ko biyar?.
Sam Sam wannan bai inganta ba , kuma abinda wasu Malamai suke rayawa cewa akwai wata Bidi'a mai kyua wannan batun bai wuce abubuwa biyu ba
Kada ta kasance Bidi'a sai dai yana zatonta Bidi'a ce
Ta kasance Bidi'ar Mummuna ce amma baisan Muninta ba
To dukkan abinda aka kira da cewa Bidi'a ce Mai kyau to Amsa game da hakan irin waccan Amsar ce, kuma kan haka ne to babu wata kafa da ta ragewa "yan Bidi'a wajen samun daman sanya Bidi'arsu ta zama Kyakkyawa kuma a hannunmu akwai Takobi mai kaifi daga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi.kowace irin Bidi'a Bata ceLallai cewa wannan Takobi mai kaifi an kerata ne kawai a masana'antar Annabtaka da Manzataka ,
12
kuma ba'a kerata a kwarababben Masana'anta ba, kuma an kera ta a Masana'antar Annabi kuma shine ya tsara ta ta wanna sigar mai Balaga to babu yadda za'a yi ga wanda yake da irin wannan Takobin mai kaifi wani yayi futo na futo da shi da wata Bidi'a ta sa ya rika cewa wai Bidi'a Mai kyau, kuma Manzon Allah Sallallahu Aalihi wasallam yana cewa:kowace irin Bidi'a Bata cekuma ni kamar ina jin akwai wani abu da yake yawo ada yake fadin abinda kake fada game da Sarkin Muminai Umar Dan Khattab -Allah ya yarda da shi- wanda Allah ya datar da shi da dacewa da gaskiya lokacin da ya Umarci Ubayyu Dan Ka'ab da kuma Tamim Al-Dari kan cewa su yi Sallar Asham ga Mutane a Azumi sai mutane suka futo kuma Mutane sunabayan limaminsu sai ya ce:Madalla da wannan baidi'ar kuma wadanda yake bacci sunfi wadanda wadanda suke aikatata.Amsa kan haka ta fuska biyu ne:Fuska ta farko :Ba ya halatta ga mutum ya ja da maganar Annabi sallallahu alaihi wa sallam da kowacce irin Magana ko da kuw da maganar sayyidina Abubakar ce wanda shine mafificin mutane a doron kasa bayan Annabi ,ko kuma da maganar Umar wanda shine na biyun wannan al’umma bayan annabi ,ko da maganar Usman wanda shine na uku ko da maganar Ali wanda shine na hudun wnnnan al’umma bayan Annabi ‘ko da zancen wani bayan su saboda Allah ya na cewa :to wadanda suka saba Umarninsa su kiyayi kansu kada Musiba ko fitina ta sauka a kansu ko kuma Azaba mai radadi ta same suSurat Annur :63Imam Ahmad -Allah ya yarda da shi ya ce:Ko ka san maye Fitina?Fitina ita ce Shirka watakila idan akai watsi da wasu daga cikin maganganun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam cewa wani
13
abu ya fada cikin zuciyar wani na bata sai ya hallakaYa karekuma Ibn Abbas -Allah ya yarda da shi ya ce- ya ce:kuma ya kusa a saukar muku da Dutse daga Sama ina cewa Annabi ya ce kuma kuna cewa Abubakar da Umar sun ce?FUSKA TA BIYU :Hakiika mun sani tare da yakini cewa amirul mu’minin Umar Allah ya kara yarda a gare shi yana daga cikin wadanda suka fi tsananin girmama zancen Allah madaukakin sarki da Manzon sa Annabi Muhammad sallallahu alai wa sallam,ya kasance ya shahara da tsayawa kan iyakokin allah har ana siffanta shi da mai tsayawa kan zancen Allah.Ya ya qissar matar da ta gabato ma sa –in qissar ta inganta-wajen iyakance sadaki yadda da yawa suka jahilta a yayin da ta ja da shi da fadin Allah madaukakin sarkiKuma ta yaya zaku karbe shi kuma bayan shashinku ya karkata ga sashi kuma kun dauki Babban Alkawari a tsakaninku(Surat Annisa'a)To sai Umar ya hanu ga barin abinda yayi niyya na Iyakance SadakiSai dai wannan qissar sai an yi nazari kan sahihancin ta .Sai dai abin nufi anan shine cewa sayyidina Umar ya kasance mai tsayawa iyakakar haddodin ubangiji baya ketare su,ba za’a jinginawa Umar yardarm Allah ta kara tabbata a gare shi bay a zamo daga cikin masu saba maganar shugaban mutane sallallahu alaihi wa sallam da yace akan Bidi’aMadalla da da wannan Bidi'aKuma wannan Bidi'a ita wacce Annabi yake nufi da fadinsa:Kowace Bidi'a bata ceBa makawa a sanya Bidi’ar da Umar yake Magana a kanta akan mizanin Bidi’a amma ba zata kasance karkashin wacce Annabi sallallahu alihi wa sallam yak e nufi ba.a cikin maganar sa:kowace Bidi'a Bata neUmar Allah ya kara yarda a
14
gare shi anan ya na nuni ne da Bidi’ar hada mutane Limami daya yayi musu jam’I bayan sun kasance da suna rarrabe,kuma ya kasance Asalin sallar dare ta Ramadan ya zo ne daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam hakan ya tabbata a cikin sahihaini daga hadisin Aisha Allah ya kara yarda a gareta cewa Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi sallah ga mutane dare uku sai ya jinkirta musu a rana ta hudu sai y aceLallai ni ina jin tsoron kada a farlanta muku kuma kuma gaza yinta
Imam Ahmad -Allah ya yarda da shi ya ce:
Ko ka san maye Fitina?
Fitina ita ce Shirka watakila idan akai watsi da wasu daga cikin maganganun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam cewa wani abu ya fada cikin zuciyar wani na bata sai ya hallaka
Ya kare
kuma Ibn Abbas -Allah ya yarda da shi ya ce- ya ce:
kuma ya kusa a saukar muku da Dutse daga Sama ina cewa Annabi ya ce kuma kuna cewa Abubakar da Umar sun ce?
FUSKA TA BIYU :Hakiika mun sani tare da yakini cewa amirul mu’minin Umar Allah ya kara yarda a gare shi yana daga cikin wadanda suka fi tsananin girmama zancen Allah madaukakin sarki da Manzon sa Annabi Muhammad sallallahu alai wa sallam,ya kasance ya shahara da tsayawa kan iyakokin allah har ana siffanta shi da mai tsayawa kan zancen Allah.Ya ya qissar matar da ta gabato ma sa –in qissar ta inganta-wajen iyakance sadaki yadda da
15
yawa suka jahilta a yayin da ta ja da shi da fadin Allah madaukakin sarki
Kuma ta yaya zaku karbe shi kuma bayan shashinku ya karkata ga sashi kuma kun dauki Babban Alkawari a tsakaninku
(Surat Annisa'a)
To sai Umar ya hanu ga barin abinda yayi niyya na Iyakance Sadaki
Sai dai wannan qissar sai an yi nazari kan sahihancin ta .Sai dai abin nufi anan shine cewa sayyidina Umar ya kasance mai tsayawa iyakakar haddodin ubangiji baya ketare su,ba za’a jinginawa Umar yardarm Allah ta kara tabbata a gare shi bay a zamo daga cikin masu saba maganar shugaban mutane sallallahu alaihi wa sallam da yace akan Bidi’a
Madalla da da wannan Bidi'a
Kuma wannan Bidi'a ita wacce Annabi yake nufi da fadinsa:
Kowace Bidi'a bata ce
Ba makawa a sanya Bidi’ar da Umar yake Magana a kanta akan mizanin Bidi’a amma ba zata kasance karkashin wacce Annabi sallallahu alihi wa sallam yak e nufi ba.a cikin maganar sa:
kowace Bidi'a Bata ne
Umar Allah ya kara yarda a gare shi anan ya na nuni ne da Bidi’ar hada mutane Limami daya yayi musu jam’I bayan sun kasance da suna rarrabe,
16
kuma ya kasance Asalin sallar dare ta Ramadan ya zo ne daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam hakan ya tabbata a cikin sahihaini daga hadisin Aisha Allah ya kara yarda a gareta cewa Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi sallah ga mutane dare uku sai ya jinkirta musu a rana ta hudu sai y ace
Lallai ni ina jin tsoron kada a farlanta muku kuma kuma gaza yinta
Sallar dare a Ramadan ta na daga cikin suunar annabi sallallahu alaihi wa sallam umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ambace ta da Bidi’a saboda Annabi sallallahu aiaihi wa sallam iokacin da ya bar yin ta sai mutane suka cigaba da yin ta a rarrabe wani mutum zai tada sallah sai wani ya bi shi daga mutum daya ,uku ,bakwai tara har zuwa goma sai su bi shi a cikin masallacin sai sarkin muminai Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ga ya dace ya su yi sallah da limami daya wannan aikinyayi ne saboda rarrabuwar mutaneta bangaren Bidi’a kuma Bidi’a ce da aka danganta ta ba Bidi’a ce ba da aka sayyidina Umar yak ago ta domin cewa wannan sunnar dama can akwai ta a lokacin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sai dai an barta tun a zamanin Annabi sallallahu alaihi wa sallam har zuwa lokacin da Umar ya dawo da ita ,da wannan ne baya yuwuwa su ke danganta Umar da Bidi’a suna nuni da cewa akwai Bidi’a mai kyau.
kuma hakika Mai wani yana iya cewa: akwai wasu abubuwan Bidi'a wadanda Musulmi suka karbe su kuma suna aiki da su kuma ba'a sansu ba a lokacin Annabi kamar Makarantu da wallafa litattafai, da masu kama da su kuma wannan Bidi'ar ai Musulmi suna ganin tayi kyau kuma suna aiki da ita kuma suna ganin tana daga cikin ayyuka nagari to yaya zamu iya hadawa tsakanin wannan wanda dukkan
17
Musulmi sun karbeshi da kuma fadin Jagoran Musulmi da Annabin Musulmi kuma Manzon Talikai baki daya tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi.kowace irin Bidi'a Bata ceAmsar ita ce :za mu ce wannan ya na faruwa ba Bidi’a ba ce sai dai hanya ce zuwa ga abinda aka shar’anta ,sannan hanyoyi suna bambanta da banbanci na wuri da kuma lokaci ,daga cikin ka’idodin tabbatattu sannan hanyoyin suna da hukunce –hukunce ma su manufa hanyoyin shari’a nan a shari’a ne ,wadanda ban a shari’a ba ne ban a shari’a ba ne ,wadanda haramta haramun ne .Mafi alheri shi ne hanyar da za ta shiryar zuwa ga sharri sharri ce abar hani ce ka saurari fadin Allah madukakin sarki inda yake cewa:"Kuma kada ku kuskura ku zagi abinda wasu suke bautawa wanin Allah to sai suma su zagi Allah Sabida Adawa ba tare da Ilimi ba(Surat Al'an'am 108)
kowace irin Bidi'a Bata ce
Amsar ita ce :za mu ce wannan ya na faruwa ba Bidi’a ba ce sai dai hanya ce zuwa ga abinda aka shar’anta ,sannan hanyoyi suna bambanta da banbanci na wuri da kuma lokaci ,daga cikin ka’idodin tabbatattu sannan hanyoyin suna da hukunce –hukunce ma su manufa hanyoyin shari’a nan a shari’a ne ,wadanda ban a shari’a ba ne ban a shari’a ba ne ,wadanda haramta haramun ne .Mafi alheri shi ne hanyar da za ta shiryar zuwa ga sharri sharri ce abar hani ce ka saurari fadin Allah madukakin sarki inda yake cewa:
18
"Kuma kada ku kuskura ku zagi abinda wasu suke bautawa wanin Allah to sai suma su zagi Allah Sabida Adawa ba tare da Ilimi ba
(Surat Al'an'am 108)
Zagin Allolin mushirikai ba ketare iyaka ba ne sai dai ma dai –dai ne amma a muhallin da ya dace amma zagin Ubangijin talikai wuce iyaka nekuma zalunci ne ,saboda haka ne yadda zagin Allolin mushirikai yak e abin so amma kuma zai zuwa ga zagin Allah sai aka hana shi aka haramta shi wannan dalilin ya tabbatar cewa kowacce hanya ta na da manufofin hukunce –hukuncen ta ,Makarantu da wallafa littattafaida sun kasamce Bidi’a ne da ba ‘a same su lokacin Manzon Allah ba in an dube shi ta wannan fuskar baa bin nufi ba ne sai dai hanya ce kuma kowacce hanya tana da manufar hukunce –hukuncen ta .
kuma Saboda haka ko da wani zai gina makaranta dan ilmantar da ilimi haramtacce ginin ya zamo haramun ,hakazalika da wani zai gina makaranta dan ilmantar da ilimin shari’a sai ginin ya kansance shari’a .
To idan wani ya ce: Ta yaya zamu yi bayanin fadin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ?"Duk wanda ya Sunnanta wata Sunna Mai kyau a Musulunci to yana da ladan ta da kuma ladan duk wanda yayi aiki da ita har zuwa ranar Alkiyama"Kuma Sunna tana nufin Shar'anTo Amsa ita ce: Lallai cewa Duk wanda ya ce:to amsar ita ce: cewa duk wanda ya ceshine wanda ya fadi:kowace irin Bidi'a Bata cekuma ba zai taba yuiwuwa ba cewa wani abu ya futo daga
19
mai gaskiya abin gasgatawa fadin wani abu na karya , kuma ba zai taba yiwuwa ba ya rika tufka da warwara a Maganganunsa Sallallahu aalihi wasallam har Abada, kuma ba zai taba yiwuwa ba ya kawo wata ma'ana kwara daya tare da warwarar magana, kuma duk wanda ya zaci cewa zancen Allah Madaukaki ko Maganar annabi suna cin karo da juna to irin wannan zaton zai iya futowa ne kodai ta hanayar gazawa ko kuma kuya kuma hakan ba zai taba samuwa ba a cikin zancen Allah ko Annabinsa hakan ba zai faru ba har abada.kuma idan ya kasance haka to ya bayyana - afifi - rashin tufka dawarwara a cikin Hadisinkowace irin Bidi'a Bata ceSaboda Hadisinto amsar ita ce: cewa duk wanda ya ceCewa Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi ya ceDuk wanda ya fararar da wani abua Musuluncikuma kowace Bidi'a bata cikin Musulunci, da har za'a ce akwai wata mai kyauKuma Bidi'ar bata wani kyau, kuma banbanci tsakanin Sunna da Bidi'a
"Duk wanda ya Sunnanta wata Sunna Mai kyau a Musulunci to yana da ladan ta da kuma ladan duk wanda yayi aiki da ita har zuwa ranar Alkiyama"
Kuma Sunna tana nufin Shar'an
To Amsa ita ce: Lallai cewa Duk wanda ya ce:
to amsar ita ce: cewa duk wanda ya ce
shine wanda ya fadi:
kowace irin Bidi'a Bata ce
20
kuma ba zai taba yuiwuwa ba cewa wani abu ya futo daga mai gaskiya abin gasgatawa fadin wani abu na karya , kuma ba zai taba yiwuwa ba ya rika tufka da warwara a Maganganunsa Sallallahu aalihi wasallam har Abada, kuma ba zai taba yiwuwa ba ya kawo wata ma'ana kwara daya tare da warwarar magana, kuma duk wanda ya zaci cewa zancen Allah Madaukaki ko Maganar annabi suna cin karo da juna to irin wannan zaton zai iya futowa ne kodai ta hanayar gazawa ko kuma kuya kuma hakan ba zai taba samuwa ba a cikin zancen Allah ko Annabinsa hakan ba zai faru ba har abada.
kuma idan ya kasance haka to ya bayyana - afifi - rashin tufka dawarwara a cikin Hadisin
kowace irin Bidi'a Bata ce
Saboda Hadisin
to amsar ita ce: cewa duk wanda ya ce
Cewa Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi ya ce
Duk wanda ya fararar da wani abua Musulunci
kuma kowace Bidi'a bata cikin Musulunci, da har za'a ce akwai wata mai kyau
Kuma Bidi'ar bata wani kyau, kuma banbanci tsakanin Sunna da Bidi'a
kuma akwai akwai wasu Jawabi mai kyau cewa Ma'anar Duk wanda ya Sunnanta ai duk wanda ya raya Sunna daman can da ita wacce
21
aka daina aiki da ita anan sai ya zamanto Sunnantawa rabashi akayi ta wani bangare kamar yadda Bidi'a ta kasance rabata akayi ga wanda ya raya wata Sunna bayan ta Mutu.
kuma Akwai wani Jawabin na Uku wanda yake nuna dalilin da yasa Annabi ya fadi Hadisin shi kissar wasu Mutane da suka zo wajen Annabi kuma sun kasance suna cikin halin tsananin talauci sai yayi kira da a taimaka musu sai wani Mutum ya zo daga cikin Mutanen Madina a hannunsa akwai taskira ta Azurfa wanda tafi karfin daukan hannunsa sai ya ajiyeta a gaban Annabi sai Fuskar Annabi ta cika da farin ciki da Murna kuma sai ya ce:Duk wanda ya Sunnanta wata Sunna Mai kyau a cikin Musuluncito yanada ladanta da kuma ladan duk wanda yayi aiki da ita har zuwa ranar Alkiyama.To a nan Ma'anar sunnna tana iya kasancewa kirkiro aiki wajen zartar da (aiki mai Asali a Shari'a) ba wai wajen kirkiro sabo ba a Sharia, to kakan ya basi wata Ma'ana dabanDuk wanda ya farar da wani abu mai kyau a MusulunciDuk kuma wanda ya yi koyin aiki da ita ba wai kirkiro wani sabon abu a shari'a ba, domin kirkirarar sabon Abu a Shari'a Haramun ne.kowace irin Bidi'a Bata ce
Duk wanda ya Sunnanta wata Sunna Mai kyau a cikin Musuluncito yanada ladanta da kuma ladan duk wanda yayi aiki da ita har zuwa ranar Alkiyama.
To a nan Ma'anar sunnna tana iya kasancewa kirkiro aiki wajen zartar da (aiki mai Asali a Shari'a) ba wai wajen kirkiro sabo ba a Sharia, to kakan ya basi wata Ma'ana daban
22
Duk wanda ya farar da wani abu mai kyau a Musulunci
Duk kuma wanda ya yi koyin aiki da ita ba wai kirkiro wani sabon abu a shari'a ba, domin kirkirarar sabon Abu a Shari'a Haramun ne.
kowace irin Bidi'a Bata ce
kuma kusani cewa ya ku 'Yan Uwa cewa ba'a samun dacewa da biyayya sai idan aiki ya dace da Shari'a cikin abubuwa guda shida:
Na farko:idan mutum ya hada ibadarsa da wani sababi ban a shari’a ba wannan bidi’a ce abar mayarwa ga ma’abocinta,misalign haka wani bangare na mutane n suna raya daren ashirin da bakwai na watan Rajab da hujjar cewa a wannan Daren ne aka yi mi’iraji da Annabi sallallahu Alaihi wa sallam,sallar dare ibada ce sai yayin da aka hadata da wannan sababi sai ta zamo Bidi’a ;saboda sun gina wannan ibadar ne akan wani sababi da bai tabbata akan shari’a ba.Wannan siffar ta dace da ibada a shar’ance,al’amari ne mai muhimmanci da yake bayyana Bidi’a saboda da yawa suna daukar cewa Sunnah ce hakan sai dai baya daga Sunnah.
NA BIYU: JINSI dole ne ibada ta kasance ta yi daidai da shari’a ta bangaren jinsi da mutum zai yi ibada da wani jinsi da ba ba’a shar’anta ba ba za’a karbi ibadar sa ba misalign haka mutum yayi layya da Dokilayyar ba ingantacciya bace ba:saboda jinsin ya sabawa shari’a, Layya bata yuwuwa sai da ga dangin dabbobi hudu ,Rakuma,Shanu ,Raguna da Akuya.
23
NA UKU; KIMA da mutum zai so yin kari a cikin sallar farilla da sai mu ce :wannan Bidi’a ce da ta sabawa shari’a ta bangaren kimantawa ,kamar a ce mutum ya yi sallar azahar raka’a biyar hakika sallar sa bata inganta ba a baki dayan ittifakin malamai.
NA HUDU: AIWATARWA da mutum zai yi alwala sai ya fara da wanke kafa ,sannan kai ,sannan hannu , da sai mu ce Alwalar sa ta baci ;saboda yadda aka aiwatar da ita ya sabawa shari’a.
NA BIYAR:LOKACI; da mutum zai yi Layya a ranakun farko na watan Zul Hajji ba za’a karbi layyar sa ba saboda ta sabawa shari’a ta bangaren lokacin da aka yi ta .Na ji cewa wasu mutane suna yanka dabbobi a watan Ramadan dan neman kusaci da Allah Madaukakin sarki wannan aikin na ta wannan fuskar Bidi’a ne su Saboda ba bu wani abu da yake kawo kusacida Allah sai Layya,da Hadaya,da kuma Aqiqa,Yanka a Ramadan tare da kudurce neman lada kamar Layya na Idin babbar sallah Bidi’a ne.Amma yanka saboda kawai Nama ya halatta.
NA SHIDA: WURI da mutum zai yi itikafi ba’a masallaci ba , to itikafin sa bai inganta ba;saboda itikafi bay a halatta sai a masallaci.Da mace za ta ce zan yi itikafi a wajen da na ke sallah a gida itikafinta ba zai inganta ba saboda ta sabawa shari’a ta bangaren muhallin da ta yi itikafin.Wani misalign kuma wani mutum ya yi nufin yayi dawafi
24
sai ya tarar da wajen dawafin ya cunkushe sannan zagayen da yake shima ya cunkushe sai kawai ya kama dawafi a bayan masllacin dawafin sa bai inganta ba saboda in da kawai ake dawfi shine dakin ALLAH ,Allah madaukakin sarki ya na cewa Annabi Ibrahim A.S:“Ka tsarkake dakina ga masu yin dawafi”.( Suratul Hajj 26)
“Ka tsarkake dakina ga masu yin dawafi”
.( Suratul Hajj 26)
Ibada bata zamo wa aiki nagari sai ta cika sharudai guda biyu:
NA FARKO: Ikhlasi NA BIYU:Bin Annabi sallallahu alaihi wasallam shi kuma bin annabi ba ya tabbata sai da abubuwa shida da muka ambata wadanda suka gabata.
Ina cewa ga wadanda aka jarrabesu da Bidi’a wadanda manufar su mai kyau ce kuma suna son alheri idan kuna son alheri hakika mun san hanyar alheri ta hanyar magabata na kwarai Allah ya yarda da su.
Ya ku yan uwa ku yi riko da sunnar annabi sallallahu alaihi wa sallam ku kama hanyar magabata na kwarai ku kasance kan abinda suka kasance akan shi sai ku duba ku gani shin hakan zai cutar ku da wani abu
Ina cewa ina kuma neman tsari kan in fadi abinda ba ni da ilimi akan shi zaka sami da yawa daga cikin wadanda suka kwadaitu da bidi’a ba sa damuwa wajen aiwatar da duk wani abu da shari’a ta tabbatar da shi ya tabbata kuma sunnah ce idan suka gama bidi’arsu sai su riki sunna tabbatacciya ba da karfi ba wannan kuma duk ya na
25
faruwa ne sakamakon cutarwar bidi’a ga zukatan su ,cutarwar bidi’a ga zukata babba ce sa’annan hatsarurrukanta a cikin addinima su girma ne, wasu mutane ba za su farar da wata bidi’a a cikin addinin Allah ba sai sun yi sakaci da wata sunnar kwatankwacin ta ko fiye da haka,wasu daga cikin ma’abota ilimi ne suka ambaci hakan.
Idan mutum ya ji a ran shi cewa shi din yana bin sunnar annabi ne ba dan bidi’a ba wannan sai ya haifar ma sa da cikar tsoron Allah da Kankan da kai da bautawa ubangijin talikai da cikarbiyayya ga shugaban manzanni,manzon Allah annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.
Ina yin nasiha ga yan uwa musulmai wadanda suka kyautata wani abu na bidi’a abinnan ya ta’allaka da zatin Allah ne ko sunayensa ko siffofinsa ko kumaya ta’allaka da manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam da girmama shi kan su ji tsoron Allah su kum yi adalci kan hakan su gina al’amuran su akan biyayya ba akan bidi’a ba,akan kadaita Allah ba akan shirka ba ,akan sunnah ba akan bidi’a ba ,akan abinda Allah ya ke so ba kan abinda shaidan yak e so ba .Da sun ga abinda zai faru ga zuciyoyin su na daga aminci,rayuwa,nutsuwa,nutsuwar ruhi,da kuma haske mai girma.
Ina rokon Allah ya sanya mu daga cikin shiryayyu masu shiryarwa ,kuma shuwagabanni ma su gyara ,kuma ya haskaka zukatanmu da Imani ,kuma kar ya sanya abinda muka sani ya zamo nauyi akan
26
mu,ya daura mu bi sa hanyar bayinsa muminai ,ya kuma sanya mu cikin waliyyansa ma su jin tsoron sa .kuma daga cikin bayin sa masu rabauta.wasallallahu ala nabiyyina Muhammadin wa ala Alihi wa sahbihi ajma’in.
* * *