1
Jerin Littafan Shi’a Na 7
Zuwan
Shi’a
Nijeria
Umar Labxo
2
بسم الله الرحمن الرحيم
Asalin yaxuwar Shi’a a Nijeria ya fara a tsakanin matasa, yawanci ‘yan
makaranta, masu aikin yaxa addinin Musulunci waxanda aka san su da sunan ‘Yan
Uwa Musulmi. Wannan suna fassara ce kai tsaye ta sunan wata Qungiya,
Al’ikhwanul Muslimun, wacce Imam Hassan Albanna ya kafa a qasar Masar a
cikin shekarun 1930. Babbar manufar qungiyar shi ne mayar da Musulmi zuwa ga
hukunce – hukuncen Musulunci a kafatanin fagagen rayuwarsu wanda ya haxa da
fagen siyasa, tattalin arziqi, tarbiya da zamantakewa da kuma dangantakarsu da
waxanda ba Musulmi ba. Qungiyar ta yaxu a yawancin qasashen Musulmi ciki har
da Nijeriya.
Tare da qungiyar ‘Yan Uwa Musulmi akwai qungiyar Xalibai Musulmi ta
Nijeriya, watau M.S.S. wacce aka kafa ta shekaru 50 da suka wuce. Waxan nan
qungiyoyi biyu sashen su ya haxe da sashe kuma suna yin nashaxinsu a jami’o’i da
manyan makarantun qasar nan. A wani yayi nashaxinsu yana shafar ‘yan
makarantun sakandare ta hanyar tarukan horaswa da suke shiryawa xaliban
qananan makarantu a lokacin hutu. Masu shagala da aikin da’awa a qarqashin
inuwar waxan nan qungiyoyi yawancinsu matasa ne maza da mata masu karatun
fannonin ilmi dabam – daban, kamar Kimiya da Likitanci da Tattalin Arziki, amma
kaxan ne daga cikinsu suke karanta Musuluncin kansa. Wannan ya sa, koda yake
suna da son Musulunci ga kuma gafin quruciya, amma suna da qarancin ilmin
addini. Saboda haka a lokacin da Shi’a ta shigo qasar nan, a kan doron juyin juya
hali na Musulunci (!) na qasar Iran da kirarinsa mai xaukar hankali na kafa
jumhuriyar Islama da zartar da hukunci da Shari’a, sai yawancin waxannan samari
3
suka hau jirgin Shi’a da tikitin juyin Islama. Daga cikin waxan nan samari akwai
Malam Ibrahim Ya’aqub Alzakzaki.
Alzakzaki da Yaxuwar Shi’a
Sunan Zakzaki ya fara fitowa a farkon shekarun 1980 lokacin da, bayan
kammala karatunsa a fannin Tattalin Arziqi daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria,
ya qi ya je aikin bautar qasa, watau N.Y.S.C. saboda, kamar yadda ya ce, shi ba ya
bautawa qasa; Allah kaxai yake bautawa. Duk da raunin wannan magana da rashin
fahimtar addini da take nunawa a fili, wannan mataki da Zakzaki ya xauka ya ba
shi farin jini kuma ya mayar da shi tamkar wani gwarzo a idanun matasa waxanda
wutar son addini take ci a zukatansu amma qwaqwalensu sun yi duhu duxum
saboda jahilci. Zakzaki ya wayi gari ana lasafta shi daga cikin shugabannin xalibai
da matasa masu sha’awar addini.
Ba’a daxe da haka ba, sai mahukuntan qasar Iran masu bin tafarkin Shi’anci,
a cikin qoqarinsu na neman goyon bayan Musulmin duniya musamman a kan
yaqinsu na shekaru takwas da qasar Iraqi, suka riqa gayyatar malamai da matasa
masu sha’awar addini daga ko wane vangare na duniyar Musulmi domin su halarci
bikin shekara – shekara da suke yi don tunawa da nasarar juyin juya halinsu.
Zakzaki na daga cikin waxanda aka gayyata daga Nijeriya.
Mahukuntan Iran waxanda suke xaukar nauyin baqinsu zuwa da komowa,
suna nunawa baqin karamci, suna girmama su ainun kuma ga alama suna ba su xan
goro a matsayin sallama. Banda wannan, suna qoqarin cusa wa baqin nasu aqidar
Shi’anci ta hanyar laccoci, muhalarori, tarukan qarawa juna sani da kuma kyautar
littafai masu yawa. Ga alama ta wannan hanya sun yi nasarar ribace wasu da
shigar da su tafarkinsu kamar Zakzaki, wasu kuwa sun gane makircinsu sai suka
4
raba gari da su. Daga cikin waxanda aka gayyata daga Nijeriya kuma amma ba’a
yi nasarar janye su zuwa Shi’anci ba akwai Malam Abubakar Tureta daga Kaduna
da Malam Abubakar Jibril daga Sakkwato wanda ya zama a sahun gaba wajen
yaqar Shi’anci a Nijeriya.
Alaqar Zakzaki da Iran ta ci gaba da yin qarfi a hannu guda, a xaya hannun
kuma shahararsa ta bunqasa, kuma magoya bayansa suka qara yawa, a yayin da ya
buxe ressa a yawancin jihohin arewacin qasar nan, yana kira da sunan
gwagwarmayar kafa hukuncin Musulunci da yaqar waxanda ya kira xagutai.
Mabiyan Zakzaki sun yi ban gaskiya da shi ainun, sun yarda da
shugabancinsa har suna ganin wanda duk bai xauke shi a matsayin shugaba ba
kamar shi ba Musulmi ba ne, suna cewa wanda ya mutu bai yi masa mubaya’a ba
to ya mutu mutuwar Jahiliya. Shi kuwa ya yi amfani da amince masa da suka yi,
ya riqa gabatar musu da koyarwar Shi’a da aqidojinsu sannu a hankali kuma koda
yaushe aka tsorata su da kusancin shugabansu da Iran, sai ya ba su tabbacin cewa
shi babu abinda ya haxa shi da Iran sai gwagwarmaya da yaqar Amurkawa da
Yahudawa da xagutai. Amma kuma a hannu guda, Zakzaki ya ci gaba da shigo da
alamu da bukukuwan Rafilawa kamar babbaqun rawuna, bikin Ashura, da
sauransu.
Haka nan gogan naka ya ci gaba da taqiya, yana yaudarar almajiransa da
magoya bayansa har ranar da dubunsa ta cika. Wata mujalla daga cikin irin
mujallun da ake bugawa a qasar Iran ana aikowa da su Nijeriya ta buga wata
maqala wacce a cikinta aka ci zarafin Sahabin Annabi (SAW) mai shuhura watau
Abu Huraira (R.A). Wannan ya tayar da hankalin wasu daga cikin mabiyan
Zakzaki inda suka nemi ya fito fili ya la’anci wannan maqala amma ya qiya.
Wannan shi ya buxe idanun da yawa daga cikin mabiyansa, waxanda a da jahilci
5
da bin son zuciya ya rufe idanun nasu. Daga nan aka samu wani reshe a cikin
mabiyan Zakzaki wanda ya yi ta matsawa malamin lamba a kan ya fito fili ya
bayyana matsayinsa dangane da ko Shi’a yake yi ko a’a. Zakzaki ya ci gaba da
noqewa har dai daga bisani tusa ta qurewa bodari kuma gaskiya ta yi halinta. A
cikin shekarar 1995 aka yi uwar watsi bayan wani taron qure qarya da aka yi wa
Zakzaki a hedkwatarsa a Zaria. Mabiyansa da yawa, ciki har da manyan
almajiransa, suka valle, suka yi shelar barrantarsu da Zakzaki da tafarkinsa na
Rafilanci kuma suka kafa tasu qungiya ta yunqurin jaddada Musulunci a kan
tafarkin Ahlus Sunna, Jama’atu Tajdidil Islam (J.T.I.), a qarqashin shugabancin
Malam Abubakar Mujahid. A yanzu asirin Zakzaki ya tonu kuma taqiya ta qare,
amma kash! Biri ya riga ya yi varna.
Dalilan Yaxuwar Shi’a a Nijeriya
Akwai dalilai masu yawa da suka taimaka wajen yaxuwar tafarkin Rafilanci
a nan qasar. Za mu duba muhimmai daga cikinsu.
Dalili Na Farko: Gazawar Malamai
Dalili na xaya kuma mafi muhimmanci, shi ne gazawar malamai a
shugabancin jama’a da shiryar da su, da yi musu jagora da katangance su daga
vata. Domin famintar wannan dalili za mu kasa malamai gida uku.
1. Malaman zaure, ko kuma malaman buzu kamar yadda ake kiran su a wasu
wurare. Wannan kashi a cikin malamai su ne mafi girma, mafi alqadari kuma
mafi qima a idanun mutane. Amma duk da girma da qimarsu da muke gani, za mu
rufe ido mu faxi gaskiya game da su domin gaskiya ta fi ko wane mai qima qima.
Matsala ta farko da malaman zaure, yawancin su, shi ne imma dai suna da
qarancin sani ko kuma ilminsu ya sava Sunna. Xauki ilmin Tauhidi ga misali,
6
wanda shi ne mafi muhimmanci kuma mafi xaukakar dukkan ilman Musulunci.
Har yanzu malamanmu na buzu ba su rungumi tafarkin Sunna ba a babin Tauhidi;
Tauhidinsu imma Ash’ariya ne ko kuma Tauhidin masu Ilmul Kalam wanda yake
da tushensa a wajen Mu’utazilawa ko Falasifawa.
A fannin Fiqihu, wanda shi ne fannin da malaman zaure suka yi fice,
yawancinsu a Fiqihun Malikiya kawai suka tsaya. Idan mutum ya duba cewa
banda sauran mazhabobi uku fitattu, watau Hanafiya, Shafi’iya da Hanbaliya,
akwai mazhabobin Zahiriya da Zaidiya, banda mazhabobin xaixekun malamai
waxanda ba su samu yaxuwa ba kamar mazhabar Imam Thauri da Imam Auza’i da
sauransu, sai mutum ya ga cewa babu shakka malamanmu kaxan suka xebo a
Fiqihun Musulunci. Ba’a maganar fannin Usulul Fiqhi. Kuma ko a Malikiya ma,
wasu littafai ne qididdigaggu suke laqema, wasu manyan littafan mazhabar
yawancinsu ba su karanta su, kamar Tafsirin Qurxubi da Tafsirin Abubakar Ibnul
Arabi, da Altamhid na Ibnu Abdilbarri da Bidayatul Mujtahid na Ibnu Rushd, da
sauransu. A nan ba kuxin goro muke yi wa malaman ba; amma muna bayyana
halin yawancinsu ne.
A fannin Tafsiri kuwa, ya ishe ka manuniya cewa a qasar Hausa duka idan
mutum ya ce, “Na tafi wajen jalalaini,” to wajen karatun tafsiri yake nufi saboda
tafsiri shi ne jalalaini kuma jalalaini shi ni tafsiri. Wannan yana nuna yadda
malamanmu suka tsaya a kan littafin Tafsirul Jalalaini na Jalaluddinil Mahalli da
Jalaluddinis Suyuxi kawai a koyo da koyarwarsu na fannin Tafsiri. Idan aka duba
cewa wannan littafi bai kai matsayin moxa guda ba a cikin kogi dangane da abinda
aka rubuta a fannin Tafsiri, sai a ga cewa tabbas abinda malamanmu suka rasa ya fi
abinda suka samu a cikin wannan fanni. Bari batun ilmin Usulul Tafsir. A nan
ma, ba kuxin goro muke yi wa malaman ba; amma hukunci a kan mafi yawa ake
yin sa, mafi qaranci togewa ne.
7
Matsalar Luga a wajen malaman buzu makomarta ita ce ga matsalar manhaja
da tsarin koyarwa. Koyon Luga yana da rukunai uku: karatu da rubutu da furuci.
Ga alama malaman zaure karatu kaxai suke yi saboda a tsarin karatun zaure babu
zancen a bayar da aiki a rubuto, watau abinda ake cewa da Larabci “tamrinat” ko
“tamarin”, ko kuma da Turanci “exercises”. Wannan ya sa koda yake malaman
zaure yawanci suna da babbar taska ta xaixekun kalmoni, “vocabulary”, amma
magana da Larabci tana yi musu wuya, haka nan rubutawa. Kuma koda yake ana
iya lura cewa malaman buzu gwanayen rubutun waqa ne da Larabci, makomar
wannan, wata qila, shi ne cewa ita waqa ‘yar kyaikwayo ce.
Haka nan a fannonin Hadisi da Tarihi da Sira da Firaq; malaman buzu, in ka
xauke su gaba xaya, suna da qarancin rabo a cikin waxan nan ilmai. Rashin ilmin
Firaq, watau ilmin qungiyoyin bidi’a da aqidojinsu, shi ya sa malaman zaure suka
rasa ta yi a gaban kogin Shi’anci yayin da ya yi ambaliya domin ya tafi da matasan
Musulmi. Manyan littafan da aka rubuta a ilmin Firaq kamar Almilal wal Nihal na
Shahrastani da Maqalatul Islamiyina wa Ikhtilaful Musallina na Imam Abul
Hassan Al’ash’ari da Alfarqu bainal Firaq na Shaihul Islami Abdulqahir Albagdadi
da Alfisal fil Milal wal Ahwa’i wal Nihal na Ibnu Hazm Al’andalusi da sauransu,
yawancinsu ko sunayensu ba su tava ji ba.
Wannan ya sa suka xauka cewa wai Shi’anci wani wasan yara ne wanda za
su bari in sun girma! Idan aka ce su bincika abinda yake faruwa a tsakanin
Rafilawa sai su ce, haba wannan hayaniyar quruciya ce suke yi, za su bari ne. Sai
ga shi waxan nan malamai waxanda suka tashi zaune tsaye a saboda wasu ‘yan
qungiyoyi da suka ce wai suna zagin waliyai, sai ga shi ana zagin Sahabban
Annabi (SAW), ana kafirta su, amma sun yi shuru. Saboda haka malaman suka
kyautata alwala amma suka gaza sallah!
8
Abinda ya gabata dangane da ilminsu ne; amma idan muka duba ayyukansu
sai mu ga abin mamakin. Mun gabatar da bayani cewa a cikin malaman Musulunci
a nan qasar, malaman zaure su ne mafi yawa, mafi alqadari kuma mafi qima a
idanun mutane. Abinda ya sa suka zama haka shi ne cewa su magadan Jihadin
Shaihu Danfodiyo ne. Amma a yau, ayyukansu da halayensu sun sava da na
malaman Jihadi. Malaman Jihadi sun yi ilmi mai zurfi, kuma littafan da suka bari
suna shaidawa da haka, amma malamanmu na yau abin ba haka yake ba. Shaihu
Usmanu ya rubuta kimanin littafai 90, Shaihu Abdullahi kimanin 70; Muhammad
Bello xan Shaihu kimanin 80; Nana Asma’u kimanin 55; amma malamanmu na
yau, saboda gafala rubutun ma laifi suka xauke shi. Idan ka ce su rubuta littafi sai
su ce wai ba su gama da waxanda aka riga aka rubuta ba; idan kuma kai ka rubuta
sai su ce ka yi karambani. Alhali Shaihu Usmanu, a cikin littafinsa Najmul
Ikhwani, yana kira ga Musulmi da su riqa karanta littafan malaman zamaninsu,
saboda malaman ko wane zamani su suka fi sanin matsalolin wannan zamanin,
kuma wajibinsu ne su nemawa matsalolin magani.
Malaman jihadi sun yi wa’azi, malaman buzu ba sa yin wa’azi sai kaxan.
Malaman jihadi sun yaqi bidi’a, malaman zaure su bidi’ar suke yaxawa kuma duk
wanda yake yaqi da bidi’a to su shi ne abokin gabarsu. Malaman jihadi sun
nesanci sarakai da masu mulki, na yanzu kuwa shige musu suke yi. Malaman
jihadi sun yi jihadi kuma sun jaddada addini, malamanmu na yau ba su san ko inda
za’a kama bakin zaren ba. Malaman Jihadi sun tsaya tsaiwar daka, sun yi
gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da tsai da adalci, malamanmu na yau cewa
suke yi yanzu zamanin yin shiru ne da lazimtar cikin gida, kamar yadda wani
babban malamin zaure ya faxa wa Shaihu Abubakar Mahmud Gumi.1 Malaman
jihadi sun gina al’umma, malaman buzu sai aikin gina gidajensu na gado. Ko
1 Duba Where I Stand na Abubakar Mahmud Gumi, bugun Spectrum Books, Ibadan-Nijeriya, 1992, shafi na
51.
9
wane malami ya qasaita sai ka ji ya naxa khalifa, wai xan da zai gaje shi. Ko waye
ya ce musu ilmi gado ne? Malaman jihadi sun ce a yi sana’a (duba Ahkamul
Makasib na Muhammad Bello) su kuwa yawanci ba sa sana’ar, balle su ce wani ya
yi, sai cin abinda suke kira albarkacin makaranta!! Wani malamin ma har faxa
yake yi don me za’a ce Musulmi su daina bara!! Kuma qarya yake yi; shi
‘ya’yansa ba sa bara.
Kai a yau ta kai cewa malaman buzu da yawansu, ba wai kawai sun raba gari
da tafarkin Shaihu Xanfodiyo ba da tarihinsa da koyarwarsa, a’a yaqar sa ma suke
yi! Sun qaurace wa littafansa da ilminsa da koyarwarsa. Mutum zai yi shekara
guda cur bai ji sunan Xanfodiyo ya gudana a bakin xayansu ba a wajen karatu ko
wa’azi. Maimakon haka, sun rungumi koyarwar wasu jahilan malamai waxanda
bas u zo qasar nan da kome ba sai diwanin waqe-waqe.
Wannan shi ne halin yawancin malaman azure, kuma shi ne tushen kusan
dukkanin matsalolin da muke fama da su a yau. Don haka babu mamaki idan ba su
taka rawa ta ku-zo- ku-gani ba wajen hana yaxuwar Shi’anci a qasar nan.
2. Kashi na biyu na malaman shi ne wanda za mu kira da sunan Ustazai.
Wannan kashi ya haxa da dukkan waxanda suka yi karatun addini amma a
zamanance, kamar waxanda suka halarci makarantun Haya Muslim kuma suka yi
karatun diflomomi ko digiri na fannin nazarin addinin Musulunci ko Shari’a a
manyan makarantu da jami’o’in qasar nan. Kuma ya haxa da waxanda suka yi
karatu a jami’o’in qasashen Larabawa da sauran qasashen Musulmi. Waxan nan
yawanci suna da kyakkyawar manhaja ta koyon karatu kuma ilminsu yana da faxi
da zurfi koda yake wasunsu, kamar waxanda suka fita daga jami’o’in qasarnan,
ilmin nasu faxi gareshi kawai amma ba zurfi. Sai dai duk da haka suna samun
kyakkyawan harsashi wanda yake ba da dama ga duk wanda yake so cikinsu da ya
10
zurfafa. Suna tsakuro wani abu kusan daga ko wane fanni muhimmi na addinin
Musulunci kamar Alqur’ani da Hadisi (waxan nan ba su da qarfi a manhajojin
jami’o’in Nijeriya); Fiqihu da Usulul Fiqihi, Falsafa da Tauhidi (a makarantun
Nijeriya yawanci Tauhidin Ash’ariya ake koyarwa); Tarihi da Sira; da kuma
fannonin Luga dabam – daban irin su Adab, Nahawu, Sarfu, Balaga da ressanta
uku, Aruli, da sauransu. Samun qaqqarfan harsashe na Luga yana zama tamkar
wani mabuxi ga Ustazai wanda suke buxe taskokin ilmi da shi.
Kamar yadda Ustazai suka sha bamban a wajen ilminsu, da mai zurfin ilmi
da mai cikin cokali, haka nan suka sha bamban wajen ayyukansu da halayensu da
sadaukar da kansu ga addini. Akwai masu aqidar Salaf, masu bin Sunna da yaqar
bidi’a, kamar yadda akwai ‘yan gargajiya wajen aqidarsu da fahimtarsu da
rungumar bidi’a. Daga cikin waxan nan na biyun akwai waxanda suka fito daga
gidajen malaman zaure, waxanda suka fito daga gidajen sarautar gargajiya da masu
karkata ga xariqun Sufaye. A cikin Ustazai akwai masu yin wa’azi da waxanda ba
sa yi, da masu yaqar bidi’a da ‘yan ba-ruwanmu da waxanda suka sadaukar da
kawunansu domin koyar da mutane da aikin da’awa da waxanda ba sa koyarwa
sai dai a aji inda ake biyan albashi.
Yawanci waxanda suka wayar da kan Musulmi dangane da tafarkin
Rafilanci, suka bayyana vacinsa da sharrinsa da vatansa, suka yi fama don dakatar
da yaxuwar Shi’anci a tsakanin Musulmi daga cikin wannan kashi suke. Daga
cikinsu akwai waxanda suka yi amfani da koyarwa da wa’azi wajen yaqar Shi’a
kamar Shaihu Abubakar Mahmud Gumi, wasu sun yi amfani da huxuba kamar
Shaihu Abubakar Jibril Sakkwato, wasu sun yi amfani da alqalumansu kamar
Shaihu Aminuddini Abubakar Kano wanda ya fassara littafin Alkhuxuxul Arida
na Muhibbud Dini Alkhaxib zuwa harshen Hausa wanda a karon farko ya fallasa
asirin Shi’a ga jamhurun Musulmi waxanda ba sa karatun Larabci ko Turanci.
11
3 Saboda rashin kalmar da ta fi, za mu kira kashi na uku na malaman da sunan
Burazozi wanda wannan hausancewa ne na kalmar “brothers” ta Turanci wace take
nufin ‘yan uwa. Abinda nake nufi da burazozi, ko kuma ‘Yan Buraza kamar yadda
aka fi sanin su, su ne mutane, yawanci matasa, waxanda suke da son Musulunci a
zuci amma kuma galibi suke da qarancin saninsa. Yawanci suna sanin Musulunci
ta hanyar sauraron laccoci a wurin taruka, karanta qasidu da maqalu a cikin jaridu
na yau da kullum da kuma mujallu masu kulawa da al’amuran Musulmi.
Yawancinsu xalibai ne masu karatun fannoni dabam-daban a manyan makarantu
da jami’o’i kamar fannonin kimiya, fasaha, tattalin arziki, likita, lauya da sauransu.
Kaxan ne daga cikinsu suka karanta Musulunci kuma a mataki na qasa ainun,
imma I.R.K. a makarantun sakandare ko kuma qaramar faifa ta aro a jami’a.
Kamar yadda na faxi a baya, yawancin waxannan matasa ne masu tsananin son
addini da kishin sa amma kuma babu wadatar ilminsa. Idan ka haxa qarancin sani
da tsananin kishi da gafin quruciya, sai ka samu wani kwaxo mai haxari. Kuma da
yake yawanci suna jin Turanci, harshen da shi ne ake yin amfani, kuma ake burga,
da shi a makarantu, wannan sai ya ba su damar shaqe wuyan makirfon da faxi a
saurare su, koda abinda za su faxi xin ba shi da nauyi ainun. Wani babban abinda
yake qara tauye su shi ne rashin jin Larabci kuma kamar yadda aka sani duk wanda
bai jin Larabci to ba ya shan kunun Musulunci sai dai ya sha farau – farau.
Wannan kashi na “malamai” daga cikinsu ne yawancin ‘yan Shi’a suka fito, ciki
har da madugunsu Malam Zakzaki.
Wannan bayani duka ba yana nufin cewa wannan kashi na malamai bai yi
wa Musulunci kome ba; a’a. A haqiqa ‘Yan Buraza sun toshe wata babbar kafa
a makarantunmu wacce, musamman a shekarun 1970 da 1980, ba mai iya toshe
ta sai su. Sun taimaka ainun wajen tsayar da ibadoji, kamar sallah da azumi, a
makarantu, sun tari qalubalen qungiyoyin Kirista kuma sun taimaka wajen
12
yaqar malamai da xalibai masu karkata ga tafarkin Gurguzu a jami’o’inmu a
lokacin da Kwaminisanci yake yaqar addinai da al’adu a qasashe masu tasowa.
Sai dai wannan kashi na malamai, da yawa daga cikinsu, bayan sun
manyanta kuma sun taka matakin shugabanci da tasiri a cikin al’umma, har yau
abin takaici suna nan suna yaxa Shi’a, wasu a kan rashin sani wasu kuma a bisa
ganganci. Daga cikinsu, ga misali, akwai wani xan jarida mai qima a idanun
makaranta, wanda ya yi rubutu a wata jarida wacce ake mata kallon ta Musulmi
ce, yana cewa wai qiyayyar da Larabawa suke nuna wa mutanen Iran qiyayya
ce da aka gina ta a kan qabilanci, yana nufin saboda su ‘yan Iran Farisawa ne ba
Larabawa ba, kuma wai savanin dake tskaninsu ba na aqida ba ne. Babu shakka
wannan xan jaridar imma dai ya shiga fagen da ba shi da sani a kai, abinda bai
dace da xan jarida mai mutunci da amana ba, ko kuma yana yaudarar
makarantansa ne da gangan.1
Akwai wani Farfesan Tarihi (amma ba Tarihin Musulunci ba) wanda ya ba
da lacca a munasabar bikin Ashura na ‘yan Shi’a na shekarar 1432/2011 a Kano,
inda ya ce wai ranar da Hussaini(RA) ya yi shahada ita ce rana mafi muhimmanci a
tarihin Musulunci.
Abin mamaki! Ba ranar da Annabi(SAW) ya yi hijira zuwa Madina ba
(wacce Sahabbai suka zave ta, don muhimmancinta, ta zama rana ta farko a
kalandar Musulunci); ba ranar yaqin Badar ba (wacce Allah ya kira ta a cikin
Alqur’ani: Yaumal Furqani: Ranar rabewa tsakanin qarya da gaskiya); ba ranar
Sulhun Hudaibiyya ba (sulhun da Allah ya kira shi a cikin Alqur’ani: Fatahan
Mubina: Buxi mabayyani); ba ranar Fatahu Makkata ba (ranar da aka kawo
qarshen bautar gumaka a qasar Larabawa); a’a, ranar da Hussaini ya yi shahada ita
ce mafi muhimmanci a tarihin Musulunci! Ban sani ba wannan jahilci ne daga
vangaren Farfesan ko kuwa ya sha farfesun Iran ne, shi ya sa yake faxin haka da
gan-gan don ya vatar da mutane?
1 Domin tabbatar da haka, duba littafinmu Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan shi’a.
13
Kuma wasu jaridu da ake wa kallon cewa su na Musulmi ne sun xauko
wannan bankaura ta Farfesan, sun buga ta, suna yaxa ta a tsakanin al’umma. Shin
rashin sani ne wannan ko kuwa wata qullalliya ce? Ta yaya ‘yan jaridarmu za su
jahilci addininmu? Ko ta qaqa mutanen da aikinsu ne ilmantar da jama’a da
faxakar da su da wayar da su, za su komo suna yi musu rufa-ido?
Na karanta wata maqala a cikin jaridar Daily Trust fitowar Alhamis, 23 ga
watan Fabrairu, 2012 shafi na 52, inda wata ma’aikaciyar jaridar mai suna Hajiya
Wance ta ruwaito wani malamin Shi’a yana zargin Sayyidina Abubakar da
Sayyidina Umar, Allah ya qara musu yarda, da cewa wai sun yi mubaya’a ga Ali
binu Abi Xalib(RA) a kan khilafa a gaban Annabi(SAW) amma bayan rasuwar
Annabi xin sai suka warware wannan mubaya’ar.
Sai na yi mamaki yadda jaridar za ta tallata wannan zargi na Shi’a tare da
cewa zargin ya sava da tarihi ingantacce, kuma tare da cewa zargin yana tattare da
vatanci ga waxannan manyan Sahabbai. Na ce a raina da wani xan Majalisar
Dattijai ne ko Majalisar Wakilai aka yi wa wannan zargi da wata qila jaridar sai ta
tuntuve shi, ko ta tuntuvi wani mataimakinsa, kafin ta buga zargin don ya kare
kansa ko ya qaryata, kamar yadda jaridu masu mutunci suke yi. (Wani da ba na
tuhuma da qarya ya tabbatar mun da cewa sun aike da martani daga baya, amma
jaridar ba ta buga ba.)
Ita wannan musakar Hajiyar da ta rubuta maqalar da Editanta jahili, ko
munafuki, da ya buga ta ba su sani ba cewa warware mubaya’a babban laifi ne a
Musulunci wanda bai kamata a dangana shi ga gama-garin Musulmi ba, balle
Sahabi, balle shugabannin Sahabbai irin su Abubakar da Umar, musamman kuma
da yake wannan mubaya’ar an yi ta da umarnin Annabi(SAW) kuma a gabansa.
Dangana musu wannan laifi zargin su ne da aikata FASIQANCI.
Imam Muslim ya fitar da hadisi daga Abu Sa’id Alkhuduri(RA) ya ce:
Manzon Allah(SAW) ya ce, “Idan aka yi mubaya’a ga khalifofi biyu to ku kashe
na baya daga cikinsu.”1 Da yake sharhin hadisin, Imam Nawawi ya ce, “Ma’anar
hadisin: Idan aka yi mubaya’a ga wani khalifa bayan an riga an yi ga wani, to
mubaya’ar na farko ita ce ingantacciya kuma wajibi ne a cika ta. Sa’an nan
1 Sahih Muslim.
14
mubaya’ar na biyun vatacciya ce kuma haramun ne a cika ta. Haka nan haram ne
gare shi (khalifan na biyu) ya neme ta (mubaya’ar tasa).”1
Mai karatu yana iya gani a fili cewa waxannan talukai biyu, ina nufin
Hajiya musaka da jahilin Edita, sun taimaka wajen tallata wannan zargi na qarya
kuma sun dangana wa Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda, munanan
abubuwa guda biyu: barin wajibi da aikata haram. Wannan da harshen Shari’a shi
ake cewa fasiqanci. Wata qila muna iya qarawa da wani abu na uku wanda ya fi
biyun muni: savawa umarnin Annabi(SAW) da gangan, abinda yana iya zama
kafirci, wanda kuma shi ‘yan Shi’a suke nufi da wannan zargin tunda su a wajensu
waxannan Sahabban kafirai ne masu ridda. Wal iyazu billah!
Muna fata wannan zai zama gargaxi ga masu karambani a cikin ilmin
Musulunci da su sama wa kansu lafiya, su qyale masu qwarewa da fagensu.
Dalili na Biyu: Jahilci
A yayin da malamai suka gaza sai jahilci ya samu filin baje koli. Juyin juya
hali na qasar Iran ya faranta ran al’ummar Musulmi ganin yadda tutar
Musulunci ta xaukaka da yadda daular kafirci mafi girma, Amurka, ta kunyata.
Wannan ya sa Musulmi da yawa suka sha’afa da aqidar mutanen Iran a lokacin
da suka riqa duban su a matsayin wani abin koyi da ya kamata kowa ya yi koyi
da su. Da yawa daga Musulmi sun zaci cewa bajintar mutanen Iran da nasarar
da suka samu ta ‘yantar da kansu daga zaluncin Amurkawa da danniyar
Turawan yammacin duniya baki xaya, sanadinta shi ne aqidar Rafilanci da suka
qudure. Wasu jahilai kuma suka riqa zaton cewa munafunci da suke gani a
wurin wasu sarakai da shugabannin qasashen Musulmi masu bin tafarkin Sunna
tushensa shi ne aqidarsu ta Sunna wace babu bore, ba gwagwarmaya, kuma
babu qundumbala a cikinta. Wannan sai ya sa Musulmi da yawa, musamman
matasa, masu tsananin son Musulunci da qin kafirci da jin takaicin halin
1 Duba Sharhu Sahih Muslim na Imam Muhyiddin binu Sharaf Annawawi, bugun Darul Fikir, Bairut, 1401,
mujalladi na 12 shafi na 231.
15
qasqanci da koma baya da al’umma suke ciki, suka riqa ganin sun sami mafita
a cikin koyi da mutanen Iran.
Wani abu da ya qara wa mutanen Iran farin jini da haiba a idanun Musulumi
waxanda zukatansu suke cike da son Musulunci amma qwaqwalensu wayam,
shi ne wasu kalmomi masu qyalli da qyal-qyali da suka riqa amfani da su
kamar gwagwarmaya, barranta daga xagutai, gogayya da kafircin duniya, yaqi
da waxanda suka kangarewa Allah Ta’ala, fatattaqar Yahudawa da ‘yanto
masallacin Baitul Maqdis, kafa jumhuriyar Islama, yin shahada wajen xaukaka
addinin Allah, da irin waxan nan kalmomin take da kirari waxanda Rafilawa
suka yi ta burgewa da su.
Ga alama irin waxan nan kalmomi su suka burge Zakzaki da maqarrabansa
inda suka yi ta maimaita su kamar yadda akun kuturu take kyaikwayon abinda
aka gaya mata ba tare da ta san ma’anarsa ba. Da waxan nan kalmomi su ma
suka ja gayya, inda komai na Iran ya zama abin yayi, kama daga babbaqun
rawunansu zuwa manyan alkebbunsu, kai har da sunayensu da laqabansu, da
tafiyarsu da maganarsu. Hotunansu da jaridunsu da mujallunsu da uwa uba
littafansu suka cika ko ina. A cikin wannan ruxu, mugunyar aqidarsu ta yi saraf
ta shige qwaqwalen dake haihai. Da haka ne Shi’a ta yaxu a Nijeriya a
qarqashin inuwar gazawar malamai da gafalarsu.
Dalili na Uku: Talauci
Talauci shu’umin abu ne. Yana zama haxari ga lafiyar mutum da tunaninsa; ga
halayensa da xabi’unsa; ga zamantakewar iyali da zaman lafiyar al’umma; kuma
abinda ya fi kome haxari, talauci yana iya mayar da Musulmi kafirai. Wannan ya
sa Manzon Allah (SAW) a koda yaushe yake addu’a yana neman tsari daga talauci,
kamar yadda aka ruwaito yana cewa, “Ya Ubangiji, ina neman tsarinka daga
16
talauci da qaranci da qasqanci.” (Abu Dawuda da Nasa’i). Kuma yana cewa, “Ya
Ubangiji, ina neman tsarinka daga kafirci da talauci.” (Abu Dawuda). Duba ka gani
yadda ya gama tsakanin kafirci da talauci za ka fahimci cewa haxarin talauci yana
da girma.1
Talauci ya taka mugunyar rawa ta fuska biyu wajen yaxuwar tafarkin Shi’anci a
tsakanin matasa Musulmi a Nijeriya. Fuska ta xaya ita ce kasancewar matasa da
iyayensu yawanci suna fama da talauci da rashin abin yi, don haka Rafilanci wanda
yake cike da hayaniya da zanga-zanga da sauransu, sai ya zama wata mafita ce ga
matasa da za su fita daga zaman banza da suke fama da shi kuma su sami abin yi
wanda zai shagaltar da su daga matsalolin rayuwa waxanda suka dabaibaye su.
Fuska ta biyu ita ce kasancewar da’awar ‘yan Shi’a da harakarsu ta xauki salon
zuga talakawa a kan masu mulki da attajirai ta yadda koda yaushe suke maimaita
magana a kan xagutai da azzalumai wanda ya sa talakawan Musulmi, waxanda a
haqiqa an zalunce su xin, suka rufawa ‘yan Shi’a baya domin huce fushi da fatan
rama gayya a qarqashin daular Shi’awa wacce suke fatan kafawa.
Yana da wuya a yi bayani filla-filla yadda gwamnatin qasar Iran ta yi amfani da
kuxi wajen yaxa tafarkin Rafilanci a Nijeriya, amma kowa ya san da walaki wai
goro a miya. A lokacin da yake kan ganiyarsa, kafin Shi’ancinsa ya fito fili rabin
mabiyansa su valle masa, Malam Zakzaki tare da gwamnoninsa na jihohi, watau
amir-amir da ya kafa a jihohi, duka suna rayuwa maya-maya, irin rayuwar attajirai
masu hannu da shuni. Banda katafaren gidan da ya gina a garinsu Zaria, malamin
kuma yana more kayan alatu kamar zunduma-zunduman motoci, kayan sadarwa na
zamani, karikicen lantarki da sauransu. Wannan kuma shi ne halin manyan
maqarrabansa waxanda suke a hedkwatarsa a Zaria da kuma waxanda suke a
1 Domin ganin hadarin talauci da muninsa, sai a duba Mushkilatul Faqar wa Kaifa Alajahal Islam na Yusuf
Alqaradawi, bugun Maktabatu Wahaba, Alqahira, 1415/1995, shafi na 12-25.
17
jihohi. Saboda haka muke ganin cewa mutanen, kasancewar ba sa yin aikin
gwamnati ko kamfani tunda wannan a ganinsu aikin xagutu ne, ba za su rasa
samun xan hasafi ba daga wasu kafafe da vangarori wanda da shi ne suke tafiyar
da harkokin qungiyarsu kuma su samu tsabar da suke watsa wa ‘yan tsaki. Kuma
idan muka dubi talaucin da mutanen qasar nan suke fama da shi, musamman
Musulmi, tun daga farkon shekarun 1980, lallai tsaba na iya kai ‘yan tsaki ko ina,
in ya so ta baro su.
Sai dai a yanzu an samu canji a tunanin ‘yan Shi’a da ayyukansu. Tuni suka
daina qin aikin xagutu, tun da a yanzu ana samun su a cikin ayyukan gwamnati da
na kamfani, bugu da qari a kan sana’o’I dabam-daban da suke yi. Hakan ya bas u
dammar kafa tsari na tattara kuxaxe daga mabiyansu waxanda suke amfani das u
wajen jawo mutane da shigar da su tafarkinsu ta hanyar agaji da taimakon
mabukata da sauransu.
Dalili na Huxu: Tavarvarewar Zamantakewa
Wani dalili da ya taimaka wajen yaxuwar Rafilanci shi ne tavarvarewar yanayin
zamantakewa a tsakanin jama’a sakamakon sauye-sauye da suka faru a rayuwar
al’ummarmu. Waxan nan sauye-sauye sun haxa da qaura daga rayuwar karkara
zuwa rayuwar maraya, tasirin rayuwar wasu al’ummai a kanmu, raunin
dangantaka tsakanin rukunan al’umma: tsakanin iyaye da ‘ya’ya, manya da yara,
shugabanni da talakawa, malamai da mabiya, da sauransu.
A yanzu kulawar iyaye ga yaransu ta yi qaranci ta yadda uba bai sanin inda
xansa yake yin harkokinsa, ko da su wa yake hulxa. Don haka bai san abinda ya
koyo, ko ra’ayin da ya xauko ba. Ikon da manya ke da shi a kan yara a yanzu ya yi
rauni. A da ana cewa yaro na kowa ne, kuma babban mutum ko dattijo yana iya
tsawatawa yara koda bai san su ba kuma dole su saurare shi. Amma a yanzu ana
18
ganin yara suna cin karensu ba babbaka, babu mai ce musu ku ci kanku. A yau,
talakawa sun daina mutunta shugabanni waxanda suka rasa kwarjininsu saboda
qarya da sata (‘yan siyasa), jahilci da kwaxayi (sarakan gargajiya). Mawadata sun
rasa ban girman matalauta waxanda suke ganin son abin duniyarsu ya yi yawa,
kuma sun hana su haqqinsu na zakka. Malamai su ma girmansu ya faxi a lokacin
da mutane suka lura cewa suna gudu bayan abin duniya kuma sun miqa wuya ga
masu mulki da mawadata, sa’an nan sun bar matsayinsu na magadan annabawa.
Wannan sakwarkwacewa a cikin alaqar rukunan al’umma junansu da juna ta
bar matasa da gama-garin mutane a sake ba kariya, kuma wannan hali ya bai wa
baraden Dujal, kamar shugabannin Shi’a, damar su baje kolinsu kuma su ci
karensu ba babbaka. A sakamakon haka, magoya bayansu sai qara yawa suke yi
koda yake abinda suke kira zuwa gare shi halaka ne da vata.
Dalili na Biyar: Gazawar Masu Mulki
Tsare Addini, hifzud dini, yana cikin manyan manufofin Shari’ar Musulunci,
Maqasidul Shari’a, kuma tabbatar da shi aikin hukuma ne. Daga cikin hanyoyin
tsare addini akwai kiyaye shi daga dukkan abinda zai iya gurvata shi, ko ya vata
kyawunsa kamar bidi’o’i da camfe-camfe da tsurface-tsurface da duk wani abu da
ya sava wa Alqur’ani da Sunna.
Abin takaici ne cewa, tsarin siyasar da muke bi a yau tsari ne wanda babu
ruwansa da addini. Saboda haka masu mulki suke ko-in-kula da abinda ya shafi
addini sai fa idan ya zama zai amfani manufofinsu da maslahohinsu na siyasa. A
sakamakon haka, Musulunci ya zama ba shi da gata, ko wane jahili, ko wani
mugun malami Dujal sai ya shiga harkar addini ya yi abinda ya ga dama. Wani
abin mamaki kuma shi ne, ko a jihohin da suke amfani da Shari’a a yanzu, abin bai
canja ba. Koda yake an kafa ma’aikatun kula da harkokin addini a waxan nan
jihohi, amma ga alama waxan nan ma’aikatu ba su xauki yaqi da bidi’o’i a
matsayin xaya daga cikin manyan ayyukansu ba. Wannan kuwa ba abinda yake
19
nunawa sai rashin fahimtar aikinsu, ko rashin sanin makamar aikin. Idan
Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ba ta yaqi bidi’a da masu yaxa
bidi’a ba, to mene ne amfaninta?
Ya kamata gwamnatocin jihohin Musulmi, kai har ma da gwamnatin tarayya, su
fahimci haqiqanin Rafilanci da xabi’arsa. Yaxuwar Shi’anci MATSALA CE TA
TSARO, ba wai kurum matsala ce ta addini ko ta zamantakewa ba. Babu inda za’a
samu Shi’a ta yaxu a tsakanin Musulmi ba tare da sun kawo fitina da tashin hankali
da zubar da jini ba. Wannan shi ne abinda tarihi yake shaida da shi kuma shi ne
abinda muke gani a yau a dukkan qasashen da suke da ‘yan Shi’a masu yawa
kamar qasar Siriya da Pakistan da Iraqi da Lebanon, da sauransu. Saboda haka zai
zama tamkar wani kyakkyawan riga kafi ne idan Musulmin Nijeriya suka yiwa
kansu qiyamallaili, suka tsayar da yaxuwar Shi’a tun al’amarinta bai faskara ba.
Kuma abin farin ciki shi ne, har yau ba’a makara ba; amma an yi kusa!
Gudunmawar Sufaye ga Yaxuwar Shi’a
Wani abu da zai iya shiga cikin dalilan yaxuwar Shi’a a Nijeriya shi ne
taimako da malamai da mabiyan xariqun Sufaye suka bayar wajen hakan. Da ma
dai akwai alaqa mai qarfi a tsakanin Shi’a da Sufanci ta wajen kafuwarsu da
aqidojinsu. Malamai da yawa sun yi magana a kan wannan alaqa, amma za mu ba
da misali da maganar wani malami wanda babu mai zargin sa da cewa shi “mai
tsananin ra’ayin Sunna ne,” ko almajirin Ibnu Taimiyya ne, ko xan Wahhabiyya
ne. Wannan malami shi ne Ibnu Khaldun. Ga abinda yake faxi dangane da
dangantakar Rafilawa da ‘yan Xariqa:
“Sa’an nan ‘yan baya daga Sufaye suka fara magana a kan kashafi da
al’amuran gaibu, kuma aqidojin Hululu da Xayantakar Samuwa suka bayyana a
20
tsakaninsu.1 Sai suka yi tarayya da Imamiyya (Shi’a ‘yan dozin) da Rafilawa
waxanda suka qudure allantakar Imamai da Hululu. Kuma magana a kan Quxubi
da Abdalu ta bayyana a tsakaninsu, kamar suna kwaikwayon aqidar Rafilawa
dangane da Imamai da Nuqaba’u. Kuma suka aro aqidojin Shi’awa.”2
Har yau, Ibnu Khaldun yana faxi a wani wurin dabam, “Sa’an nan waxan
nan Sufaye ‘yan baya, masu maganar kashafi da al’amuran gaibu, suka zurfafa…
Kuma magabatansu sun kasance suna gauraya da Isma’iliyya Rafilawa masu
quduri da Hululu da allantakar Imamai, tafarkin da ba’a san shi ba a wajen na
farkonsu. Sai ko wanne (daga qungiyoyin biyu) ya xarsa daga tafarkin xan
uwansa.”3
To amma duk da wanan dangantaka da alaqa mai qarfi a tushe da aqidu,
qungiyoyin biyu suna da bambance-bambance masu yawa. Ga wasu daga ciki:
Da farko, ‘yan Shi’a suna kafirta Sahabban Annabi(SAW) baki xayansu in
banda guda bakwai kawai, su kuwa ‘yan xariqa ba sa kafirta ko xaya daga cikin
Sahabbai.
‘Yan Shi’a suna zagin Sahabbai, suna yi musu qazafi, suna zagin Uwayen
Muminai matan Manzon Allah(SAW) suna yi musu qazafi, su kuwa ‘yan xariqa ba
sa zagin su, ba sa yi musu qazafi, maimakon haka suna girmama su, suna qaunar
su.
‘Yan Shi’a ba su yarda da khalifancin Khulafa’ur Rashiduna ba, Abubakar
da Umar da Usmanu, sai Ali kawai, su kuwa ‘yan xariqa sun yi imani da
khalifancin guda huxun baki xaya.
1 Dangane da ma’anar Hululu da Dayantakar Samuwa, sai a duba littafinmu Sufanci da Aqidun Sufaye.
2 A duba Muqaddimatu Ibni Khaldun na Abdurrahman binu Khaldun, bugun Darul Kutubil Ilmiyya, Bairut,
1424/2003, shafi na 254.
3 Muqaddimatu Ibni Khaldun, shafi na 386.
21
‘Yan Shi’a sun yi imani da khalifanci (ko imamancin) Imamai goma sha
biyu: Ali, Hassan, Hussaini, Ali Zainul Abidin, Muhammad Baqir, Ja’afar Sadiq,
Musa Kazim, Ali Rida, Muhammad Taqiy, Ali Naqiy, Hassan Askari da na sha
biyunsu Mahadi wanda suka ce wai an haife shi amma ya vuya yana xan shekara
huxu, kuma zai komo a qarshen zamani ya kafa daular Shi’awa. Su kuwa Sufaye,
koda yake suna qaunar waxan nan Imamai a matsayinsu na jikokin Manzon
Allah(SAW), to amma ba sa xaukar su a matsayin khalifofi (tunda ba wanda aka
tava naxawa khalifa a cikinsu sai Ali kawai) kuma babu shakka ba sa xaukar su a
matsayin Imamai da irin ma’anar da ‘yan Shi’a suke nufi da wannan kalmar.1
‘Yan Shi’a suna quduri da cewa waxan nan Imaman sun fi dukkan
Annabawa da Manzanni da Mala’iku makusanta ga Ubangiji, su kuwa ‘yan xariqa
ba sa ban gaskiya da haka.
‘Yan Shi’a suna quduri da cewa Imaman sun san gaibu, sun san abinda ya
faru tun farkon halitta da abinda zai faru har bayan abada, kuma sun san abinda
yake qunshe cikin zukatan bayi, su kuwa Sufaye ba sa quduri da haka.
‘Yan Shi’a suna quduri da cewa Alqu’ani da yake hannun al’umma a yau,
wanda kuma Musulmi ke tilawarsa a safe da yammaci, ba dai-dai yake ba, an yi
qari da ragi a cikinsa, kuma wai Sahabbai ne suka yi wannan qari da ragin, su
kuwa ‘yan xariqa ba sa ban gaskiya da haka.
‘Yan Shi’a suna imani da cewa garin Karbala ta fi Makka da Madina falala,
su kuwa ‘yan xariqa ba su yarda da wannan almarar ba.
‘Yan Shi’a sun yarda da auren mutu’a kuma suna yin sa, su kuwa ‘yan
xariqa a wajensu wannan irin auren zina ce kawai.
1 Domin ganin bambanci tsakanin yadda ‘yan Shi’a da Ahalus Sunna suke duban Imaman Shi’a, sai a nemi
littafinmu Ahalul Baiti a mahangar Ahalus Sunna da ‘Yan Shi’a.
22
Amma duk da waxan nan bambance-bambance masu yawa, ‘yan xariqa,
musamman xariqar Qadiriyya, sun taimaka wajen yaxuwar Shi’a a Nijeriya. Ya
aka yi haka ta faru?
Ga alama, akwai dalilai guda biyu. Na farko: jahilcin yawancin ‘yan xariqa
dab a su san haqiqanin Shi’a bad a miyagun aqidojinsu. Na biyu: munafuncin ‘yan
Shi’a da yaudararsu, inda suka I amfani da taqiyya, suka shige wa ‘yan xariqa suna
nuna cewa sun yarda a aqidunsu da ayyukansu a lokacin da, a haqiqa, suna xaukar
su a matsayin kafirai. ‘Yan Shi’a, waxanda aqidarsu ta taqiyya ta ba su dama su yi
kome ba kome,1 sun shiga cikin ‘yan xariqa suna yin Maulidi tare da su, suna
sallah bayan su, suna halartar tarukansu na zikiri da wa’azi, da sauransu. Wannan
sai ya yaudari ‘yan xariqa, a yayin da suka xauka cewa ‘yan Shi’a ‘yan uwa ne
abokan tafiya. Amma a haqiqa abin ba haka yake ba.
Su ‘yan Shi’a suna sane da cewa alaqar su da ‘yan xariqa alaqa c eta
yaudara, amma su Sufaye bayin Allah mutanen kirki bas u sani ba. Malaman Shi’a
suna lasafta Sufaye ‘yan xariqa a sahun nasibawa maqiya Ahalul Baiti, kuma suna
kafirta su baki xaya, kamar yadda suke kafirta sauran Ahalus Sunna tun daga kan
Sahabbai, Allah ya qara musu yarda, har ya zuwa yau.
Babban shaihinsu mai suna Alhurrul Aamili, yana cewa: “Ka sani (ya kai
mai karatu) cewa wannan suna, watau Sufanci, ya kasance ana amfani da shi ga
wasu falasifawa vatattu ga barin hanya. Sa’an nan, daga baya, sai aka riqa kiran
wasu zindiqai da shi, da wasu masu sava mana, maqiyan Ahalul Baiti, irin su
Hasanul Basari da Thauri da sauransu. Sa’an nan, wasu suka zo waxanda suka bi
tafarkinsu, irin su Gazali shugaban maqiya Ahalul Baiti… Suka riqa ganin cewa
nasibawa da zindiqai a kan gaskiya suke, sai suka bar lamarin Shari’a.”
1 Domin ganin aqidar Taqiyya da yadda ta halasta wa ‘yan Shi’a su aikata abinda suke ganin haramun ne a wajen
su, sai a duba littafinmu Aqidar Taqiyya a wajen ‘Yan Shi’a.
23
Ya ci gaba da cewa, “Shaihinmu mai girma, Shaihu Baha’uddin Muhammad
Al’aamili, ya ruwaito a cikin littafin Kishkul cewa Annabi(SAW) ya ce, ‘Alqiyama
ba za ta tashi ba sai wasu mutane daga al’ummata sun bayyana, sunansu Sufaye, ba
sa daga gare ni. Kuma lallai su ne Yahudawan al’ummata, kuma sun fi kafirai vata,
kuma su ‘yan wuta ne.’”1
Za mu kula cewa a cikin wannan nassi, malamin ya kafirta manya-manyan
shaihunnan Sufaye da malamansu, ciki har da Hujjatul Islam Algazali, wanda ya
kira shi shugaban nasibawa, da Hasanul Basari wanda yawancin Sufaye suke
xaukar sa a matsayin tushen tafarkinsu. To ina kuma ga sauran shaihunnai da
waliyyai?
Haka nan, malamin Shi’awa xan hayaqi, Ni’imatullahi Aljaza’iri, ya qulla
babi musamman a cikin littafinsa, inda ya yi bayanin aqidar malaman Shi’a ta
kafirta dukkan ‘yan xariqa da shaihunnansu da waliyyansu saboda sun yarda da
khalifancin Abubakar da Umar da Usmanu, kuma ya sifanta su da mafi munin
siffofi.2
Wannan yana tabbatar da abinda muka faxi cewa, kusanta ‘yan xariqa da
‘yan Shi’a suke yi ba wani abu ba ne face yaudara, don su samu magoya baya daga
almajiransu. Abin takaici shi ne har yau malaman xaiqu da mabiyansu bas u gane
ba. Sai yaushe za su farka?
Yanayin Yaxuwar Shi’a a Yau
1 A duba Risalatul Ithnai Ashariyya fil Raddi alal Sufiyya na Alhurrul Aamili, shafi na 13-16.
2 A duba Al’anwarul Nu’umaniyya, babin Zulumatun fi Ahawalis Sufiyyati wal Nawasib, bugun Madba’atu
Baab, Tibriz-Iran, ba tarihi, mujalladi na 2 shafi na 305.
24
Tun zuwan Shi’a Nijeriya, qungiyar ta taka matakai uku na yaxuwa kamar
haka:
Na xaya, matakin yaxuwa a lokacin taqiya da munafinci da yaudara. Wannan
shi ne lokacin da shugabannin Shi’a suka yi ta kira da sunan gwagwarmaya da
sabunta addini da kafa hukuncin Musulunci. A wannan yayi, qungiyar ta yaxu
yaxuwa mai yawa a lokaci qanqani sakamakon qishirwar matasa ta sauyi da kuma
rashin sanin haqiqanin abinda da’awar ta qunsa a wannan mataki.
Mataki na biyu, shi ne lokacin da Malam Zakzaki ya fito fili ya bayyana cewa
lallai Shi’a yake yi bayan taqiya ta tsawon shekara goma sha biyar ko sama da
haka. A wannan lokaci qungiyar ta rabe biyu kusan a tsakiya, inda a shekarar 1995
aka samu vullar qungiyar Jama’atu Tajdidil Islam wacce ta yi shelar barrantarta
daga tafarkin Rafilanci kuma ta yi wa shugabancin Zakzaki tutsu. Qoqarin matasa
dake vangaren J.T.I. da qungiyar Izala da kuma malamai da almajirai masu bin
tafarkin Salafiya, qoqarin waxan nan gaba xaya wajen tona asirin Shi’a ya kawo
tsaiko ga yaxuwarta, musamman a birane inda a da a nan ne ta fi yawan mabiya.
Ga alama a yanzu, Shi’a tana shiga mataki na uku na yaxuwa, inda masu aikin
yaxa ta suka mayar da hankali zuwa qauyuka da yankunan karkara. A cikin ‘yan
shekarun nan, biyu zuwa biyar, Rafilanci yana yaxuwa kamar wutar daji a qauyuka
saboda qarancin ilmi da wayewa ta addini da kuma cewa yawancin masu wa’azi
suna tattara qarfinsu a birane, sai kaxan ke fita dawa. Wannan ci gaba, ko kuma ci
baya za mu ce, da aka samu yana da haxarin gaske. Dalili shi ne, dama Shi’anci
jahilci ne, kamar yadda mai karatu ya riga ya gani, to idan aka haxa shi da jahilcin
dake akwai a karkara, to an samu itace jiqe jagab da kananzir, babu abinda ya rage
sai qyastun wuta! Idan haka ta faru, Allah ya tsare, za mu wayi gari a wani yanayi
wanda varnar Maitatsine da ta’addancin Kiristoci za su zama tamkar wasan yara.
Allah ya kiyashe mu fargar jaji.
25
Rufewa
A cikin wannan taqaitaccen littafi mun ga yadda Shi’a ta shigo Nijeriya
kuma mun ga dalilai da suka taimaka wajen yaxuwar ta. Kuma sharrin wanan
mugunyar qungiya ga addini da rayuwar duniya a yau ba sai an faxi ba; tun da abu
ne wanda kowa yake iya gani da idanunsa.
Don haka ya zama wajibi ga dukkan Musulmi, xaixeku da qungiyoyi da
hukumomi, su taimaka wajen yaqar wannan qungiya, domin ceto waxanda suka
riga suka faxa cikin ta da tsayar da yaxuwar ta. Bai kamata wani vangare na
al’umma ya yi kamar babu ruwansa ba a wannan harka; saboda yaxuwar Shi’a
matsala ce wacce ta shafi kowa da kowa.
Kuma dole ne waxanda suka taimaka a baya wajen yaxuwar wannan
qungiya, su yi KAFFARA a yanzu ta hanyar taimakawa wajen yaqar ta. Saboda
haka, malaman xariqu da almajiransu, da ‘yan Boko waxanda a da suka yi Buraza,
da kuma ‘yan qungiyar Jama’atu Tajdidil Islam, waxanda suka tuba daga yin Shi’a
amma suka koma gefe suka zama ‘yan kallo, suna da nauyi na musamman wajen
yaqar wanan mugunyar qungiya da ganin bayan ta.
Kuma koda yake havakar qungiyar da yawan hayaniya da barazanar ta suna
ba wasu mutane tsoro, amma mu da muka san xabi’arta muna iya tabbatar wa da
mutane cewa yaqar ta da kawar da ita daga doron qasar Nijeriya abu ne mai sauqi,
in Allah ya yarda. Shuru na mutane shi ke sa ta yaxuwa ba wani abu ba. Don haka
lokaci ya yi da kowa zai ba da tasa gudunmawa.
Allah ya yi mana taimako. Shi ne abin dogaron mu.
26