Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 9


Aqidar Khumaini


da


Koyarwarsa


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


Gabatarwa


‘Yan Shi’ar Nijeriya qarqashin jagorancin Zakzaki sun daxe suna musa


cewa su ‘yan Shi’a ne. Sun kwashe shekaru da yawa, duk sa’ad da aka ce suna yin


Shi’a sai su ce ana yi musu qazafi, ana vata musu suna. Su ba sa yin Shi’a;


gwagwarmaya kawai suke yi.


A yanzu kuma da suka fito fili suna amsa sunan Shi’a, sai suke cewa su


Shi’a mai sassauci suke yi. Su kan ce, su Shi’a Imamiyya suke yi, ba Gulatu ba


masu tsaurin ra’ayi. Ba sa amincewa da abinda malamai da masu bincike suka


tabbatar cewa, a yanzu babu sauran Shi’a mai sassauci, kuma da xai Shi’a


Imamiyya ‘Yan Dozin ba su tava zama masu sassauci ba.


A haqiqa tun zamanin daular Safawiyya, a lokacin da ‘yan Shi’a a qarqashin


inuwar wannan daula suka shi’antar da qasar Iran da qarfin tuwo, suka kore Ahalus


Sunna daga qasar, Imamiyya ta yasar da duk wata sifa ta sassauci, ta rungumi


tsauri da guluwwi. Daga wannan lokaci zuwa yau, babu wata aqida mai tsauri


wacce ‘yan Shi’a Imamiyya ba su qudure ba.


Da yake muhawararmu da ‘yan Shi’a a ilmance muke yin ta, kuma a ruwan


sanyi, sai muka ga ya dace mu kawo Aqidar Imam Khumaini da Koyarwarsa a


matsayin hujja yankakkiya cewa ‘yan Shi’ar Nijeriya ba Shi’a mai sassauci suke yi


ba, a’a mai tsauri suke yi, kuma mai tsanani.


Abu ne da aka sani cewa, Shi’a ta shigo Nijeriya ne a sakamakon juyin juya


hali na qasar Iran wanda Khumaini ya jagoranta, kuma ‘yan Shi’ar qasar nan, ciki


har da madugunsu Ibrahim Alzakzaki, sun aro aqidojin Shi’a ne daga qasar ta Iran.


‘Yan Shi’ar qasar nan baki xayansu ba sa voye biyayyar su ga Khumaini, kamar


yadda ba sa voye cewa shi jagoransu ne wanda suke koyi da koyarwarsa.


Kuma koda yake muna sane da cewa akwai qarancin karatu a qasar nan,


saboda haka mutane da yawa, ciki har da ‘yan Shi’a, tana yiwuwa ba su tava


karanta ko xaya daga cikin littafan Khumaini ba, amma aqalla sun san hotunansa,


kuma suna ganin hotunan a fadar Zakzaki dake Zariya da kuma gidajen magoya


3


bayansa. Wannan ya isa hujja cewa su mabiyansa ne, masu koyi da shi. Domoin


kamar yadda hoton Shaihu Ibrahim Inyas a wajen mutum yake nuna cewa shi xan


Tijjaniyya ne mai aqidar Faila, haka nan hoton Khumaini a wajen mutum yake


tabbatar da cewa mutumin xan Shi’a ne mai riqo da aqidar Khumaini da


koyarwarsa.


To, mece ce aqidar Khumaini kuma ya koyarwarsa da ra’ayoyinsa suke?


Wannan tambaya ita ce wannan taqaitaccen littafi zai amsa, in Allah ya yarda.


Kuma amsar, kamar yadda muka saba a cikin dukkan littafanmu da lakcocinmu, za


ta fito daga littafan da Khumaini ya rubuta da hannunsa, kuma magoya bayansa


suke yaxa su da kansu, kafin juyin juya halin da ya jagoranta da bayansa. Kuma


waxan nan littafai a yau gwamnatin qasar Iran ce take buga su, tana rabarwa


kyauta a qasashen duniya, domin yaxa waxan nan aqidoji da ra’ayoyi.


Da sannu mai karatu zai gani da idanunsa cewa, dukkan miyagun aqidun


Shi’a dangane da Tauhidi, da Alqur’ani, da Sahabbai, da Imama, da Taqiyya, babu


wacce Khumaini bai qudure ba. Haka nan, duk wani mugun nufi ga al’umma, da


qiyayya ga sauran Musulmi waxanda ba ‘yan Shi’a ba, musamman Ahalus Sunna,


ba wanda Khumaini bai koyar ba a cikin littafansa. Daga bisani, wannan zai


tabbatar da cewa, da’awar ‘yan Shi’ar Nijeriya mabiyan Zakzaki cewa su Shi’a mai


sassauci suke yi, da’awa ce wacce aka gina ta imma a kan jahilci ko son zuciya.


Manufarmu da wannan littafi, in Allah ya yarda, ita ce bayanin gaskiya


domin mabiyan Shi’a, waxanda mun san da yawa daga cikinsu ba su sani ba, su


gane, kuma ya zama yankan hanzari a kansu, da sauke nauyi a namu vangaren.


Kuma gamon katarinmu bai zamo ba sai ga Allah, a gare shi muke dogaro, kuma


gare shi za mu koma ya yi hukunci a tsakaninmu cikin abinda muke savawa juna.


4


Babi Na Farko


Taqaitaccen Tarihin Khumaini


Sunansa Ayatullahi Ruhullahi Musxafa Ahmad Almusawi Alkhumaini.


Ruhullahi shi ne sunansa na yanka. Ayatullahi kuwa laqabi ne da ‘yan Shi’a suke


ba wa manyan malamansu da suka isa matsayin ijtihadi. A yayin da Musawi


danganawa ce ga Imamin Shi’a na bakwai, Musa binu Ja’afar mai rasuwa a


shekara ta 183 B.H. A kan haka, Khumaini yana xaukar kansa a matsayin jikan


Annabi (SAW) wanda ya fito daga Ahalul Baiti. Shi kuwa laqabin Khumaini


wanda ya shahara da shi, ya samo shi ne daga qauyen da aka haife shi, watau


Khumaina, wanda yake a kusa da birnin Qum, cibiyar malantar addini ta Iran.


Mahaifin Khumaini, Musxafa, malamin addini ne, kuma an kashe shi a


wajen rikici da masu mulkin gargajiya tun xansa Khumaini bai cika shekara xaya a


duniya ba. An ce ya rasa ransa sakamakon gwagwarmayar qwatowa qauyawa


haqqinsu daga hannun masu mulkin mulaka’u.


Kakan Khumaini, Ahmad, asalinsa mutumin Indiya ne, ya yi hijira zuwa


qasar Iran a shekara ta 1885 kuma ya zauni qauyen Khumaina inda aka haifi


mahaifin Khumaini, Musxafa.


Kuma koda yake iyayen Khumaini ba su daxe da barin qasar su ta asali ba,


watau Indiya, kasancewar har qasaitar Khumaini da juyin juya halinsa a shekara ta


1979 lokacin bai kai shekara xari ba, amma labarin tushensa da asalinsa ya vace


vat. Ba’a san takamaimai daga wane vangare na Indiya suka taso ba, kuma ba’a


tava sanin danginsu na can ba. Misali, shugaban Amurka baqar fata, Barack


Obama, wanda ubansa ya je Amurka ya haife shi a can kimanin shekaru sittin da


suka wuce, an san danginsa na qasar Kenya inda ya fito: kakarsa da yarsa da


goggonninsa da kawunnansa, da sauransu. Amma Khumaini ba’a tava cewa ga


danginsa na Indiya ba.


Wannan ya sa alamar tambaya kwamvaleliya a kan asalin mutumin, wanda


yake nacewa a kan cewa shi Shirifi ne jikan Annabi. Wani abin mamaki shi ne, har


5


bayan zamansa jagoran Iran mai wuqa da nama, babu wanda ya tava maganar


tushensa. Ko kafafen yaxa labarai na qasar, waxanda ya kamata a ce sun binciko


danginsa don a nunawa duniya su, kamar yadda kafafen yaxa labarai na Amurka


suka bankaxo asalin Obama tun yana takarar shugaban qasa, ba su tava cewa kome


ba dangane da wannan muhimmin batu. Wannan ya sa wasu masu bincike suke


zaton ko akwai lauje cikin naxi.


Kuma ba za’a ga laifin masu xari-xari da asalin Khumaini ba, saboda sanin


tushen mutumin da ya zama shugaba yana da muhimmanci ainun. Sau da yawa a


tarihin qasashen Musulmi, an sha duqunquno mutane, a ciccixa su, a kai su ga


matsayin jagoranci, sai daga bisani, bayan biri ya riga ya yi varna, a gane ashe ‘yan


barandan maqiya ne. Misali na kusa shi ne Musxafa Kamal Atatork, wanda ya


shugabanci qasar Turkiya, ya rushe khilafar Usmaniyya, ya shuka sharri mai yawa


wanda har yau al’umma ba ta murmure daga varnarsa ba, daga baya ta bayyana


cewa asalinsa Bayahude ne.


Ala kulli halin, har yau ba wanda ya tava cewa asalin Khumaini Bayahude


ne, amma kuma babu hujja a kan cewa shi Sharifi ne. Saboda haka, daga nan har


lokacin da mabiyansa suka bayyana asalinsa, duniya za ta ci gaba da xaukar


Khumaini a matsayin tsintacciyar mage.


An haifi Khumaini a shekarar 1320/1900 a qauyen Khumaina kuma babansa


ya rasu yana jariri, kamar yadda bayani ya gabata. Mahaifiyarsa ma ta rasu kafin


balagarsa, don haka ya taso yana maraya, qarqashin kulawar babban wansa. Ya


fara karatu a hauzar1 Ayatullahi Ha’iri a garinsu, kafin daga bisani ya tafi birnin


Qum inda ya karanta fannin Falsafa da Manxiqi. Bayan kammala karatunsa,


Khumaini ya ci gaba da koyar da waxan nan fannoni guda biyu.


Tauraron Khumaini ya fara walqawa a cikin shekarun 1960 yayin da ya soki


tsarin sarkin Iran na wannan lokaci, Shaha Muhammad Rida, dangane da rarraba


gonaki ga talakawa manoma. Wannan ya ba shi farin jini da haiba kuma ya shahara


a qasar baki xaya, har ya wayi gari ana lasafta shi a jerin malaman addini masu


gwagwarmaya, koda yake shi ba addinin tsintsa ya karanta ba.


A lokacin da sukansa ya yi yawa ga Shaha, kuma magoya bayansa


suka qaru, sai sarkin ya xaure shi a shekarar 1963. Wannan mataki da sarkin ya


1 Hauza a wajen ‘yan Shi’a kamar Zawiyya ne a wajen ‘yan darika.


6


xauka ya qara wa Khumaini farin jini kuma ya xaga matsayinsa, a lokacin da aka


riqa xaukar sa a matsayin mai jayayya da mulkin Shaha. Bayan sakinsa, sarkin ya


kore shi zuwa qasar Turkiya, inda ya zauna tsawon shekara guda, amma zaman bai


yi masa daxi ba saboda rashin maraba da shi daga vangaren masu mulkin qasar.


Wannan ya sa a shekarar 1965 Khumaini ya qara hijira zuwa qasar Iraqi, inda ya


zauni birnin Najaf, cibiyar malantar Shi’a.


A farkon zamansa a qasar Iraqi, Khumaini ya sassauta gwagwarmayarsa da


mulkin Shaha, saboda sharaxi da hukumomin qasar na wannan lokaci suka gindaya


masa. Amma a bayan zuwan mulkin Jam’iyyar Ba’ath ta Saddam Hussaini, wacce


dangantakarta da Shaha ta yi tsami, gwamnatin Iraqi ta sakar masa mara, inda ya ci


gaba da nashaxinsa na siyasa.


A zamansa na tsawon shekaru goma sha uku a Iraqi, Khumaini ya yi amfani


da zuwan dubunnan ‘yan qasarsa domin ziyarar ibada a Najaf da Karbala, ya riqa


saduwa da su, yana yaxa manufofinsa da ra’ayoyinsa a tsakaninsu. Waxan nan


masu ziyarar ibada, waxanda suke zuwa Iraqi a duk shekara, sun zama kamar


masinjoji waxanda suka riqa xaukar saqon Khumaini zuwa mutanen Iran,


musamman talakawa da xalibai da matasa da sauran su. Sannu a hankali sai


wannan ziyara ta xauki sabon salo, yayin da ta zama dama ga mabiyan Khumaini


domin sulalewa zuwa Iraqi, da saduwa da shi, da qarfafa dangantakar


gwagwarmaya. Wasu da yawa sun yi amfani da wannan dama suka tare xungurum


a Iraqi. Duka wannan nashaxi ya faru qarqashin inuwar mulkin jam’iyyar Ba’ath


mai bin tafarkin Gurguzu da sanya albarkarta.


Magoya bayan Khumaini sun yi yawa ainun a Iraqi, kuma da alama yawan


nasu ya fara zama matsala ta tsaro ga mahukuntan qasar. Babu abinda yake


tabbatar da wannan kamar kisan xan Khumaini na cikinsa, Musxafa, wanda aka ce


ya samu savani da wasu mabiyan ubansa masu tsaurin ra’ayi. Idan mabiyan


Khumaini sun kashe xan Khumaini wannan manuniya ce cewa suna iya kashe


waninsa.


A cikin shekarar 1978, hukumomin Iraqi sun kori Khumaini daga qasarsu.


Sai ya yi hijira zuwa birnin Faris na qasar Faransa, inda a cikin shekara guda ya


qarasa aikinsa na tumvuke gwamnatin Shaha.


7


A cikin shekarun qarshe na zaman Khumaini a Iraqi, huxubobin da yake


aikewa a kasset zuwa Iran da almajiransa masu zuwa su komo, sun rura wutar


rikici a qasar, wutar da zaluncin Shaha da danniyarsa suka qara mata ruruwa.


Wannan wuta ta ci gaba da ruruwa, yayin da ta kai ga juyin juya hali, a qarqashin


jagorancin mabiyan Khumaini da fuskantarwarsa, wanda ya tumvuke gwamnatin


Shaha. A cikin watan Fabrairu, 1979, Shaha Muhammad Rida ya arce daga Iran,


bayan mummunan tashin hankali da zubar da jini mai yawa. Kashe gari, Khumaini


ya sauka a qasar a mtsayin shugabanta mai wuqa da nama.


Wannan ya kawo haihuwar Jumhuriyar Musulunci ta Iran, qarqashin


jagorancin Khumaini, kuma a bisa doron aqidunsa, koyarwarsa da ra’ayoyinsa na


Shi’a.


8


Babi Na Biyu


Aqidun Khumaini da Ra’ayoyinsa


A gaba xayan rayuwarsa ta ilmi da gwagwarmaya, Ayatullahi Ruhullahi


Khumaini ya rubuta littafai guda takwas waxanda suka qunshi aqidojinsa da


ra’ayoyinsa da koyarwarsa. Haka nan ya rubuta qasidu da jawabai da huxubobi


masu yawa, waxanda kamar qarin bayani ne ga abinda littafan suka qunsa. Sai


kuma wasiyyarsa wacce ya rubuta kafin rasuwarsa amma ba’a yaxa ta ba sai bayan


mutuwarsa.


Waxan nan littafai sune:


1. Taharirul Wasila. Wannan littafi ne babba, yana cikin farkon abinda ya


rubuta, kuma ya tattauna masa’aloli da yawa na Fiqihu a cikinsa.


2. Kashful Asrari. Littafi ne matsakaici, kuma ya tattare aqidun Khumaini


dangane da Imama da Sahabbai da wasu batutuwa. Ya wallafa littafin da


harshen Farisanci kuma an buga shi sau da yawa saboda muhimmancinsa,


kafin juyin juya halin Iran da bayansa, kamar yadda aka fassara shi zuwa


harasa masu yawa, ciki har da harshen Larabci.


3. Alhukumatul Islamiyya. Wannan littafi ya qunshi ra’ayoyin Khumaini da


tunaninsa da koyarwarsa dangane da gwamnatin Musulunci, da ra’ayinsa na


Wilayatul Faqih, watau wakilcin malamai ga Imamai, da sauransu. Ana iya


xaukar littafin a matsayin jigon juyin juya halin da Khumaini ya jagoranta


da kuma tsarin mulkin gwamnatin da ya kafa.


4. Attaqiyya. Wannan littafin ya qunshi aqidar Taqiyya kamar yadda


Khumaini ya qudure ta. Yana da kyau mu ambata cewa, Khumaini ya yi


amfani da wannan aqida sosai wajen yaudarar malamai, shugabanni da


xaixekun Ahalus Sunna, musamman a bayan juyin juya halinsa (wanda ya


nuna cewa na Musulunci ne alhali a haqiqa na Shi’a ne), kamar yadda za mu


gani a nan gaba, in Allah ya yarda.


5. Zubdatul Ahkami. Ya tattauna wasu masa’aloli da batutuwa na Fiqihu.


6. Almakasibul Muharrama. Shi ma littafin Fiqihu ne.


9


7. Atta’adul wat Tarjih. Ya yi magana a kan fannin Hadisi kamar yadda aka


san shi a tafarkin Shi’anci.


8. Sirrus Salati. Wannan littafi sunansa yana nuna maulu’insa.


Qasidun Khumaini da ya rubuta sun haxa da qasidar Tafsirin Fatiha da


qasidar Jihadi, da sauransu. Jawabansa da huxubobinsa kuwa suna da yawa.


Yawancinsu an buga su a jaridu da mujallun duniya na qasashe dabam-daban, a


cikin harasa dabam-daban, kamar yadda ake buga jawaban shugabannin siyasa da


jagororin qasashe.


Abu na qarshe da Khumaini ya rubuta shi ne Wasiyyarsa. Wannan Wasiyya


tana da matuqar muhimmanci domin ta tattare xaurayar aqidojin Khumaini kuma


saboda ya rubuta ta a qarshen rayuwarsa; don haka duk abinda ta qunsa shi ne


abinda ya mutu a kai. Shi da kansa ya yi nuni a cikinta da cewa ya rubuta ta da


cikakken ‘yanci da gaba-gaxi, ba tare da tsoro ko kara ga kowa ba, saboda ya


rubuta ta alhali yana bakin kabarinsa.1


Waxan nan littafai, musamman guda uku na farko da kuma Wasiyyarsa, su


ne za mu dogara a kansu wajen bayanin aqidojin Khumaini da koyarwarsa. Kuma


mai karatu zai gamsu da cewa, babu abinda ya fi adalci irin a yi wa mutum hukunci


da abinda ya fito daga bakinsa, ko ya kattaba da hannunsa.


Aqidar Khumaini dangane da Qur’ani


Babu wani bambanci tsakanin aqidar Khumaini dangane da Alqur’ani da


aqidar sauran malaman Shi’a na zamanin da, da kuma na yanzu.2 Khumaini yana


qudure cewa, Alqur’anin da yake a hannun Musulmi a yau ba daidai yake ba,


kuma ba cikakke ba ne. An yi qari da ragi a cikinsa, kuma Sahabbai ne suka yi


wannan qari da ragin.


Sai dai shi Khumaini ba ya bayyana wannan aqida tasa a sarari a cikin


yawancin rubuce-rubucensa, a wani lokaci ma ya kan yi qoqarin qaryata ta. Kuma


wannan ba abin mamaki ba ne idan muka dubi matsayinsa na mai neman goyon


bayan jama’a don cimma burin siyasa, watau qaddamar da juyi da kafa gwamnati,


musamman da yake mutanen qasarsa da yawa Ahalus Sunna ne.


1 Duba Wasiyyar Khumaini, shafi na 93.


2 Duba littafi na 1 a wannan jerin.


10


Amma duk da haka, ya fito fili ya bayyana wannan aqida a wasu littafansa.


Misali a cikin littafin Kashful Asrari, yana cewa: “Tuhumar sauya (Attaura da


Linjila) da Musulmi suke wa Yahudawa da Nasara, irin wannan tuhuma ta tabbata


a kan Sahabbai.”1 Babu shakka wannan magana a bayyane take; domin ba’a


tuhumar Sahabbai da sauya Attaura da Linjila, sai dai a tuhumce su da sauya nasu


littafin-Alqur’ani.


Haka nan a cikin Wasiyyarsa, yana faxi kamar haka, “Ya kamata a ambata


cewa, abinda ya afka wa amanonin Manzon Allah (SAW) guda biyu na zaluncin


Xagutai, zalunci ne ga al’ummar Musulmi da ma bil Adama baki xaya, kuma abin


ya fi qarfin alqalami ya rubuta… Abinda ya faru ga Alqur’ani, wannan amana ta


Allah, da abinda Manzo ya bari, babbar musiba ce mai tayar da hankali, wacce ya


kamata a yi mata kuka da hawayen jini.”2


Abinda Khumaini yake nufi a nan da amanoni guda biyu da Annabi (SAW)


ya bari shi ne Alqur’ani da iyalin gidansa Ahalul Baiti, kuma zaluncin Xagutai


yana nufin zaluncin Sahabbai da mabiyansu. Don haka, tunda ‘yan Shi’a suna


xauka cewa Sahabbai sun kashe zuri’ar Annabi (SAW), kamar jikansa Hussaini,3


to zaluncinsu ga Alqur’ani zai zama shi ne sauya shi da vata shi.


Wani abu da yake qara tabbatar da matsayin Alqur’ani mai tsarki a wajen


Khumaini, shi ne imaninsa da “Qur’anin” Shi’a da suke kira Mushafu Faxima,


watau Kundin Faxima. Mushafu Faxima kishiyar Alqur’ani ne, wanda ‘yan Shi’a


suke quduri da cewa an yi wahayin sa ga Nana Faxima, Allah ya qara mata yarda,


kuma wai shi ne Qur’ani na gaskiya wanda Faxima ta yi shiftar sa kuma Ali, Allah


ya qara masa yarda, ya rubuta shi da hannunsa.4


Khumaini ya yi ban gaskiya da wannan littafi kuma, kamar yadda ya ce,


yana alfahari da shi. Ya ce, “Muna alfahari da cewa muna da Kundin Sajjadiyya da


Zaburar Iyalin Muhammadu da Kundin Faxima wanda Allah mai girma da


xaukaka ya yi wahayin sa ga Zahara’u yardajjiya.”5


1 Kashful Asrari na Khumaini, shafi na 114.


2 Wasiyyar Khumaini, shafi na 68.


3 Duba littafin Wa Ya Kashe Hussaini?


4 Duba littafi na 1 a wannan jerin.


5 Wasiyyar Khumaini, shafi na 68.


11


Wannan aqida ta cewa wai Allah ya yi wahayin wani littafi ga Nana Faxima,


ta warware aqidar da Alqur’ani ya zo da ita cewa babu wani da za’a yi wa wahayi


bayan Annabi (SAW), kuma tana nuna matsayin Khumaini na mai riqo da aqidojin


Gulatu masu tsananin ra’ayin Shi’a.


Aqidar Khumaini dangane da Annabi (SAW)


Allah Maxaukaki ya wajabta wasu haqqoqi a kan Musulmi dangane da


Manzonsa Muhammad (SAW), waxanda suka haxa da imani da shi, da shaidawa


da iyar da aikensa, da biyayya a gare shi, da taimakon sa, da gabatar da qaunarsa a


bisa qaunar kowa, da qudure cewa shi ne mafificin halitta baki xaya. Waxan nan


haqqoqi bayaninsu na cikin Alqur’ani da Sunna, kuma babu wani Musulmi da


yake da ja a kan su.


Sai dai maganganun Khumaini da rubuce-rubucensa suna nuni da cewa shi


bai yi ban gaskiya da waxan nan haqqoqi ba. Kai ma ana iya cewa bai yi imani da


annabtar Annabi ba, ko fifikonsa, ko isar da aikensa. Ga misalai:


1. Khumaini yana ganin cewa, Manzon Allah (SAW) bai yi nasara ba wajen


tabbatar da abinda domin sa aka aiko shi, watau shimfixa adalci. Yana ma ganin


cewa, dukkan Annabawa ba su ci nasara ba a wannan fage, kuma wanda zai yi


nasara kawai wajen tabbatar da adalci shi ne Imamin Shi’a na 12, watau Mahadin


Shi’awa wanda suke jiran bayyanarsa a qarshen zamani.1


Khumaini yana cewa dangane da haka: “Lallai Annabawa baki xaya sun zo


domin tabbatar da harsashen adalci a duniya, amma dukkaninsu ba su ci nasara ba.


Har Annabi Muhammad Cikamakin Annabawa, wanda ya zo domin gyara yanayin


bil Adama da tarbiyyar ‘yan Adam, bai yi nasara ba dangane da haka. Mutumin


kawai da zai yi nasara a cikin haka, ya kafa harsashen adalci a dukkanin sasannin


duniya da fagagen rayuwar xan Adam, shi ne Mahadi wanda ake sauraron


zuwansa.”2


Wannan magana abinda take nunawa, a zahiri, shi ne cewa Khumaini bai yi


imani da Annabi Muhammad (SAW) ba, amma ya yi imani da Iamam Fatalwa


(Mahadin Shi’a) wanda suka ce wai an haife shi tun kimanin shekaru dubu da xari


1 Domin ganin bayanin Mahadin ‘yan Shi’a, duba Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a.


2 Ya fadi haka a jawabinsa na Maulidin Mahadi, ranar 5 ga watan Sha’aban, 1400 B.H. (1980) kamar yadda mujallar


Arra’ayul Aam ta Kuwait, fitowar 17 ga watan Yuni, 1980, ta buga.


12


biyu (1,200) da suka shuxe, kuma yana nan da ransa a voye a cikin kogo, sa’an nan


zai dawo a qarshen zamani ya tabbatar da adalci a qarqashin inuwar daular


Shi’awa. Wannan yana tabbatar da matsayin Khumaini na vatacce, mai bin tafarkin


Shi’anci na guluwwi da tsanani da rashin sassauci.


2. Khumaini yana fifita Imamai a kan dukkan Annabawa ba da toge ko xaya ba.


Ga abinda ya ce dangane da haka: “Yana daga cikin abinda ya wajaba a qudure a


cikin mazhabarmu cewa, Imamanmu suna da matsayi wanda ba wani mala’ika


makusanci ko Annabi Manzo da yake isa gare shi.”1


Wannan magana a fili take cewa, Khumaini yana fifita Imaman Shi’a a kan


Annabawa, har da Annabi Muhammad (SAW), domin bai toge shi ba. Idan mai


karatu yana shakkun haka, to ya dubi wannan magana ta Khumaini: “Tabbas


Maulidin Imam Mahadi idi ne babba ga Musulmi wanda ya fi idin Maulidin


Annabi Muhammad.”2


Har yau, wani dalili mabayyani da yake nuna cewa, Khumaini yana fifita


Imamai a kan Annabi Muhammad (SAW) shi ne fifita qasar kabarin Imam


Hussaini, Allah ya qara masa yarda, a kan qasar kabarin Annabi (SAW). Ga abinda


ya ce, “Ba’a gwada ta (qasar kabarin Hussaini) da qasar kabarin waninsa, har da


kabarin Annabi (SAW) da sauran Imamai.”3


3. Khumaini yana fifita zamaninsa a kan zamanin Annabi (SAW) da mabiyansa


‘yan Shi’ar Iran a kan Sahabbai mabiyan Annabi. Ga abinda ya ce, “Ni ina faxi


gaba-gaxi cewa yanayin da mutanen Iran na wannan zamani suka sifantu da shi, da


talakawansu dodo-dodo, ya fi na mutanen Hijaz (qasar Larabawa) a zamanin


Manzon Allah (SAW).”4


Akwai ma’ana dake voye a nan. Ma’anar kuwa ita ce: Khumaini yana so ya


ce shi ya fi Manzon Allah (SAW) iya tarbiyyar mutane, kuma ya fi shi samun


nasarar kawo sauyi da juyi a rayuwar mutane, shi ya sa yanayin rayuwar mutanen


zamaninsa mabiyansa ya xara na mutanen zamanin Annabi (SAW) mabiyansa.


Shin Musulmi, wanda ya yi imani da Allah da Annabi (SAW), yana faxin irin


wannan magana?


1 Duba Alhukumatul Islamiyya na Khumaini, shafi na 52.


2 Duba Wasiyyar Khumaini, shafi na 47.


3 Duba Taharirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 2 shafi na 164.


4 Duba Wasiyyar Khumaini, shafi na 90.


13


Waxan nan misalai da muka kawo, waxanda akwai gomomi da xaruruwa


irinsu a cikin littafan Khumaini da jawabansa da huxubobinsa, suna nuna aqidar


Khumaini dangane da Manzon Allah (SAW) da annabtarsa da kuma sauran


Annabawa baki xaya da annabtarsu. Kuma a fili take cewa, mai irin wannan aqida


ba’a sifanta shi da sassauci, sai fa inda jahilci ya yi katutu, ko son zuciya ya riqe


ragama. Muna roqon Allah ya shirye mu, ya tsare imaninmu.


Aqidar Khumaini dangane da Sahabbai


Wanda yake da aqida dangane da Annabi (SAW) irin wacce muka zana a


sama, ba’a damuwa ko me ya qudure dangane da Sahabbai. Amma za mu kawo


aqidar Khumaini dangane da Sahabbai ne saboda har yau akwai ‘yan Shi’a a


Nijeriya waxanda suke musun cewa mutumin yana gaba da Sahabbai, ko yana


zagin su, ko yana kafirta su.


A haqiqa Khumaini, kamar ko wane xan Shi’a na da ko na wannan zamani,1


yana qin Sahabbai, Allah ya qara musu yarda baki xaya, qiyayya mai tsanani,


kuma yana zagin su, kamar yadda yake kafirta su, musamman manya daga cikinsu,


irin su Sayyidina Abubakar da Sayyidina Umar da Sayyidina Usman da Nana


A’isha da Nana Hafsa, da sauransu. Misalai a kan wannan ba su lasaftuwa a


littafan Khumaini da huxubobinsa da laccocinsa.


Khumaini yana qudure cewa, Sahabbai baki xayansu munafukai ne, ba su


shiga Musulunci ba sai don neman abin duniya da mulki. Wannan ya sa, a ganinsa,


da zarar rasuwar Manzon Allah (SAW) sai munafincinsu ya bayyana a fili, inda


suka sava wasiyyar Annabi (SAW) ta naxa Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara masa


yarda, a mtsayin Khalifa, suka naxa Abubakar maimakonsa.


Wannan ya sa Khumaini yake ambaton taron Sahabbai na Saqifatu Bani


Sa’ida inda suka zavi Abubakar a matsayin Khalifa da cewa shi ne tushen dukkan


sharri a tarihin Musulunci. Ga misali, yana cewa: “Dukkan savani da ya faru


tsakanin Musulmi a cikin al’amura duka, tushensa Saqifa. Ba don abinda ya afku


ba a wannan rana, da dukkan wannan savani a tsakanin Musulmi bai faru ba.”2


1 Duba littafi na 2 a wannan jerin.


2 Duba Kashful Asrar na Khumaini, shafi na 130.


14


Har yau, yana cewa, “Duk abinda Musulmi suke fama da shi a yau, ba kome ba ne


sai sakamakon ranar Saqifa.”1


Wannan matsayi na Khumaini dangane da taron Saqifa da zaven Abubakar


Khalifa, shi ne matsayin dukkan malaman Shi’a a ko wane zamani, kuma shi ne


tushen savani tsakanin aqidar Ahalus Sunna da aqidar Shi’a. A yayin da Ahalus


Sunna suke ganin taron Saqifa wata rahama ce daga Allah da ya ceci Musulunci da


ita, ya tabbatar da haxin kan Musulmi da xorewar Musulunci, su ‘yan Shi’a suna


ganin wannan taro da abinda ya wakkana a cikinsa na zaven Abubakar cin amana


ne da sava umarnin Annabi da bin son zuciyar wasu ‘yan tsuraru masu son xarewa


a karagar mulki. A kan haka, ‘yan Shi’a suka xauki matsayinsu na kafirta Sahabbai


baki xaya, in banda wasu ‘yan kaxan: uku ko bakwai.2 Khumaini yana kan wannan


matsayi daidai wa daida.


Aqidar Khumaini dangane da Abubakar da Umar


Khumaini yana qudure cewa Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda,


tun da farko sun shiga Musulunci ne da nufin biyan wasu bukatu na qashin kansu,


da burin xarewa kan karagar mulki bayan rasuwar Annabi (SAW), amma ba domin


imani da Allah da fatan sakamakon Lahira ba. Don haka yake faxi dangane da su,


“Waxan nan alaqarsu da Musulunci da Qur’ani ba ta zamo ba sai don kwaxayin


mulki da abin duniya. Kuma sun kasance suna amfani da Alqur’ani don cimma


manufofins munana.”3


Khumaini yana ganin Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda, suna


savawa Alqur’ani da gangan, suna wasa da addini, kuma suna halatta ko su


haramta abinda suka ga dama. Dangane da haka yake cewa, “Mu a nan babu


ruwanmu da Abubakar da Umar, da abubuwan da suka aikata na savawa


Alqur’ani, da wasa da addinin Allah, da abinda suka halatta ko suka haramta don


qashin kansu, da abinda suka tafka na zalunci a kan Faxima xiyar Annabi (SAW)


da ‘ya’yayenta. Amma muna tabbatar da jahilcinsu da hukunce-hukuncen Allah da


addini.”4


1 Kashful Asrar, shafi na 155.


2 Duba Bacin Tafarkin ‘yan Shi’a, babin akidar Shi’a dangane da Sahabbai.


3 Kashful Asrar, shafi na 112.


4 Duba Kashful Asrar na Khumaini, shafi na 126.


15


Wannan shi ne matsayin Abubakar da Umar, Allah ya qara musu yarda, a


wajen Khumaini. Matsayin yana nuna cewa su ba wai kawai kafirai ne munafukai


ba, a’a su maqiyan addine ne waxanda suka yi masa zagon qasa. Don haka,


addininsu da mabiyansu Ahalus Sunna ba ingantacce ba ne. Addini ingantacce shi


ne na masu sava musu ‘yan Shi’a.


Wannan ita ce aqidar Khumaini dangane da Sahabban Annabi (SAW) kuma


ita ce koyarwarsa da ya koyar ga dukkan mabiyansa da masu koyi da shi. Wannan


aqida da koyarwa ita ‘yan Shi’ar Nijeriya suke tallatawa a matsayin sassauci da


gwagwarmaya da juyin juya hali na Musulunci!


Aqidar Wilayatul Faqih


Wilayatul Faqih tsohuwar aqida ce a wajen malaman Shi’a da mabiyansu,


koda yake ba duka ba ne suka yarda da ita. Khumaini ya farfaxo da wannan aqida,


ya jaddada ta, ya raya ta, saboda ya hidimtar da ita wajen manufarsa ta tabbatar da


juyin juya hali da kafa gwamnati da xarewa a kan karagar wannan gwamnati a


matsayin shugabanta mai wuqa da nama.


Abinda aqidar Wilayatul Faqih take nufi a taqaice shi ne, ba wani zamani da


babu wani mutum da Allah ya naxa a cikinsa domin ya shiryar da mutane ta hanyar


bayyana musu hukunce-hukuncen Shari’a kamar yadda suke ba tare da tuntuve ko


kuskure ba. A zamanin Manzon Allah (SAW) shi ke xauke da wannan nauyi.


Bayan komawarsa ga Ubangiji, sai Sayyidina Ali binu Abi Xalib ya xauki nauyin a


matsayinsa na magajin Annabi. Shi kuma ya gadarwa babban xansa Hassan, daga


shi sai Hussaini, sa’an nan Ali xan Hussain. Haka abin ya kasance har zuwa ga


Imami na 12, watau Mahadin Shi’a, wanda ya fake a kogo kuma zai dawo ya


shugabanci ‘yan Shi’a a qarshen zamani.1


Vuyan Imami na 12 a cikin kogo a shekara ta 329 bayan Hijira, ya jawo


babbar matsala ga ‘yan Shi’a; domin a yanzu sun rasa mai shiryar da su, saboda shi


Imami na 12 bai bar magaji ma’asumi ba.


Sai dai malaman Shi’a ba su vata lokaci ba wajen warware wannan matsala


ta hanyar qirqiro matsayin Na’ibin Imamin da ya vuya, wanda zai xauki nauyin


aikinsa har lokacin da ya komo. Wannan matsayi shi ne matsayin Wilayatul Faqih.


1 A duba Asalus Shi’ati wa Usuluha na Muhmmad Hussain Aali Kashiful Gida, shafi na 76-77.


16


Amma wannan bai warware matsalar gaba xaya ba, saboda an riqa samun savani a


kan masu riqe wannan matsayi a zamuna dabam-daban, kasancewar su ba’a san


wanda ya gadar musu da matsayin ba. Kuma wannan savani shi ya sa wasu daga


cikin malaman Shi’a suka yi watsi da aqidar Wilayatul Faqih baki xaya.1


An yi ta ja-in-ja a kan wannan aqida a tarihin Shi’a tsakanin masu riqo da ita


da masu musun ta. Haka nan a tsakanin masu quduri da ita, an yi ta samun savani


na waye haqiqanin mai riqe da wannan matsayi a wani zamani na musamman,


domin sau da yawa malamai biyu ko sama da haka suna da’awar matsayin a lokaci


guda tare da cewa matsayin xaya ne. To a irin wannan yayi, sai wanda ya fi qarfi,


ko ya fi yawan mabiya, ya sha da matsayin, kwatankwacin irin abin nan da


Hausawa suke cewa, “Dokin mai baki ya fi gudu.”


Haka al’amarin ya yi ta tafiya har lokacin da Khumaini ya bayyana, ya fara


gwagwarmayarsa, kuma ya fahimci cewa wannan aqida za ta yi hidima ga


manufofinsa, sai ya rungume ta.


Khumaini ya yi aiki sosai wajen raya aqidar a yayin da ya rubuta littafinsa


mai suna Alhukumatul Islamiyya musamman don tabbatar da ita. Khumaini ya


rubuta cewa Imami na 12 dai bai mutu ba, yana nan a raye, haka nan haqqinsa na


jagorantar Shi’awa da ba su doka yana nan daram, kuma Wakilinsa ko Na’ibinsa


shi ne ke more wannan haqqi a maimakonsa.2 Bayan nasarar juyin juya halin Iran


na shekarar 1979, Khumaini ya yi shelar cewa shi ne Na’ibin Mahadi kuma an


tabbatar da aqidar Wilayatul Faqih a cikin kundin Tsarin Mulkin Iran.3


Khumaini ya yi amfani da wannan aqida wajen naxa kansa a matsayin sarki


mai iko ba iyaka, wanda maganarsa ita ce doka, kuma idan ya ajiye kara ba mai


tsallakawa, domin kamar yadda Rida Muzaffar yake cewa, “Faqihi na’ibin Imami


ne a lokacin vuyansa, yana da dukkan haqqoqi na Imami. Wanda ya ja da shi ya ja


da Imami, kuma wanda ya ja da Imami ya ja da Allah.”4 Khumaini ya yi amfani da


ra’ayin malaman Shi’a irin su Rida Muzaffar, ya tabbatar da shi a cikin littafinsa,


har ya yi qari a kai. Ga abinda yake cewa, “Babu shakka mun yi bincike dangane


da wannan maulu’i, watau Wilayatul Faqih, kuma ya bayyana gare mu cewa duk


1 Duba Nazariyyatu Wilayatil Faqih na Arafat Abdul Hamid, shafi na 23 da 41.


2 A duba Alhukumatul Islamiyya na Khumaini, shafi na 48.


3 Duba Kundin Tsarin Mulkin Jumhuriyyar Islama ta Iran, sakin layi na farko da na biyu.


4 A duba Aqa’idus Shi’atil Imamiyya na Rida Muzaffar shafi na 57.


17


abinda ya tabbata ga Manzo (SAW) da Imamai na haqqoqi shi ma ya tabbata gare


shi. Kuma babu kokwanto dangane da haka.”1


Wannan aqida ita ce jigon tsarin siyasar Iran a yau, kuma shi ne abu na farko


da aka ambata a kundin Tsarin Mulkin qasar (sakin layi na farko da na biyu) kafin


a ambaci Musulunci (wanda ya zo a sakin layi na goma sha biyu!). Wannan ya sa


Khumaini, kamar magajinsa a bayansa Ali Khamna’i, ya zama shi xaya tilo yana


sama da shugaban qasa da dukkan ‘yan majalisar qasa zavavvu da dukkan alqalan


qasa, ciki har da alqalin Kotun Qoli.


Mun kawo bayanin wanan aqida ne da matsayinta a wajen ‘yan Shi’a da


matsayinta a wajen Khumaini da kuma matsayinta a Tsarin Mulkin Jumhuriyyar


Islama ta Iran don mu tabbatarwa da maikaratu abubuwa kamar haka:


1. Imam Khumaini ba mai sassaucin ra’ayin Shi’a ba ne; shi mai tsananin


ra’ayin Shi’a ne wanda yake allantar da Imamai da wakilan Imamai.


2. Khumaini xan kama karyar addini ne, mai mulkin Fir’aunanci, gunki,


Xaguti, mai tsananin girman kai wanda ya bautar da al’ummarsa, kuma a


yau al’ummar tasa suke qoqarin bautar da Musulmin duniya ta hanyar yaxa


aqidojinsa da koyarwarsa, wani lokaci da qarfin tuwo, kamar yadda abin


yake faruwa yanzu haka a qasashen Iraqi da Siriya da Yaman.


3. ‘Yan Shi’ar Nijeriya qarqashin jagorancin Zakzaki, waxanda suke koyi da


Khumaini suna girmama shi suna xaukar sa a matsayin shugaba jagora,


imma jahilai ne ba su san Khumaini da aqidojinsa da koyarwarsa ba, ko


kuma vatattu ne waxanda Allah ya yi nufin halakar da su.


4. ‘Yan bokon Nijeriya, musamman ‘yan jarida da mabanka (ma’aikatan banki)


da likitoci da injiniyoyi, da sauransu, waxanda suke katsalandan a harkar


addini suna tallan Shi’a, imma jahilai ne ba su san abinda suke yi ba, wa


imma munafukai ne suke fakewa da Turancinsu domin vatar da mutane.


1 Alhukumatul Islamiyya na Khumaini, shafi na 115.


18


Babi Na Uku


Fiqihun Khumaini


Bayan wannan taqaitaccen balaguro a cikin littafan Khumaini domin


bayanin aqidojinsa, bari mu juya ga Fiqihunsa don mu tabbatarwa da mai karatu


cewa, wannan xan taliki ba a lasafta shi a cikin masu sassaucin ra’ayi, kuma


mabiyansa masu alfahari da shi, suna tallata shi a matsayin shugaba mai


gwagwarmayar qwato haqqin Musulmi, imma jahilai ne ake amfani da su wajen


biyan bukatun wasu dujalai mutakabbirai na tara mutane da cin guminsu a bisa


qarya, ko kuma vatattu ne masu bin son zuciya suke so su vatar da wasu.


Shika-shikan Fiqihun Khumaini


Khumaini yana gina fatawoyinsa da hukunce-hukuncen da yake zartarwa na


Fiqihu a kan aqidarsa ta Shi’anci kamar yadda take a littafan shehunnan Shi’a da


malamansu. Nazarin waxan nan fatawoyi da hukunce-hukunce zai bayyana shikashikan


Fiqihun Khumaini kamar haka:


1. Sun dogara da maganganun Imaman Shia’a kamar yadda littafansu na


ruwaya suka ruwaito su.


2. Akwai qarancin ambaton Alqur’ani ko Hadisin Annabi (SAW) wajen


tabbatar da fatawoyin da hukunce-hukuncen, abinda yake nuna yin nesa da


Musulunci.


3. Riqo da qa’idar Shi’a da take cewa, idan aka rasa dalili da zai rinjayar da


xaya daga cikin hukunci guda biyu masu karo da juna, to sai a xauki wanda


ya savawa Ahalus Sunna, shi ne dai-dai.


Wannan tushe na uku yana da muhimmanci saboda yadda yake nuna matsayin


Khumaini na shugaban Shi’a mai tsananin ra’ayi, wanda yake da matuqar qiyayya


ga Ahalus Sunna har ga haddin ajiye hankali gefi da aiki da son zuciya. Don haka,


yana da kyau mu ji abinda ya ce da bakinsa dangane da al’amarin.


Khumaini ya ce, “Lallai savawa Ammawa1 yana cikin abinda ake sanin daidai


da shi a tsakanin hukunce-hukunce biyu masu savawa juna.”2 A wani wajen


1 Ammawa na cikin lakaban da ‘yan Shi’a suke ba Ahalus Sunna don wulakanci. Duba littafi na 5 a wannan jerin.


2 Duba Atta’adul wal Tarjih na Khumaini, shafi na 83.


19


kuma ya ce, “Babu shakka cewa savawa Ammawa yana cikin abinda ake gane


(ra’ayi) mai rinjaye da shi a yayin savani.”1


Wannan tushe, ko kuma qa’ida, ta fitar da hukunci a Fiqihun ‘yan Shi’a


wacce Khumaini ya rungume ta kuma ya yi aiki da ita, tana nuna matsayin ‘yan


Shi’a dangane da Ahalus Sunna. Ahalus Sunna ba Musulmi ba ne; don haka ya


zama wajibi a sava musu kamar yadda ya wajaba a savawa Yahudu da Nasara.2


Bayan wannan taqaitacciyar shimfixa, za mu gabatar da misalai kaxan na


Fiqihun Khumaini don mai karatu ya ganewa idanunsa irin sharrin dake qunshe


cikin zuciyar wannan xan taliki wanda jahilai suke nuna shi a matsayin shugaba na


Musulmi.


1. Khumaini yana halatta dukiyar Ahalus Sunna: Dangane da wannan yana


faxi, a yayin maganarsa a kan hukuncin ganima da khumusi,3 kamar haka: “Ra’ayi


mafi qarfi shi ne ruskar da Nasibawa4 a cikin kafiran yaqi wajen halaccin


ganimarsu da bayar da khumusi daga cikinta. Abinda yake zahiri shi ne halaccin


qwace dukiyar Nasibi ko a ina aka same ta, kuma ko ta halin qaqa, sa’an nan a


fitar da khumusi a cikinta.”5


Wannan magana mai haxari tana nuna yadda Khumaini ya xauki Ahalus


Sunna, cewa su suna dai-dai da kafiran yaqi, waxanda ya halatta a karvi dukiyarsu


a matsayin ganima. Kuma hakan yana nufi ke nan cewa, kafiran Amana kamar


Yahudu da Nasara sun fi Ahalus Sunna alfarma a wajen Imam Khumaini.


2. Khumaini yana ganin rashin halaccin sallah ga mamaci Ahalus Sunna: Ga


abinda yake cewa, “Ba ya halatta a yi sallah ga nau’o’in kafirai, har da mai ridda.


Haka nan wanda aka yi hukunci da kafircinsa amma yana da’awar Musulunci,


kamar Nasibawa da Khawarijawa.”6


3. Khumaini yana fatawa da rashin halaccin sallah a bayan limami Ahalus


Sunna: A ra’ayin Khumaini, sallah ba ta inganta a bayan limami mai bin Sunna,


1 Atta’adul wal Tarjih, shafi na 84.


2 Duba littafi na 5: Matsayin Musulmi a Wajen ‘Yan Shi’a.


3 Khumusi wani haraji ne da ‘yan Shi’a suke baiwa malamansu.


4 Nasibawa su ne Ahalus Sunna a zaurancen ‘yan Shi’a. Duba littafi na 5.


5 Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1 shafi na 251.


6 Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1 shafi na 80.


20


kuma idan xan Shi’a ya yi ta, to dole sai ya rama. Wannan hukunci yana cikin


littafan Khumaini, kamar Sirrus Salati1 da Kitabut Taqiyya2 da Tahrirul Wasila.3


4. Khumaini yana ganin vacin sallar wanda ya kama qirji a sallah: Ya ce:


“Yana daga cikin abubuwan da suke vata sallah xora hannu guda a kan xayan


IRIN YADDA MASU SAVA MANA SUKE AIKATAWA. Amma babu laifi a yi


hakan a halin taqiyya!”4


5. Khumaini yana fatawa da rashin halaccin baiwa Ahalus Sunna zakka: Ga


abinda ya ce, “Zakka ba ta halatta ga Nasibi da kafirin yaqi, ko da sun zama ‘yan


uwa na jini.”5


6. Khumaini yana fatawa da haramcin cin yankan Ahalus Sunna: Ya ce,


“Cin yankan dukkan qungiyoyin Musulmi yana halatta, banda Nasibawa ko da


suna bayyana Musulunci!”6


7. Khumaini yana haramta auren matan Ahalus Sunna: Dangane da wannan


Khumaini yana kausasawa ainun, a yayin da ya nuna cewa auren kafiran amana ya


fi auren matan Ahalus Sunna.7


Sai dai abin mamaki shi ne, a zamanin Khumaini gwamnatin qasar Iran ta yi


amfani da aurar da matan Shi’a ga mazaje Ahalus Sunna a matsayin wata hanya ta


qoqarin yaxa tafarkin Shi’anci a tsakanin mabiya Sunna.8


A nan Nijeriya bincike ya nuna ‘yan Shi’a suna amfani da aure wajen yaxa


baqar aqidarsu. Sai dai a nan ba matansu suke aurarwa ba, matan Ahalus Sunna


suke aure, sa’an nan su juye kansu a xan qanqanin lokaci, su mayar da su ‘yan


Shi’a. Babu shakka aurar da mata ga ‘yan Shi’a bai halatta ba, kamar yadda


malamai da yawa suka ba da fatawa, ciki har da Imam Bukhari.9


1 Sirrus Salati na Khumaini, shafi na 9.


2 Kitabut Taqiyya na Khumaini, shafi na 198. A wannan littafin ya halatta sallar idan an yi ta da niyyar taqiyya!


3 Daga baya an shafe wannan mas’ala daga littafin mai fassarar Larabci, wata kila saboda taqiyya.


4 A duba Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1 shafi na 186.


5 Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1 shafi na 91.


6 Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1 shafi na 146.


7 Duba Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 2 shafi na 286.


8 Duba Al’khumaini wal Wajhul Aakhar na Zaid Al’is, shafi na 141.


9 Duba fatawarsa a cikin littafinmu, Bacin Tafarkin ‘yan Shi’a, bugu na musamman, shafi na 86.


21


8. Khumaini yana halatta auren Mutu’a: Auren Mutu’a shi ne auren wucin


gadi wanda ba wali ba shaidu kuma babu sadaki (sai lada) a cikinsa.1 Khumaini ya


halatta wannan aure a cikin littafansa masu yawa.2


Gogan bai tsaya nan ba, ya halatta a iyakancewa auren Mutu’a lokaci


qanqane, kamar dare ko wuni xaya, ko awa xaya ko awa biyu.3 Haka nan, ya


halatta auren Mutu’a da karuwa, koda yake ya ce makaruhi ne!4


Shugaban ‘yan gwagwarmayar bai tsaya a nan ba, ya qara gaba kaxan inda


ya yi wani xan ijtihadi a matsayinsa na wakilin Imamai. Ya halatta yin Mutu’a da


qaramar yarinya, har da jaririya, amma ya ce ba da haqiqanin saduwa ba sai dai da


sumbanta da runguma da kuma abinda ya kira “cinyantaka,” watau mutum ya


sanya zakarinsa a tsakanin cinyoyinta.5


Shekaru kaxan da suka wuce, wani xan siyasa a Nijeriya ya auri yarinya mai


shekara goma sha huxu a duniya, sai kafafen yaxa labarai da qungiyoyi masu rajin


kare haqqin mata suka yi ta suka. Ba mu san abinda irin waxan nan kafafen yaxa


labarai da qungiyoyi za su faxi ba dangane da Khumaini, Imami Maxanxani!


1 Domin bayanin auren Mutu’a duba littafi na 4 a wannan jerin.


2 Ga misali, duba Kashful Asrari na Khumaini shafi na 127 da Tahrirul Wasila nasa, mujalladi na 2 shafi na 288.


3 Duba Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 2 shafi na 290.


4 Tahrirul Wasila, mujalladi na 2 shafi na 292.


5 Duba Tahrirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 2 shafi na 241.


22


Babi Na Huxu


Yadda Khumaini ya Yaudari Duniya


Lokacin da Khumaini ya qaddamar da juyin juya halin da ya kira na


Musulunci, duniyar Musulmi duka ta yi murna. Musulmi a ko ina sun yi farin ciki


yayin da suka yi maraba da juyin da suka yi zaton zai xaga martabar Musulunci, ya


qwato haqqin Musulmi kuma ya qalubalanci zaluncin kafirai, musamman Amurka


da Isra’ila. Sai dai kash! Ba’a daxe ba wannan murna ta koma ciki. Sannu a


hankali ta bayyana ga duk mai ido biyu cewa juyin da Khumaini ya jagoranta ba


juyin Musulunci ba ne, amma juyin Shi’anci ne mai tsananin gaba da dukkan


Musulmin da ba sa bin tafarkin Rafilanci, musamman Ahalus Sunna.


Akwai dalilai da dama da suka sa Musulmin duniya suka yi marhabin da


juyin Khumaini. Na farkonsu shi ne jahiltar aqidar Khumaini da tsaurin ra’ayinsa.


Na biyu shi ne qishirwar sauyi da yawancin Musulmi suke ciki saboda raunin


qasashen Musulmi da ci bayansu da xarewar munafukai da jahilai a kan mulkinsu.


Na uku yaudara da taqiyyar Khumaini da sabuwar gwamnatinsa, da gagarumar


na’urar farfaganda wacce ya girke don cimma mugunyar manufarsa. Na huxu


karan tsana da manyan daulolin kafirci na duniya suka xorawa wannan juyi a


farkon faruwarsa. Wannan sai ya gaskata da’awar shugabannin juyin cewa, lallai


su sun fito ne domin dawo da martabar Musulunci, haxa kan mabiyansa da


tabbatar da maslahohinsu.


Farfagandar Iran a kan Juyinta


Banda waxancan dalilai kuma, qasar Iran a bayan juyin juya halin ta girke


na’urar farfaganda wacce ta yi amfani da ita wajen yaqo qwaqwale da zukatan


Musulmi. Makaman wannan yaqi sun haxa da:


1. Kafa Cibiyoyin Ilmi. Qasar Iran ta kafa cibiyoyin ilmi da yaxa bayanai domin


tabbatar da abinda ta kira kusanto da mazhabobin Musulunci ga juna da samar da


fahimtar juna a tsakanin Musulmi mabiya tafarkai dabam-daban da mazhabobi


dabam-daban. Ta jawo hankalin masana daga vangarori dabam-daban don yin aiki


a waxan nan cibiyoyi waxanda ta kashewa kuxaxe masu yawa. Sai dai sannu a


hankali waxan nan ta bayyana cewa kafafe ne na yaxa Shi’anci kawai.


23


2. Yaxa Littafai. Har yau qasar Iran ta yi amfani da wallafa da kuma yaxa littafai


na farfaganda da nufin tallata manufofin juyin juya halinta a lokacin da ta yi


qoqarin voye littafan malamanta, ciki har da littafan Khumaini, waxanda suke


nuna miyagun aqidun Shi’a da mummunar masufarsu. Shi ma wannan burun-burun


da wasan kwaikwayo an gano shi a lokacin da faxakakku daga malaman Sunna


suka bankaxo waxan nan miyagun littafai, suka yaxa su ga al’umma. Sai ga


bambanci ya bayyana a fili tsakanin waxan nan da waxancan.


3. Yaxa Jaridu da Mujallu. Wani makamin farfaganda da qasar Iran ta yi amfani da


shi don tallata manufofinta da kyautata surarta a duniyar Musulmi shi ne yaxa


jaridu da mujallu. Qasar ta kashe kuxaxe masu yawa wajen hayar masana da


qwararru a fagagen aikin jarida da yaxa labaru a cikin harasa dabam-daban, ta riqa


buga irin waxan nan jaridu tana raba su zuwa qasashe a kyauta. Waxan nan jaridu


da mujallu sun yi tasiri mai yawa a qasashe irin su Nijeriya.


4. Kafa gidajen Radiyo. Har yau, mahukuntan Iran ‘yan Shi’a sun yi amfani da


kafa gidajen radiyo masu yaxa shirye-shirye da harasa dabam-daban, inda suka


xauki ‘yan qasashe dabam-daban aiki a waxan nan gidajen radiyo domin fuskantar


da saqon Shi’anci da farfagandarsa ga qasashensu. Daga cikin waxan nan gidajen


radiyo akwai wanda aka buxe musamman don gabatar da shirye-shirye da harshen


Hausa.


5. Kafa Makarantu da Jami’o’i. Haka nan sun kafa makarantu da jami’o’i a cikin


qasar Iran da ma wasu qasashen waje domin koyar da ‘ya’yan Musulmi waxanda


ba ‘yan Shi’a ba, musamman waxanda suka fito daga qasashe masu fama da


talauci. Ga misali, akwai irin waxan nan makarantu a qasashen Afirka da dama,


kamar Gana da Togo da Saliyo, da sauransu. Kamar yadda suka qarfafa guiwar


mabiyansu da su buxe qananan makarantu a qasashensu, kuma suka xauki nauyin


gudanar da su. Makarantun da ‘yan Shi’ar Nijeriya suke kira Fodiyya na cikin irin


waxan nan makarantun.


6. Shirya Tarukan Qarawa Juna Sani. Wani makamin farfaganda kuma da aka


fuskantar da shi musamman ga ‘yan boko da malaman jami’a da sauransu, shi ne


shirya tarukan qarawa juna sani a lokuta da wurare dabam-daban, a cikin Iran da


wajenta, inda suke haxa masana a fannoni dabam-daban domin fakewa da tattauna


24


matsalolin duniyar Musulmi a tallata manufar qasar Iran. Yawanci a wajen irin


waxan nan taruka a kan tava a lashe, kuma a komo da hadaya da abin sayen goro.


7. Yin Amfani da Ofisoshin Jakadanci. Yawancin ofisoshin jakadancin Iran a


qasashen qetare matattarar tuggu ce da qulle-qulle domin yaxa aqidun Shi’a ta


hanyar ayyukan “taimako” da “tallafi” da “xaukar xawainiyar mabukata” da sauran


irin waxan nan kyawawan ayyuka waxanda suke qunshe da miyagun manufofi.


Waxan nan kaxan ne daga makaman farfaganda da qasar Iran ta yi amfani


da su wajen tallata manufofinta da aqidun malamanta, wanda sannu a hankali ya ja


mutane daga gwagwarmaya da yaqar Amurka da Isra’ila zuwa qudure aqidun


Shi’a.


Hanyar Shi’a zuwa Nijeriya


Babbar hanyar da Shi’a ta bi zuwa Nijeriya ita ce hanyar gwagwarmaya. Tun


kafin juyin juya halin qasar Iran, Musulmi matasa ‘yan Nijeriya, masu qishirwar


sauyi da gafin quruciya da qarancin ilmin addini, sun daxe a bisa tafarkin


gwagwarmaya. A wancan lokaci, waxanda suke koyi da su su ne ‘yan qungiyar


Ikhwanul Muslimun ta qasar Masar wacce Hassan Albanna ya kafa. Shi ya sa aka


san su da sunan ‘Yan Uwa Musulmi, ko kuma ‘Yan Buraza, wanda wannan fassara


ce kai tsaye ga sunan Ikhwanul Muslimun.


Bayan juyin juya halin Qasar Iran, da hayaniyar da biyo shi, da farfagandar


da mahukuntan Iran suke girke domin tallata shi, sai matasan Nijeriya suka juya


wa qungiyar Ikhwanul Muslimuna baya, suka koma koyi da shugabannin Iran da


malamansu. Sun xauki Khumaini a matsayin shugaba abin koyi, kuma suka riqa


ganin cewa, salon juyin juya halin day a jagoranta shi ne kaxai hanya da za ta fitar


da Musulmi.


A nasu vangaren, mahukuntan Iran da jami’an sabuwar gwamnatin juyinsu


ba kawai farfaganda suka dogara da ita ba, a’a sun ja samarin Nijeriya a jika,


kamar yadda suka ja samari masu qarancin ilmi da gogewa daga dukkan qasashen


Musulmi. Sun riqa gayyatar su zuwa qasar, suna shirya musu taruka da bukukuwa


kuma suna ba su kuxi da maqamai da guraben qaro karatu. Ta wannan hanya ne


suka qarfafi farfagandarsu da tsarin yaki-me-me da watsa tsaba ga ‘yan tsaki.


25


Kafin ka ce meye wannan sun kame waxan nan yara, sun mayar da su ‘yan Shi’a


ba da saninsu ba.


Wannan ita ce hanyar shigo-shigo-ba-zurfi da qasar Iran ta bi ta juye kan


samarin Musulmi masu kishin addinin Musulunci amma ba su san kome na addinin


ba sai sunansa kawai. Kuma daga nan, sai suka mance da gwagwarmaya, wacce da


ma koma ce ta kamun kifi, suka shiga Shi’a karurus. Sai sukaqudure dukkan


aqidun Shi’a, kuma suka xauki salon su: zagin Sahabbai da kafirta su, qudure


Imama da aikata Taqiyya, qin Musulmi Ahalus Sunna, bautar kabari da girmama


gumakan Imamai, da sauran ayyukan kafirci da shirka waxanda Khumaini ya yi


kira gare su, ya koyar da su.


Wani abu mai haxari kuma da ‘yan Shi’ar Nijeriya suka xauka shi ne tsauri


da nesantar lalama da qoqarin kawo sauyi da qarfin tuwo, kamar yadda Khumaini


ya yi a qasarsa.


Kayan Gadon Khumaini


Akwai wani abu guda da ake gwada alheri ko sharrin shugaba da tunaninsa


da koyarwarsa da aikin da ya qaddamar a rayuwarsa. Wannan abu shi ne kayan


gadon da ya bar wa mabiyansa da kuma duniya baki xaya. Mene ne kayan gadon


da Khumaini ya barwa duniya?


Khumaini ya bar Jamhuriyar Musulunci, ko kuma mu ce Jamhuriyar


Shi’anci, ta Iran. Kuma a yau, kusan shekara arba’in da kafa wannan jamhuriyar,


muna iya duban ta, mu yi mata hukunci, muna masu dogaro da abinda ta qulla wa


‘ya’yanta da maqotansu da duniya baki xaya.


Savanin abinda qasar Iran take yaxawa na farfaganda, kuma tana son duniya


ta gaskata, babu abinda qasar ta dama wa ‘ya’yanta sai salalan tsiya. Banda ‘yan


qasar waxanda ba ‘yan Shi’a ba, musamman Ahalus Sunna, waxanda juyin juya


halin Khumaini ya mayar da rayuwarsu Jahannama a doron qasa, su ma ‘yan Shi’ar


ba abinda wannan shu’umin juyi ya haifar musu sai mari a qafafunsu da takunkumi


a bakunansu.


Babu ‘yanci a qasar Iran, ba yalwa da wadata, ba zaman lafiya da kwanciyar


hankali, kuma babu kyakkyawan fata na gyaruwar al’amura gobe. Iran ta zama


wani shirgegen kurkuku a qarqashin mulkin mutum xaya tilo shi ne magajin


26


Khumaini, Jagoran Sauyi, mai riqe da kambin Wilayatul Faqih, watau Ali


Khamna’i. Mulkin wannan Babban Boka mai baqin rawani sai mutuwa, kuma


kalmarsa tana sama da kalmar zavavven shugaban qasa da zavavvun ‘yan


majalisar qasa, da duk wani gungun mutane ko qungiyar ‘yan qasa, ciki har da


malaman addini da ‘yan boko da matasa, da sauransu.


Karnukan farautar Babban Bokan su ne sojojin rundunar qasar da ake kira


Sojin Tsaron Juyin Juya Hali (Revolutionary Guards da Turanci, ko Alharsul


Thauri da Larabci) waxanda suke riqe da wuyan qasar, sai sun sassauta damqa


take iya numfashi. Kafatanin rayuwar ‘yan qasar Iran, tattalin arzikinsu da


zamantakewarsu, tana hannun zabaniyawan Sojin Tsaron Juyin Juya Hali waxanda


ba sa xaukar umarni daga kowa, kuma ba sa sauraron kowa, sai Jagoran Sauyi


magajin Khumaini.


Tsarin da Khumaini ya shimfixa a qasar Iran mulkin Fir’aunanci ne wanda


duniya ta daxe ba ta ga irinsa ba. Qasar tsit take kamar makwantai (idan ka ji motsi


jerin gwano ne irin na mabiyan Zakzaki masu zuwa Zariya a qas); ba mai magana


sai fa idan zai rera yabon Jagoran Sauyi ne, ko ya yi amshin shatansa, ko ya


maimaita abinda aka laqanta masa kamar akun kuturu. Da gan-gan aka yi wa ‘yan


qasar tarbiyar bayi, sai suka zama tamkar bisashe a hannun makiyayi, sai inda ya


kaxa su da sandarsa. Sakamakon wannan shi ne tsananin talauci da ci baya da


faxuwar qimar xan Adam da sakwarkwacewar halaye da lalacewar maraya.


Idan mai karatu yana so ya san abinda Khumaini ya gada wa maqotansa, sai


ya tambayi Lebanon da Suriya da Iraqi da Yaman, da sauran qasashen Larabawa


da Musulmi na kusa da na nesa. Jamhuriyar Shi’anci ta qaddamar da yaqi a kan


maqotanta a kafatanin fagage: fagen siyasa da diflomasiyya, fagen tattalin arziki,


fagen ilmi da al’adu, da kuma fagen fama. Kuma a wannan yaqi, qasar na amfani


da dukkan nau’in makamai: makamin kuxi da abin duniya, makamin kafafen


bayanai da yaxa labarai, makamin mutu’a da taqiyya, da makamin kisa wanda ya


fara daga bindiga da bam har ya zuwa nukiliya.


Lebanon: Wannan qasa ita ce mazaunin qungiyar Hizbullah, qungiyar ta’addanci


mafi qarfi a Gabas ta Tsakiya, wacce kuma ita ce hannun daman qasar Iran wanda


take amfani da shi a wajen ayyukanta na ta’addanci a qasashen duniya.


27


Suriya ko Sham: Qasar Iran tana taimakon gwamnatin Bashar Asad ta tsiraru ‘yan


Shi’a wacce take kafsa yaqi da ‘yan tawaye masu bin tafarkin Sunna, waxanda


kuma su ne mafiya rinjaye, tun farkon shekarar 2011. Gwamnatin Asad ta dogara


kacokan da taimakon Iran, na kuxaxe da makamai da diblomasiyya da qwararrun


soji masu ba da shawara, wajen ta’addancinta a kan ‘yan qasarta wanda ya haxa da


rushe kimanin kashi biyu bisa uku na dukkan biranen qasar, kashe sama da mutane


dubu xari biyu da hamsin, kore sama da miliyan shida daga gidajensu, da amfani


da muggan makamai waxanda aka haramta a dokokin qasa da qasa


Iraqi: Iran ta taimakawa ‘yan Shi’ar Iraqi wajen kafa qungiyoyin ina-da-kisa


waxanda suka taimaki sojojin Amurka a kan kifar da gwamnatin Saddam Hussaini


da rushe biranen mabiya Sunna, kamar birnin Falluja, da karkashe su mafi munin


kisa. A matsayin sakamako, qasar Amurka ta taimaka wa ‘yan Shi’a su mulki


qasar Iraqi da da’awar cewa wai su ne masu rinjaye.


Yaman: Qasar Iran tana taimakon ‘yan tawayen Hutsawa marasa rinjare, masu bin


tafarkin Shi’a, a qoqarinsu na vallewa daga qasar Yaman da kafa qasarsu ta ‘yan


Shi’a.


Baharain: Iran tana tallafawa ‘yan Shi’ar qasar Baharain, waxanda suke da’awar


su ne masu rinjaye wai amma mabiyan Sunna suna mulkinsu mulkin danniya. Yau


kimanin shekaru biyar ke nan babu zaman lafiya a qasar. Shekaru biyu da suka


wuce, ‘yan Shi’ar sun kusa yin nasarar tankwave gwmnatin qasar ba don taimakon


qasar Sa’udiyya ba gare su.


Idan muka bar maqotan Iran, ba zamu laluba da nisa ba sai mu dubi


Nijeriya.


Hizbullah a Nijeriya?!


Qasar Iran ta yi nasarar samar da wasu gungun mutane a Nijeriya waxanda


ta hore don zartar da mugun nufinta ga al’umma. Waxan nan mutane, qarqashin


shugabancin Ibrahim Alzakzaki, sun kwashe shekaru suna qulla maqarqashiya,


wacce ta haxa da kafa rundunar sojin sa-kai da za ta zartar da mugun nufin Iran a


Nijeriya da yammacin Afirka. Shirinsu ya yi nisa har sun fara karvar makamai


daga iyayen gijinsu.


28


A cikin watan Oktoba, 2010, jami’an tsaro sun kama kontena goma sha uku


maqare da miyagun makamai a tashar jiragen ruwa ta birnin Legas. Bincike ya


tabbatar da cewa waxan nan makamai sun fito ne daga qasar Iran, kuma ofishin


jakadancin qasar a Abuja ya amsa cewa xaya daga mutanen da aka kama da


makaman ma’aikacinsu ne. Bayan shari’a da ta xauki sama da shekaru biyu, an


samu mutane biyu da laifi, ciki har da jami’in jakadancin na Iran, kuma kotu ta


xaure su shekaru 17 ko wannensu.1


A cikin watan Fabrairy, 2013, jami’an leqen asiri na Nijeriya sun cafke wasu


samari da suka yi karatu a qasar Iran, suna shirin kai hare-haren ta’addanci da


nufin kashe wasu shugabannin Musulmi na qasar nan, ciki har da tsohon shugaban


mulkin soja Ibrahim Babangida, da Sarkin Musulmi mai murabus, Sultan Ibrahim


Dasuqi. Bayan bincike, ya tabbata cewa waxan nan samari suna yi wa qungiyar


ta’addanci da Iran ke mara wa baya, watau Hizbullah, aiki. Jaridun qasar nan da


kafafen yaxa labarai na qasashen qetare duka sun ruwaito wannan labari.2


Haka nan, a wannan shekara dai ta 2013, an gano makamai masu yawa voye


a wani gida a birnin Kano. Bayan bincike, an zargi wasu qwarori ‘yan qasar


Lebanon, waxanda ake jin suna da alaqa da qungiyar Hizbullah, da mallakar


waxan nan makaman, kuma an gurfanar das u a gaban kotu.3


Sai dai labarin da muka samu daga baya-bayan nan yana nuna cewa, kotu ta


yi watsi da wannan magana ba tare da wani dalili mai qarfi ba. Wannan ya faru a


zamanin gwamnati da ta shuxe. Amma a yanzu muna fata wannan sabuwar


gwamnati ta Muhammadu Buhari za ta sake buxe kundin shari’ar, musamman


saboda abinda ya faru tsakanin Sojojin Nijeriya da qungiyar ‘yan Shi’a ta Zakzaki


a qarshen shekarar 2015, wanda ya fito da alaqarsu da Iran a fili.


‘Yan Shi’ar Nijeriya mabiyan Zakzaki sun yi nisa da shirin buxe reshen


Hizbullah a qasar nan, don haka suke xaga tutar qungiyar a fili a cikin jerin gwano


da suke gudanarwa.4 Wannan shiri nasu ya daxa fitowa fili sakamakon abinda ya


faru tsakanins da Sojojin Nijeriya, kamar yadda muka yi nuni gare shi a sama.


1 Domin ganin wannan labari, duba jaridar Dailay Trust, fitowar 15 ga watan Mayu, 2013, shafi na 46.


2 Gidan talabijin na Aljazeera (ta Larabci) ya watsa labarin ranar 21 ga watan Fabrairu, 2013.


3 Duba jaridar Dailay Trust, Juma’a 31 ga watan Mayu, 2013, shafi na 1 da na 5.


4 Domin ganin hoton ‘yan Shi’ar Nijeriya dauke da tutocin Hizbullah, duba jaridar Dailay Trust, fitowar Talata 22 ga


watan Mayu, 2012, shafi na 3.


29


Wannan shi ne abinda Khumaini ya gadarwa duniya: jahilci da fatara da ci


baya da yaqe-yaqe, da kuma uwa uaba sunce imani da asarar duniya da lahira.Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC