
WA YA HALICCI HALITTU? WA YA
HALICCE NI ? KUMA SABODA ME ?
Kwamitin ilimi a jagorancin harkokin addini a
Masallacin Harami da Masallacin Annabi
WA YA HALICCI HALITTU? WA YA
HALICCE NI ? KUMA SABODA ME ?
Kwamitin ilimi a jagorancin harkokin addini a
Masallacin Harami da Masallacin Annabi
WA YA HALICCI HALITTU? WA YA
HALICCE NI ? KUMA SABODA ME ?
Shin Ina kan hanya ta daidai ?
Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin
su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane
yawansu?
Wa ya kera wannan gwanannan tsarin a sama ko a
kasa ?
Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da
hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar wasu
ilimai da gane hakikanin abubuwa ?
Wa ya kagi wannan gwananniyar kira a gabban
jikinka, ya kuma surantaka sai ya kyautata halittar ta
ka?
Ka yi la’akari da halittar halittu rayayyu a banbancin
Nau’ukan su, wa ya kage su a wannan kyawun da ba
shi da iayaka?
Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake
tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ka’idojin sa,
wadanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta kwarewa
tsawon wadannan shekaru?
Wa ya sanya wadannan tsare-tsare wadanda suke
tafiyar da wannan halittar (rayuwa da mutuwa,
bibikon rayuwa, dare da yini, canjin lokuta …
2
Shin wannan halittar ita ta yi kanta ? Koko ta samu
ne daga rashi? Ko kuma kwatsam aka same shi ?
Allah madaukakin sarki yana cewa:
{Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa
sũ ne mãsu yin halitta(35)
Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai
yi ĩmãnin yaƙĩni ba.
Suratut Tur, aya ta: 35-36.
Idan ba mu halicci kammu ba, kuma ba zai taba
kasancewa a ce mun zo ne daga babu ko kwatsam, to
dole abinda yake gaskiya da ba kokonto a cikinta:
Wannan halittar dole ne tana da malicci mai girma mai
iko, domin ba zai yiwu wannan duniyar ta halicci kanta
ba, ko ta zo daga babu ko kuma kwatsam.
Saboda me mutum yake yin imani da abubuwan da
ba ya ganisu, kamar: (Tunani hankali, rai, ji a jika, da
so.) ashe ba saboda yana ganin alomominsu ba ne? To
tayaya mutum zai yi mu sun samuwar Mahaliccin
wadannan abubuwa masu girma, alhali yana ganin
alamomi na halittarsa da aikinsa da kuma rahamarsa?
Babu mutumin da zai yarda a ce da shi: Ai wannan
gidan kawai ya samu ne ba tare da wani ne ya gina shi
ba. Ko a ce da shi: Ai babu ita ce ta samar da wannan
gidan!. To, ta yaya wasu daga cikin mutane suke
3
gasgata wanda yake cewa: wannan duniyar mai girma
ta zo ne ba tare da Mahalicci ba ?. Ta yaya mai hankali
zai yarda ace da shi: wannan ginin (na sama da kasa)
wanda ke cike da kwarewa ya samu ne haka kawai?
Duk wannan yana kaimu ne zuwa ga sakamako
guda daya cewa: Wannan duniyar (halittar) tana da
Ubangiji mai girma mai iko da yake kula da su, kuma
shi ne kadai ya cancanci bauta, kuma duk abinda ake
bautawa komabayan shi to bautar batacciya ce kuma
shi bai cancanci a bauta masa ba.
Ubangiji Mahalicci Mai girma.
Akwai wani Ubangiji Mahalicci guda daya, shi ne
Mamallaki mai jujjuya lamura mai azurtawa, wanda
yake rayawa yake kashewa. Shi ne wanda ya halllici
kasa. ya kuma sawwaketa, ya sanyata daidai da
halittunsa. Shi ne wanda ya halicci sama da abinda
yake cikinta na halittu masu girma. Ya sanya wa rana
da wata da dare da yini wannan nagartaccan tsarin ,
wanda yake nuni a bisa girman Ubangijinsa.
Shi ne wanda Ya hore mana iska, wacce babu
rayuwa a garemu idan babu ita, Shi ne wanda Yake
saukar mana da ruwa, kuma Ya hore mana tekuna da
ƙoramu. Shi ne wanda Yake ciyar da mu, Yake karemu
alhali mu muna tayi a cikin mahaifammu, ba tare da
muna da wani ƙarfi ba, Shi ne wanda Yake tafiyar da
jini a cikin jijiyoyin mu, tun daga haihuwar mu har
zuwa mutuwarmu.
4
Wannan Ubangijin Mahalicci Mai azirtawa,
Shi ne Allah - tsarki da ɗaukaka sun tabbatar
masa -.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta
sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma
Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini,
yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da
taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar
kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã
bayyana!}
[al-A'araf: 54].
Allah ! Shi ne Ubangiji Mahalicci ga dukkan abinda
ke cikin duniyar nan wanda muke gani da wanda ba
ma gani, duk abinda ba Shi ba to halitta ne daga
halittun Sa. Shi ne wanda Ya cancanci a bauta maSa
Shi kaɗai, kuma kada a bautawa wani tare da Shi, ba
Shi da abonkin tarayya a mulkinSa ko halittarSa ko
jujjuya lamura ko bauta maSa.
Da zamu ƙaddara cewa akwai wasu ababan bauta
tare da Ubangiji - Maɗaukakin sarki - da halittu sun
lalace; domin ba zai yiwu ba a ce alloli biyu ne suke
5
jujjuya al’amarin halitta a lokaci guda, Allah -
Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{Da ya kasance acikinsu (sama da ƙasa) akwai wasu
allolin banda Allahu to da sun ɓaci}
[al-Anbiya'a: 22].
SIFFOFIN UBANGIJI MAHALICCI.
Ubangiji - tsarki ya tabbata a gare Shi - Yana da
sunaye masu kyau waɗanda ba a iya ƙididdige su, Yana
kuma da siffofi maɗaukaka masu yawa masu girma
waɗanda suke nuni akan cikarSa.
Daga cikin sunayan na Sa:
Mahalicci, Allah. Ma’anar sa: Abin bauta wanda Ya
cancanci bautar Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya.
Rayayye, Tsayayye, Mai jin ƙai, Mai azirtawa, Mai
karamci,
Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin AlKur'ani mai
girma Ya ce:
{Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai
tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma
barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin
6
sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda
yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin
abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu.
Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da
abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa.
Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne
Maɗaukaki, Mai girma}
[Suratul Baƙarah: 255].
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci (1)
Allah shi ne abin nufi da Buƙata (2)
Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba (3)
Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi)
[al-Ikhlas: 1-4].
Ubangiji abin bauta wanda ya siffantu da
siffofin cika
Daga cikin siffofinSa Shi ne abin bauta, wanda ba
Shi ba to abin halitta ne, kuma an ɗora masa hukunce-
hukunce kuma abin umarta ne kuma abin rinjaya.
Daga cikin siffofinSa Shi Rayayye ne kuma Tsayayye
ne, to duk wani samamme a wannan halittar Allah ne
Ya rayar da shi, kuma Ya samar da shi daga babu, Allah
ne ke kula da shi ta samar da shi da arziƙin shi, da kula
da shi. Ubangiji Rayayye ne ba Ya mutuwa kuma
7
ƙarewa ta koru gare shi, Tsayayye ne ba ya bacci, a’a
gyangyaɗi ko bacci basa kama Shi.
Daga siffofinSa shi Masani ne, wanda babu wani
abu da yake ɓoyuwa a gare Shi a ƙasa ko a sama.
Daga cikin siffofinsa cewa Shi Mai ji ne kuma Mai
gani ne, wanda Yake jin kowanne abu, Yake ganin
kowanne abin halitta, Yana sane da abinda
zukatammu suke saƙawa da kuma abinda suke
ɓoyewa, babu wani abu da yake boyuwa a gare Shi,
tsarki ya tabbata a gare Shi a sama ko a ƙasa.
Daga cikin siffofinSa Shi Mai iko ne, babu wani abu
da yake gagarar Allah, kuma babu abinda zai mayar da
nufinSa, Yana aikata abinda Ya so, Yana kuma hana
abinda Ya so, Yana ƙaddamarwa Yana kuma
jinkirtarwa, Yana da cikakkiyar hikima.
Daga cikin siffofinSa Shine Mahalicci, Mai
azurtawa, Mai juya lamura, wanda Ya halicci halittu Ya
kuma juya su, halittu suna cikin damƙarSa, kuma
ƙarƙashin rinjayenSa.
Daga cikin siffofinSa Shine Yake amsawa mai
tsanain buƙata, Yana agazawa wanda yake cikin
tsanani, Yana yaye baƙin ciki, duk wani abin halitta, to
idan ya shiga damuwa da kunci, yana komawa ne
gareShi don neman taimako.
Ita
bauta ba ta kasancewa sai ga Allah -
Maɗaukakin sarki -, Shi ne cikakke wanda Ya cancanci
a bauta maSa Shi kaɗai banda wanda ba Shi ba, duk
8
abinda aka bautawa da ba Shi ba to abin bautar
ɓatacce ne kuma tawayayye ne, mai mutuwane mai
ƙarewa ne.
Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya azurta mu da
hankulan da suke riskar wani abu na girmanSa, Ya
kuma dasa mana ɗabi'ar da take son alheri, kuma take
ƙin sharri, kuma take natsuwa idan ka fake ga Allah
Ubangijin talikai, wannan ɗabi'ar tana nuni akan
cikarSa kuma cewa bazaiyiwu a siffantaShi da tawaya
ba - tsarki ya tabbatar maSa -.
Bai kamata ga mai hankali ya bautawa wani ba sai
cikakke, to tayaya zai bautawa wanda aka halitta mai
tawaya irinsa ko ma wanda bai kai shi ba!
Bazai yuwu ba abin bautawa ya kasance mutum, ko
gunki ko bishiya ko dabba!
Ubangiji Yana saman sammanSa, Ya daidaitu a kan
Al’arshinSa nesa da halittarSa, babu wani abu a
zatinSa na halittarSa, haka kuma babu a cikin
halittarSa wani abu na zatinSa, ba ya shiga ko ya narke
a cikin halittarSa.
Ubangiji babu wani abu da ya yi kama da Shi, Shi
Mai ji ne Mai gani ne, ba Shi da wani kini, Shi
Mawadaci ne ga barin halittarSa, ba Ya bacci baYa cin
abin ci, shi Mai girma ne, bazaiyiwu a ce Yana da mata
ko ɗa ba; Malicci Yana da siffofin girma wanda ba zaiyi
wu ba har abada ace Ya siffantu da buƙata ko tawaya.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra
zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah,
bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma
idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar
da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake
nẽman gare shi sun raunana} (73)
Ba su ƙaddara wa Allah haƙƙin girmanSa ba. Lalle
ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi}
[al-Hajj: 73-74].
To saboda me wannan Mahalicci Mai girma
Ya haliccemu? Kuma me Yake so daga
garemu?
Shin zai yuwu a hankalce ace Allah Ya halicci duk
waɗannan halittu, ba tare da wata manufa ba, shin Ya
haliccesu ne don wasa alhali Shine Gwani Masani?
Shin zai yuwu a hankalce cewa wanda Ya halicce
mu da wannan kyautataccen tsari, Ya kuma hore
mana abinda ke cikin sammai da ƙasa ace Ya halicce
mu ba tare da wata manufa ba, ko Ya barmu ba tare
da amsa mafi mahimmancin tambayoyi ba waɗanda
zasu ja hankalin mu, misali: Saboda me muke a nan?
10
Menene zai kasnce bayan mutuwa? Menene manufar
halittar mu?
Shin zai yiwu a hankalce cewa babu wata uƙuba ga
azzalimi da kuma sakayya ga mai kyautatawa?
Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce:
{Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da
wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba}
[al-Mua'Minun: 115].
A’a, Allah Ya aiko Manzanni domin musan abinda
ya sa aka samar da mu, kuma Ya nuna mana yadda
zamu bauta maSa, kuma mu nemi kusanci gare Shi,
kuma me Yake so daga garemu, ta yaya zamu sami
yardar Sa, Ya kuma bamu labarin makomar mu bayan
mutuwa.?
Allah Ya aiko Manzanni domin su bamu labarin
cewa Shi kaɗai Yake wanda Ya cancanci a bauta maSa,
domin kuma musan ya zamu bauta maSa, domin su
isar mana da umarninSa da kuma haninSa, kuma su
sanar da mu kyawawan ɗabi’un da idan muka yi riƙo
da su to rayuwar mu zata zama kyakkyawa, alhairai za
su gameta da kuma albarkatai.
Haƙiƙa Allah Ya aiko Manzanni masu yawa misalin:
(Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa, da Isa), Ya ƙarfafe su da
ayoyi da Mu’ujizojin da suke nuni akan gaskiyarsu,
kuma cewa su Manzanni ne daga wurinSa - tsarki ya
tabbatar maSa -, kuma na ƙarshansu ya kasance
11
(Annabi) Muhammad ne - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi -.
Kuma haƙiƙa Manzanni sun bamu labari a bayyane
cewa wannan rayuwar jarrabawa ce, kuma lalle
rayuwa ta haƙiƙa zata kasance ne bayan mutuwa
Kuma cewa a can (lahira) akwai aljanna ga muminai
waɗanda suka bautawa Allah Shi kaɗai baShi da
abokin tarayya, kuma suka yi imani da dukkanin
manzanni, hakanan kuma a can (lahira) akwai wuta
wacce Allah Ya tanadeta ga kafirai waɗanda suka
bautawa wasu allolin tare da Allah, ko suka kafirce da
kowane manzo daga cikin manzannin Allah.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga
cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNa to,
wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu
tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki (35)
Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu,
kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne
abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne}
[al-A'araf: 35-36].
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda
Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku,
tsammãninku ku kãre kanku (21)
Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama
gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya
fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda
ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu
kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane (22)
Idan kun kasance a cikin kokwanto daga abinda
muka saukar a bisa bawanmu, to kuzo da wata sura
irinsa (alkur'ani) kuma ku kira shedunku wanda ba
Allah ba, in kun kasance masu gaskya ne (23)
To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku
aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda
makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta
dõmin kãfurai (24)
Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi
ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa
13
lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna
daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da
abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce:
"Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin
haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna,
Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki,
kuma su, cikin su madawwama ne}
[Suratul Baƙarah, 21-25].
ME YASA MANZANNI SUKE DA YAWA ?
Tabbas Allah Ya aiko ManzanninSa zuwa ga
al’ummatai, babu wata al’umma face sai da Allah Ya
aika musu da Manzo, domin ya kira su zuwa ga
bautawa Ubangijin su, kuma ya isar musu da
umarninSa da kuma haninSa, kuma manufar kiran na
su ya kasance ne gaba ɗaya itace: Bautawa Allah Shi
kaɗai - Mai girma da ɗaukaka -. To a duk lokacin da
wata al’umma ta fara bari ko ta rikitar da abinda
Manzon ya zo da shi na kaɗaita Allah, sai Allah Ya sake
aiko da wani Manzon domin ya gyara tafiyar, kuma ya
kuma dawo da mutane kan tafarki na daidai, na
kaɗaita Allah da kuma yi maSa biyayya.
Har sai da Allah Ya kammala aiko Manzanni da
(Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi -, wanda yazo da Addini cikakke da
kuma shari’a tabbatacciya gamammiya ga dukkanin
mutane har ranar alƙiyama, wacce ta cika kuma ta
goge wacce ta gaba ce ta na shari’o’i, kuma Allah -
14
Maɗaukakin sarki - Ya lamunci wanzar da wannan
Addinin da kuma tabbatuwarsa har zuwa ranar
alƙiyama.
Mutum ba zai kasance mumini ba har sai ya
yi imani da dukkanin manzanni.
Allah Shine wanda Ya aiko manzanni, kuma Ya
umarci dukkanin halittarSa da yi musu biyayya, wanda
ya kafirce da sakon ɗaya daga cikinsu to haƙiƙa ya
kafircewa dukkannin su, babu wani zunubi mafi girma
fiye da mutum ya juyarwa da Allah wahayinSa, babu
makawa yin imani da dukkanin manzanni domin shiga
aljanna.
Abinda yake wajibi akan kowanne mutum a
wannan lokacin shine yayi imani da Allah da kuma
dukkanin Manzannin Allah, kuma yayi imani da ranar
ƙarshe, hakan kuma bazai kasance ba sai idan yayi
imani kuma yabi na ƙarshensu kuma cikamakinsu
(Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi -, wanda aka ƙarfafeshi da mu’ujiza
madawwamiya ita ce Alƙur’ani mai girma, wanda
Allah Ya lamunce kiyaye shi har sai ya gaje ƙasa da
waɗanda ke kanta.
Allah Ya ambata a cikin AlKur’ani cewa duk wanda
yaƙiyin imani da kowanne manzo daga cikin
manzaninSa to shi ya kafircewa Allah, kuma ya ƙaryata
wahayinSa, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da
ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin
Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni
da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã
nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan (150)
Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali,
dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa}
[Surat al-Nisa'i: 150-151].
Saboda haka mu musulmai muke imani da Allah da
ranar lahira - kamar yadda Allah Yayi umarni -, kuma
muna imani da dukkanin Manzanni da littattafan da
suka gabata, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar
zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai.
Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da
littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a
tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai)
suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman)
16
gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka
makõma take }
[Surat al-Baƙara: 285].
MENENE ALƘUR'ANI MAI GIRMA?
Alƙur’ani mai girma shine zancan Allah -
Maɗaukakin sarki - kuma wahayinSa da Ya saukar da
shi ga ƙarshan Manzanni (Annabi) Muhammad, shine
ƙololuwar mu’ujizar da take nuni akan gaskiyar
Annabtarsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi -, Alƙur'ani mai girma shine gaskiya a cikin
hukunce- hukuncensa, kuma gaskiya a cikin labaransa.
Tabbas Allah Ya ƙalubanci masu ƙaryatawa akan
suzo ko da da sure ce guda ɗaya kwatankwacinsa sai
suka kasa hakan; saboda girman abinda ya ƙunsa, da
kuma gamewar abubuwan da ya tattaro na dukkan
abinda yake da alaƙa da mutum a rayuwar duniya da
lahiya, kuma ya ƙunshi dukkanin tabbatattun
abubuwa na imani waɗanda ya wajaba ga mutum yayi
imani da su.
Kamar yadda ya ƙunshi umarni da hani waɗanda
suke wajaba mutum ya tafi akansu a tsakaninsa da
Ubangijinsa, ko tsakanin sa da kansa ko kuma tsakanin
sa da sauran halittu, dukkanin hakan a tsari na
ƙololuwar balaga da kuma bayani.
Haƙiƙa (Alƙur’ani) ya ƙunshi da yawa daga dalilai na
hankali da tabbatattun ilimi masu zurfi waɗanda suke
nuni akan wannan Littafin cewa bazai taɓa yi wuwa a
17
ce mutum ne ya ƙirkire shi ba, kai shi magana ce ta
Ubangijin mutum - tsarki ya tabbatar maSa Ya
ɗaukaka -.
MENENE MUUSULINCI?
Musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah - Maɗaukakin
sarki - da Tauhidi, da jawuwa gareShi da biyayya, da
riƙo da shari’arSa da yarda da kuma karɓa, da kuma
kafircewa dukkanin abinda ake bautawa ba Allah ba.
Haƙiƙa Allah Ya aiko da Manzanni da saƙo ɗaya
shine: Kira zuwa ga bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da
abokin tarayya, da kuma kafircewa dukkanin abinda
ake bautawa ba Allah ba.
Musulunci shi ne Addinin dukkanin Annabawa,
kuma da’awarsu ɗaya ce, shari’o’insu sun sha banban,
musulmai a yau su ne masu kaɗaita Allah su kaɗai,
masu riƙo da ingantaccen Addini wanda dukkanin
Annabawa suka zo da shi. Kuma saƙon Musulunci a
wannan zamanin shine gaskiya, kuma shi ne saƙo na
ƙarshe daga Mahaliccin mutum.
Ubangiji wanda Ya aiko (Annabi) Ibrahim da Musa
da Isah - amincin Allah ya tabbata a gare su - Shine Ya
aiko cikamakin Manzanni (Annabi) Muhammad - tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi -, haƙiƙa shari'ar
Musulunci tazo tana mai shafe dukkanin shari’un da
suka gabaceta.
Dukkanin addinai waɗanda mutane suke bauta da
su a yau - in banda Musulunci- addinai ne da mutane
18
suka ƙirƙira, ko kuma addinai ne waɗanda daga Allah
suke sai mutane sukayi wasa da su, sai suka wayi gari
a cakuɗe da ɗebe-ɗebe da tatsuniya da shaci faɗi
waɗan aka gada, kuma sauran tunanin mutum.
Amma Addinin Musulmai to Addini ne guda ɗaya
kuma a bayyane yake baya canzawa, kamar yadda
bautarsu wacce suke bautawa Allah da ita ɗaya ce,
dukkanin su suna salloli biyar, suna zakkar
dukiyoyinsu, suna azumin wata Ramadan, kuma kayi
la’akari da Littafin su shi ne Alƙur’ani mai girma shi
littafi ne guda ɗaya adukkanin ƙasashe. Allah -
Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{A yau Na cika maku Addininku, kuma Na cika
muku ni’imta a gareku, Na kuma yardar muku
Musulunci shi ne Addini, to duk wanda ya shiga
matsananciyar buƙata a yunwa ba tare da karkata ga
lefi ba, to lalle Allah Mai gafara ne Mai jinƙai}
[Suratul Ma’idah: 3].
Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin Alƙur'ani mai
girma Ya ce:
{Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka
saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da
Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka
bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã
mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma
mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne}(84)
{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama
addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a
Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra}
[Aal Imran: 84-85].
Addinin Musulunci tsari ne da ya game dukkanin
rayuwa, yayi daidai da ɗabi’a na halitta da hankali,
kuma madaidaitun rayuka suna karɓarsa, Mahalicci
Mai girma ne Ya shar’anta shi ga halittarSa, kuma
shine Addinin alheri da rabauta ga mutane baki ɗaya
a duniya da lahira, ba ya banbance ƙabila da ƙabila, ko
nuna wariyar launin fata, mutane a cikinsa daidai
suke, wani mutum a Musulunci baya fin wani sai da
gwargwadon aikinsa na gari.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ
kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar
da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã
20
musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance
sunã aikatãwa}
[Suratun Nahl: 97].
MUSULUNCI HANYA CE TA TSIRA
Musulunci Addini ne na dukkanin Annabawa, kuma
shi ne Addinin mutane baki ɗaya, ba wai addini ne na
Labawa kaɗai ba.
Musulunci shi ne hanyar samun farin ciki na haƙiƙa
a duniya, kuma ni'ima madawwamiyya a lahira.
Musulunci shi ne Addini ɗaya da yake amsa
buƙatun rai da jiki, da warware dukkanin matsalolin
mutane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya,
sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata
shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi
shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala}
Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni)
to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi,
kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho}
[Ɗaha: 123-124].
21
Me Musulmi yake fa’idantuwa da shi a
duniya da lahira?
Musulinci yana da fa’idoji masu girma, daga cikinsu
akwai: - Rabauta da ɗaukaka a duniya wato mutum ya
kasance bawa ga Allah. in ba haka bafa zai zama
bawan son zuciya da shaiɗan da sha'awe-sha'awe. - Rabauta a lahira shine Allah Ya gafarta masa,
kuma Ya saukar maSa da yardarSa, kuma Ya shigar da
shi
aljanna, ya rabauta da yarda da ni’ima
tabbatacciya, kuma mutum ya tsira daga azabar wuta. - Mumini yana kasancewa ne a ranar Alƙiyama tare
da Annabawa da siddiƙai da shahidai da kuma salihai.
Kai Amma wannan tawaga babu abinda ya kai ta daɗi,
duk wanda bai yi imani ba to ya kasance ne tare da
Ɗagutai da ashararai da fanɗararru da maɓarnata. - Waɗanda Allah Zai shigar da su aljnna za su rayu
a cikin ni’ima ta har abada ba mutuwa ba rashin lafiya
ko ciwon jiki ko tsufa ko baƙin ciki, kuma za’a biya
musu buƙatunsu na duk abinda suke buƙatarsa.
Wadanda za su shiga wuta za su kasance a cikin azaba
ta har abada a dawwame ba ta yankewa.
Acikin Aljanna akwai abubuwan jin daɗin da idanu
bai gansu ba, kunne bai ji su ba, kuma basu ɗarsuwa a
zuciyar wani mutum ba. Daga dalilan hakan faɗinSa -
Maɗaukakin sarki -:
22
{Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ
kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar
da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã
musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance
sunã aikatãwa}
[al-Nahl: 97].
Maɗaukakin sarki Ya ce:
{Kuma rai ba ta san abinda aka ɓoye musu na farin
idanuwa ba, sakamako na abinda suka kasance suna
aikatawa}
[Suratus Sajdah, aya ta 17]
Me abinda wanda ba musulmi ba zai yi
asara?
﴿ َ
Mutum zai yi hasarar mafi girman ilimi da sani, shi
ne sanin Allah, kuma zai yi hasarar imani da Allah,
wanda ya ke bawa mutum aminci da nutsuwa a
duniya, da ni'ima madawwamiyya a lahira.
Mutum zai yi hasarar tsinkaye a kan mafi girman
littafin da Allah Ya saukar da shi zuwa ga mutane, da
kuma imani da wannan Littafin mai girma.
Zai yi hasarar imani da Annabawa masu girma,
kamar yadda zai yi hasarar zama tare da su a aljanna
23
ranar alƙiyama, zai kasance abokin zaman shaiɗan da
masu laifuffuka da ɗagwitai (waɗanda aka bautawa) a
cikin wutar Jahannama tir da wannan gida kuma tir da
wannan maƙotaka.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce:
{Kace lallai hasararru sune waɗanda suka yi
hasarar kawunann su da ahalin su ranar alƙiyama, ku
saurara, wannan ita ce hasara bayyananna (15)
Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu,
kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan
Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa!
To, ku bĩ Ni da taƙawa}
[al-Zumar: 15-16].
Wanda yake nufin tsira a lahira, to ya
wajaba a kansa ya kasance musulmi mai
biyayya ga Allah, mai kuma bin Manzon
Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agare
shi-
Daga tabbatattun abubuwan da Annabawa da
Manzanni - amincin Allah ya tabbata a gare su - suka
haɗu a kansu cewa babu wanda zai tsira a lahira sai
24
musulmai waɗanda suka yi imani da Allah -
Maɗaukakin sarki -, ba su haɗa kowa da Shi a bauta
ba, kuma suka yi imani da dukkanin Annabawa da
Manzanni, duk masu bin Manzanni waɗanda suka yi
imani da su masu gasgata su, to za su shiga aljanna
kuma za su tsira daga wuta.
Waɗanda suka yi imani a zamanin (Annabi) Musa
suka yi imani da shi suka bi karantarwar sa to
waɗannan musulmai ne, kuma muminai ne salihai,
saidai bayan Allah Ya aiko da Annabi Isa ya wajaba ga
mai mabiya Annabi Musa su yi imani da Annabi Isa su
kuma bi shi.
Waɗanda suka yi imani da Annabi Isa to waɗannan
musulmai ne salihai, wanda kuma ya yi watsi da imani
da Annabi Isa ya ce, zan kasance akan Addinin Annabi
Musa, to wannan bai yi imani ba, domin ya yi watsi da
imani da Manzon da Allah Ya aiko shi.
Sannan bayan da Allah Ya aiko Manzon ƙarshe
(Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi -, ya wajaba akan kowa suyi imani
da shi, Ubangiji Shi ne Ya aiko (Annabi) Musa da Isah
kuma Shi ne wanda Ya aiko cikamakin Manzanni
(Annabi) Muhammad, duk wanda ya kafircewa
manzancin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi - ya ce zan kasance akan
bin (Annabi) Musa ko Isa to wannan ba mumini ba ne.
25
Baya wadatarwa mutum ya ce shi yana girmama
musulmai, kuma baya wadatarwa don samun tsiransa
a ranar ƙarahe saboda ya bada sadaka kuma yana
taimakawa talakawa, kai babu makawa sai ya kasance
ya yi imani da Allah da littattafanSa da ManazaninSa
da ranar ƙarshe; domin Allah Ya karɓi hakan daga gare
shi!. Babu wani zunubi mafi girma da ya kai shirka da
kafircewa Allah da ƙin yin imani da wahayin da Allah
Ya saukar da shi ko ƙin yin imani da ƙarshan
AnnabawanSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin
Allah su tabbata agare shi -.
Yahudu da Nasara da sauransu waɗanda suka ji
aiko (Annabi) Muhammad Manzon Allah - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi -, suka ƙi yin imani
da shi suka ƙi shiga Addinin Musulunci to za su
kasance a wutar Jahannama masu dawwama a cikinta
har abada, wannan shi ne hukuncin Allah ba hukuncin
wani ba ne cikin mutane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya
ce:
{Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen
Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna
madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi
ashararancin tãlikai}
[al-Bayyinah: 5].
26
Yayin da ƙarshen saƙo ya sauka daga Allah izuwa
yan Adam, ya wajaba akan kowanne ɗaya da ya ji
(bayanin) Musulunci ya kuma ji (bayanin) Annabin
ƙarshe (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi -, ya yi imani da shi kuma ya bi
shari'arsa, ya yi masa biyayya a umarninsa da haninsa,
saboda haka wanda ya ji wannan saƙon na ƙarshe
kuma ya ƙi binsa, to Allah ba zai karɓi wani abu daga
gare shi ba, kuma zai azabtar da shi a lahira.
Daga cikin dalilan haka, faɗinSa - Maɗaukakin sarki -:
{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama
addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a
Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra}
[Aal- Imran: 85].
Maɗaukakin sarki Ya ce:
{Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga
kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu
bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme
da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji,
27
baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi
shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne}
[Aal- Imran: 64].
Meye ya lazimci Musulmi?
Yana wajaba akan musulmi, yin imani da waɗannan
rukunan guda shida:
Yin Imani da Allah - Maɗaukakin sarki - kuma cewa
Shi ne Mahalicci Mai azurtawa Mai juya lamura
Mamallaki, babu wani abu da ya yi kama da Shi, ba Shi
da mata ba Shi da ɗa, kuma Shi kaɗai ne wanda Ya
cancanci a bauta maSa, kuma ba’a bauta wani tare da
Shi, kuma Ya ƙudirce cewa bautawa dukkanin wanda
ake bautawa koma bayanSa to bautarsa ɓatacciya ce.
Yin imani da mala'iku, cewa su bayin Allah ne -
Maɗaukakin sarki -, Ya halicce su daga haske, kuma Ya
sanya cewa daga cikin ayyukansu su suna sauko da
wahayi ga AnnabawanSa.
Yin imani da dukkanin littattafan da Allah Ya saukar
da su ga AnnabawanSa (kamar Attaura da Injila - kafin
a jirkita su -) kuma ƙarshen littattafan shi ne Alƙur'ani
mai girma.
Yin imani da dukkanin Manzanni, kamar (Annabi)
Nuhu da (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Musa da
(Annabi) Isa, da na ƙarshensu shine (Annabi)
Muhamad, kuma dukkaninsu daga 'yan Adam suke,
(Allah) Ya ƙarfafe su da wahayi kuma Ya basu ayoyi da
mu'ujizojin da suke nuni akan gaskiyarsu.
28
Imani da ranar ƙarshe, yayin da Allah zai tashi na
farko da na ƙarshe, Allah kuma zaiyi hukunci tsakanin
halittarSa, Ya shigar da muminai aljanna, kafirai kuma
Ya shigar da su wuta.
Imani da kaddara cewa, Allah ya san komai, abinda
ya kasance ya wuce da kuma abinda zai kasance nan
gaba, kuma hakika Allah ya rubuta haka, kuma ya so
shi ya halicci komai.
Kuma ka bautawa Allah da abinda Ya shar’anta na
sallah da zakkah da azumi da kuma hajji idan ka sami
ikon tafiya gareshi. Sannan ya wajaba akan shi ya koyi
Addininsa wanda zai zama tushen rabautarsa a duniya
da kuma tsiransa a lahira.
***
29
30
Teburin bayani
WA YA HALICCI HALITTU? WA YA HALICCE NI ? KUMA SABODA
ME ? ............................................................................................. 2
Ubangiji Mahalicci Mai girma. ..................................................... 4
Wannan Ubangijin Mahalicci Mai azirtawa, Shi ne Allah - tsarki
da ɗaukaka sun tabbatar masa -. ................................................ 5
SIFFOFIN UBANGIJI MAHALICCI. .................................................. 6
Ubangiji abin bauta wanda ya siffantu da siffofin cika ................ 7
To saboda me wannan Mahalicci Mai girma Ya haliccemu? Kuma
me Yake so daga garemu? ......................................................... 10
ME YASA MANZANNI SUKE DA YAWA ? .................................... 14
Mutum ba zai kasance mumini ba har sai ya yi imani da dukkanin
manzanni. .................................................................................. 15
MENENE ALƘUR'ANI MAI GIRMA? ............................................ 17
MENENE MUUSULINCI? ............................................................ 18
MUSULUNCI HANYA CE TA TSIRA .............................................. 21
Me Musulmi yake fa’idantuwa da shi a duniya da lahira? ........ 22
Me abinda wanda ba musulmi ba zai yi asara? ......................... 23
Wanda yake nufin tsira a lahira, to ya wajaba a kansa ya kasance
musulmi mai biyayya ga Allah, mai kuma bin Manzon Allah-tsira
da amincin Allah su tabbata agare shi- ...................................... 24
Meye ya lazimci Musulmi? ........................................................ 28