Labarai

DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA MEJIN KAI


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da iyalan sa da sahabban sa baki daya.


Mutum halitta cikin halittun Allah madaukaki a cikin wannan duniya me fadi, bangare ne wanda baza'a iya rabashi ba daga gareshi, sunada amfani da aiki wanda iyakantacce ta yadda da zasu fita daga cikin wannan aiki wanda aka iyakance masu cikin littafai wanda aka saukar daga sama domin su da wani matsala ta faru wanda hakan zaiyi tasiri ga duniya, wannan abun lura ne da kuma gani da ido alokacin da mutum ya aikata abunda aka hane shi kuma suka kawar dakai daga abunda aka masu umurni dashi suka bi son zuciyoyin suda sha'awar su sai fasadi wanda zai mamaye duniya ya bayyana a doron kasa da sama, sai cututtuka su yadu wanda mutanen da suka gabata basu san su ba, kuma yaki ya yawaita wanda yake daidaita gonaki da zuriya, kuma matsaloli na yanani ya bayyana kamar yadda ake gani na dumama yanayi da kuma karuwan zafi – wanda da al'amarin zai ci gaba da kasance wa a hakan da duniya ta kowa wuri wanda mutum bazai iya rayuwa a cikinta ba – dukkanin haka sakamakon was an mutum ne na gwajin nukiliya da daukan abunda yafi karfuin sa da kuma kamfanoni wanda suke samar da sama da bukata na mutum dukkanin haka na faruwa ne domin samun abun duniya da kuma tabbatar da bukatu da biyan sha'awa koda kuwa ya kasance ta hanyar wulakanta yan uwan sa ne cikin mutane da yancin dan adam, suna son su koshi koda kuma a cikin asusun yunwan wanin su ne, kuma su sanya tufafi koda kuwa a cikin


tsiraicin wasun su ne, da jin dadi koda kuma ta hanyar kashe wasun su ne, lallai Allah yayi gaskiya da yake fadi cewa:


“fasadi ya yadu a doron kasa da cikin ruwa sakamaon abubuwan da mutane ke aikatawa domin a ya dandana masu wasu daga cikin abunda suka aikata koda zasu dawo.” (30:41)


Sai Allah madaukaki ya bayyanawa mutum cewa ba'a halicce su ba da samar dasu cikin wannan duniya domin wasa ba, kuma ba'a kyale su haka ba kara zube, Allah madaukaki yace:


“shin kuna tsammani mun halicce ku ne kawai domin wasa kuma ku ba masu dawowa bane zuwa gare mu (115) tsarki da daukaka ya tabbata ga Allah sarki na gaskiya; babu abun bauta da gaskiya sai shi; ubangijin al'arshi me girma (116)” (23:115-116)


Ya kuma bayyana cewa hikimar halitta da samar da mutane cikin wannan duniya al'umma bayan al'umma shine domin su bauta ma Allah shi kadai kuma kada su hada wani dashi cikin bauta, shi mawadaci daga bautan su tsarki ya tabbata a gareshi sai dai domin ya masu jarabawa ya gani wanenen zai kyautata aiki, Allah madaukaki yace:


“kuma ban halicci mutum da aljani ba face domin su bauta mani (56) bana bukatar arziki daga garesu kuma bana bukatar su ciyar dani (57) lallai Allah shine me yawan azurtawa ma'abocin karfi me cikakken karfi (58)” (51:56-58)


Kamar kuma yadda madaukaki ya bayyana cajin na gwargwado su wanda gangan jikin bazai iya rayuwa ba sai dashi da fadin sa cewa:


“yaku wanda sukayi imani kuci daga abubuwa masu dadin da muka azurta ku dasu kuma ku godema Allah idan kun kasance shi kadai kuke bautatamawa (172)” (2:172)


Ya bayyana caji na daidai gwargwado wanda bazasu iya rayuwa ba face dashi, bazasu samu sukuni ba batare da imani ba kuma bazasu samu hutu b aba tare da bautan mahaliccin ta ba, kuma bazasu tabbata ba batare da aiwatar da shari'ar sa ba, Allah madaukaki yace:


“wanda sukayi imani kuma zukatansu suka samu natsuwa da ambaton Allah; hakika da ambaton Allah ne zukata suke samun natsuwa (28)” (13:28)


Domin mutum ya tabbatar da bauta ga Allah shi kadai an aiko masa da manzanni domin yayi koyi dasu kuma aka saukar masu da littattafai (shari'a) domin su shiryu da ita ya kuma kasance masu fitila me haskaka masu hanyar su, sai ta shiryar dasu zuwa ga alheri da kuma tsawatar dasu daga sharri da tsara masu al'amuran rayuwan su, ta yadda zasuyi amfani da gangan jiin su da rayukan su domin abunda aka halicce su domin sa, Allah madaukaki yace:


“mutane sun kasance al'umma daya; sai Allah ya aiko da manzanni masu bishara da gargadi ya kuma saukar masu da littattafai domin suyi hukunci tsakanin mutane cikin abunda suka samu sabani a cikin sa; kuma basu samu sabani ba game dashi sai ga wanda aka basu bayan hujjoji bayyanannu sunzo musu, sai Allah ya shiryar da wadanda sukai imani acikin abinda sukayi sabani da izininshi, lallai Allah yana shiryar da wanda yaso zuwa ga hanya madaidaiciya.” (2:213)


Ya kasance na karshen su shine Muhammad s.a.w wanda Allah ya cika manzannin sa dashi ha kuma cika addinin sa dashi, ya kuma zo da addini wanda ya kunshi da tattara shari'a (dokoki) na Allah ga duniya baki daya wacce ta dace da ko wani zamani da lokaci, tana tsara rayuwan mutum da kuma basu farin ciki duniya da lahira, duk wanda yayi riko dashi ya samu farin ciki wanda kuma ya barta ya tabe, Allah madaukaki yace:


“lallai wannan alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko kuma yana yima muminai bishara wanda suka aikata ayyuka na kwarai cewa suna da lada me girma (9) wanda kuma basuyi imani ba da lahira mun tanadar masu da azaba me radadi (10) kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar irin addu'ar da yakeyi ma kansa na alheri; kuma hakika mutum ya kasance me yawan gaggawa (11)” (17:9-11)


(wannan kenan a fuskar game gari ga wanda yake shiryar dasu da kuma abunda da yake shiryar dasu zuwa gashi, sai shiryarwan ya kunshi mutane da al'ummomi marasa adadi na zamani ko kuma wuri kuma ya kunshi abunda da yake shiryar dasu zuwa gareshi dukkanin manhaji da hanya, da dukkanin alheri wanda suke mutum ke shiryuwa gareshi cikin dukkanin zamani da wuri.1 Yana shiryar wa zuwa ga hanya me karko cikin duniyan me duhu da burace burace, da akida bayyananne me fadi wanda babu duhu a cikin sa, wanda take yantar da zukata daga nauyi na dimuwa da kararyaki, da kuma inganta batirin mutum na kwarai domin aiki da gini, da kuma


1 Sayyid Khudub Allah yayi mashi rahama cikin littafin sa me suna zilalul kur'an, mujalladi na 4, shafi na 2215


kulla alaka tsakanin dokoki na duniya na dabi'a da fidirar mutum ta hanya me tsari da kamala.


Kuma yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko cikin kulla alaka tsakanin zahirin mutum da badinin sa, da kuma burin sa da dabi'un sa, da akidar sa da aikin sa, kenan dukknain su suna hukunci ne zuwa ga kololuwan igiya wanda bata katsewa da kuma kai mutum zuwa ga kololuwan wuri tabbatacce akan doron kasa, kenan aiki ibada ne a duk lokacin da mutum ya nufi Allah dashi, koda kuwa aikin na jin dadi ne na rayuwa.


Kuma yana shiryar wa zuwa ga hanya ne karko cikin duniyar bauta ta hanyar kwatantawa tsakanin ayyuka da kuma iko, bata daurama rai aikin da bazata iyaba har ta kosa wurin sauke wannan nauyi. Kuma bata yin sakaci da rangwame har reai ta sangarce. Kuma bata wuce buri da daidaito da iyaka na abunda zai yiwu.


Kuma yan ashiryarwa zuwa ga hanya me karko cikin alakar mutane a tsakanin su: daidaikun su da kungiyoyin su, hukumomi da mutane, da kasashe da jinsuna, sannan kuma yana gina wannan alakar ne akan ginshiki me karfi kuma tabbatacce wanda baya tasirantuwa da ra'ayi ko kuma son rai kuma baya karkata tare da soyayya da kiyayya kuma maslaha bata canzata ko kuma buri. Ginshiki wanda masani kuma me bada labari akan halittansa ya gina, shine mafi snai ga abunda ya halitta, kuma mafi sani ga abunda ya dace dasu cikin dukkanin kasa da al'umma, sai ya shiryar dasu zuwa ga hanya me karko cikin tsari na mulki da tsari na dukiya da tsari na zamantakewa da kuma tsari na mu'ama tsakanin kasa da kasa na zamani cikin duniyan mutum.


Kuma yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko wurin bayyanar da akida me kyau, sai ta sanar da mutane mahaliccin su abun bauta na gaskiya, kuma ta sanar da mutane addini na asali, kuma alkur'ani me girma yana yima muminai bishara da lada me girma wanda shine aljanna sakamakon imanin su, da kuma yima kafirai gargadi game da azabar Allah madaukaki.


“lallai wannan alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga hanya me karko kuma yana yima muminai bishara wanda suka aikata ayyuka na kwarai cewa suna da lada me girma (9) wanda kuma basuyi imani ba da lahira mun tanadar masu da azaba me radadi (10)” (17:9-10)


Wannan ayar itace ka'idar sa ta asali cikin aiki da sakamako. Akan imani da kuma aiki na kwarai ne aka ginata. Babu imani ba tare da aiki ba, kuma babu aiki ba tare da imani ba. na farkon yankakke ne be samu kamala ba, na biyun kuma bashi da ginshi da asali. Dasu biyun ne rayuwa tane tafiya akan hanya me karko.. da kuma su biyun ne tare shiriya yake tabbatuwa da wannan alkur'ani.


Wanda kuma basu shiryu ba da wannan alkur'ani, suna masu masu bin son zuciya da sha'awar mutum. Mutum me gaggawa jahili da abunda zai amfane shi da cutar dashi, wanda baya tsara ayyukan sa koda kuwa sharri ne a bayan su a gareshi:


“kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar irin addu'ar da yake yima kansa na alheri; kuma mutum ya kasance me gaggawa.” (17:11)


hakan ya faru ne saboda besan menene karshen abubuwa ba da sakamakon su. Kuma zai iya aikata aiki wanda sharri ne, kuma yayi gaggawa dashi akansa alhali be sani ba


sai dai bazai iya yima kansa hukunci ba da iko da kansa.. to ina wannan yake ga shiriyan alkur'ani tabbatacce me shiryarwa a tsanake?)


Wannan itace shari'a ta musulunci wacce ta tabbatar da kunsanta ga komai da zamanta ta duniya baki daya da dacewan ta da kum aikon ta akan warware dukkanin wani matsala na mutum masu adalci wanda suke adalci wanda cikin wanda ba musulmai ba marasa addini, gaskiya itace abunda makiya suka tabbatar dashi yadda suka fadi da bakunan su gaskiyar da bazasu iya boye ta ba, zamu ambaci maganar su domin ya zama hujja akan mutanen su watakila zukatansu ya rabu da makauniyar biyayya sais u gane gaskiya wacce ta boye masu game da wannan shari'a me sauki yadda zukatan su zai samu natsuwa, (William Montogmery Watt) yace2:


“lallai izina na alkur'ani wanda yake hade da larabawa bazai yiwu a kore cewa ba ma'aboci ne na dabi'ar duniya, kuma wannan sako na musulunci wanda farkon say a tunkari mutanen makkaci cikin birni wacce ta kasance tana daukan iri ga duniya, ko kuma ta jasance tun farkon ta ko kuma abunda ta kunsa a farkon al'amari me nisa ne na duniya.”


Kuma yana cewa: “lallai alkur'ani ya rabauto da samun karbuwa me fadi ba tare da duba zuwa ga yaren sa; domin yan akunshe ne al'amuran mutum.”


2 William Montogmery Watt malamin tarihi ne na turawa, cikin littafin musulunci da kiristanci a wannan zamani namu, shafi na (33) (223-226)


Ya kuma kara cewa: “hakika musulunci da kansa ya jadda da aiki cewa addini ne me cin gashin kansa daga sauran addininai tsofaffi (yahudanci da kiristanci), muna fadi akan gaskiya: lallai ya kasance ya samu rinjaye akansu ko kuma ya samu nasara akansu, ko kuma yafi su daukaka!”


Shari'ar musulunta ta banbanta da banbanci a bayyane akan sauran nau'uka na dokoki; dokoki ne me cin gashin kansa, lallai shari'ar musulunci zance ne wanda ya kunshi umurnin na Allah wanda suke tsara rayuwan ko wani musulmi ta dukkanin bangarorinta.


Wannan shine addinin mu, kuma wannan itace shari'ar mu wanda muke fatan mutune baki daya su zabeta domin ba'a saukar masu da it aba face don rahama a garesu, zamuce ga dukkanin wanda ya karanta wannan littafi daga cikin wand aba musulmi ba fadin Allah madaukaki:


“idan kuma kuka juya baya zai canza wasu mutane wanda baku ba sa'annan kuma bazasu zama irin ku ba” (47:38)


• Yaudaran yan jarida na canza Kalmar shari'a.


• Manufa na yin dokoki.


• Doka na dindin din da kuma kirkiro dokoki.


1- Gazawa na dokokin da mutane suka kirkira game da hukuncin akan ayyukan barna masu girma.


2- Muhimmancin samun shari'ar Allah.


3- Doka na mutane da doka ta daji.


• Dimuwa na dokokin mutane da kuma rashin dawwamanta.


1- Kisa na jin kai.


2- Siyar da kayan miyagun kayan maye.


3- Azabar kisa.


• Shiririta na ukubar cikin doka na mutane.


1- Akidar mika wuyan mutum cikin shari'u na mutane.


• Laifukan da aka wallafa su daga cikin dokokin dan Adam


Kalmar shari'a cikin harshen larabci tana nufin doka ko hanya ko manhaji, shari'a ta dagi itace doka na wanzuwan me karfi, dokoki kuma na coci dokoki ne wanda aka tsara su domin coci da yanayin ta, shari'a ta Humurabi shari'a ce wacce sarkin Humurabi na daular Babila tsohuwa ya kafa, shari'a na fir'auna itace shari'ar da misirawa tsofaffi suka kafa domin tsara al'amuran kasar su, amma aka jingina Kalmar shari'a da addinin yahudanci ko kuma kiristanci ko muslunci anan ana nufi da ita cewa abunda Allah ya shar'anta ya kuma wajabtama mutane na akidu da hukunce hukunce da dokoki wanda suke tsara al'amuran duniyan su da kuma nuna masu hanyar alheri da rabauta a lahiran su, tare da sanin cewa anan wurin abunda muke nufi da Kalmar shari'a na yahudanci ko kiristanci shine shari'a na asali wanda Allah madaukaki ya saukar ga annabin sa Musa da annabi Isa amincin Allah ya kara tabbata agare su gabanin mutanensu su canza su, shari'a ce wacce aka shafeta da shari'ar musulunci wacce Allah ya kiyaye ta daga dukkanin wani canzawa ko kuma gyara, Allah madaukaki yace:


“kuma mun saukar maka da littafi da gaskiya me gasgatawa ga abunda ke gabanin sa na littafi kuma me rinjaye ne akansa to kayi hukunci a tsakanin su da abunda Allah ya saukar kuma kada kabi son zuciyar su game da abunda yazo maka na gaskiya; ko wanne a cikin ku mun sanya masa shari'a da manhaji; kuma da Allah yaso da ya sanya ku kun zama al'umma daya sai dai domin ya


jarabaku cikin abunda ya baku; to kuyi rigegeniya ga alheri; ga Allah makomar ku take baki daya sai ya baku labari game da abunda kuke samun sabani akai (48)” (5:48)


Kalmar”shari'a”idan aka fassara su zuwa ga wasu yaruka za'a fassara ta ne da ma'anar”doka”wannan shine asali kuma gaskiya, sai dai wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma masu manufa suna amfani da dukkanin damar su wurin nema daga musulunci da shari'ar sa me sauki kokarin bata shi da batar da hankulan mutane da nisantar dasu daga gareshi ta hanyar bata manufa na shari'ar daga Kalmar shari'ar musulunci, a duk lokacin da sukaci karo da wani wuri wanda yake da alaka da shari'ar musulunci basa fassara shi kamar yadda yake a harshen larabci”shari'a”da ma'anar sa na dai-dai a yaren su wanda yake nufin”doka", suna fassara shi ne kamar yadda ake furtashi da yaren larabci”shari'a", kuma suna rubuta shi ta hanyar”rubuta na sauti”sais u rubuta shi da haruffa na turanci kuma su furta shi da yare na daban kamar yadda ake furtashi da yaren larabci”shari'a"!!


SHARI'A = LAW


SHARI'A LAW = LAW LAW


Dalilin haka kuwa na rashin fassara shi da doka na musulunci domin kasancewar Kalmar doka tana nufin abu ne me tsari wanda yake tsara halayen mutane, sai kafafen yada


labarai batattu suyi kokarin rabawa tsakanin Kalmar doka da kuma Kalmar shari'a da kuma rabe dukkanin wani mahada a tsakanin su, domin kokarin sun a haifar da wani taswiri a kwakwalwar me sauraro game da Kalmar shari'a da cewa al'adace na me muni da rashin imani bawai me tsara rayuwan mutum bace, amma ta dayan bangaren kuma idan zasu fassara shari'ar Musa sais u fassara ta da dokan Musa, haka idan zasu fassara shari'u na coci sais u fassara ta da dokoki na coci haka dai!! Kamar yadda a lokacin aikin ta na aikin jarida na yin shiri ko kuma bahasi akan shari'ar musulunci sai ta kashe kamaranta akan dukkanin musulman da suke cikin kasashe na duniya wanda adadin su yakai kusan biliyan biyu na musulmai sai gta tafi da dukkanin kamaranta zuwa ga tafiya me nisa tana tsallake tashoshi da garuruwa har sai ta isa zuwa ga dutsen Kandahar wanda wata matalauciyan kabila take rayuwa wanda yawan su be wuce wani adadi takaidacce ba, bata da abunda zataci sannan kuma basu samu dama ba na karatu kai hatta ruwan da zasu sha me kyau basu samu daman samun hakan ba balantana a suranta wahalhalun rayuwan su kuma duniya sun zaburar akan taimaka masu, tana tashi ne domin zaburar da duniya game da taimakon su da kuma sawwara su a matsayin sune wakilai na musulunci sannan kuma dukkanin ayyukan su musulunci ne a karon kansa!! Duk a wannan lokaci dai kuma take sawwara kiristoci da cewa su al'umma ce wayayyu masu ilimi kololuwa da ci gaba na ilimi cikin kokarinta na kirkiran sura cikin hankulan duniya na koma bayan musulunci, sannan babban abunda ya kawo masu wannan koma bayan shine dalilin binsu da sukeyi na karantarwan addinin musulunci, sannan kuma dalilin ci gaban kiristoci da wayewar su yana komawa ne dalilin binsu da sukeyi ma karantarwan addinin kiristanci!! Hakika kafafen yada labarai sun manta da wani


abu cewa wannan fa wacce take aiki na kwatantawa tsakanin kabilun musulunci wanda suke rayuwa akan tsaunin Kandahar da kuma ko wace kungiya me kabilanci na kiristanci cewa ya wajaba a kwatanta da kabilar Gajar na kiristanci wacce ta cika dukkanin kasashe na turawa!!! Yadda dayawa cikin kasashen turawa suke wahala domin tsugunar da wannan kabila ta gajar cikin mahalli na natsuwa saboda cewa wannan kabilar taki zama a wuri daya domin sun zabi rayuwa na zango zango daga nan wuri zuwa wani wuri na daban.


Hakika wannan kabila na gajar tayi fama kiyayya na bangaranci me tsanani da kuma toye masu dayawa cikin hakkokin su cikin kasashen su, dukkan haka fa sun manta dashi sannan kuma sun kashe hasken kamaransu akan sa domin boye hakan ga duniya wanda da ace wannan kabilar ta gajar tana bin addinin musulunci ne da kamaransu ta dauke su da sawwara su da cewa hakan shine musulunci a karon kansa kuma karantarwan shari'ar musulunci itace ta sanya rayuwan su ya zama na yada zango daga wannan wuri zuwa wani wuri!!! Kamar kuma yadda kafafen yada labarai suka manta har wayau ta hasko mana malamaun musulunci wanda suke rayuwa a yau a kasashen turai ne ko kuma amerika ko austireliya ko asiya ko kuma afirka, wanda suke jagorantan duniya cikin dayawa na bangarorin ilimi ko tattalin arziki ko siyasa ballantana ace maluman musulmai na zamanin can wanda suka haskaka duniya da ilimin su a zamanin da ba'asan turai ba watan zamanin tsakiya ko kuma kuma zamanin duhu, a lokacin da turai ta kasance koma baya cikin dukkanin bangarorin ilimi da wayewa tun shekara 400 miladiyya har zuwa kusan shekara na 1400 miladiyya a lokacin da coci ta kasance tana fada da dukkanin abunda yake da alaka da ilimi ko kuma maluma, har wani cikin maluman tarihi na turawa me


suna Edward Jeebon yafadi wata maganar sa shahararriya game da wannan zamani:


“shekara dubi na cin nasarar hamajiyya da kuma addini.” 3


Lallai manufa daya dilo nayin dokoki da kuma rubuta kundun tsarin mulki shine tsara halin mutane shin ta bangaren zamantakewa ne ko kuma tattalin arziki ne ko kuma siyasa..., bayan nassi akan hakkokin da wajibobi na kowani mutum cikin al'umma na akaron kansa da kuma kasancewar sa daya cikin al'umma, da kuma nassi akan yanci mutum da kuma iyakokin sa, yancin ko wani mutum ba kai tsaye take ba babu iyaka a'a tana tsayawa ne akan yancin sauran mutane, watan ma'ana kada yake ta yancin wasu da yancin sa ko kuma ya zama ya ketara iyaka da barna, da haka ne ya zama dukkanin doka yana nassanta bangarori na ladabtarwa da kuma azabtarwa ga dukkanin wanda yak eta hakkin wasu.


Akan wannan abunda ya gabata lallai banbancin na tsira ko kuma rashin nasara na ko wani doka yana ginuwa ne akan ikonsa na tabbatar da burin da aka ambata abaya, da kuma samar da ukuba wacce ta kunshi tabbatar dashi da kuma yin ukuba ga duk wanda ya saba mashi, da kuma lura da cewa


3 Edward Gibbon: cikin shinfidar wannan juzu'I na tarihi ' na kuma bayyana nasara na zamanin jahilci da addini'. Cikin littafin kafuwa da kuma faduwar masarautan Ruma' juzu'I na 3, ch. LXXI, shafi na 1068.


ukuba baya wajaba ace ta wuce iyaka inda zata cucar da me kuskure a'a ya wajaba ya zama tana da hadafi ne na tabbatar da abubuwa masu zuwa Kaman haka:


1. GYARAN KUSKURE: kamar yadda yake cikin ukubar biyan kayan da aka lalata ta hanyar biyan kudi na gwargwadon abunda aka lalata ko kuma tara na kudi ga mutumin da aka cutar.


2. GINA ME LAIFI: gina shi da kuma hurar dashi ta yadda zai zama mutum tsayayye wanda al'umma zasuyi marhaba dashi.


3. TSAWATARWA ga mai laifi: da kuma hana aikata irin wannan laifi nan gaba.


4. TSAWATAR WA GA MUTANE: saboda kada suyi koyi da mai laifi cikin aikata laifin irin nashi suma, bayan sunga irin ukubar da aka masa.


GAZAWA NA DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA GAME DA HUKUNCIN AKAN AYYUKAN BARNA MASU GIRMA:


A cikin wannan duniya tamu tayau muna ganin dayawa daga cikin kungiyoyi na dokoki da masana'antu na shari'u da kwalejoji na hakkoki da masalisun dokoki na kasashe na ciki da waje, bugu da kari kuma ga rundunoni na yan mutanen dokoki wanda ya kunshi lauyoyi da alkalai da masana kundin


tsarin mulki da shuwagabanni na kasashe da sauran su, bugu da kari kuma da rundunoni wanda suka kunshi yan sanda da kuma miliyoyi na fursinoni da wanda ake tsare dasu, kmar yadda kuma muke ganin dayawa na kokarin kirkiran doka wanda zai tabbatar da manufar da muka fadi a baya, shin sun iya kirkiro wannan doka wanda wanda yake basu daman tabbatar da ganin cewa an tsawatar da mutane daga keta hakkokin wasu?!! Ko kuma dai har yanzu bamu gushe ba muna rayuwa cikin wannan duniya namu cikin manyan laifuka cikin kasashe da dama?!! Ko kuma ta wani fuskar muce shin wannan dokoki sunyi nasara wurin samar da tsaro ga duniya kuma shin yayi nasara hukunci na alkalanci akan manyan laifuka da matsaloli wand muke ganin su ayau kuma suna karuwa a kullum?!!! Idan haka ne ashe duniya tana da bukata na kawo wani doka wanda zai tabbatar da da hakan sai dai kuma ta yaya?


MUHIMMANCIN SAMUN SHARI'A NA ALLAH MADAUKAKI:


A cikin zamunan baya can da dadewa shin akwai kungiyoyi na dokoki ko kuma alkalanci ko kuma me sa ido wurin samar da doka da kuma aiki dashi wanda zai tsarama mutane al'amuran su?!! Saboda haka kodai Allah madaukaki ya saukar da doka daga gareshi me tsararriya da kuma tsara al'amuran mutum wanda baya mukatar wasu masu kirkiro doka su kawatashi ko kuma yi masa gyara, ko kuma doka na dawa yayi aiki me karfi yaci mara karfi!!


Ya kasance daga cikin adalcin sa da rahamar sag a bayin sa ya saukar masu da shari'a (dokoki), wacce bata canzawa, dawwamanta da adalcinta baya canzawa da shudewan zamani ko kuma wuri, babban laifi a cikinta babban


laifi ne wanda babu yadda za'ayi har Abadan ya koma abu me kyau, sannan gaskiya a cikinta gaskiya ne bazai taba canzawa ba zuwa barna, dukkanin su daya suke a gaban adalcinta, amma hukunce hukuncen ta suna sabunta lokaci bayan lokaci ta hanyar manzanni wanda Allah yake aiko su domin su shiryar da mutane su kuma kawo masu shari'a wacce take tsara masu al'amuran su na rayuwa, bayan yahudawa sun manta da canza hukunce hukuncen na shari'ar su, sai Allah ya aiko da annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi domin ya sabunta hukunce hukunce na shari'ar Allah, baya kiristoci sun manta da kuma canza hukunce hukunce na shari'ar su, sai Allah ya rufe shari'ar sa da manzancin Muhammad s.a.w, sai ya aiko shi da shari'a da hukunce hukunce masu kyau wanda suka dace da dukkanin zamani da wuri basa canzawa ko jujjuyawa da shudewan zamani, shari'a ce wacce take cikamako na shari'u, Allah madaukaki yace:


“sa'annan kuma muka sanya ka akan shari'a na umurni saboda haka ka bita kuma kada kabi son zuciya na wanda basa sani” (45:18)


Wannan zai bayyana maka a bayyane cikin kwatantawa ukuba na cikin shari'a da abunta take gadarwa, ya sanya tsanani na ukuba gwargwadon girman laifi da kuma hatsarinta ga al'umma, shari'a bata karkata ko kuma yin hidima ga son zuciya da daga kafa ko munafunci, tana daidaito tsakanin wanda suka cancanci ukuba kuma bata dauke ukuba akan wani babban mutum me alfarma domin matsayin sa cikin mutane ko kuma alfarman sa ko kuma mulkin sa, sannan kuma bata dauke ukuba akan me kudi domin yawan kudin sa, wannan a bayyane yake cikin fadin manzon Allah s.a.w:


“lallai yana daga cikin abunda ya halakar da mutane da suke gabanin ku shine, sun kasance idan wani babban mutum a cikin su yayi sata sais u kyale shi, amma


idan kuma me raunin cikin su yayi sata sai su yanke masa hukunci, ina rantsuwa da Allah da ace Fatima diyar Muhammad [manzon Allah] zatayi sata da sai na yanke mata hannu” (buhari ne ya rawaito shi)


DOKOKIN DA MUTANE SUKA KIRKIRA DA DOKOKI NA DAWA:


A hakikanin gaskiya dayawa daga cikin dokoki na dan Adam a wannan zamani namu wani irin fuska ne na dokokin dawa saboda wasu zababbu na cikin majalisar dokoki ko kuma wasu daga cikin masu kirkiran doka mutane ba gurbatattu masu buri dason shugabanci ko kum aduniya sais u kirkiri doka wanda a zahirinta gyara ce amma kuma a badininta kawai tana tabbatar masu da maslahar su ce da kuma yin hidima ga burin su ta hanyar yin amfani da arzikin talakawa!! Saboda haka ne kuma Allah madaukaki me ni'ima a garemu ya saukar mana da doka me adalci da hikima wanda baya banbancewa tsakanin me mulki da wanda ake mulka ko kuma me kudi da talaka ko farin fata da bakin fata ko kuma wani aji akan wasu aji, doka ne me adalci wanda ya nisanta daga son zuciya ko zalumci ko buri!! Allah madaukaki yace:


“yanzu shin hukunci na jahilci suke so da kauna; kuma wanene yafi Allah kyawu na hukunci ga mutane masu sakankancewa” (5:50)


RASHIN DACEWAR MUTUM WURIN KIRKIRAN DOKOKI KANANA BA TARE DA KOMAWA ZUWA GA DOKAN ALLAH:


Lallai mutum tun fil azal sun banbanta, daga cikin su akwai me kabilanci sannan akwai jarumi sannan akwai mara hankali sannan akwai mujirimi sannan akwai dan fashi kuma


akwai me tausayi kuma akwai mugu, daga cikin su akwai balarabe da dan china da dan indiya sannan akwai baki kuma akwai farin fata, kuma daga cikin su akwai dan jari hujja sannan kuma akwai dan mazan jiya da dai sauran su. Saboda wannan banbancin ne ya zama dalili babba na samun rashin tabbatar ra'ayi na dan Adam da kuma iyakanci hakkoki da wajibobi da kuma iyakance abubuwa masu kyau daga aikin barna, a zamanin Hitila misali an kawo dokoki wanda yake banbance tsakani gwargwadon dangantakan mutum ko kuma banbancin kalan fata, yadda suke daukan cewa jinsin da ake kira da suna Ariyawa su sukafi cancantar zama masu mulkin duniya baki dayan sa, sannan kuma shi mutum dan jinsin Ariyawa misali a ganin Hilta shine fari me idanu biyu masu kalan fatsi fatsi kuma dogo, wanda hakan yaba mutanen almaniyawa a farkon shekaran 1933 miladi daman yin aiki na mugunta akan mutane dayawa wanda ba jinsun ba na Ariyawa, kamar bakyaken mutane yan gudun hijira wanda yawan su yakai dubu 30 a almaniya a wannan lokaci, da nakasassu na almaniya ko kuma wanda aka Haifa kurma ko makaho ko mahaukaci dukda cewa suma yan almaniya ne, sai dai wanann nakasa nasu ko kuma rashin lafiyar su ya haramta masu a dauke su a matsayin jinsin ariyawa masu tsarki.


A kasar Amerika kuma misali anyi kisan kare dangi ga yan indiya da kuma kwace gonakin su, yadda aka kashe mutum miliyan dari na indiyawa, kuma hakika Hilta ya dauki darasi daga wannan kisa na kare dangi wurin yima yahudawa kisan kare dangi shima wanda kuma hakika an fadi hakan cikin bugun farko na littafi me suna”KAFAHI”4.


Kuma sama da jihohi 30 na amerika sun hana auren wasu wanda ba asalin turawa ba na mutanen bakin fata ko china ko kuma almaniya ko indiya ko malayo ko magul.


4 Mein Kampf


Sannan an kirkiro daywa daga dokoki na masu nuna banbanci wanda suke fifita da bayar da dama ga wasu bangare na mutune wanda sune farare na Anjilo Saskon daga protastanant. Sannan kuma abun Ambato ne cewa dukkanin shuwagabannin amerika sun fito ne daga cikin wannan bangare banda John kenedy da Barak ubama.


Su kuma bakin fata anyi dokoki na kabilanci akan su wanda akafi sani da suna dokoki na Jim Crow5.


Lallai duk me duba cikin tarihi na dokoki da kuma rubutun kundun tsarin mulki zaiga cewa dokoki ne wanda mutane suka kirkira wacce take canzawa kullum yadda zakaga cewa doka baya tabbata zuwa wani dogon lokaci na zamani, abunda yake babban laifi ne a wannan lokaci ya zama cikin ayyuka masu kyau ko kuma hakki cikin wnai zamani na daban ko kuma akasin haka, misali kayan nunkaya na mace a amerika a shekarar 1850 miladi da kum shekarar 1920 ya kasance mayafi dogo wanda zai rufe dukkanin jikinta baki daya, kuma da mace zata ki juya baya irin yadda matan amerika masu nunkaya na wannan zamani namu suke juyawa akan haka da ankamata kuma an ladabtar da ita, haka kuma kamar yadda koda yake canzawa da canzawar zamani haka kuma yake canzawa da canzawan wuri, kamar misali a cikin kasashen hadin kan turawa dokar ko wace kasa ta banbanta da


5 Jim Crow laws.


na wata kasar a cikin kasashen kawancen, kai hatta a cikin kasa daya misali kasar amerika dokan wata jiha tana banbanta data wata jihar, kenan tana aiki ne ga son zuciya da burin yan siyasa wanda suke wajabta akan mutane, daga cikin misali akan haka:-


KISAN MARA LAFIYA DOMIN SAUKAKA MASA6:


Shine kisa ta hanyar taimakon wani mutum na daman, kuma ya kasu zuwa gida uku:-


1. KISAN MARA LAFIYA WANDA CIWO YA CINYE DOMIN A SAUKAKA MASA: anayin hakan ne da yardan mara lafiyan, al'amari na doka a wasu kasashe na turawa da kuma wasu hijohi cikin amerika.


2. KISAN MARA LAFIYA WANDA CIWO YA CINYE DOMIN SAUKAKA MASA: wannan anayin shi ne ba tare da yardan mara lafiyar ba, misalin irin wannan kisa ga yara cikin wani yanayi na musamman a kasar Holand karkashin tsari na Jironijin7.


3. KISA NA TILAS: wannan anayin sa ne ba tare da son mara lafiya ba.


A takaicen al'amari samun wanda suke goyon baya da wanda basa goyon bayan haka wanda ko wannan ne yana da hujjojin sa da kuma dalilan sa wanda yake ganin ingancin su, wasu kasashen kuwa tana sanya hakan ya zama doka sabanin


6 Euthanasia da turanci.


7 Groningen Protocol, 2004, Eduard Verhagen, Netherlands


wasu kasashen da suke ganin hakan yana cikin manyan laifuka.


Kuma an rubuta irin wannan yanayi na kisa tare da niyya kamar misalin halin Dakta Nigal Cox8 wanda yayi amfani dayin allura ga mara lafiyar sa Lailayan Buwis da allurer chloride potassium na guba domin ya tsayar da zuciyarta daga aiki, kuma ya kafa hujja ne a lokacin kare kansa da cewa yana son saukakawa ne a gareta na azabar radadin da take fama dashi, kuma kotun tayi masa hukunci da kulleshi a gidan yari na shekara da kuma hanashi aiki, bayan shekara daya sai ya samu lasisi na ci gaba da aikin likitancin sa kamar wani abu be taba faruwa ba.


SIYAR DA MIYAGUN KAYA NA MAYE:


Akwai wasu kasashe cikin kasashen turawa wanda sukayi doka na siyarwa da kuma yin mu'amala da miyagun kayan maye da sharadi da kuma adadi na abunda aka yarda asha ko asiyar, sannan kuma a daya bangaren kuma wasu daga cikin kasashen turawa sun haramta siyarwa ko kuma mu'amala da miyagun kaya maye, abun mamaki shine daya daga cikin kasashe kuma ta yi dokan sayar da miyagun kayan maye amma gay an kasanta kawai, yadda suka haramta hakan ga matafiya wanda sukazo bude ido da makamantan su yin mu'amala da miyagun kayan maye domin hana yawon kayan maye a cikin kasarta, wanda doka ne wanda dayawa na mutanen da suke siyar da kayan mayen sukayi fatali da ita suna masu fadin cewa hakan zai karya masu kasauwancin su da hanyan samun kudin su.


8 Nigel Cox.


UKUBA TA KISA:


Akwai daga cikin kasashen turawa da wasu jihohi na kasar amerika wanda suka haramta ukuba na kisa, wanda a dayan bangaren kuma wasu kasashe na turawa da suwa jihohi na kasar maerika suke halasta hakan cikin dokokin su kuma suna aiki dashi!!


Kenan: ina illa dawwamamme wanda zamu iya yin kiyasi akan sa da kuma sani daga gareshi cewa menene babban laifi sannan kuma menene makaruhi?! Sannan kuma menene daidai kuma menene barna?!


Atakaice: abunda akayi ittifaki akansa a wurin masu hankali shine ita gaskiya day ace kuma dawwamammiya ce bata canzawa da canzawan zamani ko kuma wuri, haka kuma halaye na gari na kwarai da kuma hayalen banza da laifuka suma tabbatattu ne basa canzawa da canzawan zamani ko kuma wuri, kuma baya halatta har abadan ace aiki aikin nagari na koma aikin banza ko kuma aikin banza ya koma aiki na gari!!.


Cikin dubi zuwa ga wasu shari'u da ukuba wanda aka kirkire su a tsawon zamani kamar a lokacin mulkin fir'auna ko kuma china ko indiya ko almaniya ko romaniya tsofaffi ko kuma shari'u na kabilun afirka da bakake zamuga cewa shari'u ne ko kuma ukuba na shiririta, hakika wannan ukubar sun


kasance masu azabtarwa ne ga me laifi na rashin tsari, kamar ukuba na kisa akan karamin abu da kuma hanyar da akebi wurin yin azabar wanda aka masa hukunci da kisa, wani lokaci a kashe shi ta hanyar yanke masa kai da abun yanke kai kamar misali abunda ya faru a lokacin mulkin firnasa louis na shida9 a shekara ta 1793 miladi, wani lokaci kuma a yanke masa kai da adda sa'annan kuma a datsa gangan jikin su zuwa gida hudu kamar misalin abunda ya faru ga Thomas Armstrong10 a shekara ta 1684 a kasar amerika, wani lokaci kuma a cire masa hanjin cikin sa da kuma yanke gabbansa da ransa sai kuma a cire zuciyar sa daga kirjin sa sai a yanke masa kai makar misali abunda ya faru ga Balthasar Gerard11 a shekara ta 1584 a kasar holand, wani lokaci kuma a yankashi da wuka, wani lokaci kuma a gicciyeshi akan bishiya sai a kona shi da ransa kammar yadda yake a cikin kotuna na bincikie na kasar spaniya da Portugal da romaniya karkashin sa idon kasawasa, wani lokaci kuma a jefa shi ga zaki me jin yunwa a cikin filin wasan romaniya, wani lokaci kuma a sanya shi akan injin daka kai da ransa, wani lokaci kuma a sanya shi akan kujeran wutan lantarki kamar yadda akayima Lynda Lyon Block12 a shekara ta 2002 a kasar amerika, a wani lokaci kuma a jefa shi cikin ruwa kamar yadda akayima masu taimakon juyin juya hali na faransa13 a shekara ta 1793 a faransa, wani lokaci kuma a daura masa karfi me zafi akai ko kuma dutse me nauyi akan kirjin sa kamar yadda akayima



Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC