Labarai




Wani abu na daban kuma shine abunda da dokan dan adam ta gafala dashi ko kuma take kokarin mantawa dashi shine Karin aure yana jawo maslaha ga mace daga namiji, yawan matan duniya sun nun-nunka maza saboda dalilai dayawa daga cikin su akwai:-


1. HAIHUWA: kididdiga na kasa da kasa ya nuna cewa yawan matan da ake haihuwa yafi na maza.


2. YAWAN MUTUWA: yawan mutuwan maza yafi yawa saboda yaki wanda akeyi kamar yakin duniya na farko dana biyu da yakuna wanda yake tsakanin kasa da kasa a wani lokaci, haka kuma yawan hatsura na hanya wanda yafi ritsawa da maza ko kuma saboda mutuwan na wuri wanda yafi faruwa da maza akan mata.


3. GAURANTAKA: saboda rashin bukatar daukan nauyi na mata da iyalai ko kuma saboda fita zakka wanda yake fuskanta wasu dayawa daga maza cikin wasu kasashe masu yawa wanda sukaci gaba ko kuma saboda maluntaka wanda yake kasancewa cikin al'ummar kiristoci na rashin yin aure.


4. KURKUKU: yadda yawan yan kurkuku mafi yawa maza ne ba mat aba.


Dukkan wannan dalilai ne wanda yake zama da wahala mace ta samu miji ita kadai a rayuwanta. Kuma hakika dokoki na dan adam sun sanya mata dayawa yarda da zama kawaye na maza koda kuwa wannan namiji yanada mata domin samun namiji!! Wanda yafi dacewa ga dokoki na dan adam dasu yi doka akan Karin aure da kuma kawar dakai ga yancin mace, aure baya yiwuwa sai da yardan ma'aurata, sannan kuma hama Karin aure yana cin karo da yancin mutum wanda wannan kasashe suke kira dashi dakansu.


Da ace mutum zai cema wata daga cikin wannan mata wanda basu samu mazaje ba kuma sunason auren namiji koda bayahudiya ce ko kirista ko musulma ko buziyya cewa Karin aure be dace ba da halaye kuma yafi dacewa da ta zauna haka babu aure wanda za'a haramta mata hakkinta na rayuwa na dabi'a kamar sauran mata masu aure, ko kuma abunda yafi shine tayi rayuwa a matsayin kawa ga namiji me mata sannan daga baya ya barta, sai kuma ta kara neman wani abokin na daban wanda hakan rayuwanta zai kare, da sannu zata amsa maka da cewa: “kai ina ruwanka? Idan bakason Karin aure ko kuma kana ganin cewa be dace ba to wannan ra'ayinka ne kuma kada ka tilastama wani ra'ayin ka


wand aba irin naka ba, duk wanda yaga dama yayi Karin aure wanda kuma yaga dama ya tsaya ga mace daya!!”


Ya yadu yanzu cikin kasashe masu yawa wanda suka ci gaba a fili canjin mata42, yadda mutum biyu zasu yi musayan matan su sai kowa ya kwanta da matar dayan, ko kuma mutum ya kwanta da matar shi da matar dayan a lokaci daya sannan bayan haka shima dayan sai ya kwanta dasu su biyun a lokaci daya. Dalili kuma na hakan kamar yadda dayawa daga cikin ma'aurata suka ambata shine kwadayin sun a canji da kuma banabantan yanayi na sha'awa da kuma daukan hakan a matsayin hanya ta abota da kuma kara dankon alaka a tsakanin su. Wani marubuci curtex berjistarland ya ambata cikin littafin sa”musayan mata a amerika”cewa wannan al'ada ta dauki yaduwa a amerika a tsakanin bangarori biyu masu yaki a lokacin yakin duniya na biyu, a lokacin da mutuwar mayakan ya karu, ya kasance mayakan sun hada al'ummar su ta musamman domin kulla alaka a tsakanin iyalansu ta hanyar da tafi, haka ya kasance mayakan suke kula da matan sauran mayakan idan sun mutu ko kuma sun bace, kuma wannan kulawar ya kasance yana wanzuwa zuwa kulawa ta tausayi da alaka sha'awa har wayau, daga cikin masalai na musayan mata wanda ya fara yaduwa a tsakanin ma'aurata a tsakanin al'ummar birane na amerika, abunda aka sani kungiyoyi na


42 Swinging ،wife swapping ،wife sharing ،partner sharing ،wife trading or wife lending.


mabudai, yadda mutum zai jefa makullin gidan sa a kasa daganan sai wata mace ta dauka ko wani mabudi a ciki ta hanyar cinka, to hakan wannan mata zata zama rabon wannan mutum me wannan mabudin cikin wannan dare43. Kuma an yadashi cikin wata kafa ta labarai ta CNN a ranara 15 ga watan satumba na shekarar 2011 cewa adadin ma'auratan da suke yin musayar mata yakai kusan miliyan 15!! Kuma ana samun hakan yanzu dayawa kogigoyin duniya wanda suke kwadaitarwa akan musayar mata da kuma shirya tafiya da kuma kungiyoyi da biki na musamman domin aikata musayan mata, yadda ba'a barin mutane shiga wannan wurin bikin sai da matan su su kuma mata ana barin su shiga koda kuwa ba tare suke ba da maza, sannan zaka samu daki cikin wurin wannan biki wanda aka ware domin aikata hakan, kuma mutum zai iya bayan ya gama kwanciya da matar wani ya daya ya kara maimata wannan kacinci kacinci a cikin wannan daren, haka kuma itama macen zata iya yin wannan abu tare da maza dayawa ko wanne daban daban!! Kuma hakika musayan mat aba laifi bane cikin dokoki na dan adam yana daukan sa a matsayin yanci na mutum da sha'awa, kuma suna daukan sa cikin dabi'u wanda suka dace yadda mayaka zasu kula da matan mayakan da suka mutu ko kuma suka bace domin su biya masu bukatun sun a sha'awa da tausayi, shi kuma Karin aure suna daukan sa a matsayin laifi!!! Da ace wani mayaki ma aure zai kara auren matan wani mayaki wanda yam utu domin ya kula da ita hakan laifi ne kuma zasu kulle shi domin tuhumar sa da Karin aure!! Sai dai hakan yaci karo da fidira!!.


43 Swinging in America: Love ،Sex ،and Marriage in the 21st Century ،By Curtis R. Bergstrand ،Jennifer Blevins Sinski.


Mafiya yawa ba'a ambatan wani annabi cikin littafi me tsarki face yanada mata dayawa, misali annabi Sulaiman da Dawud da Ibrahim da Ykubu da sauran su amincin Allah ya kara tabbata a garesu, hakika an Ambato cewa annabin Allah Sulaiman cikin littafin Safar al muluk na farko (11/3): (ya kasance yanada mata dari bakwai masu yanci da kuma bayi dari.) kuma an Ambato cikin safar al tasniya (21/15): (idan mutum ya kasance me aure da mata biyu, yanason daya daga cikin su kuma bayason dayar…).


Safar al khuruj (21/10): (amma idan ta burgeshi kuma ya aure ta, sa'annan ya dawo ya auri wata, to bazai rage mata komai ba daga cikin abincin ta da tufafinta da zamanta kewar ta.)


Kamar yadda babu wani nassi daya daya zo cikin littafi me tsarki tsohon lkawi ko kuma sabon alkawari wanda yake haramta karin aure ko kuma iyakance adadin matan da za'a aura!! Daga cikin nassoshi wanda suka tabbata a cikin sabon alkawari:


Sakon Bulus na farko zuwa ga Thimosawis (3/1): (1 gaskiya itace magana: idan daya yaso malumta, to yaso aikin kwarai. 2 ya wajaba yakasance mata: ba tare da zargi ba, mijin mace daya saliha, me hankali, kamulalle, me taran baki, wanda ya dace da karatu… 12 ya kasance ma'aikacin coki na musan man: mijin mace daya, me lura da yaran su da gidan su me kyau)


Acikin wannan nassi munga cewa Karin aure halal ne ga kowa ga duk wanda yakeson zama babban malami ko kuma ma'aikacin coci na musamman.


Kuma wata marubuciya Mathelyda juslyn ta ambata cikin littafin ta mace da coci da kasa abunda ke zuwa44: (shin wannan ba dalili bane a bayyane cikin maganganun Bulus akan siffofi na maluma - fadoji - cewa su kasance (mijin mace daya) cewa Karin aure halal ne a cikin coci shi yafi dacewa da manzanni almajiran shugaba Almasihu?!.. idan al'amarin haka yake me yasa yanzu aka kirkiro wasu siffofi wanda suka banbanta da wancan wanda manzanni suka tabbatar dashi da kansa?!)


Kuma wasu kiristoci sun kafa hujja da wasu nasooshi cikin sabon alkawari akan haramcin Karin aure, kamar misalin:


Injila ta markis (10/2): (2 sai firisiyyun suka gabato ya tambayesu: “shin ya halatta ga mutum ya saki matar sa?!!. domin su gwadashi. 3 sai ya amsa yace masu: “dame musa yayi maku wasiyya?.” 4 sai sukace: “Musa yayiizini da arubuta littafin saki, sai asaketa.” 5 sai Yusawwa'a ya amsa yace masu: “saboda bushewan zuciyar ku ya rubuta maku wannan wasiyyar, 6 sai dai a farkon halitta, miji da mace Allah ya halicce su. 7 saboda haka mutum yake barin ubansa da uwarsa ya hadu da matar sa, 8 sai su biyun su zama jiki daya. Idan basu kasance su biyun ba face gangan jiki daya. 9 wanda Allah ya hada su basa mutum baya rabasu.” 10 sa'annan kuma almajiran sa suka


44 Matilda Joslyn Gage ،‘‘Women ،Church and State’’ ،Chapter VII ،Polygamy ،page 404.


tambaye shi a gida har wayau akan haka, 11 sai yace masu: “duk wanda ya saki matar shi ya auri wata yana zina da matar farko. 12 idan kuma mace ta saki mijinta ta auri wani tana zina”)


Injila na luka (16/14): (14 firisanawa sun kasance har wayau sunajin wannan dukkan sa, kuma suna son kudi, sai sukayi isgilanci dashi. 15 sai yace masu: “kune wanda kuke sanya kanku karkashin mutane! Amma Allah yana sane da zukatan ku. Lallai me girman kai agun mutane me datti ne na kafar allah. 16 namus da annabawa sun kasance zuwa ga Yuhana. Daga wannan lokaci ake masa bishara da madafun Allah, ko wannane fisgi kansa zuwa gareshi. 17 sai dai gushewar sama da kasa yafi sauki akan fadi dugo daga na namus. 18 duk wanda ya ski matar say a auri wata yana zina ne, kuma dukkan wanda ya auri wacce aka saka yana zina ne”)


Injila ta Mathew "(5/31): (31 sai akace: duk wanda ya saki matar sa to ya bata littafin saki. 32 amma ni kuma ina ce maku: lallai duk wanda ya saki matar sa sai dai saboda tayi zina, duk wanda ya aure wacce aka saka to zina yakeyi).”


Kamar yadda muka gani cikin wannan nassuka guda uku wabda yake magana akan saki da Karin aure, a cikin jumlar (sai dai a farkon halitta namiji da mace Allah ya halicce su) wanda ake nufi anan Adam da Hauwa da aka koroshi cikin maganar da siffar kowa, amma bece Karin aure ba haramun tun farkon halitta, saboda hakan zaici karo da abunda aka sani a cikin littafi me tsarki na Karin auri musamman ga annabawa. Akan haka wannan nassuka basa dacewa da yin hujja dasu akan haramcin Karin aure sai dai ayi


hujja dasu akan haramcin saki, shin koda kuwa mata day ace ga mutum ko kuma sama da haka. Kuma nassuka sun Ambato yanayi daya wanda aka amince yin saki a ciki shine idan mace tayi zina, anan wurin ya halatta miji ya sake ta, amma idan ya saketa domin zalumci ko kuma mugunta ba tare da tayi zina ba, sai kuma ya auri wata to yayi zina da ita (ai ya ha'ince ta kamar yayi mu'amala ne na aure da wata mace wacce bata halasta a gareshi ba), amma nassin bece duk wanda ya auri wata mata ba kari akan matar sa ba tare da ya sake ta ba cewa yayi zina ko ya ha'ince ta, wance yake cikin yanayi a jumla (idan mace ta saki mijinta ta auri wani mijin na daban to tayi zina) anan wurin ya alakanta siffar zina da sakin miji ba wai da Karin aure ba, da ace abunda ake nufi anan akrin aure ne ta yaya Karin aure zai kasance cikin halin matar da ta saki mijinta ta auri wani mijin na daban (shi kadai) ko kuma miji ya saki matar say a auri wata matan (ita kadai)?!! Watan da ace matslar itace Karin aure da sakin miji ga matar sa da kuma aure wata ya zama halal!! Sai dai abunda ake nufi shine rashin sakin miji ga matan sa koda kuwa yana da mata sama da daya. A cikin wani jumlar (duk wanda ya auri wacce aka saka to yana zina ne) anan wurin wannan jumlar yana nuna wa a bayyane cewa mijin daya auri macen da aka saki koda kuwa farkon auren sa da ita kenan, to hakan zina ne, bawai saboda Karin aure bane domin kuwa shi beyi karin ba, a'a dalili shine ya auri wacce aka saka.


Anan wurin zamuga tsantsan sabanin cikin nassi a tsakanin injila na Markis da Injila na Luka, maganar su ya Ambato labari daya ne sai dai da nassi mabanbanci matuka cikin abunda yake nuna rashin dacewar kafa hujja da dukkanin su da kuma daukan su a matsayin nassi me tsarki wanda akayi wahayi dashi daga wurin Allah ko


kuma a jingina su ga shugaba almasihu amincin Allah ya tabbata a gareshi.


Sakon bulus na farko zuwa ga corinthians (7/1): (1 amma ta bangaren al'amurar da kuka rubutumin akan su: abunda yafi shi kada mutum ya taba mace. 2 amma saboda zina, kowa ya kasance yana da mata, kuma kowa ta kasance tana da miji…8 sai dai ina fadi ga wanda basu da aure da zaurawa, cewa yafi masu kyau su zauna kamar yadda nake. 9 amma idan bazasu iya kamewa ba to suyi aure. Domin aure yafi dacewa dasu dayin motsi.)


Anan wurin yana cewa (kowa ya kasance yana da mata) ma'anar wannan maganar bata da alaka da haramta Karin aure, tana nufin kada wani ya taba matar da ba nashi ba, watan kada yayi zina da ita, wannan shine cikin cewa: kowa a cikin mu ya kula da yaron shi, ko kuma kowa acikin mu yak are gidan sa ko dukiyan sa ko kasuwan cin sa, kuma kamar yadda aka fadi cikin Safar samuel na farko (15/3): (3 yanzu tafi sarakuna kuma ku haramta duk abunda suka mallaka, kada kuma ku masu afuwa, ku kashe miji da mata, yaro da wanda ake shayarwa, shanuwa da akuyoyi, rakumi da jaki) anan ba ana nufin ka kashe miji daya da mace daya da yaro daya da jaki daya, ana nufin dukkanin jinsin namiji da mace yara da jakuna zuwa karshe. A cikin fadin sa cewa (saboda aure yafi dacewa dasu akan motsi) babu nuni akan haramta Karin aure, cewa yayi yin aure ko kuma barin shi abude yake.


Akwai daya wa maluma – fadoji – da kiristoci na bangarori masu yawa wanda suke tabbatar da rashin samun haramci na Karin aure cikin kiristanci, kuma dayawa daga cikin su sun auri mace sama da daya, kamar sarkin sharlyman,


Imbiradur faltiniyan na farko, Lusar da sauran su, kuma hakika marubuciya mathilanda juslyn ta ambaci haka tana cewa:


“lallai yana cikin abunda aka sani a cikin tarihi wanda babu jayayya a cikin sa, cewa ko wanne cikin coci na kiristanci da kasar kiristanci tsohon zamani mabanbanta da kuma kasan bukatu mabanbanta, wanda sukaba shuwagabannin su dacewa na Karin aure. Imbiradur faltiniyan na farko a karni na hudu na miladi yaba kiristoci hakkin auren mata biyu, a kuma karni na takwas sarki sharlyman wanda shine shugaban coci da kasar kiristanci, ya auri mata shida kuma wasu daga cikin masana tarihi sun Ambato cewa matan shi tara.. lusar dakansa me rike da littafi me tsarki na tsohon da sabon alkawari yana cewa: ina tabbatarwa daga gareni cewa idan mutum yanason auran mace biyu ko sama da haka, bazan iya haramta mashi hakan ba, kuma aikin sa be sabawa littafi me tsarki ba.”45


Augustine me tsarki yace: “yanzu a zamanin mu wannan, bayan munyi aiki da doka na romaniya, mutum bazai iya auren wata mata ba kari akan matar sa matukar matar sa tananan da rai.”46


Wannan yana nuni akan dalilin haramcin Karin aure shine dogaro da doka na romaniya bawai saboda nassuka ba na addini. Kuma ya kara cewa Augustine me tsarki:


45 Matilda Joslyn Gage، ‘‘Women، Church and State’’، Chapter VII، Polygamy، page 398.


46 St. Augustine of Hippo، ‘‘Moral Treatises Of St. Augustine’’.


“wani lokaci na daban, Yakubu dan Ishaq an tuhume shi da aikata laifi babba saboda ya auri mata hudu, sai dai ba'a samu asali ba na wannan tuhumar, saboda Karin aure ba lafi bane saboda ansan haka, sai dai yanzu ya zama laifi saboda ana daukan shi haka a al'adance… dalili daya tilo na daukan Karin aure a matsayin laifi shine saboda al'ada da doka sun haramta shi.”47


Domin fahimtar mahangan musulunci game da karin aure ya wajaba musan abubuwa masu zuwa hakan haka:


1. Lallai musulunci bashi kaidai bane addinin daya shar'anta Karin aure, sai dais hi kadai ne addinin daya iyakan ce adadin matan da mutum zai iya aure wanda hakan halal ne a cikin sauran addinan baki daya, Haris dan Kais yace:


(na musulunta inada mata takwas, sai nafadama manzon Allah s.a.w hakan sai manzon Allah s.a.w yace: “zabi hudu acikin su”) (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi)


2. Lallai Karin aure a musulunci bawai yana cikin al'amura na wajibi bane akan ko wani musulmi wanda idan be


47 Philip Schaff، ‘‘Nicene and Post-Nicene Fathers’’: First Series، Volume IV St. Augustine: The Writings Against the Manichaeans، and Against the Donatists، Book XXII، Page 289.


aikata ba zayyi zunubi da kuma daukan sa a matsayi me nakasashen addini, a'a Karin aure yana cikin ayyuka ne na halal duk wanda yaso ya aikata wanda kuma beso ba bazai aikata ba, misalin sa kamar misalin sauran ababe halal ne a musulunci. Wanda ba'a kama musulmi da laifi idan be aikata su ba.


3. Sanin dalilin saukar ayar Karin aure, gabanin karanta ayar alkur'ani me girma wacce ta halasta Karin aure da kuma iyakance shi da hudu ya kamata mu karanta ayoyin alkur'ani wanda ta gabace ta da kuma fahimtar su da fahimtar dalilin saukar ta domin musan cewa bata sauka ba face domin bada kariya ga mace da kuma kiyaye mata hakkokinta.


Allah madukaki yace:


“yaku mutane kuji tsoron ubangijin ku wanda ya halicce ku daga rai daya ya kuma halitta masa mata daga gareshi sannan ya yada a tsakanin maza dayawa da mata; kuji tsoron Allah wanda kuke roko kuma kuke sada zumunta domin shi; lallai Allah ya kasance me sa ido akan ku (1) kuma kuba marayu dukiyoyin su kuma kada ku cudanya datti da me kyau kum akada kuci dokiyoyin su cikin dukiyoyin ku; lallai hakan ya kasance laifi me girma (2) idan kuma kunji tsoron cewa bazaku iya adalci bag a marayu to ku auri abunda ranku yaso cikin mata biyu ko uku ko hudu; idan kuma kunji tsoron cewa bazaku iya adalci ba to ku auri daya ko kuma abunda kuka mallaka na bayi; hakan shi yafi domin kada kuyi zalumci (3) kuma kuba mata sadakin su kyauta a garesu; idan sun tsammaku wani abu daga cikin sa to kuci halal ne agareku (4) kuma kada kuba wawaye dokiyoyin ku da Allah ya


sanya ku tsayayyu akai kuma ku rika azurta su a cikin sa da tufatarwa kuma ku rika fada masu magana me dadi (5) kuyi ma marayu jarabawa har idan sun isa aure kuma kun ga shiriya a tare dasu to ku basu dukiyar su kuma kada kuci ta domin barna da gaggawa gabanin su girma; wanda ya kasance mawadaci acikin ku to ya kame wanda kuma ya kasance talakawa to yaci dai-dai misali; kuma idan kun basu dukiyar su ku samu shedu akan haka; kuma Allah ya isa zama me hisabi (6)” (suratun nisa'i 1-6)


Allah madaukaki a farkon ayoyin nan masu girma ya umurce mutane da jin tsoron sa da kiyayeshi kuma suba marayu wanda aka masu wasaici akan su dokiyoyin sui dan sun kai shekarun balaga kuma sunga ikon su akan iya kiyaye dukiyar, kuma kada su zalumce su ta hanyar cin dukiyoyin, larabawa sun kasance gabanin zuwan musulunci idan kawai wasaicin wani maraya karkashin wani daga cikin su na kudi, sais u cudanya dukiyar su dana shi sais u dauki me kyau aciki su bar mai lallataccen domin suyi masu dabara!! Imam Suddi ya ambata haka:


“ya kasance daya daga cikin su yana daukan akuya kusashiya cikin akuyoyin marayu, sai ya ajiye a maimakonta a kuya ramammiya, sai yace: “akuya da akuya", sai ya dauki dirhami me kyau ya ajiye mara kyau, sai yace: “dirhami da dirhami.”


Hakika Allah madaukaki ya hana wannan laifi na satan dukiyar marayu sai yace: (lallai hakan ya kasance laifi babba) watan zunubi me girma.


Salon yin wayau ga marayu haka yaci gaba da kuma cin kudin sui dan sun kasance mata ne, hakika Urwatu dan Zubair Allah ya kara masa yarda ya tambayi Aisha Allah ya


kara mata yarda game da fadin Allah madaukaki (kuma idan kunji tsoron cewa bazaku iyayin adalci ba ga marayu) sai tace: (ya kai dan dan uwata wannan marainiyan zata kasance a dakin waliyyinta (watan karkashin kulawan sa) tana hadaka cikin kudin sa sai kudinta da kyauta ya birgeshi, sai waliyyanta yaso aurenta ba tare adalci ba wurin biyan sadakinta ya bata abunda waninshi zai bata, sai aka hanasu auren su sai dai idan zasu iyayi masu a dalci, su basu mafi kololuwa na sadakin su, sai aka masu izinin auren abunda ransu ke so cikin mata wanda basu ba). (buhari ne ya rawaito shi)


Haka abun yake lallai wannan aya me girma ta sauka ne akan mutumin da yakecin hakkin marainiya wacce take karkashin wasaicin sa da kulawan sa, idan yana son auren ta ne kuma bazai bata sadaki ba kamar yadda ake bas aura mata irinta, to Allah madaukaki ya hanashi wannan al'amari kuma ya umurce shi daya bata sadakinta wanda aka sani anaba sauran mata irinta a al'adance, ko kuma ya barta kada ya aureta yana da zabin ayren wata mace wacce ba itaba, ko mata biyu ko uku ko hudu daga cikin mata wanda hakan shine karshen. Sai dai dayawa daga cikin makiya musulunci suna zuwa ne da hadafin sun a rufa ido wacce suka saba, sai su yanke sauran ayoyin wanda suka gabata su kawo dai-dai fadin Allah madaukaki (ku auri abunda ranku keso cikin mata biyu ko uku ko hudu) kuma sais u yanke abunda ke bayan ayar wacce sharadi ne na Karin aure waton adalci tsakanin matan!!.


Lallai musulunci ba umurni yayi bag a mutum daya auri wata mata ta daban ba kari akan matar sa, a'a ya halalta masa hakan ne sannan kuma ya sanya masa sharudda wanda mutum zai kiyaye su gabanin auren mace ta biyu daga cikin wannan sharudda akwai tabbatar da yin adalci a tsakanin su cikin abinci da tufafi da abunsha da wurin kwana, Allah madaukaki yace:


(idan kunji tsoron cewa bazaku iya adalci ba to ku auri daya) (suratun nisa'i ayata 3)


Kuma ya hana yin zalumci da mugunta a tsakanin mataye da kuma karkata zuwa ga wata daga cikin su, Allah madaukaki yace:


(kuma bazaku taba iyayin adalci ba tsakanin matan koda kun so hakan amma kada ku karkata matuka sai ku barta kamar sagalalliyan riga; idan kukayi dai-daito da jin tsoron Allah to lallai Allah ya kasance me gafara me rahama) (suratun nisa'i ayata 129)


Kuma manzon Allah s.a.w yace:


“duk wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ga daya daga cikin su, zai zo ranan alkiyama me shafaffen rabin jiki” (hadisi ne ungantacce. Ahmada da abu dawud da nasa'i ne suka rawaito shi)


Ya wajaba gareka dan uwa makaranci me daraja sanin cewa musulunci addini ne da duniya baki daya an saukar dashi ga dukkanin mutane cikin dukkanin zamani da wuri bawai an saukar dashi bane ga wasu mutanen ko al'umma guda ba saboda haka ka'idojin sa da shari'un sa zuna zuwa ne domin dacewa da tunanin su da abunda suke su, saboda haka ne


musulunci ya halalta ma maza auren mace sama da daya domin fahimtar waki'ina rayuwa da kuma uziri na rayuwan saboda haka abunda wani yake ganin be dace da wannan al'umma ba zai iya dacewa da wasu al'ummar wanda basu bah aka kuma abunda be dace ba da wannan zamani zai dace da wani zamanin bayan sa, kuma hakan rahama ne ga mata wanda zasu zauna gwagware idan akace kada a maza su auri mace sama da daya, duk wanda yakeson riko da wannan sauki sai yayi ya kuma kiyaye sharuddan sa wanda kuma baya so sai ya bari!!.


• Banbanci tsakanin shari'ar musulunci da dokoki – tsaruka - wanda dan adam ya kirkira.


• Ra'ayin littafi me tsarki akan dimukradiyya.


• Yancin da yin abunda mutum keso cikin shri'ar musulunci.


Akwai dayawa na dokoki na tsarin al'umma amma wanda sukayi galaba sune guda biyu ne kacal acikin su wanda aka sani a cikin wannan al'umma tayau, tsarin dimukradiyya da kuma mulkin soja, kuma dukkanin su biyun tsari ne wanda aka tabbatar da gazawar su daga a lokacin amfani dasu a duniya tsawon karnin da suka gabata da kuma rashin tabbatar da da zaman lafiya da adalci na duniya wanda duniya ke ikirari ayau. Abun mamaki shine duniya suna neman tsari wanda zai tabbatar masu da amincin su da zaman lafiya, a lokacin da suke rayuwa da ganin shari'ar musulunci kusa dasu, sai dai wasu manyan yan siyasa masu shan jinin mutanen su sun san cewa yin amfani da ita zai sa su rasa dayawa na mulkin su da abubuwan su da suka kebanta dashi, saboda haka ne suke fadima masu rubuta dokoki abunda suke so na hukunce hukunce wanda zai basu daman riko da madafun ikon al'ummar su da basu rinjaye akan al'amarin su.


Ma'anar dimukradiyya:


Kalmar dimukradiyya kalma ce ta yunani wacce aka samota daga kalmomi biyu,”zimus”wacce take nufin”al'umma”da kuma”kiratus”wacce take nufin hukunci ko mulki, ma'ana mulkin al'ammu ga kanta, hakan ta hanyar


tsayar da tsarin majilisar kasa wanda al'umma zasu zabi wanda zasu wakilce su cikin wannan majalisa, wanda acikin shi ne za'a tattauna dukkanin dokoki da kuma tabbatar da abunda ya dace acikin su da yardan mafiya yawan mutanen cikin majalisar, ma'ana idan mafiya yawan suka tafi akan ra'ayi to wannan shine ra'ayi wanda za'a zartar dashi dole koda kuwa akwai wani ra'ayin da yake karo dashi nay an cikin majalisar, saboda haka dokokin su da tsarin ba tabbatacce bane saboda yan majalisun da mambobin sa basa tabbata ana canza su. Allah yayi gaskiya wanda ya bayyana cikin alkur'ani cewa mutum besan abunda zai gyara masa hali ba face da hukuncin Allah yadda yace:


“da ace gaskiya zai bi son zuciyoyin su da sammai da kasa da abunda ke ciki su ya lallace; sai dai munzo masu da ambatin su kuma su masu kawar dakai ne daga ambaton su” (suratul muminun ayata 71)


Ma'anar dimukradiyya:


Tsarin mulkin soja akasin tsarin dimukradiyya ne baki daya, yadda ra'ayin shugaba ko zababbu ko kuma hukumar da take mulki shine ra'ayin da za'a zartar wajibi koda kuma ya sabama ra'ayin al'umma. Allah ya fadi game da fir'auna me mulki wanda yayi barna da zalumci a doron kasa ya kuma bautar da mutanen ta:


“Fir'auna yace ba'a ganin wani abu sai abunda kuka gani kuma bana shiyar daku face zuwa hanya ta shiriya” (suratul gafir ayata 29)


Lallai dayawa daga cikin mu a yayin jin wannan kalma na dimukradiyya abunda yake fara zuwa kwakwalwan su


shine ma'ana me kyau kamar lamuni na yancin mutum da kuma martaba ra'ayin wasu da yancin fadin albarkacin baki da yancin tsayar da alamun addini ga kasashe da kuma martaba hakkokin su da maslahohin su da kuma rashin danne su, amma a agaskiyan al'amari tsarin dimukradiyya tsari ne mulkin soga ko kuma ace tsarin mulkin shugaba, hakan kuwa saboda mafiya yawan lokuta anayin dokoki ne wanda suke dacewa da abunda yake so a cikin kasa koda kuwa wannan dokoki sunci karo da maslaha ta asali ko kuma aqidun wannan kasa ko kuma zai yajo cucarwa a garesu. Akwai yanayi na wannan zamani wanda zai bayya mana wani fuskar ta daban na munin wannan tsari na dimukradiyya.


• A shekara ta 2009 da sunan dimukradiyya an kirkiro doka da kuma aiwatar da ita wacce take hana gina wurarin kiran salla, kuma wannan doka anyita ne abisa ra'ayi na mafiya yawa wacce aka haramta wa musulmi marasa rinjaye gina wuraren kiran salla a masallatan su, wannan al'amari wanda ya sanya kungiyar lafiya na kasashe bayyana bacin ranta akan sakamakon wannna zabe wacce tace hakan yana kunshe da take hakkin na tilastawa swistzland yancin fadin albarkacin baki game da akida.


• Da suna dimukradiyya a cikin wasu birane na turawa har zuwa yau ba'a yarda da gina masallatai ba ga musulmai marasa rinjaye, ko wnai lokaci musulmai marasa rinjaye sukayi kokarin samun izini na gina masallaci, sai yan majalisu masu rinjaye na wannan kasa su kada kuri'a wanda zai hana basu wannan izini na gina masallaci, idan kuma sun samu yarda na izinin ginawa to sai kaga tazo da wasu ka'idoji masu wahala wanda sun isa su hana gina wannan masallaci.


• Da sunan dimukradiyya a cikin wasu kasashe na turawa akayi dokan hana mata musulmai sanya nikabi a cikin wurare na jama'a, suna masu nokewa da wasu hujjoji, daga cewa akwai cewa be dace ba a rufe fuska a wurin jama'a da makamantan su, dukda cewa wannan dalili zai iya karbuwa ga wasu mutane ta hanyar hankali, sai dai muna ganin ita dai wannan hukumar tana wajabtama masu tuka mashin rufe kansu da fuskar su akan tituna!! Shin wannan befi dacewa bag a masu tuka mashina su bude fuskokin su suma!! Kamar yadda akwai mutane dayawa cikin kasashe dayawa na turawa da kuma kasashen gabashin asiya kamar sin da tailand da makamantan su wanda suke ganin rufe fuska ga likita, saboda suna ganin zai kareshi daga kwayoyin cututtuka da rashin lafiya, amma babu wanda ya taba magana akan wannan al'amari har Abadan da cewa hakan be dace ba na rufe fuska a wuraren jama'a!! shin acikin hana mata sanya abunda suke so da zabin su ba rashin girmama zabin su bane da kuma iyakance masu yancin su na dan adam da kuma aqidun su na addini!! Bawai cewa idan baka yarda da aqidar wani bas hi kenan sai ka tilasta mashi sai ya barta, dayawa daga cikin uyan indiya suna sanya rawuna bakake akan kawuran su da kuma barin gashin su yayi yaw aba tare da rageshi ba, kuma suna harkoki cikin yancin a turai kuma ana basu ayyuka dayawa a cikin hukuma ba tare da ansanya su ba cire rawunan su, kuma babu wani wanda yake da hakki sanya shi cire wannan rawani ko kuma aske gashin saboda be natsu da wannan rawani ba ko kuma tsayin gashin.


• Da sunan dimukradiyya a cikin wata kasar da sukaci gaba wani jam'iyya tayi nasara cikin zabuka a birane


dayawa , sai ya kasance dokan sun a farko shine zasu hana kai abincin halal ga dalibai musulmai a makarantu wanda suke birane da sukaci nasara acikin su a zabuka, kuma haka aka wajabtama makarantu kai abinci wanda suka kunshi laman alade da kuma wasu namukan wanda ba'a yanka su ba abisa karantarwan shari'ar musulunci ga dalibai musulmi, wanda yafi dace dasu da kawo dokoki wanda zasu dakila barna da kuma lamuntan yanci.


• Da sunan dimukradiyya a cikin wata kasa wanda suka ci gaba anyi doka wanda zai hana hanyar yankan halal a cikin kasar, abunda yake nufin hana musulmai samun naman da aka yandai dai dai da karantarwan musulunci, kuma hadafin haka shine kuntatawa musulmai domin su fice daga kasar zuwa wata kasar wacce zata martaba iqidunsu, dukkanin wata dabba wacce aka kashe da wutan lantarki ko kuma ta hanyar cire mata kai da wuka na karfe har ta mutu ko kuma aka shaketa ko kuma rufeta a inda babu iska ko nutsar da ita cikin ruwa musulmai bazasu iya cin namanta ba.


Wannan kadan ne daga cikin misalai nayin amfani da masu jinyaje a toye hakkin marasa rinjaye, hatta hakkinta na gudanar da addinin ta cikin yanci ba tare da tsangama ba ko kuma kuntatawa, ko kuma hakkinta na zabin irin kayan da zasu sa ko kuma kai hatta irin abincin da sukeson ci!! Daga cikin wannan misali da sauran su zai bayyanan maka cewa tsarin dimukradiyya ko kuma almaniyawa a zahirin magana bazai iya rayuwa ba sai ga karon kansa kadai, amma ga marasa rinjaye yana furta abubuwa dayawa na hujjoji domin ya danne su da kuma kuntata masu yana me zargin cewa bazasu iya rayuwa ba da wasu tsarin na daban!! Ita kuwa


shari'ar musulunci sabanin haka ne, ya tattara dukkanin mutane bisa banbancin addinin su hakika ya nassanta hakkokin marasa rinjaye ya kuma sanya wannan hakkokin ya fita daga ikon masu rinjaye, kai ya kuma wajabta ma masu rinjaye lamuni na kiyaye wannan hakkoki da kuma rashin ketare su, koda kuwa ra'ayin masu rinjayen ya sabama hakan, anan wurin ba'ayi hujja ba da ra'ayin masu rinjaye matukar yaci karo da hakkokin wanda shari'a ta nassanta akan lamunin. Duk wanda yake neman Karin bayani akan wannan maudu'i akwai littattafai masu yawa wanda suke magana akan hakkoki na wand aba musulmai wanda suke cikin kasashen musulmai, zasu iya komawa zuwa garesu, kuma Allah yayi gaskiya:


“kuma idan kayi biyayya ga mafiya yawan mutanen duniya zasu batar dakai daga hanyar Allah; ba komai suke bi ba face zata kuma su din ba komai sukeyi ba face kiyastawa” (suratul an'am ayata 116)


Babwa wata tsari na mutum duk yadda takai wacce zata iya tabbatar da rayuwa lafiyayye ga al'umma haka kuma rayuwa lafiyayye a cikin al'umma kanta kamar yadda shari'ar musulunci tayi kuma dalilin haka shine ita tsari ne da dokoki na Allah wanda ya saukar dasu ga mutane kuma shine mafi sanin abunda ya dace dasu, Allah madaukaki yace:


“shin wanda yayi halitta besan halittansa ba kuma shi me tausayi ne kuma masani” (suratul mulku ayata 14)


Amma shi littafi me girma yayi gifa da dimukradiyya baki dayan sa Bulus yana cewa cikin sakon sa zuwa ga mutanen Rumiyya (13/1): (1 kowa yayi biyyay ga shuwagabinni manya, saboda babu wani sarki sai daga Allah, kuma shuwagabanci martaba ne daga Allah 2 har wanda yake fito na fito ga shugaba yana fito na fito ne ga tsarin Allah, masu fito na fito za'a su kama kansu anan duniya. 3 lallai shuwagabanni basu da tsoro ga ayyukan su na kwarai sai ga na sharri. Shin kuna son sabama shugaba? Ka aikata abunda ya dace zai ya zaman maka yabo akan haka, 4 domin kuma me gyara kadimin Allah ne! amma idan ka aikata sharri kaji tsoro, domin wuka bata daukan wasa, saboda kadimin Allah ne, me hukunci ga wanda ya aikata sharri. 5 saboda haka ya wajaba kayi biyayya a gare shi, bawai saboda fushi ba kawai, a'a saboda wakilinsa. 6 lallai ku saboda haka zake bayar da jiziya, saboda kadimin Allah ne masu dagewa akan haka. 7 ku bayar da dukkanin hakkokin su: jiziya ga wanda yake da jiziya. Kariya ga wanda yake da kariya. Tsoro ga wanda yake da tsoro. Girmamawa ga wanda yake da girmamawa.)


Shari'ar musulunci ta nassanta akan yancin fadin albarkacin baki wanda yake aka iyakance da sharuddu na shari'a wanda zasu gyara al'umma kuma bazasu batata ba da kuma hada kai tsakanin mutane da kuma tabbatar da hadafin


su wanda suke musaya a tsakanin su, bawai yanci bace wanda babu tsari me rusha gina da lalatawa da kuma haifar da gaba a tsakanin al'umma, yanci wacce bata ta'aji akan hakkokin mutane da kuma take su, Allah madaukaki yace:


“yaku wanda sukayi imani kada wasu mutane su rika yima wasu mutane isgilanci me yuwa sunfi su alheri; ko kuma mata su rika yima mata me yuwa sunfi su alheri, kada ku rika aibanta kawunan ku kuma kada ku rika jifan juna da sunayen banza, tur da sunan fasikanci bayan imani; duk kuma wanda be tubaba to wannan sune azzalumai” (suratul hujurat ayata 11)


A daidai lokacin da muke ganin shiri na kushewa na zolaya wanda suka cika kafafen yada labaru cikin kasashe dayawa a duniya wanda suke ikirarin ci gaba amma basu damu ba da halin wanda suke kushewa ba ta salon a wasa na wulakantacce, wannan izgilancin wanda dokan dan adam ke kira da sunan yanci na ra'ayi wanda ya kunshi yancinta! Kuma ya tabbata cewa wannan shiri a cikin wasu kasashe shiri ne kawai na misiltawa basu da wani alaka da yancin fadin albarkacin baki, inda suke samun gudun mawa na kudi gada wurin wasu yan siyasa domin raunata abokin hamayyar su da kuma janye masa mutane.


Amma shi yanci na ra'ayi a shari'ar musulunci an takaitashi da wasu sharudda wanda da mutum zai wuce su to zai zama wanda yayi ta'adi ga hakkokin mutane ko kuma al'umma, misali al'amarin izgilanci ga manzon Allah s.a.w menene sakamakon da zai biyo bayan sa, sannan kuma menene abunda za'a samu na alheri sakamakon haka? Shin acikin haka babu ingiza kiyayya a tsakanin zukatan mutane ko kuma a zuciyar musulmi da wanda baya yin musulunci a cikin


al'umma, shin ta'adi akan mamata da kuma rashin mutunta su wani alama ne ci gaba gabanin ace addini ne? ina da yakinin cewa duk wanda ya aikata haka ko taimakawa akan haka da wani zai zagi mahaifan sa ko kuma yaran sa ko dan wani wasan sa dayake so ko dan film wanda yakeso bazai tsaya ya lankwashe hannu ba yana gani zayyi kokarin kare shi ta ko wani hanya, ka sani cewa wannan kasashe da aka muzanta annabi cikin annabawan Allah a cikin su suna karkashin inuwar fadin albarkacin baki, laifi ne a shari'ar su muzanta wani shugaban kasa ko kuma firaminista ko kuma rage masa mutunci ta ko wani irin yanayi ne!! shin bazai yiwu bane yin zanen shugaban kasa na shagube domin muzantawa duk a karkashin yancin fadin albarkacin baki?!!


Kuma hakika musulunci ya haramta zagin addinin wasu domin gudun jawo fitina da kisan wasu mutanen al'umma, saboda haka ya zama wajibi akan masu hankali su kama hannun wanda yake son kunna fitina da rura kiyayya tsakanin al'umma wanda sakamakon ta zai iya zama yaki wacce zataci kowa, Allah madaukaki yace:


“kada ku zagi abunda suke kira koma bayan Allah sai su zagi Allah suma domin kiyayya ba tare da ilimi ba; da kaman haka ne muka zayyanawa ko wace al'umma aikinta sa'annan zuwa ga ubangijinsu zasu koma sai ya basu labari akan abunda suke aikatawa” (suratul an'am ayata 108)


Ka sani cewa al'amarin isgilanci ga manzon Allah s.a.w bawai sabon abu bane wanda aka kirkira a wannan zamani, ya fara tun daga lokacin da aka aiko shi, hakika sun kira akan haka da suna makaryaci da boka da mawaki da mahaukaci, kuma alkur'ani ya mabato haka cikin fadin sa cewa:


“kuma hakika mun sani cewa zuciyan ka na kunci saboda abunda suke fadi; kayi tasbihi da godiya ga ubangijin kuma ka zama cikin masu sujjada; kuma ka bautawa ubangijin ka har sai yakini yazo maka” (suratul hijri ayata 97-99)


Iyakance yancin fadin albarkacin baki kuwa bawai sabon abu bane wanda ya takaita ga shari'ar musulunci kawai bane a'a, wasu al'ummomi ma sun takiata yancin fadin albarkacin baki ga mutanen ta dai-dai da addini da kuma maslahar mutanen ta, birtaniya misali ta hana yada fim akan Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi da hujjar cewa addinin kiristanci yana cikin tsari na kasa wanda ya zama wajibi a mutuntashi da kiyaye shi. Kuma kasashe dayawa suma sun takaita yancin fadin albarkacin baki akan mutanen ta idan wannan yancin zai taba yancin yahudawa ko kuma kawo cikas ga Holocaust yadda wannan kasashe suke himmatuwa da wannan ayyuka da kuma yin ukubar dauri a gidan kurkuka akan hakan.


Hakika shari'ar musulunci ya shirya ga yancin wacce take kira zuwa ga kyakyawan aiki da kuma hani ga mummunan aiki wuri me kyau wacce zata girma a ciki da tabbata taba ko wani mutum hakkin sa nayin goganya da fadin ra'ayi akan abunda ya shafe al'umma kuma fadakarwa na Allah be sauka akan hakan bay a sanya hakan wurin yin shawara a tsakanin su, Allah madaukaki yace:


“da rahamar Allah ne ka zama mai tausasawa garesu, amman da ace ka zama mai tsanani kuma mai fishi da sun waste daga gefenka, ka musu yafiya kuma ka nema musu gafara sannan ka zama mai shawartarsu cikin lamuranka, idan kuma ka yunkura yin wani abu saika


dogara ga Allah, lallai Allah yana san masu tawakkali” (suratu ali Imran aya ta 159)


Kuma ya wajabta cewa yancin fadin ra'ayi nauyi ne akan kowa domin hakan ya zama me fayyacewa tsakanin gaskiya da karya, saboda fadin Abdullahi dan mas'ud Allah ya kara masa yarda:


“kada ku zama masu dogaru akan ra'ayin wsu kuce idan mutane sun kyauta sun kyauta idan sunyi zalumci munyi zalumci sai dai ku shirya kawunan ku idan mutane sun kyauta kuma ku kyauta idan kuma sunyi kuskure kada kuyi zalumci” (sunan al tirmizi, hadisi ne maukufi – wanda aka jingina shi ga sahabi)


Wannan yancin bata zama wacce ta takaitu ga ga wasu mutane kawai a'a ta kowa ce karkashin ka'idoji na shari'a, wacce wanda aka aiko rahama ga talikai ya zartar da ita a aikace domin al'ummar bayan sa suyi koyi dashi, Abu Sa'id al khudri yana cewa:


“wani mutum bakyauye yazo gun manzon Allah s.a.w wanda bashi yamai katutu akai sai al'amarin ya mashi kamari har yace mashi: bazan bark aba har sai ka biyamun bashi na, sai sahabban sa suka masa tsawa sukace: kaicon ka kasan wanda kake yima magana kuwa? Sai yace ni hakkina nake nema, sai manzon Allah s.a.w yace: lallai kuna tare da me hakki, sai yayi aike zuwa ga Kuwaila yar Kais yace mata: idan akwai dabini agunki ki ranta mani har akawo mana dabinon mu sai na biyaki, sai tace: eh ya manzon Allah nabada mahaifana fansa agareka, sai yace: sai ta ranta mashi ya biyama wannan bakyauye bashi kuma ya ciyar dashi, sai yace: ka cika kaima Allah ya cika maka, sai yace: wannan sune


zababbun mutane, lallai al'umma bata samun tsarkaka matukar basa amsan ma me raunin cikin su hakkin sa ba tare da wahala ba” (albani ya ingantashi cikin sahihu sunan Ibn Majjah da kuma sahihul jami'u: 1857)


Sahabban sa da suka zo bayan sa sunyi koyi dashi a lokacin da akayima Abubakar Assiddiq Allah ya kara masa yarda mubaya'a da khalifanci yah au minbari yayima mutane huduba wacce ta kunshi ginshikai na shugabanci a musulunci na abubuwan da mutane basu tabbatar dashi ba a karkashin shari'u na dan adam wanda yake yima son rai hidima da burin a siyasa da tattalin arziki, sai yace: (yaku mutane, hakika na zama shugaba akanku bawai nafiku alheri bane, idan kunganni akan gaskiya to ku taimake ni, idan kuma kun ganni akan bata to ku mun gyara. Ku mun bayayya matukar nayima Allah biyayya a cikin ku, idan kuma na saba masa to kada kumun biyayya, ku saurara kuji me karfi acikin ku me rauni ne aguna har sai na amsa hakki a hannun sa, kuma me raunin cikin ku me karfi ne a guna har sai na amsan masa hakkin sa, ina fadin wannan magana nawa kuma ina rokon Allah gafara gareni da ku baki daya.)48 (siratun nabawiyya na Ibn Hisham, da dabakat na Ibn sa'ad, da nihaya wal bidaya na Ibn kasir kuma yace isnadin shi ingantacce ne).


Yancin yi addini: shari'ar musulunci ta nassanta akan lamunin yanci na yin addini ga wand aba musulmai ba na yahudawa da kiristoci ba tare da tsangwame ba, ba'a tilastawa


48 Littafin Asar na Ibn Badis


wani barin addinin say a koma musulunci, Allah madaukaki yace:


“babbu tilastawa cikin addini; hakika shiriya ya bayyana daga bata” (suratul bakara ayata 256), a lokacin da tarihi yake Ambato mana tsangwamen da kiristoci ke fama dashi a tsakanin su sakamakon banbancin aqida.


Yancin yin ilimi: shari'ar musulunci ta nassanta akan yancin yin ilimi da karatu da kuma daukaka martaban malamai zuwa kololuwa, a daidia loakcin da tarihi yake Ambato mana ciwon kai me tsanani tsakanin coci da ilimi da maluma wanda aka hana yancin yin ilimi.


Haalima shari'ar musulunci ta wajabta wa ko wnai musulmi neman ilimi, manzon Allah s.a.w yana cewa:


“neman ilimi wajibi ne akan ko wani musulmi” (abu dawud da Ibn majjah ne suka rawaito shi kuma yana cikin sahihul jami'u)


Kuma shari'ar musulunci ta daga darajar malamai zuwa kololuwa, Allah madaukaki yana cewa:


“Allah zai daga wanda sukayi imani acikin ku wanda kuma aka basu ilimi suna sama a daraja; kuma Allah masani ne game da abunda kuke aikatawa” (suratul mujadala ayata 11)


Kamar yadda muka gani cikin sakon Bukus zuwa ga mutanen Rumiyya (13/1), wannan sakon tayi watsi da dukkanin abunda yake da ma'anar dimukradiyya ko yancin yin abunda kakeso, hasalima ta assasa ka'idoji ne na mulkin soja da kuma sarauta da biyayya ga shugaba biyayya kai tsaye mara shamaki.


• Halin duniya gabanin a rarraba iyakoki da kuma bayan bayyanar musulunci.


• Mutane akan tafarkin addinin sarakunan su.


• Wajabta addinin kiristanci da bakin takobi.


• Jihadi da kuma lamuni na yancin yin addini.


• Sakwannin manzon Allah s.a.w domin kariya ga kiristoci.


• Jihadi a musulunci da kuma karka suwan sa


1. Matakai na jihadi.


2. Abubuwan da suke hana jihadi.


3. Hadafi da manufa na yin jihadi.


4. Suwa ake nufi da jihadi.


5. Ka'idoji na jihadi.


• Shin ko wani yaki ne na musulmi yake jihadi.


• Yaki me tsarki.


• Banbanci tsakanin yaki da jihadi.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH