1
Jerin Littafan Shi’a Na 1
Aqidar
‘Yan Shi’a
dangane da
Alqur’ani
Umar Labxo
2
بسم الله الرحمن الرحيم
Gabatarwar
Jerin Littafan Shi’a
Aikina na yaqar bidi’ar Shi’a ya fara a garin Sakkwato, a wajejen
shekarar 1993, bayan na kwashe kimanin shekaru biyar ina koyar da fannin
Alfiraqul Islamiyya (Qungiyoyin Bidi’a a Musulunci) a Jami’ar Usmanu
Xanfodiyo.
Wannan aiki ya lafa bayan da na shiga gwagwarmayar kafa Shari’a a
jihohin Sakkwato da Kebbi a qarshen shekarar 1999. Daga baya kuma aikin
ya tsaya cik a lokacin da na tafi qasar Uganda domin koyarwa a Jami’ar
Musulunci ta Uganda (IUIU) dake garin Mbale a Uganda.
Bayan komowa Nijeriya a farkon shekarar 2003, na sabunta nashaxina
na yaqar Shi’a a Sakkwato, inda na fitar da littafin Vacin Tafarkin ‘Yan
Shi’a Da Aqidojinsu a qarshen shekarar 2004.
Ayyukana na rubuce-rubuce da lakcoci sun ci gaba a tsawon zamana
na shekaru huxu a Katsina, yayin da na fitar da littafin Larabci mai suna
Bayanu Fasadi Aqa’idis Shi’a. Da na koma Kaduna a qarshen shekarar
2009, na ci gaba da nashaxina, inda na buga littafai biyu: Dangantaka da
Auratayya Tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai da Wa Ya Kahse Hussaini?
A duk tsawon wannan lokaci, na kasance ina mai amanna da
muhimmancin karatu da rubutu a cikin ko wace al’umma. Wannan ya sa
koda yake ina wa’azi da lakcoci, amma ban fiye damuwa da yaxa su ta
hanyar kasakasai ba. Wani lokaci ma na kan hana a xauki karatuna a rikoda,
saboda ba na son mutane su dogara da sauraro maimakon karatu. A koda
3
yaushe, na fi qarfafa guiwar mutane da su karanta littafai, maimakon su
saurari kasset da radiyo.
A lokacin da na komo gida Kano, kuma na mai da hankali zuwa
qauyuka da yankunan karkara (saboda ganin makircin Shi’a na shiga
qauyuka), yaqinina da muhimmancin karatu da rubutu ya qaru. To sai dai na
fuskanci wata matsala guda: Yawancin mazauna qauyuka da yankunan
karkara suna tsoron littafi idan yana da girma, wani lokaci kuma ya kan yi
musu tsada. Qoqarin warware wannan matsala shi ya kawo tunanin rubuta
Jerin Littafan Shi’a.
A haqiqa ba mazauna qauyuka ne kawai suke tsoron karatu, ko suke
qin sa ba. Yawancin al’ummarmu suna da qiwar karatu da qyamarsa; sun fi
son su saurari radiyo ko rikoda. Sai dai abu ne da yake tabbas cewa, ba wata
al’umma da za ta ci gaba matuqar ba ta karatu.
Yawancin malaman zamani sun biye wa Malam Bahaushe, suna ganin
tunda mutanenmu ba sa son karatu, to sai a bar su da abinda suke so: kasset
da rikoda. Amma ni ban yarda da wannan ra’ayi ba. Ina ganin ba dai-dai ba
ne a biye wa mara lafiya da ya qi karvar magani don yana zaton maganin
yana da xaci. Maimakon haka, kamata ya yi a riqa ba shi kaxan-kaxan, yana
kurva sannu a hankali, har ya saba, kuma ya warke! Warakar al’umma na
cikin karatu.
Wannan shi ne abinda na yi da qananan littafai na wannan jeri. Kuma
abin ya yi nasar har na fara rubuta na Larabci da na Turanci.
Waxan nan jerin littafai, daga na xaya zuwa na tara, sun qunshi
duk abinda mai karatu yake bukata ya sani dangane da ‘yan Shi’a da
aqidojinsu da hukunce-hukuncensu da ibadojinsu da halayensu da xabi’unsu
da tarbiyyarsu da dangantakarsu da sauran Musulmi, musamman Ahalus
Sunna. Kuma, kamar yadda mai karatu zai gani qarara, a cikin waxan nan
4
al’amura duka, ‘yan Shi’a suna yin nesa da Musulunci da duk abinda ya
qunsa na aqidoji da hukunce-hukunce da ibadoji da halaye da ladubba da
xabi’u da tarbiyya. A taqaice, ‘yan Shi’a suna yin nesa da koyarwar
Alqur’ani da Sunnar Annabi da tafarkin Sahabbai da Ahalul Baiti baki xaya.
Wani abu muhimmi da wannan jerin littafai suka yi fice da shi, shi ne
dogaro kacokan wajen bayanin aqidojin ‘yan Shi’a da hukunce-hukuncensu
da ibadojinsu da halayensu da dangantakrsu da sauran Musulmi a kan
littafan malamansu da shaihunnansu waxanda suka yarda da su, tare da
lazimtar amana wajen naqalto maganganunsu daga littafan nasu. Saboda
haka, abinda mutum zai karanta a cikin waxan nan littafai dangane da ‘yan
Shi’a kai-tsaye ne daga bakin mai ita. Duk abinda aka faxi dangane da su
daga littafansu aka xauko, ba daxi, ba ragi. Wannan kuma domin a yi adalci
ne gare su, kuma a lazimta musu hujja.
Ina roqon Allah Maxaukaki da ya shiryi mutane da waxan nan ‘yan
littafai, ya rubuta mun ladansu, ya yi sakamako da alheri ga duk wanda ya
taimaka wajen buga su, ko yaxa su, ko sada su ga makaranta ta kowace
hanya.
Kano Umar Labxo
Afrilu, 2016
5
Aqidar ‘Yan Shi’a Dangane da Alqur’ani
‘Yan Shi’a suna qudure cewa Alqur’ani mai girma wanda yake a
hannun Musulmi a yau ba cikakke ba ne; domin, a ganinsu, Sahabbai da
suka tattara Alqur’ani a zamanin Abubakar da Usman, Allah ya qara yarda a
gare su, sun sauya abubuwa da dama a cikinsa ta hanyar yin qare-qare da
rage-rage a cikin ayoyinsa. Suka ce wai wannan Alqur’ani da muke karanta
wa a yau babu abinda yake cikinsa daga abinda aka saukar ga Annabi
(SAW) sai xan kaxan.
‘Yan Shi’a suna zargin Sahabbai da sauya Littafin Allah, da canja
ayoyinsa. Suka ce wai Sahabban sun yi haka ne ta hanyar xebe ayoyi masu
yawa da aka saukar waxanda suke tona asirinsu da kuma ayoyi da suke nuna
falalar Ali binu Abi Xalib(RA) da zuri’arsa. Abinda suke nufi da tona
asirinsu, wai bayyana kafirci da munafuncin Sahabbai. Wal iyazu billahi!!
Saboda haka a wurin ‘yan Shi’a, ayoyi da yawa dake cikin Alqur’ani
ba maganar Allah ba ce, wannan ya sa suke zavar abinda ya dace da son
zukatansu a cikin Alqur’ani, saura kuwa su yi burus da shi.
Wani babban malaminsu mai suna Hashim binu Sulaiman Albaharani
yana faxi a cikin wani littafi nasa da ya rubuta a kan Tafsiri, “Ka sani cewa a
haqiqanin gaskiya wacce babu kokwanto a cikinta, gwargwadon ruwayoyi
mutawatirai, wannan Alqur’ani da yake hannunmu sauye-sauye sun faru a
cikinsa bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) kuma waxanda suka tattara shi
bayan Annabi sun xebe kalmomi da ayoyi masu yawa daga cikinsa.”1
A cikin littafin Alkafi , littafin da ya fi ko wanne inganci a wajen ‘yan
Shi’a, an yi bayanin gwargwadon abinda aka xebe daga cikin Alqur’ani.
Marubucin littafin, watau Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, ya ce, “An
1 Duba Alburhan fi Tafsiril Qur’an na Hashim binu Sulaiman Albaharani, bugun Almadaba’atul Ilmiyya,
Qum-Iran, 1393, shafi na 36.
6
ruwaito daga Abu Abdullahi (watau Imamin Shi’a na shida) cewa
Alqur’anin da Jibrilu ya zo da shi ga Muhammad (SAW) aya dubu goma sha
bakwai (17,000) ne.”1 Wannan yana nufin ke nan cewa Kur’anin da yake
hannunmu xan ragowa ne kawai; domin kuwa a bisa ga wannan ruwaya
waxanda suka tattara littafin a bayan rasuwar Annabi (SAW) sun xebe
kimanin sulusi biyu na littafin. Za mu tabbatar da haka idan muka lura da
cewa Alqur’anin da yake hannunmu, wanda Musulmi suka sani a yau,
ayoyinsa dubu shida da xari biyu da talatin da shida ne (6,236) kawai, kamar
yadda malaman Sunna suka tabbatar.2
Akwai ruwayoyi masu yawa a cikin littafan malaman Shi’a da suke
izna da su, waxanda suka tabbatar da wannan mugunyar aqida tasu. Wani
malaminsu mai suna Ni’imatullahi Aljaza’iri da ya qididdige ruwayoyin ya
tabbatar da cewa sun fi dubu biyu.3 Saboda haka, ita aqida ce wacce dukkan
‘yan Shi’a, ciki har da na Nijeriya, suka yarda da ita. Kuma idan ka ji suna
musun ta, to taqiyya ce kawai suke yi, watau munafunci da yaudara!!
Wani qasurgumin malamin Shi’a, mai suna Hussain binu Muhammad
Annuri Alxabarsi, ya rubuta shirgegen littafi musamman don ya tabbatar da
aqidar ‘yan Shi’a cewa Alqur’anin nan da yake a hannunmu a yau ba
cikakke ba ne, kuma akwai sauye-sauye, da qare-qare, da rage-rage, a
cikinsa. Littafin wanda ya sa wa suna Faslul Khixab fi Ithbati Tahrifi Kitabi
Rabbil Arbab, (watau Yankakkiyar Magana A Kan Tabbatar Da Sauya
Littafin Mamallakin Mamallaka), ya qunshi dubunnan ruwayoyi daga
Imaman Shi’a da malamansu waxanda suke tabbatar da cewa wai waxan
nan sauye-sauye, da qare-qare, da rage-rage Sahabbai, waxanda suka haxa
1 A duba Alkafi na Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, Darul Kutubil Islamiyya, Teheran-Iran, ba tarihi,
mujalladi na 2, shafi na 634.
2 Duba Tafsiru Ibnu Kathir na Isma’il binu Kathir, bugun Maktabatus Safa, Alqahira, 1423/2002,
mujalladi na 1, shafi na 7.
3 Duba Faslul Khidab na Hussain binu Muhammad Taqiyyud Din Aldabarsi, ba tarihi, shafi na 248.
7
da Abubakar da Umar da Usman, Allah ya yarda da su baki xaya, su ne suka
zartar da su. A cikin littafin har ila yau, an tabbatar da cewa malaman Shi’a
kaf, magabatansu da na bayansu, sun haxu a kan wannan aqida.1
‘Yan Shi’a suna da nasu Alqur’ani dabam, wanda suke kira Mushafu
Faxima, watau Kundin Faxima. Dangane da wannan littafi, malaman Shi’a
suna dangana ruwaya ga Imaminsu na shida, Imam Ja’afar Sadiq, cewa wai
ya ce, “Faxima ta bar wani kundi wanda ba Qur’ani ba ne, amma kuma
kalmar Allah ce da ya yi wahayin ta zuwa gare ta. Shi kundin shiftar Annabi
ne kuma rubutun hannun Ali.”2 A wata ruwayar kuma, ya ce: “Shi kundi ne
da ya ninka Qur’ani uku kuma amma, na rantse da Allah, babu kalma xaya a
cikinsa ta Qur’aninku.”3
A ganinsu, Mushafu Faxima shi ne Qur’ani na gaskiya wanda
Imamansu suka gado shi daga Nana Faxima xiyar Manzon Allah (SAW) da
mijinta Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara musu yarda. Muhammad binu
Hassan Alsaffar, wanda ake lasafta shi daga cikin manyan malaman Shi’a
magabata (ya rasu a shekara ta 290 B.H.), ya ruwaito a cikin littafinsa,
Basairud Darajati , daga Imam Abu Ja’afar wai ya ce, “Babu wani da zai iya
da’awar cewa ya tattare Alqur’ani dukkaninsa, zahirinsa da baxininsa, sai
masu wasici,” yana nufin Imamai. Har yau, a cikin littafin ya ruwaito daga
gare shi yana cewa, “Babu wani daga mutane wanda zai ce ya tattare
Alqur’ani dukkaninsa, kamar yadda Allah ya saukar da shi, sai maqaryaci.
Ba wanda ya tattare shi, ya haddace shi kamar yadda aka saukar da shi, sai
Ali binu Abi Xalib da Imamai a bayansa.”4
1 Duba Faslul Khidab na Aldabarsi, shafi na 34.
2 A duba Basa’irud Darajat na Alsaffar, shafi na 176.
3 Duba Alkafi na Kulaini, mujalladi na 1, shafi na 171,
4 Duba Basa’irud Darajatil Kubra fi Fada’ili Aali Mahammad na Muhammad binul Hassan binu
Farrukh Alsaffar, bugun Manshuratul A’alami, Teheran-Iran, 1362, shafi na 213.
8
Qur’anin ‘yan Shi’a ya sha bamban da Alqur’anin Musulmi ta fuskoki
masu yawa. Mun riga mun gabatar da bayanin bambancinsu ta wajen
jimillar ayoyinsu, inda Qur’anin ‘yan Shi’a yake da adadin ayoyi dubu goma
sha bakwai (17,000) dai-dai wa daida, a yayin da namu yake da ayoyi dubu
shida da xari biyu da talatin da shida (6,236) kacal. Ta fuskar tsawon surori
ma, littafan guda biyu sun sha bamban. Ga misali, ya zo a cikin Kitab
Sulaim binu Qais, mashahurin littafin nan na Shi’a wanda saboda ingancinsa
a wajensu suke masa laqabi da A.B.C. Din Shi’a, cewa wai Suratul Ahazab
wacce take da ayoyi 73 a Qur’aninmu, su a nasu Qur’anin adadin ayoyin
Baqara ne da ita, watau 286. Suratun Nur kuwa, wacce take da ayoyi 64, su
a wajensu ayoyi 160 ke gareta. Suratul Hujurati kuma, wacce a cikin
Qur’anin da muka sani ayoyinta 18 ne kacal, su a nasu Qur’anin ayoyinta 90
ne dai-dai wa daida.1
Ta fuskar adadin surori ma, akwai xan bambanci saboda akwai wasu
surori waxanda ‘yan Shi’a suke qudure cewa an xebe su daga cikin
Alqur’ani. Misali shi ne wata sura da suke kira Suratul Wilaya wacce suka
ce wai a cikinta Allah ya yi umarni da a naxa Ali binu Abi Xalib a matsayin
Khalifa bayan rasuwar Annabi (SAW). Wannan sura ba mu san ta ba, babu
ita a cikin Alqur’aninmu, amma su ‘yan Shi’a suna qudure cewa wai
Sahabbai ne suka xebe ta don cin amana, a faxinsu, domin su hana Ali binu
Abi Xalib haqqinsa na gadar Annabi, suka naxa Abubakar a makwafinsa.
Wannan ita ce aqidarsu. Wal iyazu billah!!
Dangane da kalmomi da lafuzza da ma’anoni, babu wata sura a cikin
Alqur’ani kamar yadda muka san shi face ‘yan Shi’a sun zo da savanin
kalmomi ko ayoyi a cikinta. Za mu ba da ‘yan misalai kaxan. A qarshen
1 Duba Kitab Sulaim binu Qais na Sulaim binu Qais Alhilali Alkufi, bugun Mu’assasatul A’alami, Bairut,
ba tarihi, shafi na 122.
9
Suratul Fatiha suna karanta: Ihdinas siraxal mustaqim. Siraxa man an’amta
alaihim, gairil magdubi alaihim wa gairid dalin. A farkon Suratul Asri, suna
karanta: Wal asr innal insana la fi khusr. Wa innahu fihi ila akhirid dahr.
Illal lazina amanu wa amilus salihati, wa’atamaru bit taqwa, wa’atamaru bis
sabr. Suratul Fili kuma, watau Alam Tara Kaifa, suna fara ta kamar haka:
Alam ya’atika kaifa fa’ala rabbuka bi ashabil fili.
Waxan nan ‘yan misalai ne kawai muka kawo domin mai karatu ya
ganewa idanunsa. Wanda yake son ya ga waxannan sauye-sauye filla-filla,
to sai ya koma ga littafin Alshi’atu wal Qur’an na Ihsan Ilahi Zahir, Allah ya
yi masa rahama, domin shi ya tsamo waxan nan canje-canje waxanda suka
shafi surorin Alqur’ani guda 114 baki xaya daga littafan ‘yan Shi’a kuma ya
jera su, ya rattaba su, tare da ruwayoyinsu.
Wataqila mai karatu ya yi tambaya: Don me ‘yan Shi’a ba sa buga
wannan tafkeken “Qur’ani” nasu, wanda ya ninka na Musulmi har sau uku,
su sayar a kasuwa? Amsa ita ce, abinda yake hana su bayyana wannan littafi
nasu shi ne taqiya, watau munafunci da yaudara!! A haqiqa ‘yan Shi’a ba
Qur’aninsu kaxai suke voyewa ba; aqidarsu ta taqiya tana umarnin su da su
voye manyan littafan malamansu, waxanda suka qunshi aqidojinsu da
manufofinsu, sai ga manyan mabiyansu waxanda suka riga suka yi zurfi a
cikin tafarkinsu. Kaxan daga cikin littafansu suke sayarwa a kasuwa,
sauran sai dai a same su a manyan cibiyoyinsu da makarantunsu.
Qur’aninsu kuwa, idan akwai shi cikakke, to babu shakka ba mai ganin sa
sai manyan shaihinnansu, sai kuma almajirai amintattu.
Wannan ya sa ‘yan Shi’a suke qalubalantar mutane da cewa, idan
gaskiya ne suna da nasu Qur’ani dabam, kamar yadda ake dangana musu (ko
da yake mai karatu yana iya ganin cewa ruwayoyinsu ne suka tabbatar da
10
samuwarsa) to don me ba’a fito musu da shi su gan shi? Su kan yi tambaya:
Ina Qur’anin nasu yake?
To wannan tambaya tasu malamansu sun amsa ta da kansu. Shaihinsu,
Hussain Alkhurasani yana cewa, “ Mu ‘yan Shi’a muna qudure cewa akwai
wani Alqur’ani da Imam Ali ya rubuta da hannunsa mai albarka, bayan da
ya qare yi wa Annabi sutura kuma ya zartar da wasiyyarsa. Littafin ya ci
gaba da zama a hannun Imamai a matsayin amana daga Allah har ya iso ga
Imam Mahadi wanda ya adana shi kuma zai fito da shi a yayin da zai
bayyana.”1
Wannan ruwaya tana tabbatar da cewa Qur’anin ‘yan Shi’a ya kasance
akwai shi, kuma ya ci gaba da zama a hannun Imamai har na tsawon
kimanin shekaru 250 daga zamanin Sayyidina Ali(RA) zuwa zamanin
Mahadinsu (watau Imaminsu na 12) wanda aka haife shi a shekara ta 255
bayan Hijira. Wannan Imamin nasu shi ne ya tafi da littafin a lokacin babbar
fakuwarsa, kuma zai komo da shi a lokacin da zai bayyana a qarshen duniya.
‘Yan Shi’a suna qudure cewa Imaminsu na 12, wanda suke kira
Mahadi ya faku fakuwa biyu, babba da qarama. A lokacin qaramar fakuwa,
wacce ta yi tsawon shekara 65, ya riqa saduwa da manyan almajiransa
waxanda ya riqa aiko su da saqwanni zuwa ga mabiyansa. Kuma a shekara
ta 259 bayan Hijira, ya shiga fakuwa babba, wacce yake kai har zuwa yau,
kuma wacce a cikinta ba ya saduwa da kowa. Wannan babbar fakuwa za ta
qare a qarshen duniya, sa’ad da Mahadin zai bayyana don ya qaddamar da
wasu ayyuka masu ban tsoro da ban mamaki.2 Mai son ganin waxan nan
ayyuka, sai ya duba littafinmu mai taken Mugun Nufin ‘Yan Shi’a ga
Al’umma.
1 Duba Al’islam ala Dau’it Tashayyu’i na Hussain Alkhurasani, ba tarihi, shafi na 204.
2 Domin bayanin wannan tatsuniya, duba A Critical Revision of Shi’ah na Imam Musa Musawi, bugun the
Supreme Islamic Council, Columbia-Amurka, 1412/1992, shafi na 77-78.
11
Har yau, wani malamin nasu ya ba da bayani mai kama da wannan.
Ya ce, “Bayan rasuwar Annabi, Sarkin Musulmi (yana nufin Ali) ya xauko
Alqur’ani a cikin mayafinsa, ya kawo wa Abubakar da Umar suna zaune a
Masallaci su da wasu mutane. Ya ba su shi, amma sai suka ce: Ba ma
bukatar Qur’aninka; muna da namu Qur’anin, ya ishe mu! Sai ya ce: Shi ke
nan, ba za ku qara ganin sa ba daga yau, sai Mahadi ya bayyana!”1
Waxan nan bayanai daga malaman Shi’a, idan sun gaskata, suna
tabbatar da cewa Qur’anin ‘yan Shi’a ya kasance akwai shi a hannun
Imamansu, kuma almajiran Imamai sun karanta shi har lokacin da Imami na
12 ya shiga das hi kogo inda ya faku fakuwarsa ta qarshe. Saboda haka sai
su jira shi daga nan har sanda jaki ya tsuri qaho!
Akwai wani xan Shi’a wanda ya tava yin wata burga. Ya xauko
Qur’ani cikakke na Musulmi, wanda aka buga a qasar Iran, ga tambarin
Jumhuriyar Islama rangaxau a bangon littafin. Sa’an nan ya ce, “Kun ce
‘yan Shi’a ba su yarda da Qur’ani ba, ya aka yi suka buga wannan?” Sai aka
ce masa, ai buga Qur’ani ba shi ne yarda da shi ba. Idan ‘yan Shi’a sun yarda
da Alqur’ani don me suke kafirta waxanda ya yi wa shaida da imani, watau
Sahabban Annabi(SAW)? Sai gogan naka ya yi turus! Allah ya tsarshe mu
vata.
Bayan mun gabatar da bayani a kan wannan aqida kamar yadda take a
cikin littafan ‘yan Shi’a masu inganci a wajensu, muna ganin babu wani
Musulmi da yake buqatar wani qarin bayani dangane da abinda aqidar ta
tattare na kafirci da jahilci da vata. Amma saboda yankan hanzari ga masu
kiran kansu ‘yan Shi’a, bari mu yi bayanin kafircin wannan aqida a taqaice.
1 Duba Nur Al’anwar fi Sharhis Sahifatis Sajjadiyya na Ni’imatullahi Aljaza’iri, bugun Darul Mahajjatil
Baida, Bairut, 1420, shafi na 175.
12
Da farko dai aqidar ta qaryata Alqur’ani mai girma saboda a cikinsa
Allah mai girma da xaukaka ya tabbatar da cewa ya tsare Littafinsa ta yadda
qari ko ragi ba za su shige shi ba. Ubangiji Maxaukaki ya ce, “Lalle, mu ne
muka saukar da Ambato (Alqur’ani), kuma lalle mu, masu kiyayewa ne gare
shi.” (Suratul Hijr: 9). A wata ayar kuma, ya tabbatar da cewa varna ba ta
shiga wannan littafi ko ta halin qaqa: “Waxan nan da suka kafirta game da
Alqur’ani a lokacin da ya je musu, kuma lalle ne, haqiqa, littafi ne
mabuwayi. Varna ba za ta je masa ba daga gaba gare shi, kuma ba za ta zo
ba daga baya gare shi. Saukarwa ce daga Mai Hikima, Godadde.” (Suratu
Fussilat: 41 – 42).
Na biyu, wannan aqida har ila yau, tana qaryata Alqur’ani ta wata
fuskar dabam; domin tana kafirta ko fasiqantar da waxanda Allah ya bayar
da labari cewa ya yarda da su kuma ya yi musu gafara: su ne Sahabban
Annabi(SAW), Allah ya qara musu yarda baki xaya. Aqidar ta kafirta
Sahabbai ta hanyar dangana musu sauya Alqur’ani, da voye abinda Allah ya
saukar, da yin qari da ragi a cikinsa. Allah yana faxi dangane da Sahabban
Annabinsa: “Kuma magabata na farko daga Muhajirina da Ansar da
waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda daga gare su, su kuma
sun yarda daga gare shi, kuma ya yi musu tattalin gidajen Aljanna: qoramu
suna gudana a qarqashinsu, suna madauwama a cikinsu har abada. Wancan
ne babban rabo mai girma.” (Suratut Tauba: 100).
Xan uwa mai karatu ka dubi abinda Allah ya ce dangane da Sahabban
Annabinsa, har ma da waxanda suka bi su da kyautatawa, sa’an nan ka dubi
abinda ‘yan Shi’a suka jingina musu na sauya maganar Allah da cin amanar
Manzonsa, za ka san cewa lalle ‘yan Shi’a sun yi nisa daga barin shiriya.
Muna roqon Allah ya arzuta su da tuba kyakkyawa, da komawa ga
13
tafarki madaidaici: tafarkin Sunnar Annabi(SAW). Mu kuma, ya nesantamu
da irin wannan vata mabayyani.