Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 5


Matsayin


Musulmi


a wajen


‘Yan Shi’a


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


Gabatarwa


Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman


taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna neman tsari da Allah daga


sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi,


babu mai vatar da shi kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina


shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da


abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma


Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi, da Alayensa, da


Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.


Bayan haka, ‘yan Shi’a suna yawan yin magana dangane da haxin kan


Musulmi. Ba sa barin wata munasaba ta wuce ba tare da sun maimaita kira


izuwa haxin kai ba, da sukan rarraba da karkasuwa zuwa qungiyoyi da


mazhabobi. Sau da yawa sukan yi kira da haxin kai tsakaninsu da Ahalus


Sunna, suna masu qarfafa cewa bai kamata a samu savani ba domin hakan


yana raunana Musulmi a gaban abokan gabansu. A wasu lokuta sukan nuna


cewa abubuwan da suka raba su da Ahalus Sunna ba wasu muhimmai ba ne,


kuma su da Ahalus Sunna duka abu guda ne tunda Shi’a ita ma mazhaba ce


kamar sauran mazhabobi.


A wasu qasashe, ‘yan Shi’a suna kira da abinda suke wa laqabi da


Attaqrib bainal Mazahib, ko kuma Atta’aruf, watau kusantar da mazhabobi


ga junansu ko kuma fahimtar juna, suna nufin kusanci da fahimtar juna


tsakanin tafarkin Shi’a da na Sunna. A nan Nijeriya kuwa, mun san su da


kirarin Islam One, wanda suke bin gine-ginen hukuma kamar makarantu da


ofisoshi suna rubutawa, wai suna nufin Musulunci xaya ne, babu bambanci


tsakanin wani tafarki da wani, ko kuma wata mazhaba da wata.


Amma mene ne haqiqanin abinda ‘yan Shi’a suka xauki mai bin


tafarkin da ba nasu ba, musamman Ahalus Sunna? Shin gaskiya ne suna


xaukar dukkan Musulmi xaya ne, ko kuwa kawai yaudara ce suke yi don su


samu karvuwa a wajen mutane? Mene ne abinda manyan malaman Shi’a


suke faxi dangane da Ahalus Sunna, da sauran Musulmi duka, a da da kuma


yanzu? Shin sun yarda su Musulmi ne kamar yadda su ma suke da’awar


Musulunci, ko kuwa suna xaukar su dabam? Ya suka xauki imaninsu da


3


sallarsu da azuminsu da hajjinsu da yankansu da auratayyarsu da sauran


ma’amalolinsu da ayyukansu na addini?


Wannan xan qaramin littafi zai yi qoqarin amsa waxannan


tambayoyi, da ma wasunsu, in Allah ya yarda, kuma amsoshin duka za su


fito kai tsaye daga bakin manyan malaman ‘yan Shi’a, ta hanyar littafansu


waxanda suka yarda da su. A qarshe mai karatu zai fita da sahihiyar fahimta


ta matsayin Ahalus Sunna, da sauran Musulmi, a wajen ‘yan Shi’a ta yadda


zai yi hukunci da kansa a kan wannan da’awa ta Rafilawa ta kira zuwa ga


haxin kai da kusanto da mazhabobi da fahimtar juna idan gaskiya ce ko


kuwa qarya ce da yaudara.


Manufarmu a nan, in Allah ya yarda, ita ce bayanin gaskiya da sauke


nauyin da yake kanmu na al’ummarmu, don wanda ya halaka ya halaka a


bisa sani kuma wanda ya shiriya ya shiriya a bisa sani. Kuma gamon


katarinmu bai zamo ba sai ga Allah, a gare shi muke dogara, kuma gare shi


muke komawa.


4


Babi Na Xaya


Ma’anar Ahalus Sunna A Wajen Rafilawa


Mai karatun littafan Shi’a zai lura da wasu sunaye, ko kuma laqabai,


da suke kiran Ahalus Sunna da su. Waxannan laqabai suna cikin littafan


malamansu na farko da malamansu na zamani. Ba safai sukan kira su da


sunan Ahalus Sunna ba sai nadiran. Sunayen dukkaninsu suna nuna qazafi


da vatanci da wulaqanci. Zai yi kyau mu fara bayani da waxannan sunaye


kafin mu shiga magana a kan ma’anar Ahalus Sunna a wajen Rafilawa.


Sunayen Ahalus Sunna A Wajen ‘Yan Shi’a


Akwai sunaye guda uku da Rafilawa suke amfani da su don ambaton


Ahalus Sunna a cikin littafansu da maganganunsu waxanda suka haxa da


huxubobinsu da laccocinsu da wa’azozinsu. Waxannan su ne:


1. Nasibawa. Asalin sunan da Larabci nasib, jam’insa nawasib, watau mai


qulla gaba, ko wanda ya kafa qiyayya. Abinda suke nufi gaba da qiyayya ga


Ahalul Baiti, musamman Ali binu Abi Xalib da Faxima, Allah ya qara musu


yarda, da kuma imamai goma sha biyu daga zuri’arsu. Wannan suna shi ne


mafi muni kuma mafi yaxuwa a tsakaninsu wanda suke ambaton Ahalus


Sunna da shi.


Malaminsu mai suna Hussain Aali Usfur Addarazi Albahrani, yana


cewa, “Al’ada ta gudana, kai har ma da hadisan imamai, a kan cewa nasibi


shi ne wanda a wajensu suke kira Sunni.”1


A wajensu, yana nufin a wajen Ahalus Sunna. Amma su a nasu wajen


nasibawa suke ce da su. Dubi yadda ya yi nuni ga Ahalus Sunna da lamirin


“su” domin ya bambance su da “mu” wanda a zancensa yake nufin ‘yan


1 Almahasin Annafsaniyya na Albahrani, bugun Jam’iyyatu Ahalil Baiti, Bahrain, 1399 B.H. shafi na 147.


5


Shi’a. Wannan kawai ya isa ya nunawa mai karatu yadda xan Shi’a yake


xaukar kansa da Ahalus Sunna; watau abin mu ne da su.


Malamin Shi’a na wannan zamani wanda ya shahara da tsaurin kai,


Muhammad Tijjani Samawi, yana cewa, “Abu ne da ba ya buqatar a faxi


cewa mazhabin nasibawa shi ne mazhabin Ahalus Sunna wal Jama’a.”1


Haka yake kamar yadda malamin ya faxi. Wannan abu ba ya buqatar a faxi


saboda ya shahara a tsakanin Rafilawa kuma a cikinsu babu mai ja a kai.


2. Amawa. Wannan shi ne suna na biyu da Rafilawa ke kiran Ahalus Sunna


da shi. Asalinsa da Larabci aami, jam’insa awaam, watau gama-gari, ko


tarkacen mutane. Kuma sunan kishiyar lafazin khaas ne (jam’insa khawaas),


wanda yake nufin na musamman, ko na-gari. Watau ‘yan Shi’a su ne na


musamman, masu nagarta, Ahalus Sunna kuwa tarkace, gama-gari. Daga


cikin malaman Shi’a da suka yi amfani da wannan suna akwai Alhurrul


Amili wanda ya rubuta wani babi mai taken “Babin Hani Ga Barin Riqo Da


Abinda Ya Dace Da Amawa” a cikin littafinsa mai suna Alfusulul


Muhimma. A qarqashin wannan babin, ya ruwaito imaminsu na shida,


Ja’afar Sadiq, yana cewa idan aka samu hadisai guda biyu masu karo da


juna, to a xauki wanda ya sava wa ra’ayin Amawa, a qyale wanda ya dace


da su.2


3. Suna na uku shi ne Jumhur. Wannan suna haka yake ko a Larabci, kuma


ba shi da tilo sai jam’i kawai. Ma’anarsa ta yi kama da gama-gari koda yake


a wani yayi yana nufin agalabiya, watau mafiya yawa, masu rinjaye, ko


kuma majorati, kamar yadda ake faxi da kalmar Turanci ta aro.3


Waxannan sunaye su ne ‘yan Shi’a suke amfani da su wajen ambaton


Ahalus Sunna a cikin littafansu, maganganunsu, laccocinsu da huxubobinsu.


Kuma ma’anarsu a fili take; suna nuna yadda ‘yan Shi’a suka xauki masu


bin tafarkin Sunna a matsayin abokan gaba masu qiyayya ga imamai, bare


1 A duba Ash Shi’atu Hum Ahalus Sunna na Muhammad Tijjani Samawi, bugun Mu’assasatul Fajri, Landan,


bugu na 10, 1423 B.H. shafi na 161.


2 A duba Alfusulul Muhimma fi Usulil A’imma na Munammad binu Hassan Alhurrul Amili, bugun


Maktabatu Basirati, Qum-Iran, ba tarihi, shafi na 225.


3 Alfusulul Muhimma, shafi na 219.


6


waxanda ba na gida ba, kuma koma-baya waxanda suke gama-gari ne su,


tarkace.


Banda waxannan sunaye, akwai wasu lafuza da malaman Shi’a ke


amfani da su domin nuni ga duk wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu,


wanda yana iya haxawa da Ahalus Sunna da wasunsu. Waxannan sun haxa


da almukhalif, watau mai sava mana, da gairuna, watau waninmu, da


munafiq, watau munafiki, da sauransu.


Ma’anar Ahalus Sunna A Wajen ‘Yan Shi’a


Amma idan muka koma ga haqiqanin ma’anar Ahalus Sunna a wajen


‘yan Shi’a, to sai mu ga cewa sun gina ta a kan abubuwa uku.


1. Abu na farko: Fifita wanin Ali binu Abi Xalib(RA) a kansa. Dangane da


wannan ma’ana ne malaminsu xan hayaqi, Ni’imatullahi Aljaza’iri, yake


faxin wai, “An ruwaito daga Annabi(SAW) cewa alamar nasibawa ita ce


gabatar da wanin Ali a kansa.”1 Watau wanda ya ce wani Sahabi ya fi Ali,


ko yana gaba da shi a wajen daraja da falala, ko shi ne Khalifa na farko ba


Ali ba, to wannan ya zama nasibi. Babu shakka Ahalus Sunna suna ganin


cewa Abubakar da Umar da Usman suna gaba da Ali a wajen falala da fifiko


da kuma jerin khalifanci.2 Kai a cikin qungiyoyin Musulunci ma kaf, ba mai


fifita Ali a kan Abubakar da Umar sai ‘yan Shi’a (koda yake an samu wasu


waxanda suka fifita shi a kan Usman). Saboda haka a kan wannan, duk


wanda ba xan Shi’a ba nasibi ne ke nan.


2. Abu na biyu: Yarda da amincewa da khalifancin Abubakar da Umar,


Allah ya qara musu yarda.3 Watau ko da mutum bai fifita su ba, idan dai ya


yarda da cewa su khalifofi ne, to ya zama nasibi.


1 A duba littafinsa, Al’anwarun Nu’umaniyya, bugun Muassasatul A’alami lil Madbu’at, Bairut, 1404 B.H.,


2/307.


2 Duba littafinmu, Dangantaka da Auratayya Tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, bugun Zomo Press,


Kaduna, 2010, babin Fifikon Sahabbai a Junansu, shafi na 5-6.


3 A duba Nurul Barahin na Ni’imatullahi Aljaza’iri, bugun Muassasatun Nashril Islami, Kum-Iran, 1417 B.H.


shafi na 57-58.


7


3. Abu na uku: Jivintar Jibtu da Xagutu, kamar yadda suke faxi.1 Abinda


suke nufi da Jibtu da Xagutu su ne Abubakar da Umar, Allah ya qara musu


yarda. Watau ba fifita su ba, ba yarda da khalifancinsu ba, ko jivintar su ma


kawai, watau son su da xaukar su a matsayin ‘yan uwa Musulmi, yana mai


da mutum nasibi.


Yana daga cikin aqidun Rafilawa sanannu cewa mutum ba ya zama


Musulmi sai ya barranta daga Abubakar da Umar da manyan Sahabbai tare


da su, kuma ya barranta daga duk mai son su, ko jivintar su. Babban


malaminsu, Muhammad Baqir Almajalisi, ya tabbatar da wannan aqida tasu


inda yake cewa, “Aqidarmu ta barranta ita ce cewa mu muna barranta daga


gumaka huxu: Abubakar da Umar da Usmanu da Mu’awiya; da mataye


huxu: A’isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam; kuma muna barranta


daga dukkan mabiyansu da magoya bayansu; kuma muna qudure cewa su ne


mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa; kuma cewa imani da Allah da


Manzonsa da imamai ba ya inganta sai an barranta daga maqiyansu.”2


Daga waxannan bayanai da suka gabata zai bayyana a fili cewa a


ganin ‘yan Shi’a duk wanda bai qudure aqidarsu ba ta cewa Ali binu Abi


Xalib shi da ‘ya’yansa su kaxai su ne khalifofi, ko imamai, kuma cewa


Abubakar da Umar da Usmanu ba wai kawai su ba khalifofi ba ne a’a su


kafirai ne gumaka, wanda duk bai qudure wannan aqida ba to shi ne nasibi


kuma imaninsa da Allah da Manzo bai inganta ba. Wannan yana nufi, a


taqaice, duk wanda ba xan Shi’a ba kafiri ne, tun daga kan Abubakar(RA)


har ya zuwa ga kai mai karatun wannan littafin, in kai ba xan Shi’a ba ne.


To jama’a, ina qaryar haxin kai? Ina qaryar taqrib da ta’aruf da


“Islam One”? Ina da’awar cewa Musulmi duka xaya ne? Yaya masu


barranta daga Abubakar da Umar da Usmanu da A’isha da Hafsa da


mabiyansu da magoya bayansu za su haxa kai da wani? Shin ana haxa kai da


kafiri wanda yake goyon bayan mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa?


1 A duba Alfusulul Muhimma na Alhurrul Amili, shafi na 227.


2 A duba Haqqul Yaqin na Muhammad Baqir Almajalisi, bugun Darul Adwa, Bairut, ba tarihi, shafi na 519.


8


Amma ba a nan batun ya qare ba. Saurari hukuncin nasibawa


waxanda suka yarda da khalifancin Abubakar da Umar, suka fifita su a kan


Ali.


9


Babi Na Biyu


Hukuncin Ahalus Sunna A Wajen ‘Yan Shi’a


Malaman Shi’a sun gina hukunce-hukunce masu haxarin gaske a kan


Ahalus Sunna, da ma duk wani Musulmi wanda bai qudure irin qudurinsu


ba. Waxannan hukunce-hukunce suna cikin littafansu na da da kuma na


wannan zamani, kuma a kansu suke gina alaqarsu da sauran Musulmi. Ga


muhimmai daga cikin hukunce-hukuncen waxanda ya kamata duk Musulmi


ya sani domin ya san matsayinsa a wajen ‘yan Shi’a kuma ya tantance


alaqarsa da su.


Su Kafirai Ne Mushirikai


A wajen ‘yan Shi’a, Ahalus Sunna kafirai ne kuma mushirikai.


Babban malaminsu, Almajalisi, yana cewa, “’Yan Shi’a masu ban gaskiya


da imamai goma sha biyu sun yi ittifaqi a kan cewa duk wanda ya yi musun


imamar xaya daga cikin imamai, ko ya musanta abinda Allah Maxaukaki ya


wajabta masa na yi musu biyayya, to shi kafiri ne, vatacce, wanda ya


cancanci ya dauwama a wuta.”1


Wani babban shehinsu mai suna Abul Qasim Almusawi Alkhu’i


yana faxi, “Babu wata tantama dangane da kafircinsu (yana nufin Ahalus


Sunna); saboda musun wilaya da imamai, kai ko da xaya daga cikinsu, yana


wajabta kafirci da zindiqanci.”2


Har yau, wani malamin nasu da ake kira Muhsin Al’muallim, yana


cewa, “Ra’ayi mafi bayyana shi ne cewa nasibi yana cikin hukuncin kafiri,


1 Biharul Anwar na Majalisi, bugun Mu’assasatu Daril Wafa, Bairut, 1403 B.H. 23/390.


2 A duba Misbahul Faqaha na Abul Qasim Alkhu’i, bugun Darul Hadi, Bairut, 1412 B.H. shafi na 11.


10


ko da yana bayyana kalmar shahada biyu, kuma ya yi imani da Ranar


Lahira.”1


Su Masu Dauwama Ne A Wuta


Rafilawa suna xauka cewa Ahalus Sunna za su dauwama a wuta.


Malaminsu, Almajalisi, ya ce, “Ka sani cewa sanya kalmar kafiri da


mushiriki a kan wanda bai yi quduri da imamar Sarkin Musulmi ba (yana


nufin Ali binu Abi Xalib) da imamai zuri’arsa, aminci ya tabbata a gare su,


yana nufin cewa shi kafiri ne mai dauwama a wuta.”2 Irin wannan magana ta


gabata, daga shi wannan malamin, inda ya yi amfani da lafazin “wanda ya


cancanci dauwama a wuta.”


Wannan hukunci haka yake ko da mutumin bai nuna qiyayya ga


imamai da ‘yan Shi’a ba. Malaminsu Abdullahi binu Shabbar yana cewa,


“Amma sauran masu sava mana, waxanda ba su qulla gaba ba, ba su yi


taurin kai ba, ba su yi ta’assubanci ba, to ra’ayin wasu daga cikin malaman


Imamiyya, kamar su Sayyid Almurtali, shi ne cewa su kafirai ne a duniya da


lahira. Kuma ra’ayi mafi yawa, mafi shahara, shi ne cewa su kafirai ne masu


dauwama a wuta.”3


Sai mu dubi wannan nassi da kyau. Abinda yake nufi, matuqar dai


mutum bai yi imani da tafarkinsu ba, to shi kafiri ne mai dauwama a wuta,


ko da bai qulla gaba da imamai ba. Suna faxin wannan saboda sanin cewa


Ahalus Sunna suna nuna so da qauna ga Ali da Faxima da Hassan da


Hussaini, Allah ya qara musu yarda, da ma sauran zuri’arsu baki xaya.


Amma tunda yake ba su qi Abubakar da Umar ba, ba su barranta daga gare


su ba, to wannan so da suke wa Ali ba shi da amfani. Watau a taqaice idan


mutum bai saki tafarkin Sunna ya kama na Shi’a ba, to ko bai yi gaba da


‘yan Shi’a ba, bai nuna taurin kai ko ta’assubanci ba, to har yanzu dai shi


1 Duba Annasbu wan Nawasib na Muhsin Al’muallim, bugun Darul Hadir lil Diba’ah, Bairut, 1418 B.H. shafi


na 609.


2 Biharul Anwar na Majalisi, 23/390.


3 A duba Haqqul Yaqin fi Ma’arifati Usulin Din na Abdullahi binu Shabbar, bugun Darul Kitabil Islami,


Bairut, ba tarihi, 2/188.


11


kafiri ne. Watau ke nan, ko mutum ba ya gaba da ‘yan Shi’a, to su suna gaba


da shi.


Halaccin Jininsu


‘Yan Shi’a suna qudure halaccin jinin Ahalus Sunna, watau halas ne a


kashe su ba don wani laifi ba sai don zama Ahalus Sunna kawai. Malaman


Rafilawa masu yawa sun ruwaito wannan halaccin daga imamansu. Wani


mai ruwayarsu da ake kira Dawud binu Farqad ya ce: Na ce da Abu


Abdillahi (yana nufin Imam Ja’afar Sadiq), “Me za ka ce dangane da kisan


nasibi? Sai ya ce: Jininsa halal ne; sai dai ina jiye maka tsoro. Don haka idan


ka samu iko ka rusa masa gini a ka, ko ka nutsar da shi a ruwa, don kada a


samu shaida, to ka aikata haka. Sai na ce: To me kake gani dangane da


dukiyarsa? Ya ce: Ka yashe ta inda duk ka samu iko.”1


Halaccin Dukiyarsu


Kamar yadda jinin Ahalus Sunna ya halatta a addinin Shi’a haka nan


dukiyarsu halas ce. Nassin da muka kawo a sama daga imaminsu na shida,


Abu Abdillahi Ja’afar Sadiq, yana tabbatar da haka. Kuma imaminsu na


wannan zamani, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini, ya yi wani qarin bayani a


kan wannan nassi, ya ce, “Idan ka samu iko ka karvi dukiyarsa, karve ta ka


aiko mana da khumusi!”2 Wannan qarin bayani na Khumaini yana da


muhimmanci saboda yana nuna cewa aqidar halaccin jinin Ahalus Sunna da


dukiyarsu ba wai ‘yan Shi’a na da ne kawai suke qudure ta ba, a’a har da


‘yan Shi’a na wannan zamani.


1 A duba Ilalush Shara’i’i na Muhammad binu Ali binul Hussain wanda suke ma lakabi da Assaduq, bugun


Muassasatul A’alami, Bairut, 1408 B.H. shafi na 326. Kuma akwai riwayar a cikin Biharul Anwar na


Majalisi, 27/231 da Wasa’ilush Shi’a, 18/463.


2 Kashful Asrar na Sayyid Hussain Musawi, bugun Darul Iman, Masar, ba tarihi, shafi na 89.


12


Halaccin Mutuncinsu


Rafilawa suna qudure halaccin mutuncin Ahalus Sunna da yi musu


qazafi da keta irilinsu. Babban shaihinsu mai suna Abul Qasim Almusawi


Alkhu’i yana cewa, “Lallai ya tabbata cikin riwayoyi da (littafan) addu’o’i


halaccin la’antar masu sava mana, da wajabcin barranta daga gare su, da


yawanta zagi a kansu, da zargin su, da afkawa cikin irilinsu, watau yi musu


giba, domin su ‘yan bidi’a ne masu musun (aqidojinmu).”1


Cin mutucin Ahalus Sunna da la’antar su da zagin su da yi musu


qazafi ba wai kawai halas ba ne a wajen ‘yan Shi’a, a’a shi wata ibada ce da


suke neman kusanci ga Allah da ita, da kyakkyawan sakamako a Ranar


Lahira. Kuma ko da yaushe wanda ake ci wa mutunci xin ya fi girma a


addini, to ladan ya fi yawa. Wannan ya sa suka fi mayar da hankali wajen


cin zarafin Sahabbai, da la’antar su, da jifan su da miyagun abubuwa na


vatanci. Haka nan kuma, ba su qyale manyan malamai ba da qananansu tun


daga zamanin Tabi’ai har ya zuwa yau.


Ga misali, sun yi qazafi ga Sarkin Musulmi, Umar binul


Khaxxabi(RA), suka jefe shi da liwaxi. Malaminsu xan hayaqi, mai tsaurin


ra’ayi, Ni’imatullahi Aljaza’iri, ya ce, “Umar binul Khaxxabi ya kasance


yana da wani ciwo a duburarsa (idan ya motsa) babu abinda yake sanyaya


shi sai ruwan maza.”2 Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!


Haka nan, sun jefi Usman binu Affan(RA) da irin wannan mummunan


aiki. Ni’imatullahi Aljaza’iri, har yau, yana cewa, “Usman ya kasance yana


daudu, kuma ya zama ana wasa da shi.”3 Wannan shi ma jifa ne da liwaxi ga


wannan babban bawan Allah, tsarkakakke, mai kunya da kamun kai, surukin


Annabi, wanda Manzo(SAW) yake jin kunyar sa, kuma mala’iku ma suke


jin kunyar sa.


1 Misbahul Faqaha na Abul Qasim Alkhu’i, shafi na 11.


2 Al’anwarun Nu’umaniyya na Ni’imatullahi Aljaza’iri, 1/63.


3 Al’anwarun Nu’umaniyya, 1/65.


13


Ummul Muminina, A’isha, Allah ya qara mata yarda, wacce malamin


Shi’a, Ali Al’amili Albayali, yake kira Ummul Shururi(uwar sharruka!)1 ba


ta tsira ba daga qagen Rafilawa da qazafinsu. Har yau har gobe suna


gaskata, kuma suna maimaita, qazafin da munafukai suka yi mata a zamanin


Annabi(SAW), inda suka jefe ta da alfasha, wanda kuma Allah Maxaukaki


ya barrantar da ita, ya kuvutar da ita daga wannan zargi. Amma ‘yan Shi’a


ba su gamsu ba; ba su yarda da ayoyi goma sha takwas da Allah ya saukar a


cikin Suratun Nur ba domin barrantar da ita. Suna ganin waxannan ayoyi


mahaifinta Abubakar ne ya soka su cikin Alqur’ani don ya wanke sunan


xiyarsa, amma ba Allah ya saukar da su ba!


Don haka suke ci gaba da laqa mata wannan zargi. Har ma suna


faxin, idan Mahadinsu ya bayyana a qarshen zamani zai fito da ita daga


kabarinta ya tsayar mata da haddi.2 Kafircin da yake cikin wannan magana


ba’a voye yake ba. Domin kuwa, bayan qaryata Alqur’ani qarara, da qazafi


ga wannan babbar baiwar Allah, matar Annabi a duniya kuma matarsa a


aljanna, maganar har yau tana nuna suka da zargi ga Annabi(SAW) cewa shi


bai tsayar mata da haddi ba. Allah ya kiyashe mu tavewa!


Wannan xan misali ne kawai muka bayar don mai karatu ya gane wa


idanunsa yadda Rafilawa suka mayar da qazafi ga magabatan wannan


al’umma ibada. Da za mu bibiyi irin waxannan misalai na qazafi da qage,


mu tsamo su daga littafan malaman Shi’a, mu rattaba su a nan, da sai littafin


ya yi tsawo ainun.


Halaccin La’antar Su


‘Yan Sh’a suna qudure halaccin la’antar Ahalus Sunna da ma duk


wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu. Kuma Ahalus Sunna xin ba wai


kawai xaixekunsu da gama-garinsu ba, a’a har da shugabanninsu da


magabatansu, kama tun daga Sahabban Annabi(SAW) har ya zuwa ko wane


1 A cikin littafinsa, Assirudul Mustaqim ila Mustahiqqi Attaqdim, bugun Madba’atul Haidari, Bairut, ba


tarihi, 3/161.


2 A duba Tafsirul Kummi na Ali binu Ibrahim Alkummi, bugun Darul Kitab, Kum-Iran, 1387 B.H. 2/377.


14


qaramin Musulmi da yake rayuwa a yau. A haqiqa ma, la’antar da suke wa


Sahabbai ba sa yi wa qananan Musulmi irinta.


Ruwaya ta gabata, a baya kaxan, daga shaihinsu Alkhu’i inda yake


cewa, “Lallai ya tabbata cikin ruwayoyi da (littafan) addu’o’i halaccin


la’antar masu sava mana…” Wannan shi ne hukuncin wanda duk yake sava


musu, watau ba ya bin tafarkinsu na Rafilanci. Su kuwa Sahabbai,


musamman manya-manyansu kamar Abubakar da Umar da Usmanu da


A’isha da Hafsa, Allah ya qara musu yarda, to su la’antar su ibada ce wacce


ake samun lada mai tarin yawa da ita.


Akwai ruwayoyi masu yawa a littafan Rafilawa da suke nuna ladan


la’antar Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda. Ga xaya daga


cikinsu:


Mulla Kazim, wanda yake mashahurin malami ne na Shi’a, ya karvo


ruwaya, yana dangana ta bisa qarya ga Ali Zainul Abidin binul Hussain binu


Ali binu Abi Xalib. Ya ce, Abu Hamza Althumali ya karvo daga Ali Zainul


Abidin ya ce, “Wanda ya la’anci Jibtu da Xagutu (yana nufin Abubakar da


Umar) la’ana guda, Allah zai rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare


masa zunubi dubu sau dubu kuma ya xaukaka masa daraja dubu sau dubu


saba’in. Kuma wanda ya la’ance su da yammaci la’ana guda za’a rubuta


masa kamar haka. (Mai ruwaya) ya ce: Sai shugabanmu Ali binu Hussaini


ya wuce (bayan ya faxi wannan magana, ni kuma) sai na shiga wurin


shugabanmu Abu Ja’afar Muhammad Albaqir na ce masa: Ya shugabana,


wata magana ce na ji daga mahaifinka. Sai ya ce: Faxe ta mu ji, ya kai


Thumali. Sai na maimaita masa maganar. Sai ya ce: Haka take, Thumali.


Ko kana so in yi maka qari? Sai na ce: E, ya shugabana. Sai ya ce: Wanda


ya la’ance su la’ana guda a ko wace safiya ba za’a rubuta masa zunubi ba a


15


wannan wunin har yammaci, kuma wanda ya la’ance su la’ana guda da


yammaci ba za’a rubuta masa zunubi ba har ya wayi gari.”1


Wannan ya sa malaman Rafilawa suka wallafa addu’o’i na


musamman don la’antar Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda,


waxanda ‘yan Shi’a suke maimaitawa safe da yammaci, da kuma a bayan


salloli na farilla, kamar yadda Musulmi suke wurdi da lazimi. Mafi shahara a


cikin waxannan addu’o’i ita ce addu’ar nan da suke kira Du’a’u Sanamai


Quraishin, watau Addu’ar Gumakan Quraishawa Biyu (suna nufin Abubakar


da Umar).2


Har yau, akwai wata addu’ar la’ana mai lugude, wacce ta qunshi


la’antar magabata guda tara, waxanda suka haxa da Sahabbai da Tabi’ai,


tare da maimaita la’ana ga Umar sau tara. Ga yadda lafazin addu’ar yake:


Allahumma il’an Umara, thumma Ababakarin wa Umara, thumma


Usmana wa Umara, thumma Mu’awiyya wa Umara, thumma Yazid wa


Umara, thumma Ibna Ziyadin wa Umara, thumma Ibna Sa’adin wa Umara,


thumma Shamran wa Umara, thumma Askara hum wa Umara. Allahumma


il’an A’ishata wa Hafsata wa Hindan wa Ummal Hakam. Wal’an man radiya


bi af’ali him ila yaumil qiyamah.3


Ga ma’anar addu’ar: Ya Allah ka la’anci Umar, sa’an nan Abubakar


da Umar, sa’an nan Usmanu da Umar, sa’an nan Mu’awiyya da Umar, sa’an


nan Yazidu da Umar, sa’an nan Ibnu Ziyad da Umar, sa’an nan Ibnu Sa’ad


da Umar, sa’an nan Shamru da Umar, sa’an nan Askar nasu da Umar. Ya


Allah ka la’anci A’isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam, kuma ka


la’anci (duk) wanda ya yarda da ayyukansu har ya zuwa ranar Alqiyama.


Wannan babbar addu’a ta ‘yan Shi’a tana bukatar darasu. Da farko dai


bari mu bi sunayen da suka zo a cikinta domin mu san su waye. Abubakar da


Umar da Usmanu da Mu’awiyya, Allah ya qara musu yarda, ba sa bukatar


bayani; kowa ya san su. Haka nan A’isha da Hafsa. Yazidu kuwa shi ne xan


1 A duba Ajma’ul Fala’ih na Mulla Kazim, 513.


2 Domin ganin wannan addu’a, sai a duba littafin Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a da Aqidojinsu, babin Aqidar


‘Yan Shi’a Dangane da Sahabbai.


3 A duba La’ali’ul Akhbari na malaminsu Muhammad Attursirkani, bugun Qum, Iran, ba tarihi, 4/92.


16


Mu’awiyya wanda ya gaje shi a mulkin daular Musulunci, kuma wanda a


zamaninsa ne aka kashe Hussaini(RA). Ibnu Ziyad shi ne gwamnan Kufa a


zamanin mulkin Yazidu, kuma rundunarsa ce ta kashe Hussaini(RA). Shi


kuwa Ibnu Sa’ad (sunansa Umar binu Sa’ad binu Abi Waqqas) shi ne


kwamandan rundunar da ta kashe Hussaini(RA).1 Shamru ban san shi ba;


ban gane wanda suke nufi da shi ba. Ga al’adar Rafilawa idan suka yi amfani


da kalmar Askar to A’isha suke nufi da ita, saboda raqumin da ta hau a


yaqin Jamal sunansa Askar. Kuma da yake an ambace ta da suna a cikin


addu’ar, muna iya xauka cewa ita ma an ninka mata la’ana ne saboda


tsananin qiyayya, kamar yadda aka ninninka wa Umar. Hindu kuwa ita ce


mahaifiyar Mu’awiyya(RA) kuma Ummul Hakam ita ce kakar Marwan


binul Hakam, uban yawancin khalifofin Banu Umayya, ciki har da Umar


binu Abdil’aziz khalifa mai adalci, Allah ya yi masa rahama.


Dalilin la’antar waxannan manyan bayin Allah a wajen ‘yan Shi’a


abu ne mai sauqi. Su dai Abubakar da Umar da Usmanu, Allah ya qara


musu yarda, laifinsu a wajen Rafilawa shi ne wai sun hana Ali binu Abi


Xalib khilafa, kuma sun hana ma Faxima(RA) gado na gonar da mahaifinta


Annabi(SAW) ya bari. Ita kuma A’isha(RA) ta yi faxa da Ali a Yaqin Jamal.


Hafsa(RA) ba ta yaqi Ali ba, kuma ba ta yi ma Faxima kome ba. Don haka


muna iya xauka cewa wata qila qiyayyar ubanta, Umar binul Khaxxabi, ce


ta nashe ta, ta ja mata wannan la’ana. Mu’awiyya kuwa, Allah ya qara masa


yarda, shi ne uban masu laifi, a ganin ‘yan Shi’a, domin shi ya yaqi Ali


kuma ya tankwave masa khilafa a bayan da ya same ta. Kuma wannan


babban laifi nasa shi ya shafi mahaifiyarsa, Hindu. Ummul Hakam, kakar


Marwan binul Hakam, ‘yan Shi’a suna xauka cewa jikanta, Marwan, shi ne


ya zuga Usmanu ya yi gaba da Ali. Kuma ga shi jikokinsa sun yi ta more


mulki, suka hana jikokin Ali xanawa. Su kuwa Yazid da Ibnu Ziyad da Ibnu


Sa’ad su suka kashe Hussaini(RA). Wannan ita ce aqidar ‘yan Shi’a da


1 Domin bayanin rawar da Yazidu da Ibnu Ziyad da Ibnu Sa’ad suka taka wajen shahadar Hussaini(RA) a


Karbala, sai a nemi littafinmu Wa Ya Kashe Hussaini? bugun Zomo Press, Kaduna, 2010.


17


fahimtarsu, kuma ita ta sa suke la’antar waxannan manyan bayin Allah ba


dare ba rana.1


To sai dai shin ko mai karatu ya san don me aka yi ma Umar(RA)


luguden tsinuwa da la’ana a cikin wannan addu’ar? Me ya sa aka fara la’anar


da shi, kuma aka yi ta maimaita sunansa tare da sauran? Amsar wannan


tambaya dogon labari ne, amma muna iya taqaice shi da cewa, a cikin


Sahabban Annabi kaf, kai a cikin wannan al’umma duka, kai a cikin bil


Adama baki xaya tun daga Annabi Adamu har ya zuwa yau, kai a cikin


halitta dukkaninta, mutum da aljan, ba wanda ‘yan Shi’a suka fi qi kamar


Sayyidina Umar, Allah ya qara masa yarda.2 Don me? Saboda ya rushe


daular kakanninsu Majusawan Farisa, ya maye makwafinta da daular


Musulunci. Wannan shi ne laifinsa wanda ‘yan Shi’a ba za su tava yafe


masa ba har abada!


Su Najasa Ne


‘Yan Shi’a suna qudure cewa Ahalus Sunna najasa ne. Malamansu


masu yawa sun tafi a kan haka, kamar Ni’imatullahi Aljaza’ir3 da Muhsin


Almu’allim.4 Kuma a kan wannan suka gina hukuncin haramcin amfani da


duk abinda mai bin tafarkin Sunna ya yi amfani da shi, kamar akushinsa da


tulunsa da randarsa da qore ko qoqunansa, da sauransu, kamar yadda za mu


gani a nan gaba kaxan, in Allah ya yarda.


Sun Fi Kare Najasa


A ganin Rafilawa, Ahalus Sunna ba wai kawai su najasa ba ne, a’a


najasarsu ma tana da tsanani, har ta fi ta kare. Wani mai ruwayarsu da ake


1 Domin darasun ra’ayin Ahalus Sunna dangane da wannan aqida da fahimta ta Rafilawa, sai mai karatu ya


nemi littafan Kaddara Ta Riga Fata na Muhammad Mansur Ibrahim da Wa Ya Kashe Hussaini? na Umar


Labdo.


2 Duba abinda suka fadi dangane da shi a cikin littafinmu Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a.


3 A cikin littafinsa, Al’anwarul Nu’umaniyya, 2/307.


4 A cikin littafinsa, Annasbu wan Nawasib, shafi na 609.


18


kira Ibnu Abi Ya’afur ya ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi


Ja’afar Sadiq, wai ya ce: “Na hore ka kada ka yi wanka da ruwan banxakin


wanka na haya domin tana yiwuwa a sami ragowar ruwan Bayahude ko


Banasare ko Bamajuse ko Nasibi mai gaba da mu Ahalul Baiti, kuma shi


(Nasibi) shi ne mafi sharrinsu. Lallai Allah mai girma da xaukaka bai halicci


wani abin halitta ba wanda ya fi kare najasa. Kuma lallai Nasibi mai gaba da


mu Ahalul Baiti ya fi shi (karen) najasa.”1


Wannan shi ne matsayin masu bin tafarkin Sunna, a idanun ‘yan


Shi’a. Kare ma ya fi su; saboda haka idan suka kira su zuwa ga haxin kai, ko


‘yan uwantaka, to a haqiqa isgili ne kawai suke yi. Amfani suke so su yi da


su don su cimma manufarsu ta yaxa gubarsu a tsakanin jama’a. Allah ya isar


mana sharrinsu.


Su Shegu Ne, ‘Ya’Yan Karuwai


‘Yan Shi’a suna xaukar Ahalus Sunna a matsayin shegu, ‘ya’yan zina,


kuma ‘ya’yan karuwai. Wannan shi ne faxin bakinsu, ba qage ne ake musu


ba. Wani mai ruwayarsu da ake kira Ali binu Asbax ya karvo daga


imaminsu na shida, Ja’afar Sadiq, wai ya ce: “Lallai Allah mai girma da


xaukaka yana fara duban masu ziyarar kabarin Hussaini binu Ali(AS) da


yammacin (ranar) Arafa. (Mai ruwaya ya ce:) Sai na ce: Kafin ya dubi masu


tsayuwar Arafa?! Ya ce: E. Na ce: Yaya haka?! Ya ce: Saboda a cikin


waxancan (masu tsayuwar Arafa) akwai ‘ya’yan zina, amma a cikin


waxannan (masu ziyarar kabarin Hussaini) babu ‘ya’yan zina.”2


Sai mai karatu ya dubi wannan hadisi na Rafilawa da idanun basira.


Banda qazafi da aka yiwa taron Musulmi mafi girma a duniya kuma a rana


mai alfarma, har yau hadisin xoyin Majusanci na tashi daga cikinsa. Domin


idan aka dubi hadisin da kyau, za’a ga yana yaqar xaya daga cikin shikashikan


Musulunci guda biyar, watau Hajji, wanda yake nuna qarfin Musulmi


1 A duba Annasbu wan Nawasib na Muhsin Almu’allim, shafi na 609.


2 A duba Biharul Anwar na Majalisi, bugun Mu’assasatu Daril Wafa, Bairut, 1403 B.H., Babin Falalar Ziyarar


Hussaini a ranar Arafa da Idi Biyu, 101/85.


19


da haxin kansu. Waxannan abubuwa kuwa, watau qarfin Musulmi da haxin


kansu, yana cikin abinda Majusawa waxanda suka yafa mayafin son Ahalul


Baiti, ba sa qauna. Saboda haka wannan hadisi na ‘yan Shi’a yake kira da a


bar taron Arafa kuma a bar taron Idi, aje ziyarar kabarin Hussaini! Muna


roqon Allah ya turmuza hancin masu yiwa addinin Annabi


Muhammad(SAW) zagon qasa.


Kuma ba wai kawai Ahalus Sunna ‘yan Shi’a suke yiwa qazafi da


cewa su shegu ba ne, a’a har da sauran Musulmi duka waxanda ba sa bin


tafarkinsu. Mai ruwayarsu, Abu Hamza, ya karvo daga imaminsu na biyar,


Abu Ja’afar Muhammad binu Ali binu Hussain binu Ali binu Abi Xalib, wai


ya ce: “Na rantse da Allah, ya Abu Hamza, mutane duka ‘ya’yan karuwai ne


in banda ‘yan Shi’armu.”1


Mai karatu dubi wannan katovara, kuma ka dubi yadda aka dangana ta


ga babban bawan Allah, jikan Annabi(SAW). Ya Ubangiji, muna shaidawa


cewa dukkan ruwayoyin Maguzanci da fajirci da malaman Shi’a suke


dangana wa zuri’ar Annabinka, qarya ce tsagwaronta.


Hukuncin Garuruwansu


‘Yan Shi’a suna qin garuruwan Ahalus Sunna da biranensu, kuma na


farkonsu su ne Makka da Madina. Mai ruwayarsu, Abu Basir, ya ruwaito


daga imaminsu na shida, Ja’afar Sadiq, wai ya ce: “Lallai mutanen Makka


suna kafircewa da Allah a fili kuma mutanen Madina sun fi su mugusci.


Mutanen Madina sun fi mutanen Makka zama miyagu ninki saba’in.”2


Qin Biranen Makka da Madina masu tsarki aqida ce zaunanniya a


tafarkin Shi’anci. Kuma ba wani abu suke qi ba a waxannan birane sai


masallatan nan masu alfarma waxanda su ne tushen Musulunci. Wannan ya


sa suka ruwaito cewa idan Mahadinsu ya bayyana zai rushe su. Babban


malaminsu, Muhammad Baqir Almajalisi, ya ruwaito kamar haka, “Lallai


1 A duba Arraudatu minal Kafi na Kulaini, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Bairut, 1375 B.H., 8/285.


2 A duba Al’usul minal Kafi na Kulaini, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Bairut, 1388 B.H., 2/410.


20


Mahadi zai rushe Masallaci mai Alfarma har sai ya mayar da shi ga


harsashensa. Kuma zai rushe Masallacin Annabi zuwa harsashinsa.”1


Waxannan ruwayoyi, banda kasancewarsu qarya ce da aka lanqayawa


imamai, kuma suna nuna mugun nufin ‘yan Shi’a da matuqar qiyayyarsu ga


addinin Musulunci, kamar yadda suke fallasa asalinsu na Majusanci wanda


suka lulluve da mayafin son Ahalul Baiti.


Kuma kada mai karatu ya xauka cewa wannan aqida ta qin Makka da


Madina tsohuwar aqida ce ta Rafilawan farko, kuma a yanzu ta mutu. A’a,


wannan aqida tana nan da ranta a cikin zukatan shugabannin ‘yan Shi’a na


wannan zamani da mabiyansu. Shaida ita ce abinda Sayyid Hussaini Musawi


ya ruwaito daga Khumaini yana cewa, “Sayyid Hussain, lokaci ya yi na


zartar da wasiyyar imamai…. Za mu shafe Makka da Madina daga doron


qasa saboda waxannan birane biyu sun zama mafakar ‘yan Wahhabiyya.”2


Sa’an nan, ba Makka da Madina kaxai ‘yan Shi’a suke qi ba. Akwai


wasu muhimman qasashen Musulunci da suke cikin jerin wuraren da suke


qi. Waxannan sun haxa da Misira da Dimashqa da Basra. Sun lanqaya


ruwaya ga Annabi(SAW) shi da kansa, suka ce wai ya ce, “Kada ku doshi


Misira, kada ku yi nufin zama a cikinta.”3 A wata ruwayar kuma suka ce wai


Ali binu Abi Xalib(RA) ya ce dangane da Misira, “Kada ku ci abinci a cikin


akusanta kuma kada ku wanke kawunanku da kwatarniyoyinta; domin yin


haka yana gadar da qasqanci kuma yana tafi da kishi.”4


Babu shakka wannan ruwaya ta Rafilawa dangane da Misira qarya ce


tsagwaronta. Abinda aka sani shi ne cewa Annabi(SAW) ya yi wasiyya da a


kyautatawa mutanen Misira, kamar yadda ya inganta a ruwayar Imam


Muslim da waninsa. Innar Muminai, Ummu Salama(RA) ta ruwaito cewa,


Annabi(SAW) ya yi wasiyya ga al’umma a lokacin rasuwarsa, ya ce, “Ina


gam muku da Allah dangane da Qibxawan Misira. Lallai ku da sannu za ku


1 A duba Biharul Anwar na Majalisi, 52/338. Kuma har yau, akwai wannan ruwaya a cikin Kitabul Gaiba na


babban malaminsu, Abu Ja’afar Muhammad binu Hassan Aldusi, shafi na 282.


2 A duba Kashful Asrar na Sayyid Hussain Musawi, bugun Darul Iman, Iskandariyya, 2002, shafi na 91.


3 Biharul Anwar na Majalisi, 40/211.


4 Biharul Anwar, 40/211.


21


yi rinjaye a kansu, kuma za su zame muku tattali da taimako wajen xaukaka


addinin Allah.”1


A wani hadisin kuma ya ce, “Lallai ku za ku buxe Misira (watau za ku


ci ta da yaqi), kuma ita qasa ce da ake ambaton qiraxi a cikinta. Idan kuka


buxe ta, to ku kyautata wa mutanenta domin lallai su suna da alqawari da


zumunta,” ko kuma cewa ya yi, “alqawari da surukuta.”2 Malamai suka ce


zumunta saboda Hajaru uwar Annabi Isma’il(AS) daga cikinsu take,


surukuta kuma saboda Mariya Alqibxiyya, kuyangar Annabi kuma


mahaifiyar xansa Ibrahim, daga cikinsu take.3


Waxannan hadisai ingatattu suna nuna falalar qasar Misira da falalar


mutanenta, savanin abinda ‘yan Shi’a suke da’awa.


Hukuncin Akusansu Da Tukwanensu


Ya gabata cewa Rafilawa suna qudure najasar Ahalus Sunna, kuma a


kan haka suka gina hukuncin amfani da abubuwan da Ahalus Sunna suka


tava na kayan amfani na yau da kullum. A baya kaxan maganarsu ta gabata


inda suka ruwaito daga Ali binu Abi Xalib(RA) yana hani ga barin amfani


da akusan Misira da kwatarninta. A kan haka, dukkan kayan amfani na masu


bin tafarkin Sunna, kamar kwanuka da tukwane, kofuna da butoci, ludaya da


cokula, da sauransu, najasa ne kuma bai halasta xan Shi’a ya yi amfani da su


sai bayan tsaftacewa irin ta Shari’a, watau wanki wanda yake gusar da


najasa.


Shaixan Na Shafar Su A Lokacin Haihuwarsu


Malaman Shi’a suna qudure cewa, Shaixan yana shafar jira-jiran


Ahalus Sunna a yayin haihuwarsu. Kuma ga alama sun yi haka ne don su


1 Haithumi ya ambaci wannan hadisi a cikin Majma’uz Zawa’id, ya ce Dabarani ya ruwaito shi kuma masu


ruwayarsa adalai ne.


2 Imam Muslim ya fitar da hadisin a cikin Sahih nasa, da Imam Ahmad a Musnadinsa.


3 Imam Nawawi ya ambata wannan a cikin littafin Riyadus Salihin. Don karin bayani, duba littafinmu


Dangantaka Da Auratayya Tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai, shafi na 47-48.


22


gamsar da mabiyansu a kan cewa sharrin masu bin tafarkin Sunna asali gare


shi don yana farawa tun a sa’ar da suka shigo duniya. Wani mai ruwayarsu


da ake kira Abu Yahaya ya ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi


Ja’afar Sadiq, wai ya ce: “Babu wani abin haihuwa da za’a haifa face Ibilis


ya halarci haihuwarsa. Idan Allah ya san cewa shi xan Shi’armu ne, sai ya


tsare shi daga Shaixanin (ba zai tava shi ba). Idan kuwa ba xan Shi’armu ba


ne sai Shaixan ya kafa xan yatsansa a cikin duburarsa idan namiji ne sai ya


zamo lalatacce. Idan kuma mace ce sai ya kafa xan yatsansa a cikin farjinta


sai ta zama fajira. Wannan ya sa jariri yake kuka mai tsanani a yayin da ya


fito daga cikin mahaifiyarsa.”1


Malamai suka ce qaryar jahili tana rushe kanta da kanta. Shin jariran


Shi’a su ba sa kuka a yayin da aka haife su?


Abinda ya inganta dangane da kukan jariri a lokacin haihuwarsa shi


ne abinda Imam Muslim ya ruwaito dangane da falalar Annabi Isa (AS) da


mahaifiyarsa cewa Manzo(SAW) ya ce, “Babu wani abin haihuwa da za’a


haifa face Shaixan ya tsunkune shi, sai ya fashe da kuka saboda tsunkunin


Shaixan, banda Xan Maryamu da Mahaifiyarsa.”2 Watau su kaxai su ne


Shaixan bai tsunkune su ba.


Sallarsu Banza, Azuminsu Banza!


‘Yan Shi’a suna qudure cewa dukkan ibadojin Ahalus Sunna, kamar


sallah da zakka da azumi da hajji da sadakoki da sauran ayyukan alheri,


duka Allah ba zai karve su ba saboda ba su yi imani da imamai goma sha


biyu ba, kuma saboda ba su barranta daga azzalumai ba, watau Sahabban


Annabi(SAW).3


Saboda haka, masu bin tafarkin Sunna hukuncinsu xaya da kafirai:


sallarsu banza, azuminsu banza!


1 A duba Tafsirul Ayashi na Muhammad binu Mas’ud Al’ayashi, bugun Mu’assasatul Bi’itha, Qum-Iran,


1421 B.H., 2/398.


2 A duba Sahih Muslim, Kitabul Fada’ili, babu Fada’ili Isa, alaihis salam.


3 A duba Kisasul Anbiya na Ni’imatullahi Aljaza’iri, bugun Darul Balag, Bairut, 1417 B.H., shafi na 344.


23


Rayuwarsu Banza, Mutuwarsu Banza!


Mai ruwayar Rafilawa, Abdullahi binu Sinan, ya tambayi imaminsu


na shida, Abu Abdillahi Ja’afar Sadiq, Allah ya rahamshe shi (kuma ya yi


masa sakayya qarerayin da ‘yan Shi’a suka laqa masa), dangane da Ahalus


Sunna masu jihadin kafirai idan aka kashe su a fagen fama, shin ana cewa


sun yi shahada? Sai ya ce: “Suna gaggautawa kansu mutuwa ne kawai.


Rayuwarsu banza ce, mutuwarsu banza. Na rantse da Allah ba mai shahada


sai xan Shi’armu, koda ya mutu a kan gadonsa.”1


To Falasxinawa da Musulmin Jos, sai ku aje makamanku; domin


jihadinku aikin banza ne, inji malaman Shi’a! Ku kuwa Rafilawa, ‘yan gata,


sai ku miqe qafa, ku yi barci da minshari, ku mutu a kan gadajenku, imamai


sun yarje muku!


Wajabcin Sava Musu


‘Yan Shi’a suna qudure wajabcin sava wa Ahalus Sunna a cikin


aqidoji da hukunce-hukunce da ra’ayoyi. Mai ruwayarsu, Ali binu Asbax, ya


ce: Na tambayi Imam Rida(AS) dangane da lamari ya bijiro mun a garin da


babu malamin Shi’a da zan tambaya fatawa. Sai ya ce, “Ka tambayi


malamin garin (wanda ba xan Shi’a ba) kuma hukuncin da ya faxa maka sai


ka yi aiki da savaninsa.”2


Wannan qa’ida ce daga cikin qa’idojin addinin Shi’a: savawa Ahalus


Sunna. Don haka idan xan Shi’a ya rasa sanin hukunci na wata mas’ala, ko


wani aiki na ibada, sai kawai ya duba yadda Ahalus Sunna suke yi sai ya


sava musu. Duk abinda suke yi, to savaninsa shi ne hukuncin gaskiya, shi ne


dai-dai. Wannan ya sa suka ce:


1 A duba Wasa’ilus Shi’a na Alhurrul Amili, bugun Mu’assasatu Ahlil Baiti, Bairut, 1413 B.H., 15/31.


2 A duba Uyun Akhbaar Rida na Ibnu Babawaihi Al’kummi, bugun Tehran-Iran, ba tarihi, 1/275.


24


Shiriya Na cikin Sava Musu


‘Yan Shi’a sun ruwaito daga imaminsu na takwas, Imam Ali binu


Musa, wanda suke ma laqabi da Rida, Allah ya jiqan sa, wai ya ce, “Abinda


duk ya savawa Amawa, to shiriya na cikinsa.”1


Kuma wannan babu mamaki, domin kuwa,


Allansu Dabam, Namu Dabam


Don savani tsakanin ‘yan Shi’a da Ahalus Sunna ya zama cikakke,


kuma kada a samu tsammanin haxin kai koda watan-wata rana, sai


malamansu suka yi shelar cewa: Ubangijinsu dabam, namu dabam,


Annabinsu dabam namu dabam, kamar yadda Khalifansu dabam namu


dabam.


Malaminsu xan hayaqi, Ni’imatullahi Aljaza’iri, ya ce, “Lallai mu ba


ma tarayya da su (yana nufin Ahalus Sunna) a Uabngiji ko Annabi ko


Imami. Domin su suna cewa Ubangijinsu shi ne wanda Muhammadu yake


Annabinsa, kuma Abubakar yake Khalifansa a bayansa. Mu kuwa ba ma ban


gaskiya da wannan Ubangijin, ko wannan Annabin. Mu muna cewa,


Ubangijin da Khalifan Annabinsa shi ne Abubakar, to mu ba Ubangijinmu


ba ne, kuma wannan Annabin ba Annabinmu ba ne.”2


Imam Khumaini ma ya yi irin wannan magana a cikin littafinsa,


Kashful Asrari, wacce take nuna su ubangijin da suke bautawa dabam yake


da Ubangijin Ahalus Sunna. Ya ce, “Mu muna bauta wa ubangijin da muka


san cewa ayyukansa suna ginuwa a kan harsashin hankali kuma ba ya aikata


wani abu da yake sava wa hankali, ba ubangijin da yake gina gini


gawurtacce ba na allantaka da adalci da addini sa’an nan ya rusa shi da


hannunsa, ya ba da sarauta ga irin su Yazidu da Mu’awiya da Usmanu binu


Affan da sauran masu kama da su ‘yan wafce, kuma ba zai bayyana wa


1 A duba Atta’adul wat Tarjih na Khumaini, bugun Daru Nashri Athar Khumaini, Tehran-Iran, 1417 B.H.,


shafi na 171.


2 A duba Al’anwarun Nu’umaniyya, na Ni’imatullahi Aljaza’iri, 2/278.


25


mutane abinda ya kamata su yi ba a bayan Annabi, sai ya bari a assasa


zalunci da cuta.”1


Wannan magana ta Khumaini wataqila tana da xan shiga duhu kaxan.


Abinda yake nufi a taqaice su ba sa bautawa Ubangiji Allah wanda ya gina


gawurtaccen gini, watau Musulunci, kuma ya rusa shi da hannunsa tunda bai


faxa wa mutane su naxa Ali binu Abi Xalib khalifa ba a bayan


Annabi(SAW); amma ya qyale shugabancin Musulmi ya zama zave, don


haka ‘yan wafce, masu warwaso, irin su Mu’awiya, suka qwace mulkin


alhali ba su cancanta ba don haka sai suka assasa zalunci da cuta. Za’a lura


cewa Aljaza’iri ya ambaci Abubakar a yayin da Khumaini ya waske, ya


ambaci Mu’awiya da Usmanu a maimakon sa, koda yake ya qara da


ambaton “masu kama da su”.


To, ina Musulmi masu sassaucin ra’ayi? Ina masu kyakkyawar niyya,


da wayewa da rashin tsanani? Ina masu zargin wasu da cewa su ne masu


raba kan Musulmi? Ina ‘yan jaridarmu masu tallan Shi’a ga Musulmin


Nijeriya a cikin jaridunsu? Ga ra’ayin ‘yan Shi’a da aqidarsu dangane da


Ahalus Sunna da ma sauran Musulmi baki xaya waxanda ba sa bisa kan


aqidarsu. Idan a da ba ku sani ba, to a yanzu kun gani da idanunku. ‘Yan


Shi’a suna yekuwa da babbar murya: Lakum dinukum, wa liya din!


1 A duba Kasful Asrari na Khumaini, shafi na 142.



Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC