Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 10


Wajabcin


Yaqar Bidi’a


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


Gabatarwa


Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga


shugabanmu Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi


Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.


Bayan haka, wasu ‘yan uwa Musulmi suna ganin cewa kira zuwa ga tafarkin


Sunna, da yaqar bidi’a, wata tsatsuba ce da qaqale da tsaurin ra’ayi. Wasu ma suna


ganin irin wannan kira kalan faxa ne da neman tashin hankali. Irin waxan nan


mutane suna ganin cewa, ya isa su zama su Musulunci ne kawai; ba ruwansu da


wata Sunna! Suna zaton cewa ita ma Sunna wata qungiya ce kamar sauran


qungiyoyi, saboda haka kira zuwa ga Sunna, a ganinsu, kira ne zuwa ga


qungiyanci, haka nan bin Sunna bin wata qungiya ne!


Babu shakka wannan fahimta da wannan ra’ayi suna nuna rashin sani a fili.


Abu na farko da masu irin wannan fahimata suka jahilta shi ne cewa, Sunna ita ce


Musulunci, domin ma’anar Sunna shi ne tafarkin Annabi (SAW). Bidi’a kuma,


kamar yadda abin yake hatta a karin maganar Hausawa, ita ce kishiyar Sunna.


Saboda haka ita kishiyar Musulunci ce.


A haqiqa, duk wanda ya san ma’anar Sunna, ya san abinda Allah


Maxaukaki ya faxi dangane da Sunna, ya san abinda Manzon Allah (SAW) ya faxi


dangane da Sunna, ba zai tafi a kan waccan fahimta da wancan ra’ayi da aka


ambata a sama ba.


Haka nan, duk wanda ya san ma’anar bidi’a, ya san abinda Allah Maxaukaki


ya faxi dandgane da bidi’a, ya san abinda Manzon Allah (SAW) ya faxi dangane


da bidi’a, ba zai yi bidi’a ba, ba zai yi wasa da yaqar bidi’a ba.


Don haka, a taqaice, rashin sani shi ne babban abinda yake hana mutane bin


Sunna, kuma shi ne babban abinda yake sa mutane yin bidi’a.


3


Idan haka ne, ashe ya zama wajibi a kan malamai, da almajirai irina, su tashi


tsaye wajen ilmantar da mutane da sanar da su ma’anar Sunna da matsayinta da


kuma ma’anar bidi’a da sharrinta.


Wata fahimta kuma da wani ra’ayi da rashin sani ya haifar shi ne zaton


cewa, Sunna baquwa ce a qasar nan, bidi’a ita ce mai asali, ‘yar gida.


Mutane da yawa da an ce “Sunna” abinda yake fara zuwa qwaqwalensu shi


ne “Izala”, ko kuma “Salafiyya.” Irin waxan nan mutane yawanci ba su san kome


ba dangane da Shaihu Usman Xanfodiyo da tajdidinsa da jihadinsa. Ba su san cewa


tutocin da suke kaxawa a Kanwuri (fadar Sarkin Musulmi a Sakkwato) da Qofar


Kudu (fadar Sarkin Kano) da Qofar Fada (fadar Sarkin Katsina) da sauran fadojin


sarakunan Musulunci na qasar Hausa, duka an qulla su ne a kan Sunna ba. Ba su


san cewa, wanan al’ummar, ina nufin al’ummar Musulmin Nijeriya, wacce ta kafu


a sakamakon jihadin Xanfodiyo da tajdidinsa, an gina ta ne a kan durakun Sunna


ba.


Wanda duk ya san matsayin Sunna a tajdidin Xanfodiyo da jihadinsa, ya san


yadda raya Sunna da kashe bidi’a (Ihiya’us Sunna wa Ikhmadul Bidi’a) ya zama


qashin bayan gwagwarmayar Shaihu da jihadinsa da tajdidinsa da daular da ya kafa


da al’ummar da ya haifa,1 ba zai xauki Sunna a matsayin baquwa ba, ko kuma ya


xauka cewa Izala ce ta kawo Sunna.


Ke nan matsalar duka ta rashin sani ce da jahilci. Saboda haka maganinta shi


ne yaxa ilmi da yaqar jahilci. Wannan kuma shi ne manufar wannan xan qaramin


littafi: yaxa ilmi dangane da ma’anar Sunna da muhimmancinta, da kuma yaqar


jahilci da sharrin bidi’a. Bayan karatun wannan littafi, ana fata, dalili zai bayyana a


fili don me ya zama wajibi mu yaqi bidi’a, mu yaxa Sunna.


Muna roqon Allah Maxaukaki ya arzuta mu da tsarkin niyya da kyakkyawar


fahimta da aiki mai nagarta.


1 Domin ganin wannan, sai a duba littafinmu Rayuwar Shehu Danfodiyo da Ayyukansa.


4


Ma’anar Sunna da Bidi’a


Yaqar bidi’a hidima ce ga Sunna; saboda biyun kishiyoyin juna ne. Sunna ba


ta haxuwa da bidi’a kamar yadda wuta ba ta haxuwa da shiva. Haka nan fahimtar


xaya na taimakawa a gane xayan; saboda ana gane abubuwa da fahimtar


kishiyoyinsu. Wannan ya sa yake da muhimmanci mu fara da bayanin ma’anar ko


wacce daga cikinsu.


Ma’anar Sunna


Sunna ita ce duk abinda ya fito daga Annabi (SAW) na magana ko aiki ko


tabbatarwa ko sifa, da abinda yake nasa na halitta ko halayya, ko labarin rayuwa.


Watau Sunna ita ce maganar Annabi (SAW) da aikinsa, da abinda aka faxi ko aka


aikata a gabansa ya tabbatar (bai musa ko ya hana ba), da halittarsa kamar launin


fatarsa da kamannin fuskarsa da tsawon zatinsa, da halayyarsa kamar haqurinsa da


cika alqawarinsa da jarumtarsa, da labarin rayuwarsa kamar tafiye-tafiyensa, da


yaqe-yaqensa, da ma’amalarsa da mabiya ko magautansa, da sauransu.


Sunna, a taqaice, ita ce duk abinda Manzon Allah (SAW) ya zo da shi na


addini da shari’a da shiriya da haske. Duk gaba xaya; ba tare da gefe ba. Kuma


wannan ya haxa da Alqur’ani mai girma, saboda maganarsa da aka ce ana nufin


duk abinda ya fito bakinsa, har da maganar Allah da ta gudana a kan harshensa, ya


isar da ita ga al’umma. A taqaicen taqaicewa, Sunna ita ce Annabi xungurungum


xinsa a matsayinsa na Jakadan Allah.


Saboda haka, Sunna ita ce Musulunci; ba daxi, ba ragi.


Mai bin Sunna shi ne wanda yake bin maganar Annabi, umarni da haninsa;


yake kwaikwayon aikin Annabi; yake riqo da abinda Annabi ya tabbatar; yake koyi


da halayyar Annabi; yake bin duddugin labarin Annabi domin koyi da


kwaikwayawa.


Daga abinda ya gabata za mu fahimci cewa, mutum ba ya zama mai bin


Sunnar Annabi (SAW) sai ya san Annabi (SAW). Sai ya san maganganunsa da


ayyukansa da tabbace-tabbacensa da kamanninsa da halayensa da tarihin


rayuwarsa. Wannan ya sa Ahalus Sunna suka mayar da ilmi mafi wajabcin wajibai.


5


Ilmin Alqur’ani da Hadisi da Sira (tarihin rayuwar Annabi) da ilmin al’amuran


Sahabbai waxanda suka rayu da Annabi (SAW) da maganganunsu da fiqihunsu da


sifofinsu da halayensu da tarihin rayuwarsu, da duk abinda yake da alaqa da su.


Umarni da Bin Sunna a cikin Alqur’ani


Akwai xaruruwan ayoyi da suke umarni da bin Annabi (SAW) da koyi da


shi, watau bin Sunnarsa, kuma suke nuna cewa bin sa shi ne bin Allah, kuma shi ne


Musulunci. Za mu kawo ‘yan misalai kaxan:


“Kuma ku yi xa’a ga Allah da Manzonsa ko a yi muku rahama.” (Suratu Aali


Imrana: 132).


“Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi xa’a ga Manzo, ko


kwa samu rahama.” (Suratul Nur: 56).


“Kuma abinda Manzo ya ba ku, to, ku riqe shi, kuma abinda ya hane ku, to, ku bar


shi.” (Suratul Hashr: 7).


“Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya


kasance yana fatan rahamar Allah da Ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah da


yawa.” (Suratul Ahzab: 21).


“To, a’aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka (ya Muhammad), ba za su yi imani ba, sai


sun yarda da hukuncinka ga abinda ya sava a tsakaninsu, sa’an nan ba su sami


wani qunci a cikin zukatansu ba, daga abinda ka hukunta, kuma su sallama


sallamawa.” (Suratun Nisa: 65).


Da wanin waxan nan na ayoyi masu yawa da suke nuna wajabcin xa’a ga


Annabi da yi masa biyayya da koyi da shi, wanda wannan shi ne bin Sunnarsa.


Hadisai da suke umarni da Bin Sunna


Har yau akwai hadisai da yawa da suke umarni da bin Sunna da koyi da


Manzon Allah (SAW) da bin umarninsa da hanuwa ga barin hane-hanensa. Ga


misalai kaxan:


6


Manzo (SAW) ya ce, “Na umarce ku da bin Sunnata da Sunnar Khalifofi


Shiryatattu. Ku yi riqo da ita da kyau.”1


A wani hadisin kuma ya ce, “Na bar muku abubuwa guda biyu, waxanda idan kuka


yi riqo da su, ba za ku vata ba har abada: Littafin Allah da Sunnar Ma’aikinsa.”2


Har yau, a wani hadisin yana cewa, “Allah ya ni’imtar da mutumin da ya ji magana


daga gare mu, ya kiyaye ta, ya isar da ita ga wasu.”3


Har yau dai, ya faxi a wani hadisin. Ya ce, “Wata tawaga daga cikin al’ummata ba


za su gushe ba suna masu rinjaye a kan gaskiya har Alqiyama ta tashi.”4


Da yake sharhi a kan hadisin, Imam Ahmad binu Hanbal, Allah ya rahamshe


shi, ya ce: “Waxan nan malaman Hadisi ke nan.”5 Har yau, Alqali Iyal, Allah ya


jiqan sa, ya yi qarin bayani a kan maganar Imam Ahmad, ya ce: “A nan Ahmad


yana nufin kafatanin Ahalus Sunna da dukkan waxanda suke bin tafarkin malaman


Hadisi.”6


Ayoyi da hadisai da suka gabata suna nuna mana wajabcin bin Suunar


Annabi (SAW) da kira zuwa gare ta da yaxa ilminta. Kuma daga wannan za mu


fahimci haramcin bin bidi’a, domin it kishiyar Sunna ce, da wajabcin yaqar ta da


bushe ta daga doron qasa.


Ma’anar Bidi’a


Malamai da dama sun yi bayanin ma’anar bidi’a a cikin littafansu.


Mashahurin malamin Sunna, Alshaxibi, ya ce: Bidi’a ita ce, “Qagaggiyar hanya a


cikin addini, wacce ta yi kama da addini amma ba addinin ba ce, tare da nufin


wuce gona da iri a bautar Allah Maxaukaki.”7 Mujaddadi Usmanu Xanfodiyo ya


1 Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Maja sun ruwaito da hadisin.


2


3 Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Maja.


4 Bukhari da Muslim sun ruwaito shi.


5 Duba Sharhin Imam Nawawi a kan Sahih Muslim.


6 Sharhin Nawawi a kan Sahih Muslim.


7 Duba Al’itisam na Ibrahim binu Musa Alshadibi, bugun Madba’atut Tahrir, ba tarihi, mujalladi na 1 shafi na 127.


7


ce, “Bidi’a ita ce qagar wani abu a cikin addini wanda ya yi kama da addinin,


amma ba ya cikin addini.”1


Waxan nan bayanai na bidi’a sun fito da ma’anarta fili. Yawancin ayyukan


bidi’a suna kama da addini domin suna xaukar yanayinsa, amma su ba addinin ba


ne saboda ba Annabi ne ya zo da su ba. Ba sa cikin maganganun Annabi (SAW) ko


ayyukansa ko tabbatarwarsa ko sifarsa, ta halitta ko ta halayya, kuma ba sa cikin


tarihin rayuwarsa.


Mu xauki misali da salatin bidi’a, wanda ba Annabi ne ya koyar da shi ba,


amma wani malami ne ko waliyyi ko shaihi ya qago shi. Wannan salati yana iya


yin kama da salati na shari’a ko na Sunna ko na Musulunci, saboda shi ma sunansa


salati kuma Annabi (SAW) ake wa shi, amma da yake ba Annabin ne ya zo da shi


ba to sai ya zama ba ya cikin addini, saboda shi qagen wani ne.


Mu daxa xaukar misali da nafilfilun bidi’a, kamar sallar daren tsakiyar


watan Sha’aban. Ka ga irin wannan nafila sallah ce, saboda tana da dukkan sifofin


sallah kamar tsayuwa da karatu da ruku’i da sujada, amma da yake ba Manzon


Allah (SAW) ne ya zo da ita ba, to sai ta zama ba ta cikin addini, saboda addini shi


ne kawai abinda Manzo (SAW) ya zo da shi. Duk abinda ba Ma’aiki ne ya zo da


shi ba, to wannan abin ba ya zama addini, kome kyawunsa a idanun wanda ya qago


shi, ko wanda ya karva daga gare shi.


Ko misalign azumin bidi’a, kamar azumin watanni biyu da suke kira azumin


tsofaffi. Ka ga azumi ne, da sahur da buxa-baki, da yunwa da qishirwa, kamar


azumin Musulunci, to amma ba ya cikin azumin Musulunci saboda ba Annabi


(SAW) ne ya koyar da shi ba, wani ne kawai, ko wasu, suka qago shi wai don su yi


ibada mai yawa, wanda shi ne ma’anar wuce gona da iri xin.


Ko fidda’u da ake taruwa ana yi wa mamaci a ranar uku, ko bakwai, ko


arba’in da rasuwarsa. Ka ga wannan addu’a ce kuma Allah ake roqa, amma da


yake ba maganar Annabi ba ce bai ce a yi ba, ba aikinsa ba ne bai tava yi ba, ba


tabbatarwarsa ba ce tunda wani bai yi haka a gabansa ya yi shiru ba, to wannan


addu’a ta zama bidi’a kuma Allah ba zai karve ta ba, sai ma ciko ya biyo gyartai


idan ba’a gamu da gafarar Allah ba.


1 A duba Ihya’us Sunna wa Ikhmadul Bidi’a na Usmanu Danfodiyo, bugun Darul Fikir, Bairut, 1962, shafi na 22.


8


To wannan a taqaice ita ce bidi’a: abinda ba’a ji daga Annabi (SAW) ba,


ba’a ga ya aikata be, ba’a aikata a gabansa ya yaba ko ya yi shiru ba, kuma ba


halinsa ba ne ba sifarsa ba ce, sai dai kurum ya yi kama da xayan waxan nan. To ai


kama da wane ba ta wane. Allah ya ganar da mu.


Hani ga barin Bidi’a daga Alqur’ani


Akwai ayoyi a cikin Littafin Allah mai tsarki waxanda suke nuni ga hani ga


barin bin duk wata hanya savanin hanyar da Annabi (SAW) ya zo da ita, wacce ita


ce hanyar Allah, kamar faxin Allah Maxaukaki, “Kuma lalle wannan ne tafarkina,


yana madaidaici: sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi, su rarrabu da ku


daga barin hanyata. Wannan ne Allah ya yi muku wasiyya da shi, ko kuna samun


taqawa.” (Suratul An’am: 153).


Wannan aya Manzon Allah (SAW) ya fassara ta da kansa ta wata hanya mai


qaye, kamar yadda Abdullahi binu Mas’ud (RA) ya ruwaito. Ya ce: Manzon Allah


(SAW) ya zana wani zane da hannunsa, sa’an nan ya ce, “Wannan ne tafarkin


Allah yana madaidaici.” Kuma ya yi zane a daman wannan zanen da hagunsa


(kamar surar qayar kifi), sa’an nan ya ce, “Waxan nan ne hanyoyi. Babu wata


hanya daga cikinsu face akwai shaixan a kanta yana kira zuwa gare ta.” Sa’an nan


ya karanta: “Kuma lalle wannan ne tafarkina, yana madaidaici: sai ku bi shi, kuma


kada ku bi wasu hanyoyi, su rarrabu da ku daga barin hanyata.”1


Idan mai karatu ya dubi wannan aya da idanun basira, ya auna ta da


ma’aunin hankali, zai fahimci cewa tana nuni ga hanyoyin da shaixanu suke yin


kira zuwa gare su waxanda sune bidi’o’i; domin hanyar Allah ita ce hanyar


Annabi, kuma guda xaya ce madaidaiciya, duk wata hanya wacce ba ita ba, to babu


ruwan Annabi da ita, kuma ta zama bidi’a.


Haka nan sauran ayoyi da suke kira izuwa riqo da igiyar Allah, suna hani ga


barin rarraba, duka suna nuni ga tafarkin Allah da Annabi, wanda shi ne abinda


Manzo (SAW) ya zo da shi, shi ne Sunna, shi ne Musulunci, suna hani ga barin bin


1 Ahmad da Ibnu Maja suka ruwaito hadisin kuma Albani ya inganta shi a cikin littafinsa, Zilalul Jannah fi Tikhriji


Ahadisis Sunnah.


9


tafarkin shaixan. Domin tafarkan biyu ne kawai; daga na Allah da Annabi, sai na


shaixanu.


Hadisai da suke Hani ga barin Bidi’a


Imam Muslim ya fitar da hadisi a cikin Sahihinsa cewa, Manzon Allah


(SAW) ya kasance yana faxi a cikin huxuba, bayan ya godewa Allah ya yi masa


kirari, “Wanda Allah ya shirye shi babu mai vatar da shi, kuma wanda ya vatar da


shi babu mai shiriya tasa. Mafi alherin zance Littafin Allah kuma mafi alherin


shiriya shiriyar Muhammad. Mafi sharrin al’amura qagaggunsu kuma dukkan


qagaggen al’amari bidi’a ne.”1


A wata ruwayar, yana cewa: “Kashedin ku da qagaggun al’amura; lallai


mafi sharrin al’amura su ne qagaggunsu. Dukkan qagaggen al’amari bidi’a ne,


kuma dukkan bidi’a vata ce.”2


Yaqar Bidi’a Aikin Mabiyan Annabawa


Imam Muslim ya ruwaito cewa, Annabi (SAW) ya ce: “Babu wani Annabi


da Allah ya aiko a cikin wata al’umma gabanina face ya kasance a cikin


al’ummarsa yana da mataimaka da Sahabbai waxanda suke riqo da Sunnarsa, su yi


koyi da umarninsa. Sa’an nan daga baya, sai wasu masu mayewa su maye musu, su


riqa faxin abinda ba sa aikatawa, suna aikata abinda ba’a umarce su da shi ba.


Wanda ya yaqi waxan nan da hannunsa, to shi mumini ne, wanda ya yaqe su da


harshensa, shi ma mumini ne. Haka nan, wanda ya yaqe su da zuciyarsa, shi ma


mimini ne. Amma a bayan haka babu imani koda na qwayar zarra.”3


Wannan hadisi ingantacce yana nunawa a fili cewa, alamar rashin imani ne


mutum ya ga ana bidi’a bai hana ba, idan yana iyawa. Idan ko har ba ya iyawa, to


wajibi ne ya qyamaci abin a zuciyarsa, ya nesanci masu aikatawa. Wannan shi ne


mafi qarancin abinda Musulmi zai iya yi, kuma wanda ya gaza haka, to babu imani


a gare shi ko qanqane.


1 Sahihu Muslim, kitabul Jum’ah.


2 Sunanu Ibni Maja, Almuqaddimah.


3 Imam Muslim ne ya fitar da hadisin.


10


Wannan ya sa Sahabban Annabi (SAW), Allah ya qara musu yarda, suka fi


kowa yaqar bidi’a da gargaxi a kan sharrinta.


An ruwaito Abdullahi binu Mas’ud (RA) yana cewa, “Yak u mutane, kada


ku yi bidi’a, kada ku yi shisshigi, kada ku zurfafa. Kuma ku yi riqo da abinda aka


gada (daga Annabi).”1 Kuma an ruwaito yana cewa, “Taqaitawa a cikin Sunna ya


fi qoqari a cikin bidi’a.”2 Watau mutum ya yi aiki xan kaxan wanda ya dace da


Sunnah, ta fi ya yi aiki mai yawa na bidi’a. Domin aikin bidi’a, kome yawansa


kuma kome girmansa, aikin baban giwa ne!


Yaqar Bidi’a Ya Fi Aikin Ibada


Malamai daga cikin magabatan al’umma na gari sun yi maganganu masu


yawa da suke nuna fafala da fifikon aikin yaqar bidi’a. Imam Ahmad binu Hanbal,


Allah ya rahamshe she, ya tabbatar da cewa yaqar bidi’a ya fi aikin ibada na nafila.


An tambaye shi dangane da mutumin da yake wuni azumi, ya kwana salla, kuma


yana cikin i’itikafi, das hi da mai yaqar bidi’a: Wane ne ya fi?


Sai ya ce, “Idan mutum ya yi sallar dare, ya yi azumi, ya yi i’itikafi, wannan


kansa yake yiwa. Amma mai yaqar bidi’a, shi Musulmi yake amfana. Don haka shi


ya fi.”3 A nan, Imam Ahmad ya ba da wannan fatawa gwargwadon qa’idar Shari’a


da take cewa, aikin ibada wanda alherinsa yake gudana, ya yi naso ga wasu, ya fi


wanda ladansa yake tsayuawa a kan mai shi kawai.


Yaqar Bidi’a Ya Fi Jihadin Kafirai


Kai ba ibadar nafila ba, hatta jihadin kafirai yaqar bidi’a yana gaba da shi;


saboda shi kafiri kashe rai kawai zai yi, shi kuwa mai bidi’a kashe addini zai yi.


Kuma tsare addini yana gaba da tsare rai a cikin Maqasidu na Shari’a, watau


manyan manufofinta.


1 Sunan na Imam Darami.


2 Darami a cikin Sunan nasa.


3 A duba Majmu’atur Rasa’il wal Masa’il na Ibnu Taimiyya, mujalladi na 5 shafi na 110.


11


Wannan ya sa Imam Yahya binu Yahya yake cewa, “Kare Sunna ya fi jihadi


falala.” Da aka tambaye shi: Yanzu mutum ya ciyar da dukiyarsa, ya wahalar da


kansa, ya yi jihadi, amma wancan ya fi shi? Sai ya ce, “E, ninkin ba ninki.”1


Misalai daga Rayuwar Magabata


Sanin haxarin bidi’a da muhimmancin yaqarta shi ya sa magabatan al’umma


na gari, tun daga zamanin Sahabbai da Tabi’ai, da kuma malamai da suka bi


gurabunsu har ya zuwa yau, suka mayar da yaqar bidi’a da hannaye da alqaluma


da harasa babban aikin rayuwarsu.


Imam Ibnul Qayyim, Allah ya yi masa rahama, yana cewa, “Inkarin


magabata da manyan malamai, Allah ya jiqan su, a kan bidi’a ya tsananta. Sun yi


ca a kan masu bidi’a daga dukkan vangarorin qasa. Sun yi gargaxi a kan fitinarsu


mafi tsananin gargaxi, kuma sun isa matuqa a cikin haka fiye da gargaxinsu a kan


alfasha da zalunci da qetare haddi. Wannan kuwa ya faru saboda illar bidi’a da


rusawarta ga addini da wargaza shi ya fi kome tsanani.”2


Akwai misalai masu yawa a rayuwar malamai na qwarai da kayan gadon


ilmi da suka bari ga al’umma ana amfana da su a tsawon zamani. Da wuya a samu


wani babban malami wanda a cikin ayyukansa bai yi magana ko rubutu domin


gargaxi ga barin bidi’a da bayyana illolinta ga addini da rayuwa ba, ko ya mayar


da martini ga malaman bidi’a, ya tona asirinsu, ya bayyana vatansu.


Ga ‘yan misalai na wasu mashahuran malamai.


1. Imam Malik binu Anas: Ya yi suna da riqo da Sunna da girmama ta, da


tsananin qyamar bidi’a da masu bidi’a. Daga cikin littafansa na yaqar bidi’a


akwai Alqadar wal Raddu alal Qadariyya.


2. Imam Ahmad binu Hanbal: Ya yi fama da ‘yan bidi’a kuma ya sha


wahalhalu iri-iri a kan haka. Ya fuskanci wulaqanci da qasqanci da xauri


daga wasu mahukunta waxanda suka xaurewa ‘yan bidi’a gindi, amma


wannan bai sa ya saurara ba a yaqinsa da bidi’a. Daga cikin littafan da ya


1 Aduba Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyya, mujalladi na 3 shafi na 13; da Siyaru A’alamin Nubala na Zahabi,


mujalladi na 10 shafi na 518.


2 A duba Madarijus Salikin na Ibnul Kayyim.


12


rubuta don mai da martini a akan ‘yan bidi’a akwai Alraddu alal Zanadiqa


wal Jahamiyya.


3. Imam Bukhari: Ya rubuta Alraddu alal Jahamiyya musamman don mayar da


martani ga Jahamawa, kamar yadda ya qwanqwashi wasu ‘yan bidi’ar a


cikin wasu littafan nasa. Ga misali, a cikin littafinsa mai suna Khalqu Af’alil


Ibad yana faxi dangane da ‘yan Shi’a kamar haka: “Duka xaya ne a gare ni


yin sallah a bayan Bajahame ko xan Shi’a da yin sallah a bayan Bayahude


da Kirista. Kuma ba’a yi musu sallama, ba’a dubo su (idan ba su da lafiya),


ba’a auratayya da su, ba’a karvar shaidarsu kuma ba’a cin yankansu.”1


4. Abu Zur’ata Arrazi: Babban malamin Sunna, zararren takobi a kan bidi’a.


Ya yi fama da nau’i dabam-daban na ‘yan bidi’a, musamman ‘yan Shi’a da


zindiqai. Daga cikin littafansa a wannan fage akwai Alraddu ala Ahlil Ahwa.


5. Imam Darami: Ya rubuta Alraddu ala Bishrin Almarisi inda ya mayar da


martini a kan wani malamin bidi’a dujali mai suna Bishr Almarisi.


6. Imam Ibnu Qutaiba: Ya rubuta Alraddu alal Jahamiyya wal Mushabbiha.


7. Shaihul Islam Abdulqadir Jilani: Yana cikin malamai mafiya tsanani wajen


yaqar bidi’a da ‘yan bidi’a, musamman ‘yan Shi’a; don haka ya zama daga


cikin waxanda ‘yan Shi’a suka fi matuqar qi. Qiyayya tsakanin ‘yan Shi’a


da Shaihu Abdulqadir ta wanzu har bayan rasuwarsa, inda suka karkashe


mabiyansa, suka rusa makarantarsa, suka tone kabarinsa a wani hari da suka


kai birnin Bagadaza.2


Wannan ya sa ya zama abin takaici yadda wasu masu da’awar cewa su mabiyan


Shaihu Abdilqadir ne a qasar nan suke yin Shi’anci a bayyane, suna amfani da


jahilcin mabiyansu, suna cin amanarsu. Wani yankin bidiyo da yake kewayawa a


kwanan nan, ya nuna yadda xaya daga cikin ‘ya’yan Shaihu Nasiru Kabara ya je yi


wa Zakzaki ta’aziyyar rasuwar ‘ya’yansa uku, yana cewa wai abinda Zakzaki yake


kai shi ne abinda ubansu ya koyar a rayuwarsa. Akwai ban mamaki yadda mutum


zai yi wa ubansa qarya, ya dangana masa mummunar aqida a bayan mutuwarsa,


don kawai neman kostomomi.


Shaihu Abdulqadir ya rubuta littafai don yaqar bidi’a da bayyana aqidar Sunna,


ciki har da littafinsa mai shuhura Alguniyya li Xalibi Xariqil Haqqi Azza wa Jalla,


1 Duba Al’intisaar lis Sahabi wal Aal na Amir binu Ibrahim Alruhaili, shafi na 132.


2 Mai son ganin wannan labari da waninsa, sai ya duba Addaulatul Zankiyya na Ali Muhammad Sallabi, bugun Darul


Ma’arifa, Bairut, 1430/2009, shafi na 415-416.


13


wanda a cikinsa ya yi tur da aqidar Shi’a, ya nuna muninta.1 Amma wasu shakiyai,


marasa tsoron Allah, sai suka ce wai littafin ba na ainihi ba ne. Wai ‘yan


Wahhabiyya sun yi qare-qare a cikin littafin. Suka ce wai su suna da na ainihin,


amma don rashin kunya sun kasa fitowa da shi, mutane su amfana. Allah ya raba


mu da son zuciya, da tattalin gina gidan gado da sunan addini.


8. Imam Gazali ya rubuta littafai da yawa, banda gwagwarmayar da ya yi da


‘yan bidi’a, musamman ‘yan Shi’a. Daga cikin littafansa a wannan fanni


akwai, Almunqizu minal Dalal da Faisalut Tafriqa bainal Islami wal


Zandaqa da Tahafutul Falasida, da sauransu. Gazali ya rubuta littafi


musamman don tona asirin ‘yan Shi’a wanda ya kira da sunan Fala’ihul


Baxiniyya wanda a ciki ya bayyana cewa an kafa Shi’anci ne don yaqar


Musulunci daga ciki.2


9. Shaihul Islam Ibnu Taimiyya ya fafata da ‘yan bidi’a, musamman Sufaye da


‘yan Shi’a, ya yaqe su da hannunsa da harshensa da alqalaminsa. Daga cikin


littafansa a wannan fanni akwai: Minhajus Sunnatin Nabawiyya da wasu


gomomin littafai waxanda lasafta su a nan zai yi tsawo.


10. Imam Ibnul Qayyim ya sha fama da ‘yan bidi’a tare da malaminsa, Ibnu


Tayyimma. Sun shiga kurkuku tare ba sau xaya ba (Ibnu Taimiyya a gidan


kaso ya rasu), an wulaqanta su, an qasqanta su, amma suka jure har suka


gamu da Ubangijinsu. Daga cikin littafan da Ibnul Qayyim ya wallafa don


tona asirin ‘yan bidi’a akwai Assawa’iqul Mursala alal Jahamiyyati wal


Mu’axxila da Shifa’ul Alil fi Masa’ilil Qada’i wal Qadari wal Hikmati wal


Ta’alil da qasidar Alkafiyya fil Intisari lil Firqatin Najiya mai baiti dubu


shida ba hamsin (5950), wacce a cikinta ya mai da martini a kan Mulhidai da


Zindiqai kuma ya bayyana ingancin tafarkin Sunna.


11. Shaihu Mujaddadi Xanfodiyo ya tafiyar da rayuwarsa baki xaya wajen yaqar


bidi’a da tabbatar da Sunna. Tarihin rayuwarsa da littafansa masu dama suna


nuna haka a fili. Daga cikinsu akwai: Ihya’us Sunna wa Ikhmadul Bidi’a da


Bayanul Bida’ish Shaixaniyya, da wasu littafan masu yawa banda waxan


nan.


12. Shaihu Abubakar Mahmud Gumi shi ma ya tafiyar da rayuwarsa wajen


yaqar bidi’a da tabbatar da Sunna. Ya yi amfani da alqalami da harshe, ya


1 Duba Alguniyya na Shaihu Abdulkadir, bugun Sharikatul Quds, Alkahira-Misra, 1427/2006, shafi na 146-152.


2 Duba Daulatul Salajiqa na Ali Muhammad Sallabi, bugun Darul Ma’arifa, Bairut, 1430/2009, shafi na 409-413.


14


hore kayan fasaha na zamani kamar radiyo da talabijin da sauransu wajen


qaddamar da wannan aiki, kamar yadda ya kafa qungiyar Jama’atu Izalatil


Bid’a wa Iqamatis Sunna don xora al’umma a kan tafarkin yaqar bidi’a da


tabbatar da Sunna. Daga cikin littafansa akwai: Al’aqidatus Sahiha bi


Mawafaqatish Shari’a.


Wannan xan misali ne qanqani na irin ayyukan malamai wajen yaqar bidi’a


da tabbatar da Sunna. Kuma kamar yadda malamai suka yi amfani da ilminsu


wajen yaqar bidi’a, haka nan masu mulki suka yi amfani da qarfin mulkinsu wajen


daqile ayyukan ‘yan bidi’a da maganin miyagun malaman bidi’a da hukunta su. A


wasu lokuta hukuncin masu mulki a kan malaman bidi’a ya kan kai ga kashe su


kisan haddi, domin ije sharrinsu ga addini da al’umma, kamar yadda ya faru ga


Muhammad binu Mansur Alhallaj (wani qasurgumin Sufi) da Ja’adu binu Dirham


(wani mai musun sifofin Ubangiji), da sauransu.


Mafi Sharrin Bidi’a


Dukkan bidi’a vata ce, kamar yadda hadisin Annabi (SAW) ingantacce ya


bayyana, amma wata bidi’a ta fi wata. Bidi’ar aqida, wacce ta shafi qudurcequdurce,


ta fi bidi’ar aiki wacce ta shafi ibadoji, muni.


Daga cikin kashi na farkon akwai bidi’ar Jahiliyya ta camfe-camfe wacce


Mushirikan zamanin Jahiliyya suka qirqira suka dangana ga Allah Maxaukaki,


kuma suke riya bauta masa da ita, kamar nau’in abinci da dabbobi da suke


haramtawa daga qashin kansu kuma su danganta haramcin ga Allah a bisa qarya da


camfi.


Allah Maxaukaki yana faxi dangane da irin wannan bidi’a ta camfi da


shirka, “Kuma sun sanya wani rabo ga Allah daga abinda ya halitta na shuka da


dabbobi, sai suka ce: Wannan na Allah ne, da riyawarsu, kuma wannan na


abubuwan Shirkinmu ne.” (Suratul An’am: 136). Haka nan ya ce, “Kuma suka ce:


Abinda yake a cikin cikkunan waxan nan dabbobi kevantacce ne ga mazanmu,


kuma haramtacce ne a kan matanmu. Kuma idan ya kasance mushe, to, a cikinsa,


su, abokan tarayya ne.” (Suratul An’am: 139). Har yau ya ce, “Kuma Allah bai


sanya wata bahira ba, kuma haka sa’iba, kuma haka wasila, kuma haka ham.”


15


(Suratul Ma’ida: 103). Irin wannan bidi’a ta qunshi camfi da shirka da qala qarya


ga Allah da kuma haramta abinda ya halatta ko halatta abinda ya haramta.


A wannan kashi ne kuma ake ruskar da bidi’ar quduri irin ta ‘yan Shi’a


dangane da Imamansu, wacce ta qunshi qaryata ayoyin Allah da dangana masa


qarya, da bidi’ar munafukai waxanda suke qudure kafirci a zukatansu amma su


bayyana Musulunci don tsare rayukansu da dukiyoyinsu.


Sai kuma bidi’ar qungiyoyi waxanda suka bar Sunna, amma qudurcequdurcensu


ba su kai ga matsayin kafirci ba, koda yake akwai savani a kan


kafircinsu, kamar Khawarijawa da Qadariyyawa da Murji’awa, da sauransu.


Bidi’ar aiki an yi ittifaqi a kan cewa ba kafirci ba ce, amma ita aikin savo ne


wanda ya fi kaba’ira. Abinda ya sa ya fi kaba’ira shi ne wuyar tuba ga mai yinsa,


saboda mai yin sa yana ganin bauta wa Allah yake yi; saboda haka yaushe zai tuba


ya dena? Misalinsa shi ne qagaggun ayyuka, kamar azumi ko sallah ko addu’a,


kamar wurdi da wazifa, waxanda ba su da tushe a cikin Littafin Allah ko Sunnar


Manzonsa (SAW), sai dai an qago su ne da niyyar isa matuqa wajen bauta.


A cikin wannan kashi ne ake sanya ayyuka qagaggu a addini kamar su


maulidi da wurde-wurden masu xariqu da ziyarce-ziyarcensu zuwa qaburbura, da


sadakar uku ga mamaci, da ayyuka masu kama da waxan nan. Amma wasu daga


cikin waxan nan suna iya kaiwa ga matsayin kafirci idan suka qunshi aikin da yake


warware imani, kamar sujada ga kabari, da sauransu.1


Babu shakka mafi sharrin bidi’a a Musulunci ita ce bidi’ar Shi’a, saboda


dalilai masu yawa:


Dalili na farko kasancewarta ita ce bidi’a ta farko da ta vulla a Musulunci;


don haka sai ta zama uwar bidi’o’i.


Dalili na biyu kasancewarta ta game tsakanin munafunci da qudurcequdurcen


da suke warware imani. Yahudawa da Farisawa (Iranawa), waxanda


Musulunci ya buwaye su a fagen fama, su ne suka shiga addinin a munafunce,


sa’an nan suka samar da tafarkin Shi’anci a matsayin wata qungiya ta asiri wacce


1 Domin karin bayani sai a duba Al’itisam na Abu Is’haq Ibrahim binu Musa Alshadibi, bugun Darul Hadis, Alkahira-


Misra, 1424/2003, juzu’i na 2 shafi na 297-298.


16


suka yi fatan amfani da ita wajen rusa Musulunci, suna masu yafa mayafin son


Ahalul Baiti domin vad da bami.


Dangane da warware imani kuwa, aqidun Shi’a na Bada da Raja’a da Imama


da aqidar sauya Qur’ani da aqidarsu dangane da Sahabbai, ko wacce guda daga


cikin waxan nan tana warware imani, ina ga idan suka haxu baki xaya?1


Dalili na uku baqin tarihin Shi’a da cutar addini da yi masa zagon qasa ta


hanyar vata aqidunsa da yaxa alfasha a tsakanin mabiyansa da taimakon kafirai


wajen yaqarsa, da sauran nau’i-nau’i na yaqar Musulunci waxanda babu wani


addinin kafirci da ya qaddamar da kamarsu a tsawon tarihi. 2


Dalili na huxu tsananin gaba da qiyayya ga Musulmi tun daga zamanin


Sahabbai, Allah ya qara musu yarda, har ya zuwa yau. Ba’a tava samun wata


qungiya mai da’awar Musulunci da take qunshe da gubar qiyayya da sharri da cuta


ga al’ummar Annabi (SAW) ba kamar qungiyar Shi’a.3


Yaqar dukkan nauo’in bidi’a wajibe ne, amma ko ba’a faxi ba yaqar mafi


sharrin bidi’a ya fi nauyin wajabci. Don haka ya zama wajibi a kan dukkan


Musulmi su yaqi Shi’a. Malamai da almajirai da attajirai da sarakai da ‘yan book,


dole kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen qaddamar da wannan aiki, kowa


gwargwadon ikonsa.


Mahukunta kuwa, ina nufin gwamnatocin jihohi da na tarayya, wajibi ne su


yi amfani da qarfin iko da Allah ya ba su domin kawar da haxarin Shi’a daga qasar


nan; saboda Shi’a ba wai kawai matsala ce ta addini ba, a’a MATSALA CE TA


TSARO. Idan a da suna shakku a kan haka, to a yanzu shakkun ya kwaranye;


domin abinda yake voye ya fito fili bayan rikicin da ya faru tsakanin Soja da ‘yan


Shi’a a Zariya a watan Disamba na shekarar 2015.


Mai hikima shi ne wanda yake izna da abinda ya faru ga wani. Abinda yake


faruwa a qasashen Iraqi da Siriya da Yaman a yau ya isa abin izna.


Gwamnatocin baya, da wasu ‘yan siyasa sun zuba ido Shi’a na yaxuwa,


wasu ma sun taimaka wajen yaxuwarta da qarfafa ta, kamar yadda wasu


1 Duba littafin Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a da Akidojinsu domin bayani.


2 Duba littafi na 8 a wannan jerin. Haka nan, a duba littafin Matsayin Ahalus Sunna a wajen ‘Yan Shi’a.


3 Duba littafi na 5 a wannan jerin.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA