da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Dukkan godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzan Allah, da kuma dukkan wanda suka jibince shi, da iyalan sa da sahabban sa da kuma tabi’ai, da kuma duk wanda yabi tafarkin shiriyar su, bayan haka:
Wadannan wasu jerin rubuce-rubuce ne marasa yawa wadanda zasu haskaka wa musulmai hanya kuma su baiyana musu akidun batattun kungiyoyi dan su guje musu, musamman ma wasu daga cikin su muryoyin su sunyi sama a wadannan kwanakin kuma suna ta yunkuri wajan yada barnar su, hakika mun fara wannan jerin rubuce-rubucen akan kungiyar (shi’a masu limami goma sha biyu), saboda mabiyanta sunfi yawa a yanzu, suna nan a kasar Iran da Iraqi da bangaraen kasashen larabawa...
Kuma mabiyan wannan kungiyar suna yawan cewa mazhabin su baida banbanci da mazhabin ahlussunah, kuma suna cewa ana zaluntar su kuma ana masu karerayi, kuma suna kokarin kare shi’ancin su, da kuma yada littattafai da rubuce-rubuce da yawa dan yada barnan su, da kuma bibiyar littattafan Ahlussunnah da yinkurin yi masu raddi, wanda babu hakan a wajen sauran kungiyoyin.
Yayinda littattafan shi’a suka yawaita a wannan lokaci fiye da lokutan da suka gabata, kuma suke ta yunkurin yada su ta kowace irin hanya a kowani wuri
Hakan sai ya zama wajibi akan mu mu dauko wadannan littattafan muyi musu tsirara mu baiyana abunda ke cikin su na
4
munanan aqidu wadanda suke ta kokarin boye su, kamar yadda wani mai magana ne yace: (daga bakin ku zamu gane addinin ku)!!
Muna rokon Allah madaukaki ya daga tutar sunnah da mabiyan ta, kuma ya kaskantar da karya da bata da kuma mabiyan ta.
Kuma Allah madaukaki shi ne abun nufi da wannan rubutu kuma shi ne mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.
Wanda ya rubuta :
5
❖ Daga cikin aqidar i’yan shi’a masu limamai goma sha biyu: lallai su suna tabbatar da cewa lallai shi’a asalinta yahudanci ne, tushen ta yana komawa ga wani bayahude da ake kira Ibn saba’a alyahudi(bayahude), kuma lallai lallai sayyidina Aliyu dan Abi dalib Allah ya kara masa yadda ya kona su da wuta kuma ya barranta daga gare su.
Duba cikin: littafin (Firaqush shi’a), na Annubakhty, shafi na 22,
Kuma duba cikin littafin (ikhtiyar ma’arifaturrijal) na Addusy, shafi na 107
❖ Kuma sune suke fada suna masu alfahari da suna rafilawa da kuma dalilin da yasa aka sa masu sunan.
Duba cikin littafin (Biharul anwar) na Almajalisy, shafi na 65/97 .
❖ Kuma sune suke fadin cewa: lallai mu Allahn mu ba daya bane da nasu (wato Ahlussunnah), baza mu hadu ba wurin bauta wa Allah daya ba kuma Manzan mu ba daya bane haka nan kuma shugaban mu da na su ba daya bane, domin su Ahlussunnah suna cewa: lallai Ubangijin su shi ne wanda ya kasance annabi Muhammadu ne manzan sa, kuma halifan sa shi ne Abubakar, to mu kuma bamu yadda da wannan Ubangijin ba a matsayin ubangijin mu, kuma bamu yadda da wannan Annabin ba, mu muna cewa ne: lallai wannan ubangijin da halifan Annabin sa shi ne Abubakar to mu ba Ubangijin mu bane, kuma wannan Annabin ba Anabin mu bane.
6
Duba cikin littafin (alanwarun nu’umaniyya), na Ni’imatullahi aljaza’iry, mujalladi na biyu shafi na 278, (2/278).
❖ Kuma sune masu cewa: lallai ba’a ganin Allah ranar alkiyama, kuma shi ba’a siffan ta shi da wani wuri ko kuma wani zamani kuma ba’a nuni gare shi, kuma duk wanda yace lallai shi yana saukowa saman duniya, ko kuma shi yana baiyan ga iyan aljannah kamar wata, ko kuma makamancin haka to kamar ya kafurta ne da shi.
Duba cikin littafin (aqa’idul imamiyya), na Muhammad Rida muzwaffar, shafi na 58.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah zai ruko kwankwasan mumini ranar alkiyama, shima mumini zai ruko kwankwasan Allah sai ya tuna mai zunuban sa.
Sai aka ce : meye ma’anar zai ruko kwankwasan sa? Yace: sai ya dora hannun sa akan qugun sa (kwankwaso), sai yace: haka kamar yadda dayan mu ke zantawa da dan uwansa akan wani abu da yake faranta masa rai.
Duba cikin littafin (al-usulu assittata asahar) bin diddigi: diya’u addin almahmudy, shafi na 203.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah yana saukowa zuwa kasa ranar arafah a farkon zawali akan wani rakumi mara lafiya yana zubda miyau kuma yana taba wadanda suke arafa da cinyoyin sa dama da hagu.
Duba cikin littafin (al-usulu assittata asahar) bin diddigi: diya’u addin almahmudy, shafi na 204.
❖ Su ne suke cewa: lallai fuskantar kabari ayi sallah dole ne, koda bai dace da alkibila ba, kamar yadda fuskantar kabari yake a matsayin fuskantar alkibla nanne (fuskar Allah), wato bangaren da Allah ya umarci utane da su fuskanta a wannan halin.
7
Duba cikin littafin (Biharul anar) na Almajlisy, 101/369.
❖ Su ne suke cewa: lallai lafazin (AAH) suna ne daga cikin sunayen Allah mafi kyau, duk wanda yace: (AAH) to hakika ya nemi agaji ne daga Allah.
Duba cikin littafin (Mustadrakul wasa’il), na Nury Addabarsy 2/148.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah yana kawo ma Hussaini dan Aliyu Allah ya kara musu yadda ziyara, kuma yana musafaha da shi, kuma yana zama tare da shi akan gado.
Duba cikin littafin (Sahifatul Abrar), na Mirza Muhammad Taqy, 2/140.
❖ Su ne suke cewa an canza alkur’ani mai girma kuma wai alkur’ani bai cika ba, kuma wai ingantaccen alkur’ani yana hannun Mhadin su wanda baya nan.
Daga cikin manya-manyan malaman iyan shi’a masu limamai goma sha biyu wanda suka ce an canza alkur’ani akwai:
Aliyu ibn Ibrahim alqummy, Ni’imatullah aljaza’iry, Alfaidh alkashany, Ahmad Addabarsy, Muhammad Baqir Almajlisy, Muhammad bun Annu’man Almulaqqab bi Almufid, Abul hasan Al’amily Adnan Albahrany, Yusuf Albahrany, Annury Addabarsy, Habibullahi Alkhu’iy, Muhammad bn Ya’qub Alkulainy, Muhammad Al’aiyashy, da ma wadan su wanda ba su ba da yawa.
Duba cikin littafin (Asshi’a Al’isna Ashariyya wa tahriful kur’an), na : Muhammad saif, da kuma littafin (Mauqifurrafida Min alkur’an), na : Mamadu Karambiry.
8
❖ Su ne suke cewa: lallai lafazin (Aali Muhammad da kuma Aali Aliyu) an cire su daga cikin alkur’ani.
Duba cikin littafin (Minhajul bara’ah Sharhu Nahjul balagah), na Habibullah Alkhu’iy, 2/216.
❖ Su ne suke cewa: babu wanda ya tattaro alkur’ani kuma yasan ma’anonin sa sai dai malaman su kawai (wato malaman su guda goma sha biyu), kuma wai su sun san ilimin alkur’ani dukkan sa baki saya.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/228.
❖ Su ne suke cewa: Alkur’ani ba hujja bane sai an hada shi da maganar malaman su,
Duba cikin littafi (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/169.
❖ Su ne suke cewa: akwai wata surah sunan ta suratul Wilaya, ta fara ne da cewa (Ya ku wadan da sukayi imani kuyi imani da haske guda biyu) wai Saiyidina Usman Dan Affan Allah ya kara masa yadda ne ya cire ta daga alkur’ani, kamar yadda suke riyawa.
Duba cikin littafin (Faslul kidab fi Tahrifi kitabi Rabbil Arbab), na Annury Addabarsy, shafi na 18.
❖ Su ne suke cewa: akwai wani alkur’ani mai suna (mushafu Fatimah) wato ma’ana, sunan shi Alkur’anin Fatimah Allah ya kara mata yadda, kuma wai akwai irin Alkur’anin mu a cikin sa har sau uku.
Duba cikin littafin (Usulul kafy), na Alkulainy, 1/239.
❖ Su ne suke canza fadar Allah madaukaki suna cewa, a cikin ayar da Allah yake cewa: “ ka isar da abun da aka saukar maka daga Ubangijin ka, in kuma baka aikata haka ba to baka isar da sakon Ubangijin ka ba” [ suratul ma’idah ; aya ta 67 ], sai suka ce: “ ka isar da abunda aka saukar maka daga ubangijin ka- gameda Aliyu- in kuma baka baka aikata haka ba to baka isar da sakon Sa ba”, sai suka kara kalmar (gameda Aliyu) da molan kansu!!
9
Wato ma’ana: wai Annabi (S.A.W) ya manta ko kuma ya bar wannan kalmar, wai wata kila yana jin tsoran munafukai ne, kamar yadda ya baiyana haka cikin labarai masu yawa.
Duba cikin littafin (Faslul Kidab fi Tahrifi Kitabi Rabbil Arbab), na Annury Addabarsy, shafi na 182.
❖ Su ne suke cewa: basa inkari ga mai cewa an canza alkur’ani (wannnan abu ne mafi nauyi) amma a wurin iyan shi’a duk wanda ya fadi haka suna mai kallan cewa shi mujtahidi ne, amma kuma duk wanda yake inkarin wilayar sayyidina Aliyyu (nauyi mai sauki), a wurin iyan shi’a shi kafiri ne babu shakka cikin kafurcin sa.
Duba cikin littafin (Al-i’tiqadat), na Ibn Babawaihy Alkummy, shafi na 103.
❖ Su ne suke cewa: sun umurci mabiyan su iyan shi’a da su karanta wannan Alkur’anin dake nan a cikin sallah da kuma yin aiki da hukunce-hukuncen sa har zuwa lokacin da shugaban su zai baiyana, a lokacin za’a dauke wannan alkur’anin daga hannun mutane a tafi da shi zuwa sama sai a kawo Alkur’ani na asali wanda Shugaban muminai Aliyu Bn Abi Dalib ya rubuta , sai ayi ta karanta shi kuma ana aiki da hukunce-hukuncen sa.
Duba cikin littafin (Alanwaru Annu’maniyya), na Ni’matullah Aljaza’iry, 2/363.
❖ Su ne suke cewa: kada ku koya wa matan ku suratu Yusuf, kuma kada ku karanta musu ita, saboda a cikin ta akwai fitintinu, amma ku koya musu Suratun Nur, saboda a cikin ta akwai wa’azozi,
Duba cikin littafin (Alfuru’ mina Alkafy), na Alkulainy 5/516.
10
❖ Su ne suke cewa: lallai duk wanda baiy imani da imamanci ba to imanin sa bai cika ba har sai yayi imani da ita kuma ya kudurce ta.
Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Ridah Muzaffar, shafi na 78.
❖ Su ne suke cewa: imamanci ci gaban annabci ne, kuma dalili ne da ke wajabta aiko da manzanni da turo da Annabawa, kuma shi ne ke wajabta nada shugaba bayan manzo.
Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Rida Muzaffar, shafi na 88.
❖ Su ne suke cewa: ma’anar imamanci wato wani tsari ne na Allah wanda yake nads shugaba n da ya zabe shi da ilimin sa na tun asali game da bayin sa, kamar yadda Allah ke zaban Annabi, kuma yana umurtar Annabi yayi nuni zuwa gare shi kuma yayi umarni da bin shi.
Duba cikin littafin (Aslush shi’a wa Usuluha), na Muhammad Husain Kashifu Algidwa, shafi na 102.
Ai ma shi imamanci asali ne daga cikin asullan addini, imani bai cika sai anyi imani da shi, a wata maganar suna cewa ne: imamanci cigaban annabci ne.
❖ Su ne suke cewa: lallai duk wanda ya musanta imamancin (shugabanci) shugaban muminai Aliyu Dan Abi Dalib da kuma imaman da suka zo a bayan sa to kamar wanda ya musanta annabcin Annabawa ne, kuma lallai duk wanda ya yadda da shugaban muminai Aliyu amma kuma sai bai yadda da daya daga cikin imaman da suka zo a bayan sa ba to kamar wanda ya yadda da dukkan Annabawa ne amma ya ki yadda da annabcin Annabi Muhammad (S.A.W).
❖ Su ne suke cewa : lallai duk wanda ya musanta imamancin daya daga cikin su-wato ma’ana limamai goma sha
11
biyu- to kamar wanda ya yi musun annabcin dukkan Annabawa ne, Allah ya kara aminci a gare su baki daya.
Duba cikin littafin (Minhaju Annajati), na Faidh Alkashany, shafi na 48.
❖ Su ne suke cewa: iyan shi’a Imamiyya sunyi ittifaki akan cewa duk wanda yayi musun imamancin daya daga cikin imamai kuma ya musanta abunda Allah madaukaki ya wajabta a kansa na wajabcin yi musu biyayya to shi kafiri ne kuma batacce, ya cancanci ya dawwama a cikin wuta.
Duba cikin littafin (Haqqul yaqeen Fi Ma’arifati Usuliddeen), na Abdullahi Shibr, 2/189.
❖ Su ne suke cewa: lallai amfani da kalmar Shirka da kuma kafurci suna tabbata ne akan duk wanda bai kudurce imamancin shugaban muminai ba da kuma imamai daga cikin yaran shi, kuma ya fifita wasu akan su, hakan na nuna cewa su iyan wuta ne kuma zasu dawwama a cikin ta.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 23/390.
❖ Su ne suke cewa: lallai Annabi (S.A.W) lokacin da aka haife shi ya yi kwanaki ba nonan da za’a shayar da shi, sai Abu Dalib ya dauke shi ya dora shi akan nonon sa, sai Allah ya zuba ruwan nono a cikin nonon Abu Dalib sai ya shayar da Annabi na wasu kwanaki har zuwa lokacin da Abu Dalib ya samu Halimatu Assa’diya sai ya mika shi zuwa gare ta.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/448.
❖ Su ne suke cewa: lallai Saiyidina Aliyu Allah ya kara masa yadda yafi Annabi (S.A.W) jarunta, wai asali ma Annabi (S.A.W) bai da jarumtaka.
Duba cikin littafin (Al’anwaru Annu’maniya), na Ni’matullahi Aljaza’iry, 1/17.
12
❖ Su ne suke cewa: Annabi (S.A.W) baya iya bacci har sai ya sumbaci kumatun Fatimah ko kuma ya sumbaci tsakanin nonuwanta (kirjinta).
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 24/43.
❖ Su ne suke cewa: Annabi baida yara mata, fadima ce kawai yarinyar sa, kuma su Rukaiyya da Ummu kulsum da Zainab su agolansa ne kaai.
Duba cikin littafin (Da’iratul ma’arifil Islamiyyah Asshi’iyyah), 1/27.
❖ Su ne suke cewa: lallai Hasan dan Aliyu Allah ya kara musu yadda shi ne wanda ya tozarta muminai, saboda yayi wa Mu’awiyah Allah ya kara masa yadda mubaya’a.
Duba cikin littafin (Rijalul Kusshy), na Alkusshy. Shafi na 103.
❖ Su ne suke cewa: lallai matar Annabi (S.A.W) zata iya zama kafira kamar matar Annabi Nuhu da Annabi Lud,
Abunda suke nufi da matar Annabi (S.A.W) ita ce uwar muminai Aisha Allah ya kara yadda a gare ta ita da mahaifin ta.
Duba cikin littafin (Hadisul Ifk), na Ja’afar Murtada, shafi na 17.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aisha Allah ya kara mata yadda tayi ridda bayan rasuwar Annabi (S.A.W) kamar yadda Sahabbai da yawa suma sunyi ridda.
Duba cikin littafin (Asshubuhatun tthaqib Fi Bayani Ma’anan Nasib), na Yusuf Albahrany, shafi na 236.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aisha Allah ya kara yadda a gare ta ta tara dinari arba’in na yaudara da sata, ta raba su ga makiya Aliyu Allah ya kara yadda a gare shi!!
13
Duba cikin littafin (Mashariqu Anwarul Yaqin), na Rajab Albarsy, shafi na 86.
❖ Su ne suke cewa: lallai uwar muminai Aisha Alah ya kara yadda a gare ta tayi Zina muna neman tsarin Allah, a cikin fadar Allah madaukaki :” wadannan an barrantar da su daga abun da suke fada”, sai iyan shi’a suka ce: wannan aya tsarkaka ce ga Annabi daga aikata Zina, ba wai ita ba (suna nufin Aisha Allah ya kara yadda a gare ata).
Duba cikin littain (Assiradul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/165.
❖ Su ne suke cewa: lallai Hafsah ta kafurta lokacin da ta ce: “ waye ya baka wannan labarin” { suratut tahrim :3}, sai Allah yace game da ita da kuma Aisha :” in kun tuba zuwa ga Allah to hakika zukatan ku sun tsarkaka” { suratut Tahrim : 4}, sai sukace ma’ana : zukatanku sun karkata, shi kuma karkata shi ne kafurci, kuma lallai Aisha da Hafsah sun hada kai dan su shayar da Annabi (S.A.W) guba, lokacin da Allah ya bashi labarin abunda suke so su aikata, sai yayi yunkurin kashe su, sai suke ta rantsuwa da Allah akan cewa basu aikata ba, sai Alah ya saukar da fadar sa:” ya ku wadanda suka kafurta baza’ayi muku uzuri ba a yau” { suratut Tahrim : 7},
Duba cikin littafin (Assiradul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/168.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah madaukaki yayi magana ne da Manzan Allah (S.A.W) a daren da yaje sama da muryar Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda da kuma yaren sa.
14
Duba cikin lttafin (Kashful Yaqin Fi Fada’ili Ameeril Muminin), na Hasan bn Yusuf bn Almudahhir Alhully, shafi na 229.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah ya tattauna da Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi a garin Ta’if, kuma mala’ika Jibrilu yana tsakanin su.
Duba cikin littafin (Basa’irud Drajat), na Assaffar, 8/230.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib shi ne mai raba aljannah da wuta, zai shigar da iyan aljannah cikin aljannah kuma zai tura iyan wuta zuwa wuta.
Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Assaffar, 8/235.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah zai shigar da wanda yayi wa Aliyu da’a aljannah koda kuwa ya saba wa Allah madaukaki ne, kuma lallai Allah zaishigar da wanda ya saba wa Aliyu cikin wuta, koda kuwa yayi wa Allah da’a ne.
Duba cikin littafin (Kashful Yaqin Fi Fada’ili Ameeril Muminin), na Hasan bn Yusuf bn Almudahhir Alhully, shafi na 8.
❖ Su ne suke cewa: lalai Aliyu dan Abi Dalib shi ne sirrin Annabawa, kuma lallai Allah madaukaki yace: ya kai Muhammad, na aiko Aliyu tare da Annabawa a sirrance kai kuma na aiko ka tare da shi a baiyyane yana mai karfafa ka.
Duba cikin littafin (Al-asrarul Ulawiyya), na Muhammad Almas’udy, shafi na 181.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu ayah ne ga Annabi Muhammad (S.A.W), kuma lallai Annabi Muhammad yana kira ne zuwa ga yin wilaya ga Aliyu Allah ya kara yadda a gare shi.
Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Muhammad Assaffar, shafi na 91.
❖ Su ne suke cewa: babu wani Annabi Allah zai aiko face sai ya umarce shi da yin wilaya ga sayyidina Aliyu yana so ko baya so.
15
Duba cikin littafin (Al-asrarul Ulawiyya), na Muhammad Almasudy, shafi na 190.
❖ Su ne suke cewa: lallai addini bai cika sai da yin wilaya ga sugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi.
Duba cikin littafin (Al’ihtijaj), na Addabarsy, 1/57.
❖ Su ne suke cewa: lallai Manzan Allah (S.A.W) yace: ku saurara lallai mala’ika Jibrilu ya zo wuri na sai yace: ya kai Muhammad, Ubangijin ka yana umurarka da san Aliyu dan Abi Dalib, kuma yana umurtar ka da yi masa wilaya.
Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Muhammad Assaffar, shafi na 92.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib zai shiga aljannah kafin Annabi Muhammad (S.A.W) ya shiga.
Duba cikin littafin (Ilalu sshara’ii), na Ibn Babawaihy Al-qummy, shafi na 205.
❖ Su ne suke cewa: lalli tsawa tana zuwa ne daga umarnin Mutumin ku,
Sai aka ce ; waye mutumin mu?
Sai sukace: sugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.
Duba cikin littafin (Al-iktisas), na Al-mufid, shafi na 327.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dn Abi Dalib yana raya matattu kuma yana yaye bakin ciki da damuwa daga wadan da suke cikin bakin ciki da damuwa
Duba cikin littafin (Uyunul Mu’jizat), na Husain Abdulwahhab, shafina 150, da kuma littafin (Halalul Mashakil), da kuma kissar Abdllah Alkhattab ta karya.
❖ Su ne suke cewa: lallai ba wanda zai shiga aljannah sai da izinin Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.
Duba cikin littafin (Manaqibi Amiril Muminin), na Aliyu bn Almagazily, shafi na 93.
16
❖ Su ne suke cewa: duk wanda saba wa Aliyu to ya kafurta, kuma duk wanda ya fifita wani akan Aliyu to yayi ridda.
Duba cikin litafin (Bisharatul Mustafa Li shi’atil Murtada), 2/79.
❖ Su ne suke cewa: lallai Alah yayi alfahari ga mala’iku da Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.
Duba cikin littafin (Bisharul Mustafa Li shi’atil Murtada), 1/66.
❖ Su ne suke cewa: lallai Annabawa da Manzanni an aiko su ne dan su tabbatar da wilayar Aliyu dan Abi Dalib ne Allah ya kara masa yadda.
Duba cikin littafin (Alma’alimu Azzulfa), na malamin su Hashim Albahrany, shafi na 303.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib yayi nuni da hannun sa zuwa sama , sai wani girgije ya zo shi kuma wai sai yayi sama, sai yazo yayi sallama ga Aliyu dan Abi Dalib, sai yace wa Ammar: zo ka hau wannan dokin tare da ni, kuma kace: “ da sunan Allah ne take tafiya kuma take tsayawa” [ suratu Hud : 41], sai Ammar ya hau kan dokin sai sukayi sama har suka bace daga ganin mu.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar) na Almajlisy.
❖ Su ne suke cewa: lallai wani kare ya ciji wasu mutum biyu cikin Sahabbai dan yin ramuwa ga Aliyu dan Abi Dalib, bayan ya fusata da irin fushin larabawa, kuma lallai wani jaki ya shaida cewa lallai Aliyu waliyyin Allah ne kuma shi ne wanda Annabi yayi wasiyya da a bashi jagoranci a bayan sa.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 41/247, da kuma 17/306.
17
❖ Su ne suke cewa: fatima da Hassan da Hussaini ma’asumai ne, da kuma yaran Hussaini amma banda yaran Hassan.
Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Rida Muzaffar, shafi na 89, da kuma shafi na 98.
❖ Su ne suke cewa: ba dan Aliyu ba da ba’a halicci Annabi Muhammadu ba, su kuma biyun ba dan Fatima ba da ba’a halicce su ba.
Duba cikin littafin (Al-asrarul Fadimiyya), na Muhammad Almas’udy, shafi na 98.
❖ Su ne suke cewa: lallai Fatima Allah ya kara yadda a gare ta yani yanki ne na Allah mai jujjuya al’amura, amma sai ya baiyana a siffar mace.
Duba cikin littafin (Al-asrarul Fadimiyya), na Muhammad Al-mas’udy, shafi na 355.
❖ Su ne suke cewa: lallai Fatima Allah ya kara yadda a agare ta ta kasance tana yi wa mahaifiyar ta magana tun tana cikin ta ba’a haifeta ba.
Duba cikin littafin (Fatimatuz Zahra’ Minal Mahdi Ilallahdi), na Muhammad Al-qazwiny, shafi na 38.
❖ Su ne suke cewa: lalai imaman iyan shi’a goma sha biyu sunfi Annabawa da Manzannni falala da daraja.
Duba cikin littafin (Al-anwarun Nu’maniyya), na Ni’matullah Aljaza’iry, 3/308.
❖ Su ne suke cewa: lallai imaman iyan shi’a sun san duk abunda ya faru a da da kuma wanda zi faru nan gaba, kuma su babu wani abu da ya boyu a gare su wanda basu san shi
18
ba,kuma su basa mutuwa sai dai in su suka zabi hakan suka damar mutuwa da kan su.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/258.260.
❖ Su ne suke cewa: lallai kowane imami yana da wani wuri a ranar lahira na yabo da wata daraja madaukakiya, da kuma halifanci mai karfi wanda dukkan halittun duniya suna kasancewa ne karkashin sa.
Duba cikin littafin (Tahrirul Wasila), na Alkumainy, shafi na 52.
❖ Su ne suke cewa: lallai limamai goma sha biyu suna da wilaya ta halitta, zasu iya halitta komai amma banda Allah mahalicci, kuma wannan wilayar kamar wilayar Allah ce akan halittun sa.
Duba cikin (Misbahul Fuqaha), na Abil Qasim Alku’iy, 5/33.
❖ Su ne suke cewa: lallai mu muna da wasu darajoi a wurin Allah, babu wani mala’ika makusanci da yake da su ko kuma wani Annabi Manzo- wato ma’ana, imamai goma sha biyu- .
Uba cikin littafin (Tahrirul Wasila), na Alkumainy, shafi na 94.
❖ Su ne suke cewa: lallai imamai goma sha biyu in sun zartar da abu to babu abun da ya isa hana wanan abun faruwa, hakanan in sun so faruwar wani abu a lailatul kadari to babu makawa wannan abun sai ya faru da makamancin haka, kuma dukkan wadannan abubuwan babu makawa sai sun tabbata.
Duba cikin littafin (Alburhanul Qadi’), amsoshi ne na tambayoyi game da aqida da shari’ah, na malamin su Muhammad Taqiy Albahjat, shafi na 14.
❖ Su ne suke cewa: lallai wasiyyai (wato ma’ana, imamai goma sha biyu) ana daukar cikin su ne a cikin mahaifa kuma a haife su ta cinya, kuma su najasa bata taba su.
Duba cikin littafin (Madinatul Mu’ajiz), na Hashim Albahrany, 8/22.
19
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah da mala’ikun sa da Annabawan sa da Muminai dukkan su suna ziyartar kabarin shugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kra yadda a gare shi.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 4/580.
❖ Su ne suke cewa: lallai imami kamar Annabi ne shima ya wajaba ya zamo ma’asumi daga dukkan laifi da alfahsha ta baiyane da boye, tun daga yarunta har zuwa mutuwa, da ganganci ko kuma da mantuwa, domin su imamai sune masu tsare shari’ah kuma sune suke tsaye akan al’amuran shari’a, halin su akan haka kamar halin Annabi ne.
Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na malamin su Ibrahim Azzanjany, 3/179.
❖ Su ne suke cewa: lallai mala’iku an halicce su ne dan su zama masu hidima ga ahlul baity.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 26/335.
❖ Su ne suke cewa: dukkan shabbai sun kafurta, musamman ma Abubakar da Umar da Usman da Khalid bn Alwaleed da Mu’awiya dan Abi Sufyan da Mugira dan Shu’bah, sai da mutum uku ne kawai basu kafurta ba.
Duba cikin littafin (Arraudah mina Alkafy), na Alkulainy, 8/245.
❖ Su ne suke cewa: (aqidar mu (wato aqidar iyan shi’a) a game da barranta: lallai mu mun barranta daga gumaka guda
20
hudu: Abubakar da Umar da Usman da Mu’awiyah, kuma mun barranta daga mata guda hudu : Aisha da Hafsah da Hindu da Ummul Hakam, kuma mun barranta daga dukkan mabiyan su da masoyan su, kuma lallai su ne mafi sharrin halintar Allah a doron kasa, kuma lallai imani da Allah da Manzan sa da Imamai baya cika sai bayan an barranta daga makiyan su).
Duba cikin littafin (Haqqul Yaqin), na Almajlisy, shafi na 519.
❖ Su ne suke cewa: lallai saiyidina Abubakar da Umar kafurai ne, kuma duk wanda ke san su shi ma kafuri ne.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 69/137,138.
❖ Su ne suke cewa: lallai Abubakar da Umar tsinannu ne, kuma lallai su sun mutu kafurai masu shirka da Alah Madaukaki.
Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Assaffar, 8/245.
❖ Su ne suke cewa: Annabi (S.A.W) ya dauki Abubakar ne lokacin hijira suka shiga kogo dan jin tsoran kada ya nuna wa kafuran kuraishawa in da yake.
Duba cikin littafin (Tafsirul Burhan), na Hashim Albahrany, 2/127.
❖ Su ne suke cewa: lalai Abubakar ya kasance yana sallah a bayan Manzan Allah (S.A.W) amma kuma ya rataya gunki a wuyan sa, kuma in yayi sujada to gunkinnan yake yiwa sujada.
Duba cikin littafin (Al-anwarun Nu’maniyyah), na Ni’matullah Aljaza’iry, 1/53.
❖ Su ne suke cewa: lallai Umar yana da wata cuta ba abunda ke warkar da ita sai dai maniyyin maza, kuma lallai kakar sa ma shegiya ce ta hanyar zina aka haife ta. (Muna neman tsarin Allah daga irin wannan zantuttukan).
Duba cikin littafin (Al-anwrun Nu’maniyyah), na Ni’matullah Aljaza’iry, 1/63, da kuma littafin (Assiradul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/28.
21
❖ Su ne suke cewa: ya wajaba a dinga girmama wata rana da ake kira ranar nairuz, kuma a dinga biki a lokacin zagayowar ranar da aka kashe Umar dan Khaddab, kuma suna kiran wanda ya kashe Umar (Baba jarumin Addini), kuma suna kwadaitarwa akan ziyartar kabarin sa dan sakamakon yadda ya kashe Umar Allah ya kara yadda a gare shi.
Duba cikin littafin (Aqduddurar fi Baqr Badni Umar), na Yasin Assawwaf, shafi na 120.
❖ Su ne suke cewa: lallai karanta addu’ar tsinuwa ga gumakan kuraishawa, wato (Abubakar da Umar) yana daga cikin Ibadu mafi girma kuma mafi falalar da’a, kuma su ne suke kiran Abubakar da Umar Jibti da Daguti
(gumaka kuma kafurai).
Duba cikin littafin (Ihqaqul Haqq), na Almar’asy, 1/337.
❖ Su ne suke cewa: lallai Mahadin su zai zo sai ya raya Abubakar da Umar Allah ya kara yadda a gare su sai ya rataye su kuma ya kona su, sai kuma ya raya Uwar muminai Aisha Allah ya kara yadda a gare ta sai ya tsayar mata da haddin zina.
Duba cikin littafin (Arrajmah) na Ahmad al=ahsa’iy, shafi na 116, da 161.
❖ Su ne suke cewa: lalai Usman mazinaci ne, kuma dan daudu ne, kuma yana buga ganga (duff).
Duba cikin littafin (Assiratul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/30.
❖ Su ne suke cewa: lallai Mala’ika Jibrilu da Mika’ilu da kuma Kursiyyu da Lauhu da Alkalami dukkan su suna kaskantar da kai ga mahadin su kuma suna jin tsoran sa, saboda shi mahadi ya kasance mai zubda jini ne.
22
Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyyah), na Muhammad Rida Muzaffar, shafi na 102.
❖ Su ne suke cewa: lallai jikin Mahadin iyan shi’a kamar jikin ba isra’ile ne.
Duba cikin littafin (Al’imamul Mahdy minal Wiladati Ilal Zuhuri), na Muhammad Alqazwiny, shafi na 53.
❖ Su ne suke cewa: lallai Mahadin su zai zo da wani Abu sabo da kuma sabon littafi da kuma sabon hukunci mai tsanani akan larabawa, lamarin sa takobi ne kai baya neman wani ya tuba, kuma baya tsoran zargin mai zargi.
Duba cikin littafin (Algaibah), na Muhammadun Nu’man, shafi na 154.
❖ Su ne suke cewa: idan Mahadi ya baiyana babu wani abu tsakanin shi da larabawa da kuma kuraishawa sai dai takobi.
Duba cikin littafin (Algaibah), na Muhammad Annu’man, shafi na 154.
❖ Su ne suke cewa: babau wani abu da ya rage tsakanin mu da larabawa sai dai yanka, sai yayi nuni da hannun sa zuwa maqogwaran sa.
Duba cikin littafin (Algaibah), na Muhammad Annu’man, shafi na 155.
❖ Su ne suke cewa: lallai Mahadi in ya zo zai rusa masallacin Ka’abah da Masallacin Annabi, kuma zai yi hukunci ne da irin hukuncin Annabi Daud, kuma zai dinga magana da Allah da yaran sa na ibraniyanci, kuma zai kashe biyu bisa uku na mutanen duniya.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 52/338, da kuma littafin (Usulul Kafy), 1/397, da kuma littafin (Algaibah), na Annu’many, shafi na 326, da kuma littafin (Arraj’ah), na Ahmad Al-ahsa’iy, shafi na 51.
❖ Su ne suke cewa: baya halatta ayi jihadi sai in Mahadi ya baiyana ya fito daga kogo. Kamar yadda suke rayawa.
23
Duba cikin littafin (Rasa’ilu Sshi’ah), na Hurr Al-amily, 11/37.
❖ Su ne suke cewa: lallai ziyarar kabarin Hussaini dan Aliyu Allah ya kara yadda a gare su, ya fi falala akan zuwa aikin hajji, kai masu ziyarar Husssaini sunfi tsarki, amma wadanda ske zuwa aikin hajji kuma suyi tsayuwar arfa akawi yaran zina a cikin su.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 98/85.
❖ Su ne suke cewa: lallai ziyarar kabarin Hussaini dan Aliyu Allah ya kara yadda a gare su tana daidai da hajji sau miliyan biyu (2.000.000), da kuma umarah miliyan biyu (2,000,000), da kuma jihadi miliyan biyu, kuma zai samu lada kamar wanda yayi hajji da umarah kuma yaje yaki tare da Manzan Allah (S.A.W) da kuma halifofin sa shiryayyu masu shiryarwa.
Duba cikin littafin (Nurul ain fil mashyi ila ziyarati qabril Husain), na Muhammad Al-asdahabanany, shafi na 265.
❖ Su ne suke cewa: lallai karbala ne mafi tsarkin wuri a musuluni, kuma yafi Makkah da Madinah da Qudus girma da falala.
Duba cikin littafin (Masabihul jinan), na malamin su, Abbas Alkashany, shafi na 360.
❖ Su ne suke cewa: lallai cin kasar da ke kabarin Hussaini Allah ya kara yadda a gare shi waraka ne daga dukkan cuta.
Duba cikin littafin (Almazar), na malamin su Almufid, shafi na 125.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aba Abdullah (Ja’afar Assadiq) Allah yayi masa rahama yana cewa: wallahi da zan baku labarin falalar ziyarar kabarin Hussaini da kuma falalar kabarin
24
sa, da kun bar zuwa hajji kai tsaye, da ba wanda zai kara zuwa hajji daga cikinku, a’aha, ashe baku san cewa Allah ya riki karbala a matsayin wuri mai alfarma kuma amintacce mai albarka ba tun kafin ya maida makkah ta zama wuri mai alfarma?!
Duba cikin littafin (Kamiluzziyarat), na malamin su Ibn Qulawaihi Alqummy, shafi na 449.
❖ Su ne suke cewa: lallai yin sallah a makabarta yafi falala akan yin sallah a masallatai, kai an ce ma: lallai yin sallah a masallacin Aliyu dan Abi Daib yafi lada akan yin sallah a masallaci mai alfarma na makkah har ya ninka shi sai biyu.
Duba cikin littafin (Manhajus Salihin), na malamin su, Aliy Assistany, 1/187.
❖ Su ne suke cewa: lallai mafi girman idi a musulunci ba idil fitr da idil Adha ba ne, Idi mafi girma shi ne Idin Gadeer wanda suka kirkiro, wanda baida tushe a musulunci.
Duba cikin littafin (Idul Gadeer), na malamin su, Muhammad Asshirazy, shafi na 11.
❖ Su ne suke cewa: daga cikin bunda yasa Allah yayi fushi da mutanen kufa shi ne cewa lallai su ne suke soki Hassan dan Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi, kuma su ne suka kashe Hussaini dan Aliyu Allah ya kara masa yadda bayan cewa su ne suke kira shi suka cr ya zo garin kufah.
Duba cikin littafin (Tarikul Kufah), shafi na 113.
❖ Su ne suke cewa: lallai Hussaini yace: ya Allah kayi hukunci tsakanin mu da wasu mutane wadanda suka kira mu dan su taimake mu amma sai suka kashe mu.
Duba cikin littafin (Muntahal Aamal), 1/535.
25
❖ Su ne suke cewa: lallai Hussaini yace: lallai wadannan sun tsorata ni, wato ma’ana (iyan shi’ar kufah), kuma ga wadannan littattafan na kufah sun hakaito haka, kuma iyan kufah su ne suka kashe ni.
Duba cikin littafin (Maqtalul Hussain), na Abdurazzaq Almuqrim, shafi na 175.
❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu yaron Hussaini Allah yayi masa rahama yaga mutanen kufah suna kuka kuma suna ta ihu bayan kashe hussaini, sai yace musu: kuna kuka da ihu saboda mu ne? To waye ne ya kashe mu in ba ku ba??.
Duba cikin littafin (Nafsul Mahmum), na Abbas Alkummy, shafi na 357.
❖ Su ne suke cewa: (sai mutane dubu ashirin sukayi wa Hussaini mubaya’a daga cikin mutanen Iraqi amma sai suka yaudare shi, kuma sukayi masa tawaye alhalin sun mai mubaya’a, sai a karshe suka kashe shi).
Duba cikin littafin (A’ayanus Shi’ah), na Muhammad Al-amin, 1/32.
❖ Su ne suke cewa: wajibi ne a taimaki makiya dan su samu galaba akan daulolin musulnci, kuma kada a yaki makiya musulunci iyan kama karya.
Duba (fatawoyin babban malamin su Assistany), a wannan kwanan watan 4/3/2003. Yace baya halatta a kashe amurkawa da sukazo suna yakar Iraqi, kuma wani malamin su ya karfafa wannan maganar wanda ake kira Muhammad Almihry, yace lalli fatawoyin da suke fitowa daga malaman shi’a da suke garin iraqi wanda suke cewa ya wajaba a yaki sojojin da suka shigo garin Iraqi to wannan fatawoyin basu da hujja, kma ba wani abu da ke cikin su face taqiyya da tsoro da kuma son rayuwa dan suna cikin takura da rashin ji dadi, kuma wani abu da ke karfafa haka shi ne fatawar da aka samo ta malamin su mai suna Sadiq Asshirazy wanda ke zaune a garin Qumm, yayi fatawa cewa ya halatta a taimakawa amerika dan a kakkabe
26
mulkin Iraqi. Duba cikn (jaridar kasar Kuwait- juma’ar da tayi daidai da 27/9/2002).
❖ Su ne suke cewa: duk wasu musulmai da suke yakar kafurai a iyakar daular musulunci to wadannan matattu ne a duniya da lahira,kuma babu shahidai sai dai iyan shi’ar imamiyya koda kuwa sun mutu a kan gado ne.
Duba cikin littafin (Tahzibul Ahkam), na Addusy, 6/98.
❖ Su ne suke cewa: lallai mutanen makkah sun kafurce wa Allah a fili, kuma lallai mutanen madinah sunfi muni da lalacewa fiye da mutanen makkah har ninki saba’in.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 2/410.
❖ Su ne suke cewa: lallai mutanen masar an tsine musu ta harshen Annabi Daud, sai aka maida wasun su suka zama birai da aladu.
❖ Su ne suke cewa: lallai Allah baiyi fushi da mutanen bani isra’ila ba sai da yasa su suka shiga (masar) kuma bai yadda da su ba har sai da ya fitar da su daga cikin ta. kuma suna cewa: lallai Abu Ja’afar malamin su ma’asumi yace: lallai ni ina kyamar inci wani abu da aka dafa da tukunyar da ta fito daga (masar), kuma ni bana san in wanke kaina daga tabon ta in ya same ni dan jin tsoran kada kasar ta ta haifar mun da kaskanci kuma ta tafiyar mun da kishi na na addini, ku fice daga garin masar kada ku sake kuce zaku zauna a cikinta,-mai ruwayar yace- kuma ina tunanin yace: zama a masar yana haifar wa mutum rashin kishin iyalin sa.
27
Duba cikin littafin (Tafsirul Qummy), na Alqummy, 2/241, da kuma littafin (Tafsirul Burhan), na Hashim Albahrany, 1/456, da kuma littafin (Furu’ul Kafy), na Alkulainy, 6/501, da kuma littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 60/211.
❖ Su ne suke cewa: madalla da kasar sham amma tir da mutanen da ke cikin ta, lalai mutanen Roma kafurai ne amma basuyi gaba da mu ba, amma su kuma mutanen sham sun kafurta kuma suna gaba da mu, kada kuce daga mutanen sham sai dai kuce daga mutanen shu’umci-mutanen banza-.
Duba cikin littafin (Tafsirul Burhan), na Hashim Albahrany, 1/456, da kuma littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 2/410, kuma ka duba littafin (Tafsirul Qummy), na Alqummy, 2/241.
❖ Su ne suke cewa: kumusin da ake bayarwa na kudi ga dangin Annabi to masu rawuna ne zasu karba, wai da hujjar cewa su masu rawani suna matsayin imamin su ne wanda ke cikin kogo.
Duba cikin littafin (Wasa’ilus Shi’a), na Hurr Al-amily, 6/383.
❖ Su ne suke cewa: lallai dukan jiki da kuma zubda jini daga jiki da kuma sanya bakaken kaya a ranar ashura da kuma yin kururuwa da ihu duk yana daga cikin ,manya-manyan aiyukan lada ga Hussaini Allah ya kara yadda a gare shi, ai wadannan aiyukan dukkan su ababan so ne ababan yabo.
28
Duba cikin : fatawoyin Muhammad Kashiful gidaa, da kuma Arrauhany, da kuma Attabrizy, da wadansu daga cikin malaman shi’ar imamiyya.
❖ Su ne suke cewa: lallai mutum zai iya auren mutu’a da mata dubu, domin ita mata ta mutu’a ba’a sakin ta kuma bata yin gado, ita an dauko ta haya ne kawai.
Duba cikin littafin (Al-istibsar), na Abi Ja’far Addusy, 3/155.
❖ Su ne suke cewa: lallai yaron da aka haifa ta hanyar mutu’a yafi falala fiye da yaran da aka haifa ta hanyar aure.
Duba cikin littafin (Manhajussadiqin), na Mula fathullah Alkashany, 356.
❖ Su ne suke cewa: ya halatta ayi auren mutu’a da karuwai da kuma matan da suka shahara wajen fasikanci, kai harma kwadaitarwa suke yi akan hakan.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 100/319, 320.
❖ Su ne suke cewa: lallai matar da aka dauko ta dan mutu’a ba’a kirga ta cikin mata hudu da aka ce a aura, saboda ita ba’a sakin ta kuma bata cin gado, ita an dauko ta haya ne kawai.
Duba cikin littafin (Alfuru’u minal Kafy), na Alkulainy, 5/415.
❖ Su ne suke cewa: ya haltta ayi mutu’a da kyawawan mata ko da kuwa matan aure ne ko kuma karuwai.
Duba cikin littafin (Alfuru’u minal kafy), na Alkulainy, 5/462.
❖ Su ne suke cewa: lallai mafi karancin mutu’a shi ne namiji yayi mutu’a da mace sau daya kawai.
Duba cikin littafin (Alfuru’u minal Kafy), na Alkulainy, 5/460.
29
❖ Su ne suke cewa: ya halatta ayi mutu’a da mazinaciya, sai dai kawai makaruhi ne in tana cikin karuwan da suka shahara da yin zina.
Duba cikin littafin (Tahrirul wasilah), na Alkumainy, 2/256.
❖ Su ne suke cewa: a dinga yin taqiyya, taqiyya ita ce dayan su ya baiyana sabanin abun da ke boye a ransa, ko kuma kamar yadda wani daga cikin malaman su yayi bayanin ta yace, taqiyya itace: ka fadi wani abu ko kuma ka aikata wani abu sabanin abunda ka kudurce a ranka dan ka tunkude wa kanka cutarwa ko kuma dan ka kiyaye mutuncin ka.
Duba cikin littafin (Asshi’a Fil Mizan), na Muhammad Jawad Mugniyah, shafi na 48.
❖ Su ne suke cewa: kaso tara cikin goma na addini yana cikin taqiyya, kuma babu addini ga wanda baya taqiyya.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 2/217.
❖ Su ne suke cewa: lallai ku kuna kan wani addini, duk wanda ya boye shi to Allah zai daukaka shi, duk kuma wanda ya baiyana shi to Allah zai kaskantar da shi ya tozarta shi.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 2/222.
❖ Su ne suke cewa: Hussaini ya kasance yana shan nono ta babban yatsan Annabi (S.A.W) kuma yana isan shi kwana biyu zuwa uku.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/67.
❖ Su ne suke cewa: babu wanda suke kan addinin musulunci sai dai mu da su kawai, ma’ana (babu musulai sai
30
iyan shi’a masu imamai goma sha biyu da kuma mabiyan su iyan shi’ar imamiyya).
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/223,224.
❖ Su ne suke cewa: lallai Mahadi zai zo ya dauma iyan shi’a fansa akan makiyan su musulmai, amma su yahudawa da kiristoci zai yi sulhu da su kuma ya zauna da su lafiya.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 52/376.
❖ Su ne suke cewa: duk wanda yake mana raddi kamar Allah yake wa raddi, kuma duk mai mana raddi to kamar yana shirka ne da Allah.
Duba ciki littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/67.
❖ Su ne suke cewa: mutane dukkan su yaran zina ne sai dai iyan shi’a kawai.
Duba cikin littafin (Arraudah minal Kafy), na Alkulainy, 8/285.
❖ Su ne suke cewa: baubu wani yaro da za’a haifa face akwai yani shaidani da zai zo wurin haihuwar, in ya san cewa wannan yaran dan shi’a nemsai hakan ya hana shaidanin zuwa, in kuma yaron ba dan shi’a bane sai shaidan ya tura hannun sa a duburar yaron sai yaran ya zama dan iska, in kuma ta mace ce sai ya sa hannun sa a farjin ta sai ta zama fajira mutuniyar banza.
Duba cikin littafin (Tafsirul Aiyashy), na Muhammadul Aiyashy, 2/218.
❖ Su ne suke cewa: duk wanda ba dan shi’a bane, ko kuma baiyi imani da daya daga cikin imamai goma sha biyu ba, ko kuma ya musanta daya daga cikin su to ya kafurta, kuma a lahira makomarsa ita ce wuta.
Duba cikin littafin (Jami’u Ahadisu Sshi’a), na Barujardy, 1/429.
❖ Su ne suke cewa: lallai abunda za’a amfana daga hadisai wadanda suke nuni akan hukuncin kafurci da kuma shirka a lahira to wannan yana tabbata ne akan duk wanda ba dan shi’a bane masu imamai goma sha biyu.
31
❖ Su ne suke cewa: lallai (musulmi) jinin sa halal ne, sai dai kada ka kashe shi a baiyane, in ka samu ikon wurgo masa katon dutse ko kuma ka jefa shi a cikin ruwa to ka aikata dan kada a bada shaidar haka a kan ka, sai aka ce: to me kake gani game da dukiyar sa? Sai yace: ka cinye in ka samu iku.
Duba cikin littafin (Wasa’ilus Shi’a), na Hurr Al-amily, 18/463.
❖ Su ne suke cewa: lallai diyyar ran Ahlussunnah in an kashe shi kamar diyyar dan bunsuru ne, kai bunsuru ma yafi shi alheri, bata wuce diyyar dan karamin su wato shi ne karen farauta, babban su kuma diyyar sa bata wuce diyyar bayahude.
Duba cikin littafin (Al-anwarun Nu’maniyyah), na Ni’matullah Aljaza’iry, 3/308.
❖ Su ne suke cewa: ka amshe dukiyar banasibe (musulmi) duk inda ka same ta mu kuma ka kawo mana kumusi.
Duba cikin littafin (Wasa’ilus Shi’a), na Hurr Al-amily, 6/340.
❖ Su ne suke cewa: lallai ranar lahira za’a kwaso ladar Ahlussunnah a ba dan shi’a, a kwaso zunuban dan shi’a a lafta wa Ahlussunnah, sai a tura su wuta.
Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 5/247,248.
❖ Su ne suke cewa: Ahlussunnah najasa ne kuma jinin su ya halatta da kuma dukiyoyin su, kuma in sun mutu zasu dawwama a cikin wuta baza su taba fitowa daga cikin ta ba.
Duba cikin littafin (Al-anwarun Nu’maniyyah), na Ni’matullah Aljaza’iry, 2/306, da kuma littafin (Haqqul yaqeen fi ma’rifati usuliddeen), na Abdullah Shibr, 2/188.
❖ Su ne suke cewa: idan dan shi’a yace wa dan shi’a (ya kai dan sunnah), to sai an mai hukunci na ta’aziri, kuma wanna ta’azirin da za’a yi mai ya tabbata a shari’ance dan kar ya sake.
32
Duba cikin littafin (Hayatul Muhaqqiqul Karki wa Aasaruhu), 6/237.
❖ su ne suke cewa: wasu daga cikin mala’iku sunyi jayayya akan wani abu, sai suka bukaci wanda zai yanke hukunci tsakanin su a cikin iyan adam, sai Allah yayi musu wahayi cewa ku zabi wanda kuke so yayi hukuncin, sai suka zabi Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi.
Duba cikin littafin (Musnadu Fatima), na Hussain Attuwaisir Kany, shafi na 296.
❖ Su ne suke cewa: wani jaki mai cizo yayi wa Manzan Allah (S.A.W) magana sai yace: mahaifina da mahaifiya ta fansa ne a gareka ya Manzan Allah, lallai baba na ya bani labari daga baban sa shima daga kakan sa, shima kuma daga baban sa, cewa lallai shi ya kasance tare da Annabi Nuhu a cikin jirgin ruwa, sai Annabi Nuhu yazo ya shafa bayan sa sai yace: wannan jakin za’a samu wani jaki da zai fito daga tsatson sa wanda shugan Annabawa zai hau shi kuma cikamakin su, sai jakin yace; ina gode wa Allah da yasa ni ne wannan jakin wanda zaka hau ya manzan Allah.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/237.
❖ Su ne suke cewa: lallai imamin su Albaqir ya hada wata giwa ta kasa sai kuma ya hau kanta, sai ta tashi da shi sama ta kai shi makkah.
Duba cikin littafin (Madinatul Ma’ajiz), na Hashim Albahrany, 5/10.
❖ Su ne suke cewa: fitsarin imamai da kashin su babu kazanta a ciki kuma babu wari, kamshi yake yi kamar turaren almiskul azfar, kai duk wanda ma ya sha fitsarin su da kashin su da jinin su to Allah ya haramta masa shiga wuta kuma wajibe ne ma ya shiga aljannah.
33
Duba cikin littafin (Anwarul Wilaya), na Ayatullah Al-akwand Mulla Zainul Abideen Alkalbayakany, shafi na 440.
❖ Su ne suke cewa: lallai ababen da ke fita daga jikin imamai na (fitsarin su da tusar su da kashin su), duk kamshi suke yi kamar kamshin almiski.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/319.
❖ Su ne suke cewa: lallai sanya bakin takalmi yana da illoli guda uku, sai nace: menene su in zama fansa a gare ka?? Sai yace: suna raunata gani, kuma suna sa azzakari yayi rauni, kuma suna gadar da damuwa da bakin ciki.
Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 6/465.
❖ Su ne suke cewa: lallai sanya korayen takalma yana haifar da abubuwa guda uku: suna karfafa gani, kuma suna sa azzakari yayi karfi, kuma suna yaye damuwa da bakin ciki.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 6/465.
❖ Su ne suke cewa: cin karas yana kawo zafin koda, kuma yana sa azzakari ya mike, kuma yana taimakawa wajen yin jima’i.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 6/372.
❖ Su ne suke cewa: lallai shaidan yakan zo wa mace har ya hau kan jikin ta kamar yadda namiji ke hawa kan jikin ta, sai ya sadu da ita kamar yadda namiji ke saduwa da ita, kuma ya aure ta kamar yadda namiji ke auranta, sai nace: to ta yaya za’a gane hakan?? Sai yace: ta hanyar san mu da kuma kin mu, duk wanda yake san mu kuma yake kaunar mu to shi ya fito ne daga maniyyin mutum, duk kuma wanda yake kin mu to ya fito ne daga maniyyin shaidan.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 5/502.
❖ Su ne suke cewa: lallai al-aura guda biyu ne (gaba da baya), amma baya-dubura- an rufe shi da iyaiyan maraina biyu, to in ka rufe azzakari da kuma maraina to shi kenan ka rufe al-aura.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 6/221.
34
❖ Su ne suke cewa: amma sauran jin dadi da mace kamar su shafa ta da sha’awa da kuma rungume ta da kuma shafa cinyoyin ta babu laifi a cikin hakan, kai koda kuwa da iyar jinjira ce wadda ake shayarwa.
Duba cikin littafin (Tahrirul Wasilah), na Alkumainy, 2/221.
❖ Su ne suke cewa: ya halatta ayi jima’i da mai haila kafin tayi wanka in hailar ta tsaya.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 5/395.
❖ Su ne suke cewa: ya halatta a sadu da mace ta duburar ta.
Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 5/540.
❖ Su ne suke cewa: mai haila zata iya yin sallar jana’iza, sai dai baza ta tsaya cikin sahu ba.
Duba cikin littafin (Manla yahduruhul Faqih), na Ibn Babawaihi Alkummy, 1/179.
ALLAH YAYI SALATI GA ANNABIN MU MUHAMMAD
DA IYALAN SA DA SAHABBAN SA KUMA YAYI SALLAMA.