Labarai




9 Louis XVI.


10 Hanged, drawn and quarter, sir Thomas Armstrong.


11 Disembowelment or evisceration, Balthasar Gerrard.


12 Lynda Lyon Blok.


13 Drownings at Nntes, Noyades de Nantes.


Giles Corey14 a shekara ta 1692 a amerika, wani lokaci kuma a jefa shi cikin mai me zafi kamar yadda akayima Richard Rice15 a shekara ta 1531 a kasar amerika, wani lokaci kuma a sanya shi cikin dakin iska na guba, wani lokaci kuma a birne shi da ransa kamar yadda ya faru ga mazuna birni yan kasar china daga rundunan almaniyawa a wani mayanka me suna Nanakij a tsakiyan yakin duniya na biyu, wani lokaci kuma sassake jikin sa daga sama zuwa kasa da zarto na karfe16, wani lokaci kuma a daureshi da igiya sannan a yankashi da dates kansa da wuka kamar yadda ya faru da Germier Branrich a shekara na 1817, wani lokaci kuma a daureshi akan turaku guda hudu ta yadda zai rabashi gida hudu kamar yadda ya faru ga Tobak Amaro ashekara na 1781 a beru a hannun masu mulkin mallaka na spaniya17, wani lokaci kuma a fasa cikin mutum da ransa kamar yadda ya faru ga Juzeaf Marchand18 a shekara na 1835 a garin pantanamo, wani lokaci kuma a tsoke shi, wani lokaci kuma a harbeshi da harsashi, wani lokaci kuma a tilasta masa kwanciya rubda ciki ya bude bakinsa sai yasa kan kaifin takobi abakin sa sai yani mutum da taka kansa yadda takobin nan zai yanke masa baki da kansa sai yam utu wannan itace hanya wacce tafi a wurin mutanen Naziyya na kasar amerika wurin kashe bakake19, da sauransu na hanyoyin daban na rashin imani da shiririta wanda yasha banban wurin azabtarwa mabiya da hukuncin kisa a lokacin zartar da wannan hukunci a garesu kamar yadda dokokin su ya


14 Kisa ta hanyar rataya, Giles Corey.


15 Richard Rice.


16 Kisa ta hanyar yanka mutum da zarto.


17 Dismemberment, Peru, Tupac Amaru II


18 Slow slicing, Joseph Marchand.


19 Bite the Curb, or Curb stomp.


tanada!!! Saboda haka lallai shari'ar Allah rahama ce, wanda baya fadi wani ukuba mara amfani, kuma bai bar mana wata kafa ba kara bita domin son zuciya ko kuma wasan masu kirkiran dokoki na shiririta. Hatta tare da dabbobi hakika shari'ar musulunci ya fadi cewa a rika yin rahama da tausayi ga dabbobi hatta a lokacin yanka su domin cinsu, hakika manzon Allah s.a.w yace:


“lallai Allah ya wajabta kyautata akan komai, idan zakuyi kisa to ku kyautata kisan, sannan idan kuma zaku yanka dabbobi ku kyautata yankan, dayanku ya wasa wukarsa domin ya hutar da dabbar sa” (muslim ne ya rawaito shi)


Mutanen amerika ta tsakiya sunyi aqidar yankan mutum20 a masarauta ta Ibriradhuriyya Aztik21 wanda mulkinsa ya dauretun daga karni na sha hudu na miladiyya har zuwa karni na sha shida miladi, sunyi mulki a jihar da ake kira ayau kasar Mexico, yadda bokaye suke halartar yankan mutane sais u sanya su akan dutse babbasai boka ya tashi ya tsaka cikin wannan mutumin da za'a yanka da ransa ya fito da zuciyar sa shi kuma yananan kwance yana kallon rana domin neman yardan allan Rana wanda ake kira huitzilopochtli22-


20 Yanka mutane.


21 Aztec.


22 Huitzilopochtli.


Allah yayi mana tsari-, ko kuma dan neman yardan allan Ruwa wanda ake kira Tlaloc23, ko kuma neman yardan allan Rana wanda ake kira Huehueteotl24 ta hanyar hada wani biki na addini domin wannan alheri wanda zasu jefa mutanen da ransu cikin wuta kafin su mutu sai a fito dasu daga wutan a tsaga cikin su a cire zuciyar.


Daga cikin kayaryakin wannan masarauta na Imbiradhuriyya xewa lallai allar Xipe Totec25 ya yanka fatansa domin ya baima dan adam abunda yakeso na zirra, saboda haka ne ya nema daga dan adam daya ya rika bashi fatar jikin sa a madadin wannan fata nashi, a dalilin haka ne bokaye suke tashi domin karrama wannan allan ta hanyar yanka fatar wanda za'a yanka cikin mutane sa'annan su sanya wannan fatar ta mutanen da suka yanka a jikin sun a tsawon kwanaki ashirin bayan wannan kwanaki sai su jefa fatar a wuta!!


A Afirka kuma misali akan irin wannan abu suna da yawa, kamar misali a bukin shekara na masarautan Dahumi26 wanda aya ake kiranta da suna jamhuriyya ta Benin27 a yanmacin Afrika, sun kasance suna zuwa fursinoni da bayan da aka kama agun yaki sais u yanka su amatsayin bangare dokokin wannan buki na shekara, kamar yadda a lokacin mutuwar sarki suke yanka dubbannin fursinoni, an yanka a cikin shekara ta 1727 miladiyya mutum 4000 a rana daya kawai!!.


23 Tlaloc.


24 Huitzilopochtli.


25 Xipe Totec


26 Annual Customs of Dahomey


27 Benin


A cikin al'adun china tsohuwa ya kasance suna birne bayi da ransu a lokacin da wani shugaba yam utu, a shekara ta 621 gabanin haihuwar annabi Isa sarki Moo28 ya mutu wanda shine sarki na bangaren Keen29, sai aka birne bayi (177) tare dashi da rayukan su.


A cikin mutanen Assalaafiyya, a cikin karni na goma sha biyu an yanka bayin da aka samo a wurin yaki da kuma gabatar dasu adomin neman kusanci ga allar mutanen aslaf30 berun31.


A kasar fabacin Asia a inda addinin Buzanci ya yadu munga hotuna a wannan zamani a kafar yanan gizo na matukar rashin imani, a ranar farko ta shekarar siniyya wasu daga cikin Buzawa suna zuwa da yan mata bayan sun nemi izini daga iyayen su, sais u wanke su da masu kwalliya da daure hannayen su daga baya sai suke su da wuka a wuyan su kamar yadda ake suke alade sai su sanya kwarya a karkashin wuyan nasu domin su tara jinin a ciki daka ya zube a kasa, daganan kuma sai su yayyanka gangan jikin su gunduwa gunduwa su raba naman su ga talakawa!!.


A cikin littafi me tsarki na kiristoci da yahudawa mungani a cikin littafin (safar) alkalai (11/29): (29 sai ra hin ubangiji ya koma zuwa ga Yaftah, sai ya wuce kasar Jil'ada da Manasaya da misfada jil'ada, daga cikinta sun gabata kamar yaran Ammun. 30 sai Yaftah yayi bakance ga ubangiji yace: << idan ka taimake ni akan yaran Ammun, 31 to idan na dawo lafiya daga wannan yaki na


28 Mu


29 Qin


30 Slavs


31 Perun


yaran Ammun, zan koma zuwa ga ubangiji konanne: farkon wanda ya fita daga cikin kofofin tsakanina da haduwa dasu>>. 32 sa'annan ya fita zuwa yakin yaran Ammaun, sai Allah bashi nasara akansu, 33 yayi kaca kaca dasu tun daga Aru'ir har zuwa Minnita kusan birane ashirin zuwa Abalil kurumi. Haka dai bani isra'ila suka mika wuya ga Ammunawa. 34 sa'annan ya Yaftahu ya koma gidan sa cikin Misfatim sai yarinyar sa dayake dashi guda daya ta fito, domin tarbansa da kida da guda. 35 a lokacin daya ganta sai ya yamutsa kayan sa da walwala yana cewa: << ya diyata, hakika kin batamun rai da tayarmun da hankali, domin kuwa nayima ubangiji bakance kuma babu hanyar yanje wannan bakance nawa>>. 36 sai yarinyar ta amsa mashi: << hakika kayi bakance ga ubangijin, saboda haka ka aiwatar da bakancenka kamar yadda kayi alkawari, kuma musamman ma ubangiji ya taimakeka akan makiyanka na yaran Ammun>>. 37 sai tace ga mahaifinta: << amma ka tabbatar mun da wannan abu nawa da nake nema: ka sauraramun na wata biyu nayi yawo a cikin su a tsakanin duwatsu naci budurci na tare da kawata >>. 38 sai yace mata << to jeki>>. Ya saurara mata na wata biyu ta kwashe wannan watanni biyu ita da kawarta a cikin duwatsu taci budurcinta. 39 sa'annan ta dawo a karshen watanni biyun zuwa ga mahaifinta sai ya konata ya mikata domin cika wannan bakance nashi, sai ta mutu tana budurwa.)


Munga cewa littafi me tsarki cikin labarin daya gabata ya rawaito kisan Yaftahu ga diyarsa ta hanyar konata da rant aba tare da wani laifi ba, kawai domin yayi bakance ga Allah cewa idan ya bashi nasara akan makiyar sa zai kona farkon


wanda ya fito domin tarban sa daga cikin mutanen gidan sa bayan ya dawo, kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: (babu cika bakance na sabon Allah) muslim ne ya rawaito shi.


Wannan labari misali ne na wannan shari'u da akidu na shiririta wanda hankali me lafiya yake korewa, kuma babu wata kasa wacce ta tsira daga cikin irin wannan akidu na barna kamar akida na yanka mutane domin neman yardan allan da jinin mutum, duk wanda yakeson Karin bayani sai ya duba cikin tarihi na akidar yankan mutum cikin duniya zai gani da kansa yadda ta yadu a amerika da turai da Austireliya da afirka da asiya!!.


Hakika duniya yaga wannan zamani na al'ada ta'addanci me muni sannan kuma ya yaketa domin munin ta ya kuma sanya hukuncin sa mutuwa ta hanyar jifa yadda al'adar kan'aniyawa shine su bayar da yaran su domin a yanka su ga alla Mulik, yazo cikin littafin (safar) allawiyyin (1-2/20):


(1 sai ubangiji yayima musa magana da cewa: 2 kacema bani isra'il: ko wani mutum cikin bani isra'ila da baki masu sauka a cikin bani isra'ila ya bada jaririn sa ga Mulik to za'a kashe shi. Mutanen kasar zasu jefe shi da duwatsu).


Yadda wannan al'ada na kan'aniyyun na bayar da garirin su domin a yankasu ga alla Mulik – Allah yayi mana tsari -.


Saboda haka yana daga cikin rahamar Allah maduakaki ga halittun say a saukar masu da shari'a daga sama domin ya tunkari wannan shari'u na shiririta wanda aka gina su akan wulakanta mutum da yanka su wanda ya yadu a tsakanin zamuna cikin duniya!!. Allah madaukaki yace:


“kace masu [ya Muhammad] kuzo zan karanta maku abunda ubangijin ku ya haranta a gareku cewa kada ku hadashi da wani cikin bauta kuma ku kyautatawa iyaye; kuma kada ku kashe yaranku domin tsoron talauci; mune masu azurtaku dasu; kuma kada ku kusanci alfasha na bayyane da na boye; kuma kada ku kashe ran da Allah ya haramta kashewa sai bisa cancanta; da wannan ne yake maku wasiyya dashi koda zaku hankalta” (6:151)


Kuma Allah me girma yayi gaskiya a lokacin daya fadi akan Muhammad s.a.w wanda ya aiko shi da addinin gaskiya wanda ya kunshi dukkanin maslaha na al'amuran mutum a duniyar su da lahiran su, me farin ciki shine wanda yayi imani da shari'ar sa:


“kuma bamu aikeka ba face domin rahama ga talikai” (21:107)


Ibn Abbas yana cewa masanin fassarar alkur'ani:


“lallai Allah ya aiko da annabin sa Muhammad s.a.w domin rahama ga dukkanin talikai, muminan su da kafiran su. Su muminan su lallai Allah ya shiryar dasu dashi, ya kuma shigar dasu aljanna dayin imani dashi da yin aiki da abunda yazo dashi daga wurin Allah, wanda kuma suka kafurta lallai ya kawar masu da bala'i dashi anan duniya wand ayake sauka akan mutanen da suka karyata manzannin su gabanin su.”


Allah ya aiko shi ga duniya baki daya domin su bautawa Allah shi kadai ba tare da hada shi da wani ba cikin bauta da kuma shafe karya na cikin al'amuran zamanin jahiliyya da al'adu na shirka da kuma ibadunsu na shiririta wanda aka sansu dashi.


Akwai laifuka dayawa ko kuma ayyuka wanda sunkai matsayin manyan laifuka wanda aka halastasu aka kuma mayar dasu doka a cikin wasu dokoki na dan Adam, misali irin su zubar da ciki da kisan jarirai!! Duk wanda besan yadda ake kashe garirai ba zai iya ganin haka cikin kafa ta yanan gizo cikin aikin zubar da ciki, wanda manyan likitoci kwararru sukeyi kuma kananan likitoci suke taimaka musu wanda ana anason su da siffa ta rahama a tattare dasu!! Abun mamaki itace wannan laifi mummuna wanda yake faruwa bayan mahaifiya dakanta ko kuma mahaifiya da mahaifi tare sun gabatar da bukatar su ga likita na kashe yaron su jariri, domin wasu dalilai wanda basu taka kara sun karya ba wand ayake nuna matakin dibmuwa na mutum wanda suke kai gareshi kasancewar basu shirya karban sa ba domin sunason jin dadi na tafiya da yanci gabanin a daura masu nauyi na kula da renon yaro, ko kuma domin dalilin matsi na talauci ko kuma wani matsala ta daban na rayuwa!!!.


Wannan aikin ya yadu cikin kasashe dayawa wanda sukaci gaba, da kuma wasu kasashe talakawa a asiya da afirka, musamman ma idan jaririn ya kasance macece domin suna daukanta akan cewa nauyi ce kawai akansu ta hanyar tattalin arziki akan iyalai sabanin yaro wanda suke daukan sa a matsayi jari da kuma ginshiki na gina iyali, suna dauke nauyin iyaye maza da taimakon su wurin samar da kudade ga iyalai. Hakika mun gani hotuna na wasu iyaye cikin wasu kasashe


matalauta a gabashin asiya suna kashe yaransu mata da ransu kamar yadda kafirai na makka gabanin zuwan musulunci suke aikatawa, wanda Allah madaukaki ya fadi akan su yana me hakaituwa akana ayyukan su me muni da ta'addanci babba:


“idan kuma akayima dayan su bushara da diya mace sai fuskarsa tayi baka yana cikin kunci da bacin rai (58) yana boyewa mutane saboda mummunan abunda ya sameshi na busharar da aka masa; kodai ya riketa cikin wulakanci ko kuma ya birneta cikin kasa [da ranta] ku saurara kuji hukuncin su ya munana” (suratun nahli ayata 58-59)


Hakika wannan laifi ya kasance doka cikin wasu dokoki tsofaffi kamar dokar rumaniya wanda aka nassanta cikin sakin layi na hudu daga cikin sa cewa “akashe dukwani jariri me ciwon alaji”32. Kamar yadda wannan laifi ya kasance ya yadu cikin rayuwan almaniyawa tsoho yadda mahaifiya bayan ta haihu zata kai abunda ta haifa ga mahaifi idan ya yarda dashi sai ya rene shi idan kuma be yarda dashi ba sai a kashe shi kamar yadda daya daga cikin tsari da dokoki na romaniyawa ta kunsa wand aka kago shi a birnin Bahnasa (wanda a baya ake kiransa da sunan birni ko kuma uksirankhus) a cikin karamar hukumar almina a kasar misra kuma ya yaduwan wannan al'ada ya bayyana a tsakanin rumaniya wanda ya kunshi wannan dokoki a rubuce daga miji zuwa ga matarsa yana cewa a cikinsa: “idan abunda aka


32 Roman Law, Table IV. A dreadfully deformed child shall be quickly killed.


Haifa ya kasance namiji ki barshi ya rayu, idan kuma ya kasance mace ki kasheta”33.


Amma shari'ar musulunci shari'a ce ta tausayi da rahama, hakika ta haranta wannan laifi mummuna, manzon Allah s.a.w yace:


(lallai Allah ya haramta maku cutar da mata, da kashe yara mata da hana hakkoki da kuma tambayan abunda bahakkin mutum ba, ya kuma karhanta maku ance kace) (buhari da muslim ne suka rawaito shi)


Kuma ya ambaci hakkoki na jarirai alhali yana cikin mahaifiyar sa wanda babban wannan hakkoki shin hakkin rayuwa!! Allah madaukaki yace:


“kuma kada ku kashe yaranku domin tsoron talauci; lallai mune muke azutra ku dasu [baki dayanku]” (suratul an'am ayata 151)


Ya kuma kore dukkanin abiunda zai kawo banbance banbance cikin mu'amala tsakanin yara mazan su da matan su, manzon Allah s.a.w yace:


“kuyi adalci a tsakanin yaran ku a cikin kyauta” (buhari ne ya rawaito shi)


33 Oxyrhynchus ،Egypt ،1 B.C. (Oxyrhynchus papyrus 744. G).


• Shari'ar musulunci


• Manufa na shari'ar musulunci


1. Kiyaye addini.


2. Kiyaye rai.


3. Kiyaye hankali.


4. Kiyaye dukiya.


5. Kiyaye dangankata.


• Haddoji a cikin shari'ar musulunci.


• Neman yin aiki da shari'ar musulunci a cikin kasashen da ba musulmai ba.


1. Kutuna na shari'a a cikin kasashen da bana musulunci ba


2. Shin yana wajaba neman kasashen da ba musulmai ba yin aiki da shari'ar musulunci.


Kamar yadda ya gabata muka fadi cewa abunda Allah ya shar'anta ya kuma wajabtama mutane na dokoki masu tsara alakar su da Allah madaukaki da kuma alakar su da mutanen da suke rayuwa tare da dabbobi da mahalli, daga cikin wannnan dokoki akwai wanda yake tsara al'amuran ibada, daga cikin su kuma akwai wanda suke tsara mu'amala na tattalin arziki da kasuwanci da zamantakewa da kuma harkokin mutum da kuma dokoki wanda suke tsara ginshikai wanda kasa ke kafuwa akai da kuma tsara ayyuka na bangaren dokoki da kuma bangaren alkalanci da kuma bangaren zartarwa.


Manufa na shari'a itace kololuwan manufa wanda shari'a tazo domin tabbatarwa, wanda sune ma'anoni wanda shari'a ta nufe su wanda kuma saboda haka ne aka shar'anta hukunce hukunce da haddoji, daga cikin manufa game gari na shari'ar musulunci akwai:


1- KIYAYE ADDINI: lallai kiyaye addini shine babban manufa na shari'ar musulunci, Allah madaukaki yace:


“kuma ubangijin ka ya hukunta cewa kada ka bautawa kowa sais hi sannnan kuma ka kyautatawa iyaye” (suratul isra'i ayata 23)


Sannan kuma shari'a ta nassanta lada me girma ga wanda ya taimakawa mutane wurin kiyaye addinin su shin ta hanyar karantar dasu addini ne hakika manzon Allah s.a.w yace:


“mafi alherin ku shine wanda ya karanta alkur'ani kuma ya karantar” (buhari ne ya rawaito shi)


Ko kuma ta hanyar gina wurin da zasu taru ko kuma shiryr shirye domin karntar da mutane al'amuran addinin su da kuma sanar dasu hakan kamar gina masallatai domin bautan Allah da kuma karatu, hakika manzon Allah s.a.w yace:


“duk wanda ya ginawa Allah masallaci koda kwatankwacin wurin kwanciyan kaza ne, Allah zai gina masa gida cikin aljanna” (sahihu Ibn Hibban)


Kiyaye addini yana daga cikin manyan wajibobi cikin shari'ar musulunci saboda haka ne aka kiyaye shi karkashin wannan abubuwa masu zuwa:


▪ Nassi akan wajabcin kare dukkanin wnai makiyi wanda zai shigo domin bata addini.


▪ Yaki da kuma haramta dukkanin wani yunkurin bata addini na cikin kasa, kamar wanda yake son izgilanci da addini ta hanyar zana wani almara wanda zai bata musulunci ko kuma karamar manzon Allah s.a.w, da ikirarin yancin fadin albarkacin baki da makamantan haka, yancin fadin albarkacin baki ba tana nufin yancin zagi bane har Abadan ko kuma tozartawa da muzantawa da nuna banbanci na kabilanci.


▪ Yaki da kuma hana dukkanin kirkiran wani abu cikin addini domin kasancewar sa addini ne cikakke, Allah madaukaki yace: “ayau ne nake cika maku addinin ku kuma yake cika maku ni'imomina agareku kuma na yardan maku da musulunci a matsayin addini” (suratul ma'ida ayata 3)


Duk wanda ya kirkiri wani abu cikin addini to hakika yayi kari a cikin say a kuma shigar da abunda baya cikin sa, shi kuma kirkiran wani abun hanya ne na rusa addini, daboda haka ne Allah madaukkai yace: “wanene yafi zalumci sama ga mutumin da ya kirkiri karya akan Allah domin ya batar da mutane ba tare da ilimi ba; lallai Allah baya shiryar da mutane azzalumai” (suratul an'am ayata 144)


2- KIYAYE RAI: Allah madaukaki ya halicci ran dan adam ya kuma haramta da'addanci akanta shin wannan ta'addinji daga mutum din ne a karon kansa ta hanyar halakar da ita, domin fadin sa madaukaki:


“kada ku jefa kawunan ku zuwa ga halaka; lallai Allah ya kasance me rahama a gareku” (suratun nisa'i ayata 29)


Ko kuma ta hanyar ta'addanci ne akan rai daga wani mutum na daban shin wannan mutumin mumini ne ko kuma kafiri, Allah madaukaki yace:


“kada ku kashe ran da Allah ya haramta face bisa cancanta” (suratul isra'i ayata 33)


Duk wanda ya kashe da gangan za'ayi masa kisasi da hkuncin alkali kuma kofar yafiya a bude take daga wurin yan


uwan wanda aka kashe na yafewa akan wannan kisasi, domin fadin Allah madaukaki:


“yaku wanda sukayi imani an wajabta maku kisasi agareku a cikin kisa; [ran] me yanci da [ran] me yanci; bawa da bawa; mace da mace; duk wanda kuma ya yafe masa daga dan uwansa wani abu to yabi haka da kyakyawa da kuma biya da kyautatawa; wannan rangwame ne daga ubangijinku da rahama; duk ya ketare gona da iri bayan haka to yana da azaba me radadi” (suratul bakara ayata 178)


3- KIYAYE HANKALI: Allah ya zaba da kuma daukaka mutum akan sauran dabbobi da ni'imar hankali ya kuma wajabta dokoki wanda zai kiyaye wannan ni'ima ya hamanta dukkanin abunda zai cutar da ita ko kuma kawar da ita kamar giya da makamantan su na miyagun kwayoyin maye wanda suke tafiyar da hankali da kuma lalatashi, domin fadin sa madaukaki:


“yaku wanda sukayi imani lallai gina da caca da dara da rantsuwa da gumaka datti ne cikin ayyukan shedan saboda haka ku nuisance su koda zaku samu rabauta” (suratul ma'ida ayata 90)


Hakika an kirata cikin musulunci da sunan Ummul kaba'isa domin girman hatsarinta shin akan mutum ne ko kuma a al'umma itace uwar dukkanin sharri da kuma dalilin laifuka miyagu.


4- KIYAYE DUKIYA: dukiya dan uwan rayuwa Allah ya sanya shi ginshiki na kiyaye ta ta dalilin sa ne maslahohi suke faruwa da kuma jawo arziki sai abinci ya yalwatu da kayayyaki da kartu da wurin zama… da sauransu, kuma hakika Allah madaukaki ya bayyana hanyoyi na shari'a na samun dukiya da kuma hanyoyi na habaka ta da kuma kashe su, saboda haka ne aka haramta dukkanin aikin wanda yake jawo halakar dukiya da kuma batashi ba tare da wani amfani ba me kyau, ya kuma haramta amfani da mutane da kuma cin dukiyar su da barna ta hanyar riba ko kuma rashawa da sata da caca da malumta, domin fadin Allah madaukaki:


“yaku wanda sukayi imani kada kuci dokiyoyin ku a tsakanin ku da barna” (suratun nisa'i ayata 29)


Ko kasheta ta hanyar da zutar da mutum ko kuma wanin sa ko kuma almubarzanci da barna wurin kasheta ba tare da bukatar hakan ba, ya kuma wajabta hakkoki a cikinta shin gay an uwa ne na jini ko kuma mabukata ne gama gari da sadaka da kuma kyautatawa domin fadin Allah madukaki:


“kuma kuba makusanta hakkin su da miskinai da matafiya kuma kada kuyi almubazaranci da; lallai masu almubazanci sun kasance yan uwan shedan; shi kuma shedan ya kasance kangararre ga ubangijin sa” (suratul isra'i ayata 26-27)


5- KIYAYE DANGANTAKWA: shari'ar musulunci ta haramta dukkanin abunda zai zama sababi na caddanyan dangantaka misali kamar laifin zina, Allah madaukaki yace:


“kuma kada ku kasanci zina domin kuwa ta kaance alfasha kuma mummunan hanya” (suratul isra'i ayata 32)


Kamar yadda ya haramta har wayau dukkanin abunda zai sama sababi na karar da dangantaka ko kuma dates ta kamar luwadi da madigo, Allah madaukaki yace:


“kuma daga cikin mutane akwai wanda maganar sa zai baka mamaki a rayuwan duniya kuma Allah yana sheda abunda ke cikin zuciyar sa kuma a kasance me yawan musu idan ya kuma ya tafi sai ya shiga kasa yana me barna a cikinta ya kuma lalata gonaki da dangantaka; Allah kuma bayason masu fasadi” (suratul bakara ayata 204-205)


An wajabta haddoji a cikin shari'ar musulunci domin kiyaye wannan dokoki da Allah ya saukar domin tsara rayuwan mutum, da kuma lamuni na aiki da ita kuma mutane su girmamata ya zama wajibi na samun doka wanda zai tsara hanyoyin kadabtarwa da ukuba ga duk wanda ya saba wannan doka saboda haka ne Allah ya shari;anta haddoji wanda (doka ne na ukuba) shari'a ta musulunci bata nassanta akan wani haddi ba face domin kiyaye hakki, kuma dayawa na abunda yake hadewa wand aba musulmai ba tsakanin ma'anar haddoji da shari'ar musulunci kanta suna masu sawwara cewa shari'ar musulunci haddi ne kawai da kuma hukunce hukunce na ladabtarwa da ukuba na yanke hannun me sata (tafin hannun sa) da kuma kashe wanda yayi kisa da dai sauransu, wannan sawwaran kuwa ba daidai bane, shi haddi ukuba ne wanda


akw aiwatar dashi akan wanda ya tsabawa shari'ar musulunci domin kariya agareta da kuma lamuni akan rashin saba mata, a cikin aiwatar da haddoji (doka na ukaba) akwai rayuwa da kuma kiyaye rayuka da dukiyoyi na abunda suka mallaka da mutuncin su da hankulan su, lallai ita lamuni ne akan kiyaye zatin mutum ita kamar canji ne kan sura na waje wanda yake kiyaye birni wanda shine (shari'ar musulunci) daga yan fashi wanda suke neman fermata da kuma ta'andacci akan mutanen ta wanda suka aminta acikinta, Allah madaukaki yayi gaskiya:


“kuma kunada rayuwa a cikin kisasi yaku ma'abota hankula koda zaku samu takawa” (suratul bakara ayata 179)


Musani cewa haddoji bawai sabon al'amari bane cikin shari'ar musulunci, a'a Allah yayi umurni da ita cikin dukkanin shari'u na sama, hakika Allah yayi umurni dayin haddi cikin attaura wanda aka saukar ma Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi, Allah madaukaki yace:


“lallai mun saukar da Attaura akwai shiriya da haske a cikinta, annabawan da suka mika wuya suna hukunci da ita ga wanda yahudawa da malamun su da fadoji daga abunda suka haddace daga littafin Allah kuma sun kasance masu sheka kansa, kada kuji tsoron mutane kuji tsoro na kuma kada ku siyar da ayoyin Allah akan lada dan kadan duk kuma wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune kafira. Kuma mun wajabta agare su a cikinta cewa rai da dai, ido da ido, hanci da hanci, kunne da kunne, hakori da hakori, raunuka kuma kisasi, duk wanda yayi yafiya dayain sadaka dashi to hakan kaffara ce a gareshi; duk wanda


baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune azzalumai” (suratul ma'ida ayata 44-45)


Kuma haka Allah yayi umurni da aiwatar da haddoji cikin Injila wanda aka saukar ga Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi, Allah madaukaki yace:


“sai muka biyo bayan su da Isa dan Maryam yan ame gasgatawa da abunda ke gaba gareshi na attaura kuma muka bashi Injla acikin sa akwai shiriya da haske kuma me gasgatawa ne ga abunda yake gaba gareshi na attaura da kuma shiriya da wa'azi ga masu takawa.* mutanen Injila suyi hukunci da abunda aka saukar masu acikin sa; kuma duk wanda baya hukunci da abunda Allah ya saukar to wannan sune fasikai” (suratul ma'ida ayata 46-47)


Lallai al'amarin zartar da haddoji akan wanda ya sabawa shari'ar sa (dokan musulunci) yayi laifin da yake jawo haddi wannan aiki ne na shugaba musulmi ko kuma mataimakin sa babu wani mutum cikin dai-daikon munanen al'umma da yake da hakkin zartar dashi, musulunci addini ne me tsari da oda da bi daki bayan daki bawai addini bane mara tari da oda, ba'a taba zai da haddi ba akan wani a azamanin manzon Allah s.a.w face da izinin sa domin shine aka wajabtawa zartar da hukunce hukunce idan kuma ya kasance shine wanda aka wajabtawa zairtar da hukunci domin kasancewar sa shugaba to lallai hakan ya zama hakki ne na


shugaba wanda yake shugabancin musulmai cikin mutanen da zasu zo a bayan sa, Allah madaukaki yana cewa:


“kuma kayi masu hukunci a tsakanin su da abunda Allah ya saukar kuma kada kabi son zuciyan su kuma ka guji su jarabeka akan wasu daga abunda aka saukar maka; idan kuma suka juya baya to kasani lallai Allah yana son ya dandana masu wani azaba sakamakon wasu zunuban su; kuma dayawa daga cikin mutane fasikai ne” (suratul ma'ida ayata 49)


1. JANYEWA DAGA IKIRARI: mafi yawan muluman fiqhu na musulunci (abu hanifa da shafi'I da Ahmad) sun tafi akan cewa ana karban janyewar mutumin da yayi ikirari idan ya janye daga haka kuma haddi yana fadi akansa, kuma ana kyaleshi idan ya gudu koda zai janye34, ma'iz dan Malik Allah ya kara masa yarda wanda ya kasance maraya cikin wasiyyar Hazal al-aslami Allah ya kara masa yarda, ya fada cikin zina tare da wata mata a cikin unguwa, sai Huzal ya nuna masa cewa yaje gun manzon Allah s.a.w ya tabbatar da laifinsa ga manzon Allah s.a.w, bayan yayi ikirari kansa har sau hudu sai manzon Allah s.a.w yayi umurni da a zartar da haddi akansa, sai dai a lokacin da ake zaitar da haddin akan sa sai ya tsorata ya gudu sai Abdulahi dan Anis ya bishi ya zartar


34 Sahihu fiqhus sunnah (4/8)


masa da haddin, bayan ya dawo ya fadama manzon Allah abunda ya faru sai yace: (kash me yasa baku kyale shi, me yiwa zai tuba, Allah ya amshi tubar sa, yakai Huzal daka suturtashi da tufafinka yafi maka alheri akan hakan da ka aikata) Ahmad ne ya rawaito shi, da Abu Dawud, da Hakim, kuma albani ya inganta shi, Huzal shine wanda ya kwadaitar da ma'iz cewa yaje ya fadama manzon Allah domin ya tabbatar da zunuban sa, fadin sa manzon Allah s.a.w cewa: “daka suturta shi da tufafinka” yana nufin daya hanashi zuwa tabbatar da laifin sa wanda ya wajabta masa haddin, Baji yace: “suturtashi ya kasance ya umurceshi dayin tuba da boye laifin sa, an fadi mayafi ne domin girmama abun”35


2. SHUBUHA: wata kila a tsayar da haddi da zata, shi haddi ana koreshi da shubuha Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda kahlifa na biyu na manzon Allah s.a.w yace: “ya kawar da haddi da shubaha yafi soyuwa a gareni da na zartar dashi da shubuha” (Ibn Abi shaiba ne ya rawaito shi)


Saboda haka ne duk wanda ya saci kudi yana tunanin yanada hakki a cikin sa to haddi ya fadi akansa.


3. TUBA: idan me laifi ya tuba gabanin a kama shi to lallai haddi ya fadi akansa, amma idan tuban ya faru ne bayan an kamashi to hakan baya kawar da wannan haddin akansa saboda fadin Allah madaukaki:


35 Almuntaqa (7/135)


“sai dai wanda suka tuba gabanin a kama su; ku sani lallai Allah me gafara ne da rahama” (suratul ma'aida ayata 34)


Ita tuba makasudin ta anan shine wacce take kawar da haddi gabanin a kama me laifi itace tuban da take da alaka da haddin tare hanya (haddin masu yaki) da haddin Ridda, wannan da ijma'in malaman fiqihu baki dayan su. Amma sauran haddojin kuwa kamar misalin zina da sata anan wurin akwai magana biyu na ra'ayin malamai akansa: ra'ayi na farko sun tafi akan cewa tana kawar da wannan haddin da tuba gabanin a kama me laifi, ita kuma ra'ayi na biyu sun tafi akan cewa ita tuba a cikin wannan haddi gabanin akama me laifi bata kawar da haddi. Amma tuban da take da alaka da haddin kazafi malamai sunyi ittifaki akan sa cewa bata kawar da haddi gabanin akama me laifi ne ko kuma bayan an kama shi. A cikin wannan matsalar akwai bayani me fadi ga wanda yake neman Karin bayani akan haka sai ya koma littattafan fiqihu na musulunci a kan wannan matsala.


4. JANYEWA DAGA SHEDA: janyewar shedu daga shedarsu bayan hukunci gabanin zartar dashi yana kawar da haddi akan wanda akayi sheda akansa me laifi.


5. YAWAITAN HADDI IRI DAYA AKAN MUTUM: idan haddi iri daya suka maimaitu akan mutum gabanin zartar da haddin shikenan haddi daya ya wadatar.


1- ATTAKLIF (HANKALI DA BALAGA) baya zartar da haddi akan yaro ko kuma mahaukaci ko mara dolo ko kuma me maye sai bayan ya warke, saboda fadin manzon Allah s.a.w:


“an dauke alkalamin rubutu akan mutum uku: akan mahaukaci har sai ya warke, dame bacci har sai ya farka, da kuma yaro har sai yayi mafarki” (Ahmad da Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi) (sahihul jami'u- na albani)


2- ZABI DA KUMA RASHIN TILASTAWA: Allah madaukaki yace:


“duk wanda ya kafurta da Allah bayan imanin sa sai dai wanda aka tilastamawa alhali zuciyar sa na cike da imani amma wanda zuciyar sa ya yalwatu da kafurci to wannan fushin Allah ya tabbata akansu kuma suna da azaba me girma” (suratun nahli ayata 106)


3- LAFIYA da kuma iko ba'a zartar da haddi akan mara lafiya ko me rauni na juhha da jiki sai bayan warakan sa.


4- ILIMI AKAN HARAMCIN HAKA.


MUSTAHABBANCIN SUTURTAWA AKAN MUSULMI37: wanda yaga wani musulmi yana aikata laifi,


36 Sahihu fiqhus sunnah (4/13)


37 Sahihu fiqhus sunnah


yana da zabi tsakanin bayar da sheda domin kira zuwa ga Allah da kare dokokin sa, ko kuma suturta dan uwan sa musulmi, wanda wannan shi yafi (kuma akwai fifiko akan sag a duk wanda yake son Karin bayani akan say a koma uwa ga littattafin fiqihu na musulunci), hakika manzon Allah s.a.w yace:


“duk wanda ya suturta musulmi Allah zai suturtashi duniya da lahira” (muslim ne ya rawaito shi)


Yana yawo a cikin kafafen yada labarai na turawa cewa haddojin da shari'ar musulunci ya sanya akan wasu laifuka (kisa da yanke hannu da jifa) ukuba ne me tsauri mara tausayi wanda bata dace ba da wannan zamani namu?!!


Amsa akan wannan shubuhar:


Lallai kowa ya yarda cewa wannan laifuka sunada cucarwa wanda suke a bayyane ga al'umma, sannan kuma dole ne a yake su da tushe su ta hanyar sanya masu ukuba, sai dai sabanin shine cikin nau'in ukubar! Kowa ya tanbayi kansa: shin ukubar da musulunci ya sanya su sunfi dace da samu nasara wurin toshe wannan laifuka ko rage su ko kuma ukubar da dokokin mutane suka tsara wanda bazat karama laifi komai face yaduwa!? Shi gaba gurbatacce dole ne a yanke shi domin lafiyar sauran gangan jiki!


• Abune sananne a hankalce cewa dukkanin ukuba dole ne akwai tsauri a cikinta domin ta zama tana tsawatarwa


da kuma hana masu laifi aikata laifi idan kuma bah aka ba to hakika ta rasa dacewar ta.


• Rashin zartar da haddi domin tsaurinta zalumci ne ga al'umma taya mutum zai samu aminci akan ransa da dukiyar sa da mutuncin sa, lallai zartar da haddi rahama ne ga al'umma da kuma wand aka zartar da haddin akan sa, misali likitan da yake tiyata domin ya yanke ko kuma cire wani bangare a jikin mara lafiya da niyyar masa magani a zahirin aikin sa rashin tausayi ne cikin yanke wannan gaba sai dai kuma rahama ce ga sauran gangan jikin domin su tsira. Kaman haka ne haddi na kisa ko kuma kawar da gurbatacce cikin al'umma domin sauran al'umma su tsira.


Asali cikin abubuwa cikin shari'ar musulunci shine halalci da halal saboda fadin Allah madaukaki:


“shin baka gani b acewa lallai Allah ya hore maka abunda yake cikin sammai da kasa kuma ya cika maka ni'imar sa agareku ya bayyanen su dana boyen su” (suratu Lukman ayata 20)


Sai dai abunda dalili cikin madogara na shari'a yazo da haramcin sa, saboda fadin amnzon Allah s.a.w:


“duk abunda Allah ya halasta cikin littafin sa to halal ne kuma abunda ya haramta haram ne, abun kuma da yayi shiru akan su sauki ne, ku amshi sauki daga Allah


domin lallai Allah baya manta bane sa'anna ya karanta wannan ayara: kuma baungijin ka be kasance me mantuwa ba (suratu Maryam ayata 64)” (Hakim da Baihaki ne suka rawiato shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin silsitul sahuha numba ta 2256)


Kenan shari;ar musulunci bata haramta dokoki wanda dan adam suka kirkira ba wanda suke tsara rayuwan mutum hasalima ta halasta ne matukar basuci karo da uta ba kamar dokar ruwa ko kuma dokar aiki… da dai suaran su, kawai ta haramta wannan dokokin ne wanda suke halasta laifuka ko kuma abunda aka haramta wanda suke da sakamako mummuna ga mutum ta fuskar hankalin sa ne ko kuma dukiyar sa ko kuma zamantakewar sa ko kuma halayen sa ko lafiyan sa, haramcin yana zama maslaha ga mutum karon karon kansa domin Allah a cikin dokokin sa ya wadatu daga bayin sa zububan su baya taba cutar dashi haka kuma biyayyar su baya amfanar dashi da komai, Allah madaukaki yace:


“kace kawai abunda ubangiji nay a haramta shine alfasha abunda ya bayyana daga gareshi da abunda buya; da zunubi da dagawa ba tare da gaskiya ba da kuma ku hada Allah da wani cikin bauta abunda ba'a saukar da hujja ba akan sa da kuma ku fadi abaunda baku sani ba akan Allah” (suratul a'araf ayata 33)


KOTUNAN SHARI'AR MUSULUNCI A CIKIN KASASHEN DA BA MUSULMAI BA:


Akwai wasu kafafe da kuma bahasi nay an jaridu wanda suke inkarin samuwan malisu ko kuma kutuna na shari'ar musulunci a wasu kasashen yamma wanda ba musulmai ba wanda suka bada dama budesu da kuma sanya su cikin doka wanda baza'a ce masu kutuna ba kai tsaye masu sunan kotu wanda aka sani a dokance kawai majalisu ne wanda suke taimakawa musulmai cikin matsalolin su na aure da saki da gado da sauran su, misali da wani zai kashe wani wannan majalisan bazasu zartar masa da hukuncin kisa ba sai dai su kais hi zuwa gay an sanda domin gabatar dashi ga kotuna na al'ada na kasar. Amma dai wannan kafafe na sadarwa da bahasi na jaridu suna son tsoratarwa ne ga mutanen wanna kasashe daga wannan majalisun sais u rika sawwarata da cewa yakine ga kasashen su wanda wannan magana ne ta shirirrita wanda ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinta an ginata ne akan jahilci ko kuma tsantsan kiyayya ga musulunci da mutanen sa, yadda zasu sa mutane su rika shakka shine za'a zartar masu da hukunce ne da shari'ar musulunci wanda cikinta yayi nesa ga idanun yan sanda!! A cikin hakikanin al'amari kuma shine wannan majalisu an gina su ne akan tafarkin al'amuran mutane wand aba musulmai ba wanda ake aiki da ita a kasashen musulunci, daga cikin saukin shari'ar musulunci shine ta yarda da ayaima wanda ba musulmi ba wanda yake zaune cikin kasar musulunci hukunci da shari'ar su cikin dayawa na matsalolin su kamar aure da saki da makamantan su, ba'a wajabta masu dokoki ba na musulunci wanda aka aiki dasu akan musulmai cikin wannan matsalolin sai idan sun yarda da hakan da suje kotun musulunci domin ayi masu hukunci. Kuma hatta acikin wasu


ayyuka wanda shari'ar musulunci ta nassanta akan haramcin su da kuma laifin su bata haramta ba akan wanda ba musulmai ba, kamar shan giya da cin naman alade domin kuwa shan giya da cin naman alade basa ganin haramcin sa dukda cewa a hakikanin akidar su shine haramcin su kuma akwai dalilai dayawa akan hakan.


Daga cikin misali akan munin wannan kafafen yada labarai da bahasi na jaridu wanda aka kafasu domin siyasa shine daya daga cikin me gabatar da shiri cikin irin wannan tuzartattun kafafe yana tambayan musulman da suke zaune cikin kasar sa: wanene yafi a wurinka tsakanin dokokin musulunci ko kuma kuma dokan wannan kasa?!! Sai musulmai suka amsa cikin yardan zuciya cewa”dokokin musulunci sune suka fi.” Wannan bayar da amsa ne na dabi'a matuka domin tambayar a karon kanta anyita ne ba a wurinta kuma baya nuni kan komai face tsantsan kiyayya da kabilanci daga wannan me gabatar da shiri. Saboda musulmi yana nufi ne cikin amsan shi cewa maganar Allah tana gaba da maganar mutum, bawai yana nufin baya girmama dokan kasa bane!! Saboda iata doka ta musulunci yana umurni da hana sata da kisa da yima mutane fince wanda shine dai abunda ke cikin dokoki na mutane saboda haka babu cin karo anan, abunda musulmin yake nufid a wannan amsa nashi cewa idan dokan da mutum ya kirkira cikin wannan kasa wacce ba musulma ba yana lahasta alfasha ko shan giya ko zubar da ciki ko cin naman alade shikenan baza'a bi wannan sauki ba hukuncin Allah za'a bi a cikinta bazai sha giya ba ko yin akfasha ba ko kuma kisan jariri ta hanyar zubar da ciki, kuma bawai yana nufi bane da amsan shin= cewa zai keta dokokin kasa ba, amma dangane da sauran ukuban kamar ukubar sata ko kisa ba'a zartarwa akan musulmi ba wanda yake dan gudun hijira


ukubar da aka nassanta a cikin shari'ar musulunci saboda rashin cikan sharuddan sa, al'amarin haddi na shugaban musulmi ne sannan kuma kasancewar say a shiga wannan kasa karkashin tsari da dokanta shi kuma musulmi an umurce shi da cika alkawari na cika akawuran sa daya dauka, mu muna magana ne anan akan musulmi wanda yake rayuwa cikin kasar kirista bawai kasar musulunci ba.


Ya wajaba akan musulmi dan gudun hijira wanda yake rayuwa a cikin kasar da ba ta musulunci ba ya mutunta da kuma kiyaye dokoki na wannan kasa mutukar basa umurtan sa da sabon Allah madaukaki, idan suka umurce sa da sabon Allah madaukaki ya wajaba yayi hijira daga wannan kasa wacce bata mutunta yancin na addini da hakkoki na mutum, kamar misali da ace wannan dokan zasu umurci mace musulma da cire hijabi, to anan ya wajaba a gareta da tayi hijira daga wannan kasa da gaggawa domin ta tsaritar da kanta daga wannan dokoki na shiririta, baya halatta agareta fada ta hanyar da be dace ba ko kuma makamanta hada da wannan dokoki, amma idan an samu cin karo tsakanin dokoki na wannan kasashe tare da hakkin musulmin da yake zaune a ciki amma ba tare da tayi masa umurni ba da aikata sabon Allah to anan wurin ya halatta ga wannan musulmi yayi mu'amala da wannan dokoki ta hanyar daya dace domin bayyana rashin yardan sa akan wannan doka!! Misasali idan ya kasance doka be yarda da gina masallaci ba ta yadda musulmai zasu samu yin sallolin su a ciki, ko kuma yana hana ma musulmi Karin aure amma kuma ta halasta mashi yin kawaye mata kari akan matar sa, to anan ya wajaba akan wannan musulmin zuwa ga kotu ko kuwa majalisu na shari'a kamar majalisar dokoki ko kuma gidan jarida domin samun damar kwato hakkin sa na


addini wanda Allah ya wajabta masa kamar salla ko kuma ya halasta masa kamar Karin aure.


SHIN YA HALASTA NEMAN DASASHEN DA BA MUSULMAI BA AIWATAR DA SHARI'AR MUSULUNCI:


Akwai wasu daga cikin muslmai yan gudun hijira ko kuma sababbi a cikin wasu kasashe na yamma wanda suke rike tuka bakyake suna rubuce akan su Kalmar shahada kyallaye wanda aka rubuta akansu shari'a a England a misali, shin wannan aikin yana da kyau ko kuma kuskusre ne?


Domin samun sani akan wannan amsar ya wajaba sauraran wannan kalmomi masu zuwa:


• Wannan mutane basu tashi ba akaron farko da karantar da mazauna wannan kasa ba menene shari'ar musulunci na gaskiya, kawai sais u fara neman aiwatar da ita kai tsaye, bayan sunada sanin cewa dukkanin abunda tunanin su game da shari'ar musulunci itace wannan ukubar da aka nasssanta a cikin shari'ar musulunci kamar yanke hannun me sata da sauran su, to taya kake tunanin zasu yarda su karbi tunanin aiwatar da shari'a akan su?!! Da wannan aiki nasu bazasu karantar dasu ba shari'ar mususlunci face kawai tsoratar dasu sukeyi daga gareta!!.


• Lallai wa'innan mutane a cikin mafi yawan halaye ya shige masu duhu tsakanin ma'anar shari'a da kuma addinin musulunci ma'ana da wannan ilimin nasu suna nufin kiransu zuwa ga shiga musulunci amma da wannan hanyar da suka bi sun nuna ma mutane cewa suna son aiwatar da shari'a ne akan


su, kena acikin fahimtar mutanen itace suna son aiwatar da wannan ukuba ne wanda aka nassanta cikin shari'ar musulunci akan su.


• Shari'ar musulunci shari'a ce ta kasashen musulunci baya wajaba neman aiwatar da ita akan kasashen da ba musulmai ba aiwatar yin aiki da ita, kamar yadda ba'a taba gani ba cikin tarihi a zamanin manzon Allah s.a.w da khalifofin sa cewa daya daga cikin su ya nemi wkasashen da ba musulmai ba aiwatar da shari'ar musulunci!! Saboda ta yaya zai yiwu kasar da yarda da addinin musulunci ba kum amafiya yawan yan kasan addinin kiristanci sukeyi ko yahudanci kuma me shugabantan su kirista ne ko bayahude da cewa su aiwatar da shari'ar da ba nasu ba?!!!.


• Neman aiwatar da shari'ar musulunci a matsayin doka ya wajaba ya zama ta hanyar haddoji na dokoki misali wannan neman ya zama ta hanyar majalisa domin itace bangaren daya tilo wacce ta kebanta da tabbatar da dokoki, domin kuwa da zai samu ta hanyar daga kyallaye a hanya to lallai hakan zai haifar da fushin mutanen kasa sannan sakamakon hakan zai haifar da akasin abun da ake nema da kuma jawo cutarwa ga kokarin masu da'awa.


• Ukubar barawo tsakanin yanke hannu da rufewa a gidan kurkuku.


• Ukubar barawoa cikin littafai masu tsarki.


• Kare kai cikin shari'ar musulunci.


• Kare kai cikin dokan da dan Adam ya kirkira.


Lallai dukkanin dokoki na ukuba ba'a sanya sub a face domin tabbatar da manufa na asali guda biyu wanda sune:-


• TSAWATARWA: domin tsawatar da me laifi kada ya sake maimaitawa da kuma tsawatar da mutane kada suyi koyi dahi wurin aikata irin wannan laifi.


• RAHAMA GA MUTUM DA MUTANE: rahama ga mutum na hanashi aikata aikin keta hakkokin wasu, da haka rahama zata tabbata akan wannan mutum da cewa bazai kusanci aikin laifi ba ta yadda ukuba bazai hau kansa ba, da kuma tabbatar da rahama ga mutane da hanyar kiyaye masu hakkokin su kada wani ya farmasu!! Anan wurin tambaya zaizo fadoma zauciya cewa wanne a tsakanin su yafi hanawa da kuma rahama a lokaci guda ga mutane, dokan musulunci ko kuma dokan da dan adam ya kirkira?! Bari mu kawo wasu misalai kamar misali laifin sata da kuma ukubar barawo a tsakanin dokan musulunci da dokan da dan adam ya kirkira mu gani wanne ne yafi nasara wurin tabbatar da manufar da muka fadi abaya!!


Farko dai ya wagaba mu sani cewa ukuba baa bun so ban eko abu me kyau, idan da ta kasance haka kuwa da ba'a kirata da suna ukuba ba kuma da ta rasa rukunin ta na farko na asali watan tsawatarwa, haka kuma idan muna son kwatantawa akan ukubar barawo tsakanin yanke hannu da kuma ukubar dauri a kurkuku to zamu kwatanta ne tsakanin abu guda biyu saboda ko wannen su a zahiri ukuba ne amma dai zamu zabi abunda yafi dama dama acikin su wanda kuma cutarwan sa yafi zama da sauki.



Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC