Da sunan Allah me rahama me jin kai.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai,
tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da
iyalan sa da sahabban sa baki daya.
Kasancewar magana akan soyayya a cikin musulunci ga
mata, ya zama dole ya kasance Muhammad manzon Allah s.a.w
shine tushen wannan magana kasancewar sa manzon allah
wanda aka aiko shi zuwa ga mutune baki dayan su domin ya
karantar dasu abunda Allah ya shar'anta kuma su samu ginshiki
da dabi'un sa, shine abun koyi ga musulmai wanda ya wajaba a
garesu su bishi da kuma koyi da sunnar sa domin aiki da
umurnin Allah madaukaki wanda yake cewa:
“ hakika ya kasance kuna da abun koyi me kyau daga
manzon Allah s.w.a ga wanda ya kasance yana kwadayin
haduwa da Allah da rana ta karshe kuma ya ambaci Allah
dayawa ” suratul ahzab ayata 21.
Shine me isarwa game da Allah saboda haka ne babu
wani abu daya buya ga musulmai game da al'amuran rayuwan
sa baki daya kananan su da manyan su, ke bantaccen su da
game garin su face an sansu kuma ya shahara a tsakanin su
kuma a rawaito shi daga wannan jama'ar zuwa wata jama'ar
kasancewar maganganun sa da ayyukan sa hukunce hukunce ne
da shari'a wanda ta hanyar su ne musulmi yake sanin addinin sa
wanda yake isar dashi zuwa ga soyayyar Allah da yardan sa da
aljannar sa, Allah madaukaki yace:
“ kace masu idan kun kasance kuna son Allah to ku bini
Allah zai so ku kuma zai gafarta maku zunuban ku, Allah
ya kasance me gafara kuma me rahama (31) ” . Surat Aal
‘Imran ayata 31
Lallai ginshikin musulunci shine soyayya wanda zata
sanyaka ta sanadiyyar ta kayi biyayya ga wanda kake so kuma
kabi umurnin sa da kuma hanuwa daga abunda ya hana , kuma
kayi kokari matukar iyawan ka na ganin ka kusance sa ta
hanyar aikata abuuwan da yake so, lallai mafi girman so da
daukaka shine son Allah madaukaki wacce ta hanyar hakan ne
ake samun damar fadakar da musulmi halaye na gari wanda zai
rabu son kai kuma ya samu daukaka da alamomin sa sai ya
yada soyayya da rahama ga halittun Allah ba tare da jiran wani
ladaba na kudi daga gare su, sai ya rabu da son kai wacce ta
ginu akan maslaha da amfanin karon kan mutum shi kadai,
daga ita kuma sai soyayyar manzon Allah s.a.w ya biyo baya
soyayya tsarkakakkiya wacce ake gabatar da ita akan son ran
mutum da dukiya da yara kasancewar sa shine sababin shiriya
da kuma nuni zuwa ga Allah da kuma addini na gari wanda
Allah ya sanya shi tsira daga wuta ga duk wanda ya bishi da
kuma shiga aljanna saboda hakane ya cancanci wannan matsayi
da daraja me girma tare kuma da ajiye shi a matsayin da Allah
ya ajiye shi watan matsayi na bauta da Kankan dakai ga Allah,
Allah madaukaki yana cewa:
“ kace idan ya kasance cewa iyayen ku da yaran ku da ‘yan
uwan ku da matayen ku da dangin ku da dukiyoyin ku
wanda kuka tara da kasuwancin ku wanda kuke tsoron
karyewan sa da kuma gidajen ku wanda suke burgeku da
son rayuwa a cikin su sunfi soyuwa a gare ku sama da Allah
da manzon sa da kuma jihadi domin daukaka addinin sa to
ku saurara ku jira har Allah yazo maku da al'amarin sa,
lallai Allah baya shiryar da mutane fasikai ” suratul taubah
ayata 24.
Duk wanda ya qudurce cewa musulunci addini ne na
tsanani da kausasawa to hakika yayi kuskure, gaskiyar itace
musulunci addini ne wanda ya kunshi komai watan ma'ana be
bar kananan abubuwa ba ko kuma manya na rayuwan musulmi
shin hakan ya shafi kudi ne ko kuma zuciya face ya fadakar da
ita fadakarwa me kyau ya kuma sanyata a wurinta daya dace,
musulunci ba addinin aqida bane da hukunce hukunce da dabi'u
bane kadai a'a addini ne kuma har wayau na soyayya ta fuskar
fahimtar sa a musulunce wanda ya kunshi komai hakan ya
tattaru cikin so da kauna da rahama da tausayi da kyautatawa
da dajara alamomi da dabi'u masu daraja da mu'amala masu
kyau ga dukkanin abunda yake kewaye da mutum cikin wannan
duniya na halittu bawai kawai ya takaitu bane akan wani
bangare guda bane wanda ya tattaru tsakanin namiji da mace na
mu'amala na magana ko kuma na aiki kawai, baya cikin
soyayya ka kasance me kyakyawan mu'amala ga wanda kakeso
kadai ba da kuma munana mu'amala ga wanin sa, saboda haka
ne zamu kawo wasu daga cikin siffofi da dabi'u na musulmi,
har mu gane ma'anar so cikin musulunci ga dukkanin wanda
yake kewaye da musulmi.
WWW.ISLAMLAND.COM
info@islamland.com
• Musulmi shine wanda mutane suka amintu dashi aminci
wanda ya kunshi komai akan rayukan su da dukiyoyin su da
mutuncin su dashi saboda fadin manzon Allah s.a.w cewa:
“ shin na baku labarin wanene mumini shine wanda
mutane suka amintu dashi akan dukiyar su da rayukan su
shi kuma musulmi shien wanda mutane suka tsire daga
harshen sa da hannun sa ” . Hadisi ne ingantacce Ahmad da
Ibn hibban ne suka rawaito shi (al sahihah) (549).
• Bawannan bane kawai musulmi shine wanda yakeson
alheri kuma yake yadashi ga mutane kuma yana aiki tukuru
domin isar dashi zuwa gare su ba tare da amsan wani hasafi ba
daga garesu akan hakan, saboda fadin sa manzon Allah s.a.w:
“ ka kiyaye abubuwan da Allah yayi umurni dasu da kuma
wanda yayi hani dasu zaka zama cikin mutane masu bauta,
ka yarda da abunda Allah ya baka zaka zama mafi arzikin
mutane kuma ka kyautata wa makwabcin ka zaka zama
mumini, kasoma mutane abunda kake soma kanka zaka
zama musulmi… ” (Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito shi
kuma albani ya ingantashi).
• Musulmi shine wanda yake kasancewa me adalci a
kansa da kuma al'ummar sa hatta makiyan sa, baya daukan
fansa akan wani da zunubin wanin sa manzon Allah s.a.w ya
kasance idan zai tura rundunar yaki cikin musulmai zuwa ga
mushrikai wanda suka cutar dashi kuma suka fitar dashi daga
gidan sa da kuma taimakawa wasu akan fitar dashi suka kuma
kashe sahabban sa da azabtar da duk wanda yabi addinin sa
yanayin wasiyya ga shugaban wannan runduna gareshi karan
kansa da jin tsoron Allah da kuma wanda suke tare dashi cikin
musulmai da alheri. Sa'annan yace (kuyi yaki da sunan Allah
domin Allah. Ku yaki wanda ya kafurcewa Allah. Kuyi yaki
kada ku wuce gona da iri kuma kada kuyi yaudara kuma kada
kuyi gunduwa gunduwa kuma kada ku kashe yara kanana)
(sahihu muslim)
• Musulmi shine wanda yake kiyaye mahallin da yake
kewaye dashi da dukkanin abunda ke cikinta na dabbobi, baya
yarda da azabtar da ita domin kuwa an wuce gaban manzon
Allah s.a.w da wani jaki wanda aka masa zane a fuskar sa sai
yace:
“ Shin be isa gare ku bane cewa na tsinema wanda yayi ma
dabba zane a fuskanta ko kuma ya duke ta a fuska? ” .
(Sunan Abi dawud kuma albani ya inganta shi.)
Kuma yana mu'amala da ita da tausayi da rahama, Aisha Allah
ya kara mata yarda tana cewa: “ manzon Allah s.a.w yana
karkatawa mage kwarya tasha ruwa ” . (hadisi ne
ingantacce) dayalisi ne rawaito shi kuma yana cikin littafin
sahihul jami'u 4958.
Kuma yana kiyaye abunda dake cikinta na tsuntsaye baya
tsorata su kuma baya farautan su haka kawai ba tare da wani
amfani ba, Ibn mas'ud Allah ya kara masa yarda yana cewa
mun kasance tare da manzon Allah s.a.w cikin tafiya sai ya tafi
domin biyan wata bukatar sa sai mukaga wata tsuntsuwa
karama tare da ita akwai jaririyan ta sai muka dau wannan
jaririya nata sai wannan tsuntsuwa tazo tana bude fuka fukanta
tana goga su a kasa sai manzon Allah s.a.w yazo sai yace: “
wanene ya tinzira wannan da jaririnta? Ku mayar mata da
jaririnta ” sai kuma yaga wani gidan tururuwa wanda
muka kona sai yace:
“ wanene ya kona wannan? ” sai mukace mune sai yace: “
lallai baya halatta yin azaba da wuta sai ga ubangijin wutan
” (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi).
• Musulmi shine wanda yake kiyaye wuraren mutane da
wurin shakatawar su, baya samar da wani abu a wurin wanda
zai hana su amfanuwa dashi ta hanyar jefar da bola a wuraren
da makamantan su, saboda faduin manzon Allah s.a.w:
“ ku kiyaye abunda suke jawo tsinuwan mutane: shine
wanda yake bayan gida a kan hanyar mutane ko kuma a
wurin inuwar su ” (abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani
ya ingantashi).
• Hasalima musulmi shine wanda yake kawar da dukkanin
wani abu wanda yake cutar da mutane saboda fadin manzon
Allah s.a.w:
“ .. kawar da cuta daga kan hanya sadaka ce ” (abu dawud
ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
• Musulmi shine wanda yake kiyaye abunda yake da
amfani ga muhalli da mutane kamar bishiya saboda fadin
manzon Allah s.a.w: “ kada ka sare bishiyar da take iyaiya,
kuma kada ka kashe dabbar da baka da bukatar ta, kuma
ka kiyaye cutar da mumini ” (abu dawud ne ya rawaito shi
cikin littafin “ marasil ” , da Sa'id dan Mansur cikin littafin san
a “ sunan ”).
• Musulmi shine wanda yake kira zuwa ga kiyaye muhalli
ta hanyar fadakarwa akan dasa bishiya da gyara kewayenta,
saboda fadin manzon Allah s.a.w:
“ da ace duniya zata tashi a hannun wanin ku akwai
karamin bishiyar da binu wanda ta fado daga jikin
mamanta to idan ya samu daman shukata ya shukata kafin
duniyar ta tashi ” (buhari ne ya rawaito shi).
• Musulmi shine wanda yake kiyaye ruwa baya lallatashi
ko kuma sanya masa datti da kazanta, Jabir Allah ya kara masa
yarda yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w yayi hani da mutum yayi fitsari a
cikin ruwan da baya tafiya ” (muslim ne ya rawaito shi).
Yana kuma yin kokari wurin kiyaye ta da kuma yi mata dukkan
hidima wanda take bukata, saboda fadin manzon Allah s.a.w:
“ musulmai suna tarayya cikin abubuwa uku: tsirrai ko
karare, da ruwa da kuma wuta ” hadisi ne ingantacce
(ahmada ne da abu dawud suka rawaito shi).
Yana kuma yin kokari iyakan iyawan sa domin kiyaye
hanyoyin samun ruwa da kuma raya su domin al'umma su
amfanu da ita da dabbobi da shuka ta hanyar rashin yin
almubazaranci da bannatar da ita ta hanyar da bashi da amfani
saboda fadin manzon Allah s.a.w ga Sa'ad lokacin daya
wuceshi yana alwalla:
“ wannan wane irin barnan ruwa ne? ” sai yace: yanzu
akwai barnan ruwa ne a cikin alwalla, sai yace: “ eh akwai
koda kuwa ka kasance ne a wurin rafi me gudana ” . (Ibn
majjah ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi).
Kasancewa an umurce mu dabin Manzon Allah Muhammad
s.a.w wanda ya tattara halaye da dabi'u masu daraja na dukkafin
ma'ana wanda ya kunshi haka da mu'amala me kyau da
dukkanin abunda kewaye dashi na halittu wannan bin da koyi
ya zama aqida ga musulmi wanda yayi imani da ita kuma yake
kokarin aiwatar da ita cikin ayyukan san a rayuwan sa domin
neman yardan Allah, Allah madaukaki yace:
“ kace masu idan kun kasance kuna son Allah to ku bini
Allah zai so ku kuma zai gafarta maku zunuban ku, Allah
ya kasance me gafara ne me rahama (31) ” Surat Aal
‘Imran ayata 31
Wannan shine musulunci soyayya ga dukkanin abunda
Allah ya halitta wanda ake aiwatar dashi ta hanyar umurnin
Allah mutum kamar yadda yake raya gangan jikin sa daci da
shah aka yake raya zuciyar sa da addini wanda yake daukaka da
ita cikin duniyan falala ya kuma nisanta shi daga cikin duniyar
dabbobi da sha'awa ya kuma tace alamomin sa , a cikin wannan
littafi karami zamuyi magana akan bangare guda cikin
bangarori na soyayya cikin rayuwan manzon Allah s.a.w tare
da mata wanda aiko shi ya zama haske me kyau ga duniya baki
dayanta da kuma mata a kebance ya daukaka darajarta ya kuma
wajabta girmamata ya kuma kawar da zulumci akanta, hakika
mata sun kasance gabanin zuwan musulunci suna rayuwa ne a
mataki na can kasa yadda Umar dan kaddab Allah ya kara masa
yarda shugaban muminai kuma khalifa na biyu na manzon
Allah s.a.w ya sawwarata cikin fadin sa cewa:
“ wallahi mun kasance cikin jahiliyya bama daukan mace a
bakin komai, har zuwa lokacin da Allah ya saukar da
abunda ya yasaukar akan su ya kuma raba ya basu abun
da zai basu na gado ” . (Buhari da muslim ne suka rawaito
shi).
A lokacin da musulunci yazo fadakarwan sa akan mata ya
kaance bayyananne ya kuma bayyana cewa daga cikin mafi
alherin maza da dabi'u masu kyau shine kyautata mu'amala tare
da mata, manzon Allah s.a.w yace:
“ mafi alherin ku shine wanda yafi alheri ga mata ” (hakim
ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi).
Sai mace ta rabautu da daraja me girma a karkashin
musulunci da kuma matsayi kololuwa wanda be ba maza ba
kuma wasu mata na wata al'umma na daban basu same shi ba,
manzon Allah s.a.w ya kasance yana son mace a matsayin san a
mutum, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ an samun son wannan abubuwan a cikin kayan duniya:
mata da turare kuma an sanya mun natsuwana da farin
cikin rayuwa na a cikin sallah ” (Ahmad da nasa'I da Baihaki
ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin littafin
mishkat 5261).
Soyayya wacce take zagaye da tausayi da so da tausasawa
yadda yace s.a.w:
“ ….. ina maku wasiyya na kyautatawa ga mata ” (muslim
ne ya rawaito shi).
Sannan kuma an kare mata hakkokin ta daga lalace aka kumayi
umurni da yin mu'amala dasu me kyau da karrama su da kuma
hana wulakanta su, kuma tana kiransa da yi mata taushi tare da
ita da kuma darajata, manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ wanda yafi cikin imani cikin muminai shine wanda yafisu
kyaukyawan dabi'u, kuma zababben mu shine zababbe ga
matan sa ” Tirmizi ne ya rawaito shi, kuma yace: (hadisi ne
me kyau kuma ingantacce) kuma albani ya ingantashi.
Sai ya daurata a matsayinta wanda aka haramta mata gabanin
zuwan musulunci ya daidaita ta da maza cikin komai sai
abubuwan da shari'a ya kebance kamar gado da bada sheda da
sauran su cikin abubuwan da dalilai suka nuna akan hakan ya
sanyata ta zama abokiyar na miji kuma rabin jikin sa wanda
yake samun kamala da ita, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ lallai mata iyan’uwan maza ne ” Ahmad da abu dawud da
tirmizi ne suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Hasalima manzon Allah s.a.w ya sanya ta cikin mafi falalar
kyautan Allah cikin wannan duniya sai yace:
“ duniya jin dadi ne kuma mafi alherin jin dadin duniya
itace mace ta gari ” muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma sanyata mubudin farin ciki cikin wannan duniya, sai
yace:
“ abubuwa hudu suna cikin farin ciki, mace ta gari da
wurin zama yalwatacce da makwabci na gari da abun hawa
me lafiya ” Ibn hibban da hakim ne suka rawaito shi kuma
albani ya inganta shi cikin “ littafin al sahihah ” (282).
Ya kuma sanyata s.a.w rabin addinin mutum itace mace ta gari
wacce take sababi wurin gfadakar da mijinta fadakarwa na gari
sai yace:
“ idan mutum yayi aure to hakika ya ciki rabin addinin sa
sai yaji tsoron Allah cikin sauran rabin ” baihaki ne ya
rawaito shi kuma yana cikin sahihul jami'u: 6148.
Kuma kamar yadda manzon Allah s.a.w yaso mace a
matsayinta na mutum ya kuma so ta a matsayin uwa sai ya
wajabta girmamata da kuma wajabta mata biyayya da kuma
damuwa da kula da ita ya kuma sanya hakan cikin sababi na
shiga aljanna, hakika Jahimatu al salami yazo wurin manzon
Allah s.a.w sai yace masa:
“ ya manzon Allah nazo ne neman shawararka inason zuwa
yaki, sai yace masa: kanada mahaifiya? Sai yace: eh sai
yace: kaje ka lazimce ta domin lallai aljannarka tana
karkashin tafikan kafarta ne ”. nisa'I ne ya rawaito shi kuma
albani ya ingantashi.
Ya kuma sanyata tana gaba da namiji wurin biyayya da sada
zumunci yadda hakan ya kasance umurnin manzon Allah s.a.w
ga mutumin daya tambaye shi:
“ ya manzn Allah wanene mafi cancantan mutane ga mafi
kyawun zamana? Sai yace: mahaufiyar ka, sai yace: sai
kuma wa? Sai yace mahaifiyar ka, sai yace: sai kuma wa?
Sai yace mahaifiyar ka, sai kuma wa? Sai yace: mahaifin ka
” buhari ne ya rawaito shi.
Kamar kuma yarda manzon Allah yaso mace a matsayin uwa
ya kuma sota a matsayin mata, yadda yace ma Amru dan Aas
lokacin daya tambaye shi:
“ wanene kafi so cikin mutane? sai yace: “ Aisha ” ,sai yace
cikin maza fa? Sai yace: “ mahaifinta ” sai yace: sai kuma
wa? Sai yace: “ Umar ” , sai ya irga maza sai nayi shiru
saboda tsoron kada yasanya ni a karshen su ” . Buhari ne ya
rawaito shi.
Kuma kamar yadda manzon Allah s.a.w yaso mace a matsayin
mata yaso ta a matsayin diya, Aisha tana cewa Allah ya kara
mata yarda:
“ bantaba ganin wani mutum ba wanda yaki kama da
manzon Allah ta wurin dattaku da kama da shiriya cikin
tsayuwarta da zamanta kamar fadima diyar manzon Allah
s.a.w sai tace: ka kasance idan ta shiga wurin manzon Allah
s.a.w sai ya tashi ya rungume ta sannan ya zaunar da ita a
wurin zaman sa kuma manzon Allah s.a.w ya kasance idan
ya shiga wurinta sai ta tashi daga wurin zamanta da
rungume shi ta zaunar dashi a wurin zamanta… ” Tirmizi
ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
Wannan mu'amalar ta kwarai ga dukkanin mutane da kuma
mata a kebance ya samu asali ne daga fadakarwan Allah ga
dukkanin musulmai na tausayi da rangwame da tausasawa ga
mata da kuma girmama su yadda yace:
“ … kuma ku zauna dasu da kyawawan dabi'u wanda aka
sani, idan kun kyamace su to kusani fa sau dayawa kuna
kyamatar abu kuma sai Allah ya sanya masa alheri me
yawa ” surat an-nisa' ayata 19.
Ibn kasir yace cikin tafsirin wannan ayar: watan ku kyautata
maganar ku a garesu sannan kuma ku kyautata ayyukan ku da
adonku gwargwadon ikonku a garesu kamar yadda kuke son
haka daga garesu, ka aikata kwatankwacin haka a gareta, kamar
yadda Allah madaukaki yace:
“ suma suna da kwatankwacin abunda ke kan su na
kyautatawa ” . [suratul bakar ayata: 228]
Kuma hakika sahabban manzon Allah s.a.w sun kasance suna
rigegeniya wurin aiwatar da wannan manhaji da fadakarwa na
Allah, wannan dan Abbas ne malamin wannan al'umma yana
cewa:
“ lallai na ksance ina yin kwalliya ga matata kamar yadda
takemun, kuma banason amsan hakkokina duka dake
kanta saboda kada hakkokinta dake kaina ya wajaba
akaina saboda Allah madaukaki yace: “ suma suna da
kwatankwancin abunda suke dashi akan su na kyautatawa
” [suratul bakar ayata: 228]. Qurdubi an Ambato haka cikin
littafin sa na Jami'un li ahkamul kur'an.
Lallai cefanen soyayya da kyautata mu'amala da tausayi da
hakuri da mutane shine manhajin musulmi na gari wanda yake
tafiya akan sa da kuma aiwatar dashi da aiki dashi da kuma
tallar sa domin aiwatar da umurnin Allah, wanann shugaban
Ahlussunah ne waljama'a yakeyima dansa wasiyya ranan
angoncin sa yana sanar dashi hakkokin matar sa akansa da
cewa:
“ ya kai dana ka sani fa bazaka taba samun farin ciki ba a gidan
ka sai da wannan abubuwa guda goma wanda zaka rika yima
matarka dan haka ka kiyaye su kuma ka himmatu dasu:
Na farko da na biyu:
Lallai mata suna son shiryarwa kuma suna son ka nuna masu
soyayya a bayyane, kada kayima matarka rowan wannan,
saboda idan kayi mata rowa zaka sanya shamaki ne tsakanin ka
da ita na tsanani da kuma tawayan soyayya.
Na uku kuma:
Su mata suna kyaman namiji me tsanani mara sakin fuska kuma
suna bautar da namiji me rauni da taushi saboda haka ka sanya
ko wace siffa a wajenta saboda hakan yana kawo soyayya da
natsuwar zuciya.
Na hudu:
Lallai mata suna son irin abunda miji yake so daga gare su na
kyautata magana da sura da kuma tsafta na kaya da kamshi
saboda haka ka kasance haka cikin dukkanin lokutan ka.
Na biyar:
Lallai gida mulki ne na mata kuma acikinsa ne takejin cewa
lallai ita tana da gadara da akan kujeran mulkin ta kuma ita
shugaba ce, saboda haka kashedin ka da ruguza wannan
mallaka nasu wanda take rayuwa aciki, kuma kashedin ka dayin
kokarin nesantar da ita daga wannan kujeran mulki, saboda
idan ka aikata haka ka kwace mata mulkinta, kuma babu
adawar da tafi adawa ga mutumin da zai kwace maka mulki
koda kuwa ya bayyana maka akasin haka.
Na shida:
Lallai mace tana son ta mallaki mijinta ba tare da tayi asarar
iyalanta ba, saboda haka kashedin ka da sanya kanka da
iyalanta a ma'auni daya, kodai kai ko kuma iyan’uwanta, domin
kuma koda ta zabe ka akan iyalanta to zata kasance cikin bakin
ciki wanda zai rika haifar da gaba zuwa ga rayuwan ka na
kullum.
Na bakwai:
Lallai mace an halicceta ne daga kasha karkatacce wannna
kuma shine sirrin kyau dinta, da kuma sirrin jayuwa zuwa
gareta wannan kuma ba aibu bane a gareta “ girakarkacewarta
shi ne kyawan ta ” , kada kayi kokarin daura mata kaya me
nauyi idan tayi kuskure domin kokarin gyara wannan lankwasa
nata sai ka karyata kuma karyata shine sakinta, kuma kada ka
kyaleta idan tayi kuskure sai ya kara karkacewan kuma ka
rufema kanka koma a kanta wanda bazata kara maka taushi ba
kuma bazata saurare k aba, ka kasance a koda yaushe tare da ita
a matsayin me mata bayani.
Na takwas:
Lallai mata an halicce su ne akan kafurcewa zaman takewa na
aure da kuma inkarin abun alheri, idan ka kyautatawa dayan su
na shawan shekaru sai ka saba mata na lokaci daya zatace: ban
taba ganin alheri ba a tare dakai duk zamana dakai ko sau daya
ba saboda haka kada wannan hali ya sanya ka kyamatar ta da
nisantarta, domin idan ka kyamace wani hali daga gareta zaka
yarda da wani hali daga gareta wanda bashi ba.
Na tara:
Lallai mace tana wuce wa cikin wasu yanayi na raunin jiki da
ciwon zuciya, har Allah madaukaki ya dauke mata wasu daga
cikin wasu wajibai akanta na ibada wanda ya daura mata cikin
wannan yanayi ya dauke mata salla baki dayan sa cikin wannan
yanayi ya kuma dakatar mata da azumi a cikin su har sai ta
dawo cikin lafiyar ta yanayinta ya daidaita, dan haka ka
kasance da ita cikin wannan yanayi da tarbiyya na Allah kamar
yadda ya saukaka mata wajibobi kaima ka saukaka mata neman
tayi maka wasu abubuwa da kuma bata umurni.
Na goma:
Kasani cewa mace baiwa ce a wurin ka, ka tausayawa wannan
bauta nata kuma ka kawar dakai daga raunin ta zata kasance
maka mafi alherin abun jin dadi da abokiyar zama..
Kamar yadda maza ke cefane a tsakanin su na soyayya ta
musulunci haka suma mata musulmai suna da rabo cikin
wannan cefane a tsakanin su al'amarin kyautata zamantakewa
da mu'amala me kyau tare da miji, wannan Ummu Iyas ce diyar
Auf dan Alamul shaibani lokacin da Amru dan Hajar sarkin
kasar Kanada ya nemi auren yarinyanta daren amarcin ta yazo
sai ta kebe da ita tayi mata wasiyya wacce ta bayyana mata
ginshinkin rayuwan aure na farin ciki a cikinta, da kuma
abunda ya wajaba agareta na hakkin mijinta, tace mata: yake
diyata da ace ana barin nasiha saboda falalar ladabi da nabar
maka haka, sai dai tana tunatar da wanda ya manta, da guzuri
game hankali, da ace mace tana wadatuwa daga miji da
iyayenta sun wadatu, saboda kuma tsananin bukatar su zuwa
gareta yasa ta zama mafiya wadatan mutane akan sa, sai dai
mata saboda maza aka halicce su, kuma suma saboda su ne aka
halicci maza.
“ Ya diyata: lallai zaki bar wani wuri da rayuwan da kika fito
daga ciki, kuma zaki bar rayuwa wacce aka tarbiyyance ki aciki
zuwa ga wani wuri da gida wanda baki sanshi ba, da gari
wanda bakyasomn sa, zai wayi gari da mulkin sa akanki a
matsayin me sa ido da iko, saboda haka ki zaman masa baiwa
zai zaman maki bawa da maki hidima, ki kiyaye masa wannan
abubuwa goma zai zaman maki madogaro:
Abu na farko dana biyu: Kankan da kai a gareshi da qana'a,
da kyakyawan biyayya da jin maganar sa.
Abu na uku da hudu: ki kiyaye ganin sa da hancin sa akanki,
kada ki kuskura ya ganki a cikin mummunan siffa ko kuma ya
shaka daga gareki sai kamshi me dadi.
Abu na biyar da shida: ki kiyaye lokacin baccin sa da abincin
sa, domin zafin yunwa akwai tunzurar wa kuma yunwan bacci
yan ahaifar da kiyayya
Na bakwai da na takwas: ki tsare masa dukiyan sa, da kuma
kula da hidimar sa da iyalan sa, kuma hikimar mallakan dukiya
shine: kyautata kimantawa, a cikin iyali kuma shine kyautata
tafiyar dasu.
Na tara dana goma: kada ki saba masa umurnin sa, kuma kada
ki yada masa sirrin sa, saboda idan kika saba umurnin sa
zuciyar sa zatayi kunci kuma idan kika yada sirrin sa bazaki
samu aminci ba daga tarkon sa, sa'annan kashedin ki dayin
farin ciki a gaban sa idan ya kasance yana cikin damuwa da
bakin ciki kuma kada ki rika nuna bakin ciki a gaban sa idan
yana cikin farin ciki. “
A cikin wannan dukan sa zai bayyanan mana girman
matsayi da daraja na kololuwa wanda mace take dashi a
karkashin inuwar shari'ar musulunci wannan kuma raddi ne ga
wanda yace lallai musulunci ya zalumci mace, taya wanda yaso
ta ya kumadayaw adaga cikin fadakarwan sa tattare da kula da
himmatuwa da ita zai zalumce ta da take mata hakki, wannan
shine abunda zai bayyanan maka yakai me karatu me daraja
cikin wannan littafi dan karami wanda zayyi magana a cikinta a
bangaren soyayya cikin rayuwan rahama na shiriyan
Muhammad dan Abdullahi s.a.w tare da iyalan sa wand
akasancewar sa me isar da addini da kuma shugaban al'umma
be sanya shi ba ya manta da kula da iyalan sa yadda ya takaita
wannan himmatuwa cikin kalmomi kadan wanda suka kunshi
ma'anoni daya ya kuma sanya shi wasiyya ga al'ummar sa
yadda yace:
“ mafi alherin ku shine mafi alheri ga iyalan sa kuma ni ne
mafi alherin ku ga iyalai na ” buhari ne ya rawaito shi.
An kiyasta alherin maza da gwargwadon alherin su ga
iyalan su da kuma kyautata zamanta kewa dasu wannan alheri
wanda take kaiwa ga soyayy da rahama shine s.a.w mafi alherin
mutane wanda alherin sa yasanya sa cikin kololuwan tsani na
kamalar mutum cikin rahama da soyayya da kyautata mu'amala
tare da mutane baki daya da kuma iyalansa musamman kuma
daga cikin abunda zayyi nuni akan haka shine lokacin da ayar
zabi ya sauka akan matar sa lokacin da suka tambaye shi
ciyarwa sama da abunda yafi karfin sa da kyalkelin rayuwan
duniya sai suka zabe shi suka kuma yarda da zama dashi cikin
rayuwa kamewa Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
lokacin da aka umurci manzon Allah s.a.w da yaba matan sa
zabi sai ya fara dani, yace:
“ lallai zan Ambato maki wani abu amma babu laifi ki
shawarci mahaifin ki akai ” sai tace: hakika kasan cewa
mahaifina bazai taba umurtana da rabuwa dakai ba, sai
tace: sai yace: “ lallai Allah madaukaki yace: ((yakai
wannan annabi kace ma matan ka idan kun kasance kuna
son rayuwna duniya ne da kyalekelinta to ku zo zan jiyar
daku kuma sai na sake ku saki mekyau. Idan kuma kun
kasance kuna son Allah da manzon sa da gidan lahira to
lallai Allah ya tanadar da wani irin lada me girma ga masu
kyautatawa daga cikin ku)) [suratul ahzab ayata: 28-29] sai
nace tab yanzu akan wannan abu ne zan shawarci mahaifi
na? lallai ni inason Allah da manzon sa da gidan lahira. Sai
tace: sa'annan matan manzon Allah s.a.w suka aikata irin
abunda na aikata nima ” muslim ne ya rawaito shi.
Wannan idan yana nuni akan wani abu to hakika nuni yake
akan so da suke masa da yarda da kuma rikon da suke masa na
abunda suka samu daga gareshi na halaye masu girma da kuma
kyawu cikin mu'amala da so da kaskantar dakai wanda suka
kunsa dukan su kuma sun samun yakini cewa fa bazasu taba
samun Kaman sa ba, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance
yana da mata tara wanda suke rayuwa a karkashin sa kuma
suna rayuwa me kyau da farin ciki, Ha'inata tace game dashi
wata marubuciya yar kasar italiya L.Veccia Vaglieri cikin
littafin ta me suna kariya game da Musulunci wacce take kare
sag a wanda ya zargesa da sha'awa: lallai Muhammad a tsawon
shekarun san a samar taka wanda sha'awar mutum yafi karfi a
cikin sa kuma dukda cewa ya rayu cikin al'ummar larabawa
wacce aure ya zama kamar wata cibiya ce ta zamanta kewa
wacce aka rasa ko kuma ace babu kuma auren mata da yawa
shine ka'aida a wurin su, kuma saki abu ne me sauki wanda
bashi da wani iyaka amma dukda haka be aura ba face mace
daya kawai wacce itace Khadija Allah ya kara mata yarda
waccce shekarun ta ya kasance sama da nashi shekarun ya
kasance yana da shekaru ashirin da biyar ya aure ta ne saboda
tsabar so kuma be sake aure ba har sai bayan rasuwan ta bayan
yakai shekaru hamsin da haiwuwa kuma hakika auren sa dayayi
ya kasance dalilin zaman ta kewa ne ko kuma siyasa saboda
burin sa cikin wannan auren shine karrama wannan matan
wanda suka siffatu da tsoron Allah zuwa samar da alaka ta aure
tare da wasu jama'a da kabilu na daban saboda fatan hada wani
hanya sabuwa na yaduwan musulunci da hakan idan aka cire
Aisha Allah ya kara mata yarda a cikin su, manzon Allah s.a.w
ya aure matan da ba masu kyau bane sosai ko kuma halitta me
ban sha'awa ko kuma budurwa shin idan haka ne ya kasance
mutum me yawan sha'awa ne kenan? Ina bah aka abun yake ba
hakika ya kasance mutum ne me tauhidi, kuma ta yiwu cewa
kwadayin da yake dashi na yara shi yasa shi yin wani aure
sabo, saboda yaran da Khadija ya haifa Allah ya kara mata
yarda sun mutu bama ba tare da cewa yana da dukiya ba me
tarin yawa ya dauki wannan nauyi na iyalai masu yawa sai dai
kuma ya lazimci daidai to cikakke tsakanin su cikin ko wani
hali be taba karkara ba ko sau daya wurin nuna banbanci na
hakki tare da daya daga cikin su kuma hakika yayi harkokin sa
ne yana me koyi da sunnar annabawa wanda suka gabata
amincin Allah ya tabbata a garesu kamar musu da makamantan
sa wanda be bayyana ba cewa wani daga cikin mutane yana
kalubalantar su akan yawan matan da suke dashi shin
sakamakon hakan zai iya koma wa zuwa da cewa mun jahilci
daya ne daga cikin yanayin rayuwan su ta yau da gobe kamar
yadda muka san komai na rayuwan manzon Allah s.a.w tare da
iyalan sa.
Lallai manzon Allah s.a.w me daraja mutum ne me girma
wanda tarihi tasan shi wacce take da tasiri me girma wurin
canza yanayin duniya a cikin shaidar masu adalci cikin
mutanen da ba musulmai ba da kuma wanda suka kwarai wurin
karanta tarihin sa suka kuma yi dubi me zurfi zuwa ga sakon sa
da kuma yaduwar ta da tasirin ta da misali ana cewa gaskiya
shine abunda makiya suka shaida yadda (Mickel Hart) yake
cewa cikin littafin sa me sunan mutum dari wanda sukayi tasiri
cikin rayuwan dan adam: lallai zabi na ga Muhammad shine na
martaban farko cikin jerin mutanen duniya da sukayi tasiri ga
mutane zai iya batama wasu makaranta rai wasu kuma zasu iya
ja da hakan sai dai ya kasance shine mutum daya tilo cikin
tarihi wanda yacimma nasara a bayyane a fannin addini da
kuma duniya.
Wannan shine abunda da mutanen da suke tare damu suke gani
na saurin yaduwar da'awar sa da kuma kwadayin mabiyan sa
akan riko da shari'ar sa da kuma kokari tukuru wajen yada
sunnar sa mutane dayawa suna shiga addinin sa kuma yan
kadan ne matuka masu fita daga cikin sa ita gaskiya idan ta taba
fadin zuciya ta hadu ruhi sai su zama suna bin ta, Bilal ,utumin
habasha a lokacin daya musulunta an azabtar dashi da bulala an
kuma daura masa dutse me zafi akan kirjin sa kuma an kifa
fuskar sa akan sahara me zafi na makka domin ya bar addinin
sa amma hakan be kara masa komai ba face tabbatar dashi da
kara masa kwarin gwewa yana maimaita kalamar sa ta tabbata
akan haka na tauhida Allah daya ne Allah daya ne.
Haka shima Sa'ad dan abi Waqqas ya kasance mutum ne me
tsananin biyayya ga mahaifiyar sa, mahaifiyar sat ace masa a
lokacin daya musulunci bazan kara cin abinci ba ko shan ruwa
har sai na mutu, sai a rika tozarta ka dani a rika cewa: ya wanda
ya kashe mahaifiyar sa. sai yace: kada ki aikata haka ya
mahaifiyata domin ni dai bazan bar wannan addini ba. sai yace:
sai ta zauna rana daya bataci abinci ba, sai ta fara rashin lafiya,
sai yace: ta kara zama rana na biyu bataci abinci ba sai wannan
rashin lafiya nata ya karu. Sai yace: a lokacin dana ga haka sai
nace: ki sani fa wallahi ya mahaifiya ta da ace kina da rai guda
dari zasu rika fita daya bayan daya har su gama fita bazan taba
barin wannan addinin nawa ba domin wani abu ba, idan kin so
kici abinci, idan kuma kinso kada kici, a lokacin da taga haka
sai taci abinci.
• Manzon Allah ta fuskan shakatawa da
iyalan sa.
Musulunci yana koyar da musulmi laluran bawa kai hakkinta
na hutu da shakatawa na halal cikin iyaka na shari'a domin ka
nisantar da ita daga kosawa da kuma samun kwarin gwewa na
kaiwa zuwa ga hanyar Allah madaukaki cikin nishadi da
kokari, sai dai hakan yana da sharadin cewa kada mutum ya
wuce gona da iri cikin wannan bangare na wasanni sama da
bangaren rahiran sa sai rayuwan musulmi ta canza zuwa ga
wasa wanda bashi da wani amfani ya kuma mantar da mutum
abunda aka halicce sa domin sa, hakika sahabban manzon Allah
s.a.w Allah ya kara masu yarda sun kasance a farkon musulunci
suna kudurce cewa lallai musulunci addini ne wanda baisan
hutu ba da wasa na halal ba da kuma shakatawa hanzalat dan
hazim al hanafi yana cewa:
“ Abu bakar ya hadu dani sai yace mun yaya kake? Ya
hanzalata! Sai nace masa ni hanzalata nayi munafunci. Sai
yace subhanallah (tsarki ya tabbata ga Allah)! Me kake
cewa? Sai nace: idan muna wurin manzon Allah s.a.w yana
tunatar damu wuta da aljanna kamar muna ganin su da
idanun mu, amma idan muka bar wurin sa sai ya shagala
da wasa da matan mu da yaran mu da kuma neman duniya,
sai mu manta abunda makaji a wurin manzon Allah
dayawa. Sai Abubakar yace: wallahi muma haka yake
faruwa damu. Sai muka tafi gun manzon Allah s.a.w ni da
Abubakar bayan mun shiga wurin sa sai nace: hanzalata
yayi munafurci ya manzon Allah s.a.w! sai manzon Allah
s.a.w yace ” me yayi? ” sai nace: ya manzon Allah! Mun
kasance idan muna wurin ka kan atunatar damu wuta da
aljanna kamar muna ganin su da idanun mu amma idan
mun bar wurin ka sai mu shagala da matan mu da yaran
mu da neman duniya mu manta da dayawa. Sai manzon
Allah s.a.w yace: “ ina rantsuwa da wanda raina ke hannun
sa! da zaku dawwama akan halin da kuke ciki a wurina da
kuma tunanin wuta da aljanna da mala'iku sun rika
gaisawa daku hannu da hannu akan hanyar ku da kuma
gadon baccin ku. Sai dai ya hanzalata! Lokaci bayan lokaciwatan idan kayi tunanin lahira da bautan Allah ka huta
sannan ka sake haka dai ” ya fada masa hakan har sau uku.
Muslim ne ya rawaito shi.
Sai dai wannan mahanga ta canza a lokacin da musulunci ya
sanya wasa tare da iyalai da kuma sanya masu farin ciki arai
cikin addini kuma ba bu mamali akan haka kasancewar
musulunci addini ne wanda ya kunshi komai domin ya tattara
jiki da ruhi da rai da hankali manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ dukkan abun da ba anbaton Allah bane to wasa ne da
bata okaci sai abu hudu kawai: wasan mutum da matar sa,
da koyan hawa doki, da koyan harbi da kuma koyan
nunkaya cikin ruwa ” . Hadisi ne ingantacce Ahmad da nasa'I
da baihaqi ne suka raaito shi.
Kuma wannan mahangar ta kara canzawa har wayau a
lokacin da suka gani daga manzon Allah s.a.w a bunda yake
nuni akan haka, jabir dan samurata yana cewa: manzon Allah
s.a.w ya kasance baya tashi daga inda yayi sallar asuba har sai
rana ta fito, idan rana ta fito sai ya tashi. Sun kasance suna fira,
har fira yazo kan al'amuran lokacin jahiliyya sai suyi daria da
murmushi. Muslim ne ya rawaito shi.
Bawai wannan bane kuma kawai a'a ya tsananta akan
awajabcin bama kai hakkinta na shakatawa da kuma hutu
wannan shine abunda manzon Allah s.a.w yace ma Abdulahi
dan Umar:
“ yakai Abdullahi, an bani labarin cewa kana azumi kullum
da rana sannan da daddare kayi sallar dare. Sai yace haka
ne ya manzon Allah, sai manzon Allah s.a.w yace:
“ kada ka aikata haka, ka rika yin azumi kana hutawa,
kuma ka rika sallar dare kana yin bacci, domin jikinka
yana da hakki akanka, idon ka shima yana da hakki
akanka, sannan matarka itama tanada hakki akanka, haka
bakonka shima yana da hakki akanka ” buhari ne ya rawaito
shi.
1. Manzon Allah me daraja s.a.w yana shakatawa da
iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana shakatawa da iyalan sa
domin canza yanayi da kuma samun dama ya sanya masu farin
ciki da kuma kore masu kosawa da damuwa, Aisha matar
manzon Allah s.a.w tana cewa: yan habasha sun shigo
masallaci suna wasa aciki sai manzon Allah s.a.w yace:
“ yake iyar fara kinason ki kalli wasan su? ” sai nace eh
inaso sai ya tashi ya tafi bakin kofa nazo na sameshi a bakin
kofa sai ya sanya gemuna akan kafadar sa, tace: daga cikin
abunda suke fadi a wannan rana itace: baban kasim
mutum ne na kwarai, sai manzon Allah s.a.w yace: “ ya
isheku haka ” sai nace: kada kayi gaggawa ya manzon
Allah. Aisha tace: banso kallon suba face kawai inason na
nunama mata matsayi na a wurin sa ne da kuma matsayin
sa aguna ”
2. Manzon Allah yana kawar dakai da hakuri domin
farin cikin iyalan sa:
Ubangijin sa ya ladabtar dashi sai ya kyautata masa ladubban
sa, ya kaance cikin dabi'ar sa s.a.w baya yima wani abun da
bayaso kuma yana yafiya da kawar dakai akan wasu abubuwa
wanda iyalan sa suke aikatawa wanda be sabama shari'a ba,
ma'anar kawar dakai shine bayyanar da rashin damuwa da abu
tare da ilimi da kuma sanin abunda za'a kawar dakai akai, Aisha
matar manzon Allah s.a.w tana cewa: Abubakar Allah ya kara
mata yarda ya shigo wurinta ya tarar da wasu bayi biyu a
lokacin ranakun muna suna mata kida, manzon Allah s.a.w
kuma ya rufe da tufafin sa, sai Abubakar yayi masu tsawa, sai
manon Allah s.a.w ya bude fuskan sai yace:
“ ka kyale su ya Abubakar, domin ranakun idi ne ” ,
ranakun muna kenan. Sai Aisha tace: naga manzon Allah
s.a.w yana kare ni, ina kallon habashawa suna wasa cikin
masallaci, sai Umar ya tsawatar masu sai manzon Allah
s.a.w yace: “ ka kyale su kuyi was an ku cikin aminci yaku
yayan Arfida ” buhari ne ya rawaito shi.
3. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana tabbatar da
farin cikin iyalan sa:
Daga cikin alamun soyayya da kuma daidaito da tabbata
tausayi shine neman dukkanin abunda zai shigar da farin ciki
cikin zuciyar wanda kake so, hakika manzon Allah s.a.w ya
kasance yana kokarin ganin ya kawo abunda zai shigar da farin
ciki ga iyalan sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ ta kasance tana wasa da yara mata a wurin manzon Allah
s.a.w kuma kawayenta suna zuwa mata sai su rika boyewa
cikin gidanta domin kunyan manzon Allah s.a.w. sai tace:
manzon Allah s.a.w ya ksance yana turo su wuri na ”
msulim ne ya rawaito shi.
4. Manzon Allah s.a.w yana wasa da iyalan sa:
Kamar yadda cikin karantarwan musulunci akwai abunda yake
gyara gangan jiki da ruhi haka akwai abunda yake gyara rai na
shigar mata da farin ciki da murna hakika manzon Allah s.a.w
ya kasance baya mantawa da wannan bangaren yana bashi
hakkin sa na himmatuwa dashi yana wasa da sahabban sa da
iyalan sa kuma baya fadi sai gaskiya, kuma an sani cewa wasa
yana daga cikin abunda rai keso wanda yake Koran damuwa da
kosawa daga zuciya da sharadin iyakance sa da iyakoki da
sharudda na shari'a kada ayi karya acikin sa ko kuma
munanawa wani dashi, Aisha Allah ya kara mata yarda tanan
cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya dawo wurina wata rana daga
jana'iza a makabartan baqi'a, sai ya tarar dani ina fama da
ciwon kai ina cewa wayyo kaina! Sai yacemun ya Aisha! ni
nafiki jin ciwon kai dinnan (domin ciwon ki zai wuce ki
warke ni kuma nawa bazai warke ba domin na kusan
mutuwa), sai yace mata: me zai dameki da zaki mutu kafin
ni, zan maki wanka na sanya maki likafani na kuma yi
maki salla da birneki?! Sai tace: ni kuma kamar ina kallon
ka cikin wannan hali wallahi da zaka aikata dukkanin
abunda ka Ambato daka koma gidana ka zama ango da
sauran matan ka! Sai manzo Allah s.a.w yayi murmushi,
sa'annan ya fara rashin lafiyar daya mutu a cikinta ” darimi
ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
5. Manzon Allah yana kewaya dan shakatawa tare da
iyalan sa:
Rayuwan sa baya rabuwa da abunda yake hutar da kai, hakika
manzon Allah s.a.w ya kasance yana fita tare da iyalan sa ya
kewaya dasu, isar da sakon sa da kuma shugabancin al'umma
baya shagaltar dashi daga kula da wannan bangare na rayuwa,
ga Aisha nan tana rawaito mana labarin wani daga cikin tafiyar
ta tare da manzon Allah s.a.w:
“ ….. kuma manzon Allah s.a.w ya kasance idan dare yayi
yana fita tare da Aisha suna fira da ita… ” muslim ne ya
rawaito shi.
6. Manzon Allah s.a.w yana dariya daga wasan da
yakeyi da iyalan sa:
Dariya al'amari ne na fidira tare da mutum yanada rabo cikin
karantarwan musulunci, manzon Allah s.a.w yace:
“ murmushin ka ga fuskar dan uwanka sadaka ce ” tirmizi
ne ya rawaito shi kuma hadisi ne ingantacce.
Haka addinin mu ya koya mana cewa ya dace ga musulmi ya
kasance me sakin fuska ba me murtukewa ba da daure fuska a
koda yaushe, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yana
dariya kuma yana bada dariya domin ya kori daure fuska daga
majalisin say a kuma cika yanayin da farin ciki da natsuwa,
shin me fadin cewa:
“ kada ka raina kankancin aikin lada koda kuwa ka hadu
da dan uwanka ne cikin sakin fuska da murmushi ”
7. Manzon Allah s.a.w yana yada ruhin farin ciki ga
ilayan sa:
Ya kasance daga cikin dabi'ar sa wasa da tsokanar wanda suke
tare, iyalan sa suna da rabo daga cikin saukin sa da fara'ar sa da
tausayin sa da kuma zaulaya tare dasu domin yak ore masu
daure fuska da kosawa daga garesu ya kuma sanya masu farin
ciki cikin zukatan su, Aisha Allah ya kara mata yarda tana
cewa: nazo wurin manzon Allah s.a.w da wani irin abinci
kamar tuwo da miya sai nace ma saudat kici ga manzon
Allah a tsakanin mu sai taki ci, sai nace mata kodai kici ko
kuma na yaba maki shi a fuska, sai taki ci sai na sanya
hannuna cikin wannan abinci na yaba mata shi a fuska sai
manzon Allah s.a.w yayi dariya sai manzon Allah s.a.w ya
daga kafarsa daya daura akan saudat domin ta iya rama
abunda na mata, sai yacema saudat kema ki yaba mata a
fuska, sai ta yaba mata sai manzon Allah s.a.w yayi dariya
sai ga umar ya wuce yana cewa ya Abdullahi ya Abdullahi
sai manzon Allah s.a.w yayi zaton zai shigo ne sai yace
mana ku tashi kuje ku wanke fuskan ku, sai Aisha tace
bangushe ba inajin tsoron Umar saboda kwarjinin sa a
wurin manzon Allah s.a.w ” Abu ya'ala al musili ne ya
rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
8. Manzon Allah yana halartan wurin mutane masu
farin ciki:
Daga cikin hikimar sa s.a.w shine yana mu'amala da kuma aiki
da kowa da irin abunda ya dace dashi matukar be sabama
shari'a ba, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya dawo daga yakin tabuka ko
khaibara acikin lalitar ta akwai wani labule sai iska tazo ta
daga gefen wannan labule na kayan was an Aisha sai yace:
“ menene wannan ya Aisha? “ sai tace kayan wasana ne! sai
yaga wani doki a cikin su yana da fuka fukai guda biyu fata
wanda ake rubutu akai, sai yace: menene wannan nake gani
a tsakiyar su? Sai tace: doki ne, sai yace menene akanshi?,
sai tace: fuka fuki ne, sai yace: wani irin doki ne da fuka
fuki? Sai tace: bakiji cewa Sulaiman yanada doki me
fuffuke bane? Sai tace: manzon Allah s.a.w yayi dariya har
hakoran sa na dadashi suka bayyana ” abu dawud ne ya
rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
9. Manzon Allah s.a.w yana farin ciki da murnan iyalan
sa:
Shigar da farin ciki da murna a zuciyar iyalai alama ce ta
alherin mutum ga iyalan sa kuma manzon Allah s.a.w ya
kasance na gaba-gaba wurin shigar da farin ciki da murna a
zuciyar iyalan sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana zaune sai yaji sauti
mabanbanta da kuma sautin yara sai ya mike sai yaga wata
mata yar habasha tana wasa ga yara a gefenta sai yace: “ ya
Aisha zo ki gani ” sai nazo na daura gemuna akan kafadar
manzon Allah s.a.w ina kallon ta sai yacemun: “ ke ishe ki
bane kallon haka ” sai nace eh be isheni ba domin naga
matsayina a wurin sa, sai ga Umar yazo yan akoran mutane
daga wannan mata sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai ina
ganin shedanun aljanu da mutane suna guduwa idan Umar
yazo ” sai tace sai nadawo ” . Tirmizi ne ya rawaito shi kuma
albani ya inganta shi.
10. Manzon Allah s.a.w yana zama da fira da iyalan sa:
Ya kasance daga cikin al'adar sa cewa yana zama da fira da
iyalan sa wanda yake wanke masu zuciya daga cikin haka daga
cikin abunda sakamakon mu'amalar yau da gobe zai haifar
kuma yanada tasiri me girma wurin kara shakuwa da dankon
soyayya, safiyyat diyar hayiyi matar manzon Allah s.a.w tana
cewa:
“ tazo wurin manzon Allah s.a.w domin masa zaria a
masallaci yana cikin ittikafi, cikin kwanaki gomam karshe
na watan ramadana, sai tazauna suka fira tare na tsawon
awa daya, sa'annan ta tashi zata tafi gida, sai manzon Allah
s.a.w ya tashi yi mata rakiya, bayan ya kawo kofar
masallaci kusa da kofar ummu salmata, sai wasu mutum
biyu cikin mutanen madina suka ganshi, sai sukayi sallama
ga manzon Allah s.a.w, sai manzon Allah s.a.w yace masu: “
ku dakata safiyya ce diyar hayiyi ” . Sai sukace: tsarki ya
tabbata ga Allah ya masnzon Allah, abun yayi masu girma,
sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai shedan yana yawo jikin
mutum kamar yadda jini yake yawo, ina tsoron ya jefa
wani abu cikin zuciyar ku ” buhari ne ya rawaito shi.
• Manzon Allah s.a.w ta bangaren tausayin
sa ga Iyalan sa:
Lallai musulunci yana kula da bangaren mutum wanda aka
halicce sa akai wanda daga ciki akwai bangaren tausayi
tsakanin miji da mata, sai yayi dubi zuwa ga sha'awa na jinsin
mutum akan lalura wacce ya wajaba a kosar da ita da kuma
rashin dadasheta, sai dai kuma dauketa daga kasance warta
sha'awa kawai na dabbanci abun kyama saboda haka ne ya
sanya hanyar biyan wannan sha'awa ta hanyar aure wanda ya
ginu akan tsarki da kamewa da kuma samar da natsuwar rai da
tabbatar da tausayi da kuma lamunce hakkoki na ma'aurata,
Allah madaukaki yana cewa:
“ kuma daga cikin ayoyin sa ya halatta maku mataye daga
jikin ku domin ku samu natsuwa a garesu kuma ya sanya
soyayya da rahama a tsakanin ku lallai acikin haka akwai
ayoyi ga mutane masu tunani ” suratul rum ayata 21.
Saboda haka ne musulunci ya umurci mabiyan sa da saurin yin
aure idan suka samu ikon haka ya kuma yi bayanin dalilin haka,
sai manzon Allah s.a.w yace:
“ yaku taron samari! Duk wanda ya samu abun yin aure to
yayi aure, domin hakan yafi wurin kame kallo da kuma
kiyaye farji, wanda kuma be samu ba to ya rika yin azumi
domin hakan kariya ne a gareshi ” Muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma yi hani daga ruhubanan ci (kebewa domin bauta
kullum) da kuma barin yin aure da kuma gudun duniya baki
daya, an karbo daga anas dan malik Allah ya kara masa yarda
yace:
“ wani mutum uku sun zo gidan manzon Allah s.a.w suna
tambayar matan sa game da bautan sa bayan sun fada
masu suka jinjina haka sai sukace mu kuma muna ina ace
manzon Allah wanda aka gafarta masa zunuban sa baki
daya wanda ya gabata da wanda zaizo yana aikata irin
wannan bauta, sai dayan su yace ni daga yau kollum sallar
dare zantayu har nabar duniya dayan kuma yace ni daga
yau kullum azumi zantayi har nabar duniya dayan kuma
yace ni daga yau ba ruwa na da mace har Abadan sai
manzon Allah s.a.w yazo yace masu kune wanda sukace
kaza da kaza, ku sani cewa wallahi na fiku tsoron Allah da
takawa amma ni ina azumi kuma ina hutawa kuma ina
bacci da yin sallar dare kuma ina auren mata kuma duk
wanda ya kyamaci sunnata to baya tare dani ” buhari ne ya
rawaito hadisi.
Muslunci ya girmama bangaren tausayi tsakanin miji da mata
ya sanya shi ya zama ibada wanda ake ba musulmi lada akai
kamar yadda ake bayar da alada akan ayyukan alheri a lahira,
manzon Allah s.a.w yace:
“ …. ” Kuma acikin jima'in dayan ku shima akwai sadaka
” sai sukace: ya manzon Allah yanzu dayan mu zai biya
sha'awar sa kuma abashi lada? Sai yace: “ ku bani labari
yaya kuke gani idan yaje ya biya sha'awar sa ta hanyar
haramun shin za'a bashi zunubi? To Kaman haka ne idan
ya biya sha'awarsa ta hanyar halal za'a bashi lada ” muslim
ne ya rawaito shi.
Ya kuma kwadaitar a wannan bangare saboda muhimmancin
dake cikin sa cikin rayuwan musulmi saboda ta hanyar sa ne
ake samun dawwama na zuciya da natsuwa ta bangaren
soyayya wanda zai bashi damar yin ibadar sa cikin natsuwa
kwakwalwa.
Kuma ya kamata mu kawo wasu daga cikin bangarori na
rayuwar manzon Allah na tausayi da soyayya tare da
iyalansa:
1. Manzon Allah s.a.w baya ha'intar iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance misali abun koyi wurin
kamewa, ya bayyana abunda ya dace musulmi ya aikata a
lokacin da shedan ya jefa masa abunda zai kaishi zuwa ga
aikata alfasha a cikin zuciyar sa, Jabir dan Abdullahi Allah ya
kara masu yarda yana cewa:
“ idan dayan ku yaga wata mace ta burge shi to ya koma ga
iyalin sa domin itama tanada irin abunda wancan mace
take dashi ” Tirmizi ne ya rawaito shi kuma albani ya
ingantahi cikin littafin al sahiha 235.
2. Manzon Allah s.a.w da shaukin sa ga iyalan sa:
Lallai saurin dawowan mutum ga iyalan sa daga tafiyar sa dalili
ne akan soyayyar sa da shaukin sa a garesu kuma akwai amfani
cikin haka wanda baya boyuwa na tabbatan zuciya da tausayi
da soyayya saboda haka ne ya kasance cikin karantarwan
manzon Allah s.a.w ya kasance a bayyane akan haka a lokacin
day ace:
“ tafiya bangare ce ta azaba, yana hayan ku baccin sa da
abincin sa da abun shansa, saboda haka idan dayan ku y
agama biyan bukatar sa a tafiyar sa to ya gaggauta dawowa
ga iyalan sa ” buhari ne ya rawaito shi.
3. Manzon Allah yana sabanta soyayya da kauna ga
iyalan sa:
Kyauta tana da muhimmanci kuma tana kara daraja idan ta
kasance daga wanda kake so saboda haka ne karantarwan
manzon Allah s.a.w ta kasance a bayya ne a lokacin da yace: “
kuyi kyauta zaku so junan ku ” buhari ne ya rawaito shi cikin
littafin sa na adabul mufrid kuma albani ya inganta shi.
Ya kuma kara fadi har wayau s.a.w: “ yaku matan musulmai
kada wata ta raina wata kyauta da zata ba wata koda kuwa
da misalin akuya ne mara nama ” buhari da muslim ne suka
rawaito hadisin.
4. Manozn Allah s.a.w yana kame kallonsa akan iyalan
sa kawai:
Kiyaye gabbai da kuma rage su akan iyalai dalili ne na
daidaitan mutum kuma shedan yana kokari akan karkatar da
wannan hali da kuma amfani da ita cikin dabi'u makaskanta
hakika an rubutama dan adam rabo na zina wanda dole ya
aikata hakan babu makawa: idanu suna zina kuma zinan su
shine kallo, kunne shima yana zina kuma zinan shi shine
sauraro, harshe ma yana zina kuma zinan shi shine magana,
hannu yana zina zinan shi shine tabawa, kafafuwa suna zina
kuma zinan su shine tafiya, zuciya yana buri da sha'awa sai farji
ya gasgata hakan ko kuma ya karyata kamar yadda manzon
Allah s.a.w ya bada labari akan haka, kuma hadisin buhari da
muslim ne suka rawaito shi. Wannan kuma lafazin muslim ne,
ruwaiyar buhari a takaici take.
Kuma hakika manzon Allah s.a.w ya kasance abun koyi ne
akan haka, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ muminai mata sun kasance idan sunyi hijira zuwa ga
manzon Allah s.a.w yana masu jarabawa da kuma masu
mubaya'a saboda fadin Allah madaukaki cewa yakai
wannan Annabi idan mata muminai sun zo maka suna
maka mubaya'a akan cewa bazasu hada Allah da wani ba
cikin bauta kuma bazasu yi sataba kuma bazasuyi zina ba
har zuwa karshen ayar sai Aisha tace duk wacce ta
tabbatar da hakan cikin wannan mata muminai to hakika
tayi mubaya'a na shari'a manzon Allah kuma ya kasance
idan sun tabbatar da hakan da maganar su sai yace masu
ku tafi hakika nayi maku mubaya'a, kuma wallahi manzon
Allah s.a.w be taba shafan hannun wata mace ba ko sau
daya kawai yana masu mubaya'a ne da magana , Aisha tace
wallahi bai taba amsar komai ba daga wurin mata sai
abunda Allah yayi masa umurni kuma tafin hannun sa be
taba shafan tafin hannun wata mace ba ko sau daya, ya
kuma kasance yana cewa masu idan ya amsa daga garesu
cewa hakika nayi maku mubaya'a da magana ” muslim ne
ya rawaito shi.