Labarai




TAMBAYOYI DA AMSOSHI 


A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH 


DA KAFIRCI





FASSARA: TAJUDDIN ISA


BITA: SURAJ BALA UMAR





GABATARWA


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI


Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah da alayensa da sahabban sa.


Bayan haka… wadannan wasu tambayoyi ne muhimmai  daga daliban ilimi da masu kira zuwa ga Allah izuwa ga malamin mu mai falala Sheikh Salih Ibn Fauzan al-Fauzan - Allah Madaukakin srki Ya kiyaye shi - yayi albarka gare shi da ilimin sa, ya kuma amfani musulunci da musulmai dashi… muna gabatar dasu gare shi don kwadayin amsa daga gareshi da abinda Allah Zaiyi masa budi na daga Al’Kurani da sunnah ko Allah Zai amfanar da su.


TAMBAYA TA DAYA (01):


Da me kafirci babba yake kasancewa ko riddah? Shin ya kebanta da kudircewa ko musu ko karyatawa, ko yafi gamewa dagahakan?


AMSA:


Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai tsira da aminci su tabbata ga Annabin mu Muhammad da alayen sa da sahabban sa, bayan haka:


Lallai mas’alolin akidah muhimmai ne sosai, kuma sanin akidah yana wajaba da dukkanin babukan ta da dukkanin mas’alolin ta da cirato ta daga ma’abota ilimi, yin tambayoyi da tarwatsa tambayoyi a cikinta baya isuwa, domin ita a duk lokacin da tambayoyi suka yawaita kuma aka amsasu, to lallai jahilci zai kasance mafi girma. Abinda yake wajibi ga wanda yake son amfanar kansa da yan’uwansa musulmai ya koyi akidah daga farkon ta zuwa karshen ta, kuma ya yi nitso a kogin babukan ta da masalolin ta, kuma ya cirato ta daga maabota ilimi da litattafan ta na asali, daga littattafan magabata na kwarai da wannan ne jahilci zai gushe daga gareshi, kuma baya bukatar yawan tambayoyi, kuma zai sami iko ya bayyanawa mutane ya sanar da jahilai, domin yanzu ya zama ahali (macancanci) a akidah.


Haka nan ba’a cirato akidah daga littattafai kawai… ko daga karatu da mudala’a, domin ba’a karbo masaalolinta tun farko daga littattafai kawai ko daga mudala’o’i, kadai ana karbo ta ne da riwaya daga ma’abota ilimi da basira wadanda suka fahimce ta suka kyautata mas’alolin ta.


     Amma abinda yake zagawa a yanzu a farfajiya na daga yawan tambayoyi dangane da akida da muhimman al’amuranta daga mutanen da basu karanceta ba tun farko, ko mutanen da suke magana a akida da al’amuran akidah akan jahilci ko dogaro da karatun su ga littattafai ko mudala’o’in su, to wannan zai karawa al’amarin rashin fashimta,  kuma  zai kara rikice-rikice wadansu rikice-rikicen daban, kuma zai hana kokari, zai farar da sabani, domin mu idan muka koma zuwa fahimce-fahimcen mu ba tare da dakko ilimi daga tushen sa ba, mu dogara kawi akan karatun mu da fahimtar mu, domin fahimce-fahimce suna sabawa kuma ruskanni suna sabawa… a karshe sabani zai yawaita a wadannan al’amuran muhimmai. Kuma Addinin mu yazo ne da haduwa da gamuwa da rashin rabrrabuwa, da soyayya ga ma’abota imani da adawa ga kafirai… to wannan baya cika sai da cirato al’amuran addini daga tushensu da malaman su da sukayi riko su daga wadanda suka zo kafin su suka karance su da sanadi suka isar dasu ga wadanda suka zo a bayansu … wannan shine hanyar ilimi sahihi a akida da wanin ta, sai dai akida itace mafi muhimmanci domin itace ginshiki, domin sabani a cikinta fage ne na bata kuma fage ne na rarrabuwa tsakanin musulmai.


Kafirci da riddah suna tabbata ne da aikata wani mai warwarewa daga masu warware musulunci, wanda ya aikata wani mai warwarewa daga masu warware Musunci wadanda aka sani gurin maabota ilimi to lallai shi da hakan ya zama mai ridda kuma ya zama kafiri, zamuyi masa hukunmci da abinda ya bayyana daga gareshi daga zancen sa ko aikin sa, zamu yi masa hukunci da wannan domin ba abinda yake gare mu sai hukunci da zahiri, amma al’amuran zuciyoyi to ba wanda ya sansu sai Allah – tsarki ya tabbatar maSa - .To wanda yayi furuci da kafirci ko ya aikata kafirici, zamu yi masa hukunci da tabbataccen zancensa da tabbataccen furucinsa da tabbataccen aikinsa idan abinda ya aikata ko ya furta yana daga al’amuran ridda.





TAMBAYA TA BIYU (02):


     Akwai wanda yake cewa: “Imani furuci ne da kudircewa da aiki, sai dai aiki sharadin cika ne a cikinsa”, kuma yana cewa: “Babu kafirci sai da kudurcewa”.. shin wannan zancen yana daga zantukan Ahlus sunnah ne ko a’a? 


AMSA:


Me fadar wannan bai fahimci imani da akida ba, wannan shine abinda muka fade shi cikin amsar tambayar data gabace shi: Yana daga wajibi akansa ya karanci akida daga maabota ilimi kuma ya cirato ta daga tushenta ingantattu, da sannu zai san amsar wannan tamayar.


Fadarsa: lallai cewa imani furuci ne da aiki da kudircewa.. sannan yake cewa: Aiki sharadi ne cikin cikar imani da kuma ingancin sa, wannan warwara ne!! ta yaya aiki zai kasance daga imani sannan yace aiki sharadi ne, kuma abin sani sharadi yana zamowa ne a wajen abinda aka shardanta, wannan warwara ce daga gare shi. Kuma wannan yana nufin ya tara tsakanin zancen magabata da zancen yan baya alhali shi bai fahimci warwara ba, domin bai san zancen magabata da hakikanin zancen ‘yan baya ba, sai yayi nufin cakudawa su.. imani furuci ne da aiki da kudircewa, aiki yana daga imani kuma shine imani, ba sharadi bane daga sharuddan ingancin imani ko sharadin cika ko wanin wannan daga wadannan zantuttukan da suke yadasu a yanzu. Imani furuci ne da harshe da kudircewa da zuciya da aiki da gabbai kuma yana karuwa da da’a yana raguwa da sabo.


TAMBAYA TA UKU (03):


   Shin ayyuka rukunai ne a cikin imani kuma wani yanki ne daga shi ko sharadin cika ne a cikinsa?


Amsa:


Wannan yana kusa da tambayar baya, mai wannan tambayar bai san hakikanin imani ba. Shi yasa yake kaikawo: Shin ayyuka wani yanki ne daga imani ko su sharadin imani ne? domin cewa shi bai cirato akida da asalillikan ta kuma daga malamanta ba. Kuma kamar yanda muka ambata babu aiki ba tare da imani ba kuma babu imani ba tare da aiki ba, sumasu lazimtar junane, ayyuka suna daga imani bari ma sune imanin: ayyuka imani ne, furutai imani ne, kudircewa imani ne, kuma matattarinta shine imani da Allah – Madaukakin Sarki - da imani da littattafanSa da manzanninSa da ranar lahira da imani da kaddara alkhairinta da sharrinta.


TAMBAYA TA HUDU (04):


Menene rabe-raben Murji’ah? Tare da ambatar zantuttukan su cikin mas’alolin imani?


Amsa:


Murj’iah sun kasu kaso hudu:-


Kashi na daya; Jahmiyyah kashi na daya: Wadanda suke cewa imani mujarradin ma’arifah ne kawai, ko da gasgatawa bata tabbata ba… wannnan shine zancen Jahmiyyah, wannan shine mafi sharrin zantuka kuma mafi muninsu, wannan kafiric ne da Allah – Madaukakin sarki- , domin mushrikai na farko da Fir;auna da Hamana da Karuna da Iblis suna san Allah kuma suna sanin imani da zuciyoyin su, sai dai tunda basu furta shi da harsunan su ba, kuma ba suyi aiki da gabobin su ba wannan maarifar bata amfanar da su ba.


Kashi na biyu: Asha’irah kashi na biyu: Wadanda suka ce imani shine gasgatawa da zuciya kawai, wannan shine zancen Asha’irah, wannan shima zance ne batacce domin kafirai suna gasgatawa da zuciyoyin su, kuma suna sani cewa Alkurani gaskiya ne kuma Manzo gaskiya ne, su kuma Yahudawa da Nasara suna sanin wannan [wadanda Muka basu littafi suna saninsa kamar yadda suke sanin diyansu]  su suna gasgata shi da zuciyoyin su! Ubangiji –Madaukakin sarki- Ya fada a cikin sha’anin mushrikai: [Lalle ne Muna sani cewa hakika, abinda suke fada yana bata maka rai. To, lalle ne su basu karyataka (a cikin zukatansu) kuma amma azzalumai da ayoyin Allah suke musu]  … wadannan basu yi furuci da harsunan su ba, basu kuma yi aiki da gabobin su ba tare da cewa su suna gasgatawa da zuciyoyin su don haka basa kasancewa muminai.


Kashi na uku: Karramiyyah kashi na uku: Wacce take mukabalantar Asha’irah sune Karramiyyah, wadanda suke cewa: Imani furuci ne da harshe koda bai kudirce da zuciyarsa ba, babu shakkah wannan zancene batacce; domin munafukai wadanda suke a kasan kasa a cikin wuta suna cewa: Muna shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma lallai Annabi Muhammad Manzon Allah ne da harsunan su, sai dai cewa su basa kudirce wannan, kuma basa gasgata shi da zuciyoyin su, kamar yadda Allah - Madaukakin sarki - Yake cewa: [Idan munafukai suka je maka sai su ce: “Muna shaidar lallai kai hakika Manzon Allah ne,” kuma Allah Yana sane da lalle kai hakika manzon Sa ne kuma Allah Yana shaida lalle munafukai hakika, makaryata ne. Sun riki rantsuwowin su garkuwa sai suka toshe daga tafarkin Allah]  , Allah - Madaukakin sarki - Yace [Suna fada da bakunan su abinda baya cikin zuciyoyin su] .


Kashi na hudu: Mur’jiah fukaha (masana fikihu) kashi na hudu: Sune mafi saukin firka cikin Irja’i, suna cewa: Imani kudircewa ne a zuciya, da furuci da harshe kuma aiki baya shiga cikin sa, wannan shine zancen Murji’ah Fukaha, shima zance ne batacce.


TAMBAYA TA BIYAR (05):


Shin sabanin Ahlus sunnah da Murj’iah Fukaha’u a cikin ayyukan zuciya ne ko gabbai? Kuma shin sabani ne na lafazi ko na maanah? Muna fatan rarrabe bayani daga falalar ku.


Amsa:


Sabanin su a aiki ne, sabanin Murjiah Fukaha’u da jumhurin Ahlus sunnah sabani ne a aiki na zahiri, kamar sallah da azumi da hajji, su suna cewa: Lallai shi baya daga imani kadai shi sharadi ne ga imani, kodai sharadin inganci ko sharadin cika, wannan zance ne batacce kamar yadda muka sani.


Sabani tsakanin su da jumhurin din Ahluis sunnah sabani ne na ma’ana bana lafazi ba, domin su suna cewa: Lallai imani baya karuwa kuma baya raguwa da ayyuka, baya karuwa da da’a kuma baya raguwa da sabo…  imanin mutane duk daidai ne, domin a wajen su gasgatawa da zuciya ne tare da furuci da harshe! Wannan zance ne batacce.





TAMBAYA TA SHIDA (06):


Menene hukuncin wanda yabar gaba dayan ayyukan zahiri, sai dai yayi furuci da shahadah kuma ya tabbatar da farillai, sai dai cewa shi baya aiki kwata-kwata, shin wannan musulmi ne ko a’a? Kuma an san cewa bashi da wani uzuri na shari’ah da yake hana shi tsaida wadannan farillan?


Amsa:


Wannan baya zamowa mumini, wanda ya kudirce a zuciyar sa kuma ya tabbatar a harshen sa sai dai baya aiki da gabobin sa, ya bar ayyuka dukkan su ba da wani uzuri ba wannan ba mumini bane, domin imani kamar yanda muka ambata kuma kamar yanda Ahlus sunnah wal jamaah suka sanar cewa shi: Furuci ne da harshe da kudircewa a zuciya da aiki da gabbai, imani baya tabbata sai da gaba dayan wadannan al’amuran, to wanda yabar daya daga cikin su to baya zamantowa mumini.


TAMBAYA TA BAKWAI (07):


Shin wannan maganar tana inganta “Wanda yace imani furuci ne da aiki da kudircewa yana karuwa yana raguwa lallai ya kubuta daga Irja’I koda yace babu kafirci sai da kudircewa da musantawa?


Amsa:


Wannan warwara ne!! idan yace babu kafirci sai da kudircewa ko musantwa to wannan yana warware fadin sa cewa imani furuci ne da harshe da kudircewa a zuciya da aiki da gabbai, wannan warwara ne a zahiri, domin idan imani ya zama furuci ne da harshe da kudircewa a zuciya da aiki da gabbai kuma yana karuwa da da’a yana raguwa da sabo… to ma’anar sa wanda ya kadaita daga wani abu daga wannan baya zamowa mumini.











TAMBAYA TA TAKWAS (08):


     Shin wannan maganar ingantacciyace ko a’a: [ Cewa wanda ya zagi Allah ya zagi Manzon Allah ba kafiri bane a kan kansa, sai dai alama ce ga abinda yake a zuciya na daga rashin kula da wulakantarwa]?


Amsa:


Wannan zance ne batacce, domin Allah Ya hukunta kafirci akan munafukai bayan imani da tabbataccen zancen su: [Bamu taba ganin irin wadan nan makarantan namu ba mafi kwadayin (cika) cikkuna, kuma mafiya tsoro a gurin gamuwa (yaki)] suna nufin Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata gare shi- da sahabban sa, sai Allah –Madaukakin sarki- Ya saukar da fadin Sa a kan su [Ka ce: Shin da Allah da kuma ayoyin Sa da Manzon Sa kuka kasance kunayiwa izgili. Kada ku kawo wani uzuri, hakika, kun kafirta a bayan imanin ku.] , sai Ya kafirta su da wannan zancen, bai shardanta a kafircin su cewa sun kasance suna kudirce wannan a zuciyoyin su ba, bari dai Ya hukunta gare su da kafirci da tabbataccen wannan zancen. Haka nan fadin Sa -Madaukakin sarki-: [Kuma hakika sun fadi kalmar kafirci kuma sun kafirta bayan musulantar su]  sai ya jeranta kafirci akan fadin kalmar kafirci.


TAMBAYA TA TARA (09):


Menene hukuncin wanda yake zagin Allah da Manzon Sa da Addini, idan akayi masa nasiha a wannan al’amarin sai ya illanta da aiki da neman abinci da kuma arziki, shin wannan kafiri ne ko musulmin da yake bukatuwane izuwa ga Ta’azir da ladabtarwa? Kuma za’a fada a nan da banbancewa tsakanin zagi da mai zagin?


Amsa:


Baya halatta ga mutum ya kafircewa Allah da magana ko aiki ko kudircewa kuma yace wannan a dalilin neman arziki ne, shi arziki a gurin Allah –Madaukakin Sarki- yake, kuma Allah –Madaukakin Sarki Yana cewa: [Kuma wanda yabi Allah da takawa, Allah Zai sanya masa mafita. Kuma Ya azirta shi daga inda baya zato.] , arziki a hannun Allah –Madaukakin Sarki- yake kuma Allah –Madaukakin Sarki- Ya hukunta kafirci akan wanda ya zabi duniya akan lahira, Allah –Madaukakin sarki Ya fada- cikin siffanta masu ridda da munafukai: [Wadancan ne kafirai domin sun fifita son duniya a kan lahira, kuma lalle ne Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai] , sai Yayi musu hukunci da cewa sun bar imanin su saboda sun nufi su rayu tare da mutane kuma su kasance tare da mutane: [Kuma da dai sun yarda da abinda Allah Ya ba su, da ManzonSa kuma suka ce:”Maishinmu Allah ne, zai kawo mana daga falalarSa kuma ManzonSa(zai bamu). Lallai ne mu, zuwa ga Allah masu kwadayi ne”] , da sun yi tawakkali ga Allah da Allah –Madaukakin sarki- Ya azurta su.





TAMBAYA TA GOMA (10):


Menene zance a cikin wanda ya kafa gumaka da kabarirrika na alfarma da kabarirrika, kuma ya gina masallatai akan su da wuraren halarta, kuma yayi waqafin maza da kudade akan su, ya sanya musu wata hai’a da ta daukaka akan su, ya tabbatar da mutane akan bautar su da dawafi a gefen su da rokonsu da yanka gare su?


Amsa:


Wannan hukuncin sa ya kafirta da wannan aikin, domin ya aikata wanan don kira zuwa ga kafirci.


Tsayar da kabarirrika na alfarma da yayi da gini da yayi saboda su da kiran mutane zuwa bautar su da kafamasu kula da su, wannan yana nuni akan yardar sa da wannan al’amarin, da kuma cewa yana kira zuwa ga kafirci zuwa ga bata, tsari ya tabbata ga Allah.





TAMBYA TA GOMA SHA DAYA (11):


Shin sallah tana inganta a bayan limamin da yake neman agajin matattu kuma yake neman madadi daga su ko a’a?


Meke ga mutumin da yake karya da gangan, kuma yake cutar da salihai, kuma yakeyiwa mutane limanci. Shin za’a gabatar da shi a sallah idan an san yana karya da fasikanci? Kuma meke ga mutumin da yake karya kuma yake karya da gangan, kuma yake cutar da salihai, kuma yakewa mutane limanci. Shin za’a gabatar da shi a sallah idan an san yana karya da fasikanci?


Amsa:


Sallah bata inganta a bayan mushrikin da shirkar sa shirka ce babba da take fitarwa daga Addini, kuma kiran matattu da neman agajinsu wannan shirka ce babba da take fitarwa daga Addini.


Wannan ba musulmi bane sallar sa bata inganta a kan kansa, kuma sallar wanda kebayan sa bata inganta, kadai an shardanta ga liman ya kasance mai imani da Allah da Manzan Sa, kuma ya kasance mai aiki da Addinin Musulunci a zahiri da badini.


Amma wancan mutumin da abinda yake aikatawa to wadannan manya ne daga manyan zunubai: Karya, da aikata manyan zunubai wadanda basu kai shirka ba da cutar da musulmai… wadannan manya ne daga manyan zunubai, basa hukunta kafirci, kuma baya cancanta a kafashi limami ga mutane, sai dai wanda yazo ya same su suna sallah alhali shine yake yi musu sallah, to yayi sallah a bayan sa kada yayi sallah shi kadai, har sai ya sami wani limami salihi mai tsayuwa akan gaskiya to sai ya tafi gurin sa.





TAMBAYA TA GOMA SHA BIYU (12):


Akwai wadansu sashen hadisai wadansu wasu suke kafa dalili da su akan cewa wanda yabar gaba dayan ayyuka to shi mumini ne mai tauyayyen imani… kamar hadisin [Basu taba aikata wani alheri ba da dai] da hadisin katin shaidah da wanin su daga hadisai, yaya amsa akan wannan take?


Amsa:


Wannan yana daga kafa dalili da abin da yake kama da juna, wannan hanya ce ta ma’abota karkata wadanda Allah -Madaukakin sarki - Yace akan su [To amma wadanda yake a cikin zukatansu akwai karkata sai suna bin abinda yake kama da juna daga gare shi] , sai su riki dalilai masu kama da juna suna barin dalilai bayyanannu ababen kyautatawa wadanda suke fassara su kuma suke bayyana su… babu makawa daga maida masu kama da juna izuwa bayyanannu, sai a ce: Wanda yabar aiki saboda wani uzuri na shari’ah bai samu damar aikata shi ba har ya mutu to wannan abin yiwa uzuri ne, kuma ana daukar wadannan hadisan akan sa.. domin wannan mutumin yayi furta kalmar shahadabiyu kuma ya kudirce su yana mai ikhlasi ga Allah –Madaukakin Sarki- sannan ya mutu a wannan halin, ko kuma bai samu damar yin aikin ba, sai dai ya furta kalmar shahada biyu yana mai ikhlasi ga Allah da tauhidi kamar yanda –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya face: [Wanda ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya kafirce da abinda ake bautawa ba Allah ba to lallai jinin sa da dukiyar sa sun haramta]  kuma yace: [To lallai Allah Ya haramta wuta ga dukkan wanda yace: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah yana mai neman fuskar Allah da hakan] , wannan bai samu damar yin aiki ba tare da cewa ya furta Kalmar shahada biyu kuma ya kudirce ma’anar su kuma yayi ikhlasi ga Allah –Madaukakin Sarki- sai dai babu wata dama data rage a gabansa na yin aiki har ya mutu, to wannan shine zai shiga aljannah da Kalmar shahada biyu, kuma akansa ne ake daukar hadisin katin shaidah da wanin sa na daga abinda yazo da ma’anar sa, kuma wadanda za’a fitar dasu daga wuta alhali su basu taba aikata alheri ba domin basu samu damar yin aiki ba tare da cewa su sun furta Kalmar shahada biyu, kuma sun shiga cikin Musulunci. Wannan shine hadawa tsakanin hadisan.


TAMBAYA TA GOMA SHA UKU (13):


 Menene hukuncin wanda yake kiran wanin Allah alhali yana rayuwa cikin musulmai kuma Alkur’ani ya riske shi? shin wannan musulmi ne da ya cudanya da sharka ko kuma mushriki ne?


Amsa:


Wanda Alkur’ani da sunnah suka riskeshi ta fuskar da yake da iko ya fahimce shi idan ya so, sannan bai yi aiki dashi ba kuma bai karbe shi ba to hakika hujjah ta tsayu akan sa, kuma ba zaayi masa wani uzuri da jahilci ba domin hujja ta riske shi, Allah –Madaukakin Sarki- Yana cewa: [Kuma anyo wahayin wannan Alkur’ani domin in muku gargadi dashi da wanda (labara) ya kai gare shi]  daidai ne ya kasance yana rayuwa tare da musulmai ko yana rayuwa da wadanda ba musulmai ba… duk wanda Alkur’ani ya isa gare shi ta fuskar da zai fahimce shi idan yaso fahimtar, sannan bai yi aiki dashi ba, to lallai baya kasancewa musulmi, kuma ba za’ayi masa uzuri da jahilci ba.


TAMBAYA TA GOMA SHA HUDU (14):


Shin an shardanta a cikin tsayar da hujjah fahimtar hujjar fahimta mabayyaniya bayyananniya ko kuma tsaida ita kawai ya isa? Muna bukatar bayani a rarrabewa a wannan tare da ambatar dalili?


Amsa:


Wannan mun ambace shi a cikin amsar da tazo kafin wannan, cewa shi idan dalili ya riske shi daga Alkur’ani ko sunnah ta fuskar da zai fahimce shi idan ya so.. ai ya riske shi da yaren sa, kuma ta fuskar da zai fahimce shi, sannan bai juya zuwa gare shi ba kuma bai yi aiki da shi ba to wannan ba za ayi masa uzuri da jahilci ba domin ya zami mai sakaci.





TAMBAYA TA GOMA SHA BIYAR (15):


   Shin kafirtawar da Sheikhul islam ibn Taimiyyah – Allah Yyai masa rahama - yayiwa jama’ar da suke hanuwa daga bayar da ibadar zakkah -lokacin da wadanda sukayi ridda daga larabawa suka aikata wannan – saboda musawar su ga wajibci ne ko saboda hani ne kawai da rashin lazimtuwa da bayarwa ne?


Amsa:


Wannan maabota ilimi sun rarrabe bayani a cikinsa, sunce: Lallai mai hana zakkah idan yana musun wajabcin ta to wannan kafiri ne kuma za’a kashe shi irin kisan riddah, amma idan hanuwar sa saboda rowa ne alhali shi yana kudirce wajabcin ta to wannan za’a yake shi har sai ya bayar da zakkah, ba za’ayi masa hukunci da kafirci ba, sai a yake shi saboda hanuwarsa daga bada zakkah har sai an karba daga gare shi. Amma abinda aka danganta ga Sheikhul Islam Taqiyuddin Ibn Taimiyyah cewa ya kafurta su kai tsaye to ni ban tsinkayi wannan zancen ba.


TAMBAYA TA GOMA SHA SHIDA (16):


Menene hukuncin wanda ya nisantar da shari’ar musulunci da maye ta da dokokin kasa kamar dokokin Faransa, Burtaniya da sauransu, tare da sanya shi doka da ake nassantowa a cikinsa cewa hukunce-hukuncen aure da gado ayi amfani da shari’ar musulunci?


Amsa:


Wanda ya nisantar da shari’ar musulunci gaba daya sannan ya canja ta da dokokin kasa to wannan dalili ne akan cewa yana ganin halaccin wannan, domin cewa shi bai yi watsi da ita ba ya mayeta da dokokin kasa ba sai don yana ganin cewa sun fi shari’ar Musulunci, da yana ganin cewa shari’ar Musulunci itace mafi kyau da bai gusar da shari’ar Musulunci ba ya mayeta da dokokin kasa, to wannan kafirci ne da Allah -Madaukakin Sarki-.


Amma wanda ya nassanta cewa hukunce-ukuncen aure da gado ne kawai zasu kasance gwargwadan shari’ah, wannan yana yin imani ne da sashen littafi yana kafircewa sashe, yana nufin yana aiki da shari’ah a wani sashen, yana hanuwa daga ita a wani sashen, Addini kuwa baya bangarantuwa, hukunta shari’ah baya bangarantuwa, babu makawa daga dabbaka shari’a dabbakawa cikakke, ba zai dabbaka sashenta kuma ya bar sashen ta ba.


TAMBAYA TA GOMA SHA BAKWAI (17):


Menene hukuncin wanda yake fadin cewa wanda yace: Wanda yabar aiki na zahiri gaba dayan sa da abinda ake kira a wajen sashen ma’abota ilimi da jinsin aiki cewa kafiri ne; cewa wannan maganar wani sashe daga sashen Murji’ah ne suka fade ta?


Amsa:


Wannan kamar yanda ya gabata. Cewa aiki yana daga imani, aiki imani ne, wanda a bar shi zai zama ya bar imani, duk dayane ya bar aiki gaba dayan sa ne dindindin bai aikata komai ba har abada, ko kuma cewa shi ya bar wani sashen aiki ne domin baya ganin yana daga cikin imani kuma baya ganin baishiga cikin imani ba to wannan zai shiga cikin Murji’ah.  


TAMBAYA TA GOMA SHA TAWAS (18):


Shin kafirtawar da magabata –yardar Allah ta tabbata gare su- sukayiwa Jahmiyyah, kafirce ne babba mai fitarwa daga Addini ko kafirci ne da bai kai kafirci ba, abin nufi dashi tsawatarwa da kausasawa kawai?


Amsa:


Kafirtawar magabata ga Jahmiyya kafirtawa ne babban kafirci, domin su sun musanta zancen Allah –Madaukakin sarki- sunce: Zancen Allah abin halicce ne, sun kuma musanta sunayen Allah da siffofin Sa su abababen wofintarwa ne, su masu karyatawa ne ga abinda yazo a cikin Alkur’ani da sunnah na tabbatar da sunayen Allah da siffofin Sa, kuma suna kudurcewa da hululi (saukowa) kuma cewa Allah –Madaukakain Sarki- mai sauka ne a dukkan wurare, Allah Ya daukaka daga abinda suke fada. Zantukansu suna hukunta kafirci babba, don haka kafirtawar da magabata sukayi musu yana daga kafirci babba, sai dai wanda yake jahili ne mai kwaikwayo ya bisu alhalin yana zaton cewa su akan gaskiya suke kuma bai san matafiyar su ba kuma bai san hakikanin zancen su ba, to wannan lallai za ai masa uzuri da jahilci.





TAMBAYA TA GOMA SHA TARA (19):


Shin maganganun magabata da suka sakesu a kafirta ayyanannun ‘yan Jahmiyyah kamar kafirtawar da (Imam) Shafi’i yayiwa Hafs al-Fard a yayin da ya fadi halittar Alkur’ani sai Shafii yace dashi: Ka kafirta da Allah Mai girma; kamar yanda aka cirato daga al-Lalka’i cikin sharhin Usulu iitikadi Ahlis Sunnah, kamar kuma kafirtawar da akayiwa Jaham ibn Safwan da Bishril Murisy da Nazzam da Abul Huzail al’Allaf kamar yanda Ibn Baddah ya ambaci haka cikin al’Ibanatus Sugrah… ana nufin kafirta ainahin  wadannanne  ko kafirta zantuttukan su ne ba ainahin su kansu ba?


Amsa:


Wanda ya furta kafirci ko ya aikata kafirci to ya kafirta a ainahin sa, wanda ya aikata kafirci ko ya furta kuma baya daga cikin wadanda akewa uzuri da jahilci to lallai shi ya kafirta a ainahin sa, kuma zamu yi masa hukunci da kafirci.


TAMBAYA TA ASHIRIN (20):


Akwai wadansu kalamai da suke zuwa a cikin littattafan Ahlus Sunnah misali: Al’iltizam (lazimtuwa), Al’ikna’I (wadatarwa), Kufrul I’irad (kafircin bijirewa), menene ma’anar wadannan kalaman?


Amsa:


Kafirci nau’o’i ne: Akwai kafirci na bijirewa, da kafircin karyatawa, daga cikinsa akwai kafircin musawantawa, dukkan wadannan nau’o’i ne na kafirci, kafirci ba nau’i daya bane kadai nau’o’i ne da yawa. Kuma kafirci yana rabuwa zuwa kafirci babba mai fitarwa daga Addini, da kafirci karami maras fitarwa daga Addini, babu makawa daga karantar wadannan al’amuran da kuma sanin su a rarrabe, kafirci ba’a haddi daya yake ba.





TAMBAYA TA ASHIRIN DA DAYA (21):


     Menene maanar fadin Sheikhul Islam Muhammad bn Abdulwahhab –Allah Yayi masa rahma- cikin mai warwarewa na uku daga abubuwan da suke warware Musulunci:” Wanda bai kafirta mushrikai ba ko yayi kokwanto a cikin kafircin su ko ya inganta mazahabrsu to shi kamar irinsu ne?:”


Amsa:


Ai haka ne, domin ya yarda da abinda suke a kansa, kuma ya dace dasu akan abinda suke akansa, wanda bai kafirtasu ba ko ya yarda da abinda suke akansa ko ya kare su to lallai shi zai zama kafiri irin su, domin shi ya yarda da kafirci kuma ya tabbatar da shi kuma bai yi inkarinsa ba.


TAMBAYA TA ASHIRIN DA BIYU (22):


Menene hukuncin wanda yace: [Lallai mutum idan bai kafirta Nasara ba saboda rashin riskuwar ayar cikin suratul Maida {Lalle ne, hakika, wadanda suka ce: “Allah na ukun uku ne,” sun kafirta}  to shi bai kafirta har sai yasan ayar}


Amsa:


Kafirtawar Yahudu da Nasarah baya takaita akan surar Ma’idah ba, bari dai kafirta su yanada yawa a cikin Alkur’ani, kuma kafircin su zahiri ne daga zantuttukan su da ayyukan su da abinda ke cikin lattattafan su wadanda suke karantawa, misalin fadin su: Isah dan Allah ne ko fadin su lalle Allah na ukun uku ne, da fadin su lalle Allah Shine Isah dan Maryam, ko fadin Yahudu lalle Uzairu dan Allah ne, ko lalle Allah fakiri ne mu mune mawadata ko hannun Allah a daure yake… ko wanin wannan daga abinda yake samamme cikin lattattafan su wadanda ke hannayensu, to kafircin su a bayyane yake a cikin wanin Surar Ma’idah.





TAMBAYA TA ASHIRIN DA UKU (23):


Menene dalili akan halaccin sharuddan shaidawa: Cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, na daga ilimi da jawuwa da gaskiya da ikhlaasi da so da karbuwa da yakini, kuma menene hukunci cikin wanda yake cewa “Babu abin bautawa da gaskiya yana isa da fadin ta kawai ba tare da wadannan sharuddadan ba”?


Amsa:


wannan ko dai mai batarwa ne yake son batar da mutane, ko kuma jahili ne da yake fadar abinda bai sani ba. La ilaha illallhu ba lafazi ce kawai ba, bari dai ba makawa gareta daga ma’ana da kuma abinda take hukuntawa, ba lafazi ce kawai da za’a fada da harshe ba. Dalili akan haka fadin sa –tsira da amincin Allah su tabbata gare shi-: [Wanda yace la ilaha illahu  kuma ya kafirta da abinda ake bautawa ba Allah ba] , ko fadin sa –tsira da amincin Allah su tabbata gare shi- [To lallai Allah ya haramta wuta ga wanda yace babu abin bautawa da gaskiya sai Allah yana nufin fuskar Allah da wannan] , da fadin Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-: [An umarce ni da in yaki mutane har sai sun ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, idan suka fade ta sun tsare jinanen su da dukiyoyin su daga gare ni sai da hakkin ta] , sai da hakkin La ilaha illallahu… baya isuwa da fadin su la ilaha illallahu kawai idan basu lazimci hakkinta ba shine aiki da abin hukuntawar ta da sanin ma’anarta, La ilahaa illallahu ba lafazi ce kawai da ake fada da harshe ba… daga gare ta ne ake dakko wadannan sharuddan guda goma wadanda muka ambata wadanda ma’abota ilimi suka ambata.





TAMBAYA TA ASHIRIN DA HUDU (24):


Muna bukatar fassarar fadin Sa –Maduaukakin Sarki-: [Wanda ya kafirta da Allah daga bayan imaninsa face wanda aka tilasta alhali kuwa zuciyarsa tana mai nutsuwa da imani]  karanta har karshen ayah, fassara mai rarrabewa tare da bayanin hukuncin tilastawa a cikin wannan ayar?


Amsa:


Wannan ayar tana nuni akan cewa wanda ya yi furuci da kalmar kafurci yana me abin tilastawa akan ta kuma shi bai kudirce ta ba, kadai ya fade tane domin ya kubuta saboda ita daga tilastawa to lallai shi abin yiwa uzuri ne. Kamar yanda yazo a cikin [Kissar Ammar bn Yasir –Allah Ya yarda da shi- yayin da mushrikai suka tilastashi akan ya zagi Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma suka cutar da shi suka ki sakinsa har sai ya zagi Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata gare shi- sai ya furta abinda suka nemashi da shi da harshensa, sai yazo yana tambayar Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yace : Yaya kaji a zuciyar ka? Yace na samu imani da Allah da manzonSa a cikin zuciyata, sai Allah-Madaukakin Sarki- Ya saukar da: [Wanda ya kafirta da Allah daga bayan imaninsa face wanda aka tilasta alhali kuwa zuciyarsa tana nutse da imani kuma wanda ya yi farin ciki da kafirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma suna da wata azaba mai girma. Wadancan ne kafirai domin sun fifita son duniya a kan lahira] .


Idan mutum ya fadi kalmar kafirci yana mai abin tilastawa akanta yana son kubuta daga tilastawa kawai bai datar dashi da zuciyar sa ba to lallai ita sauki ne Allah yayi ga wanda aka tilastawa, wannan ta kebanta ne ga wanda aka tilastawa banda waninsa. Haka nan cikin fadin Sa: [face fa domin kuyi tsaro daga gare su da ‘yar kariya. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makoma take]  ai daga kafirai, to wannan a cikin tilastawa ne, amma a wanin tilastawa to dacewa dasu baya halatta ko binsu akan abinda suka nema na daga furta kafurci ko daga aikata kafurci. 





TAMBAYA TA ASHIRIN DA BIYAR (25):


Menene hukuncin jibintar kafirai da mushrikai? Kuma yaushe ne wannan jibintar take kasancewa kafurci babba mai fitarwa daga Addini? Kuma yaushe take kasancewa zunubi da laifi babba daga manyan zunubai?


Amsa:


Allah -Madaukakin sarki -Yana cewa: [Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku riki yahudu da nasara majibinta. Sashensu majibinta ne ga sashe. kuma wanda ya jibince su daga gare ku, to lallai ne shi, yana gare su. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai] , da kuma fadinSa –tsarki ya tabata gare Shi- [Ba za ka sami mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira suna soyayya da wanda ya saba wa Allah da ManzonSa ba, ko da sun kasance ubanninsu ne, ko diyansu ko ‘yan’uwansu, ko danginsu. Wadannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma ya karfafa su da wani ruhi daga gare Shi] , don haka adawa ga kafirai yana wajaba da kin su  da rashin taimaka musu akan musulmai, da yanke zumunci dasu ta bangaren kauna da soyayya da kin abinda suke akansa na kafirci, dukkan wannan yana wajaba akan musulmi ya yanke alaka da su a cikin sa ya kuma nisancesu,  kada ya so su kuma kada ya taimakesu akan musulmai, kuma kada yayi kariya gare su, kuma kada ya inganta matafiyar su, bari dai ya bayyana kafircin su kuma yayi kira da kafircin su da batansu ya kiyaya daga su.


TAMBAYA TA ASHIRIN DA SHIDA (26):


Mecece nasihar ku ga daliban ilimi ga wanda yake son kiyaye mas’alolin Tauhidi da shirka da mas’alolin imani da kafuric? Wadanne littattafai ne sukayi magana akan wadannan mas’alolin kuma sukayi bayani a rarrabe?


Amsa:


Wannan munyi ishara izuwa gare shi a farkon amsoshi, da cewa abin dogara a wannan (sune) littattafan magabatana gari. Ya wajaba akansa ya koma ga littattafan magabatan wannan al’umma daga shuwagabanni hudu da kafin su sahabbai da tabi’ai da masu biyo musu da karnoni abanben fifitawa, wannan samemme ne cikin littattafansu godiya ta tabbata ga Allah, a cikin littattafan imani da littattafan akidah da littattafan tauhidi masu zagayawa ababen sani daga manyan shuwagabanni Allah -Yayi musu rahama -, misali littattafan Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah, da littattafan Imam Ibn al-Kayyim, da littattafan Sheikhul Islam Muhammad bn Abdulwahhab.. Da littattafan magabata na gari.. Misali Kitabush Shar’iah na al-Ajurry, da As sunnah na Abdullahi bn Imam Ahmad, da As sunnah na al-Khallal, da misalin Kitabul Akidatul Dahawiyyah da sharhinta na Izz bn Abil Izzi… dukkan wadannan suna daga littattafan Ahlul Sunnah kuma daga akidu ingantattattu ababen gada daga magabata na gari, sai musulmi ya koma gare su. Sai dai kamar yanda muka ambata takaituwa akan mudala’ar littattafai da daukar ilimi daga su basa isa ba tare da malami ba da mai karantarwa ba, bari dai babu makawa daga haduwa da malamai, kuma babu makawa daga zama a halkokin karantarwa, ko dai ajujuwan karatu ko halkokin ilimi a cikin masallatai da majalisai na ilimi, babu makawa daga cirato ilimi daga ahalin sa ko a akidah ko wanin akidah, sai dai akidah ita tafi bukatuwa ga wannan  domin itace ginshiki, kuma domin tuntube a cikinta ba kamar kuskure da tuntube ne a waninta ba.


Dacewa na ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da alayen sa da sahabban sa baki daya.





FAHRASAR AYOYI


-    wadanda Muka basu littafi suna saninsa kamar yadda suke sanin diyansu….7


-    Lalle ne Muna sani cewa hakika, abinda suke fada yana bata maka rai. To...7


-    Idan munafukai suka je maka sai su ce:………………………………….….8


-    Suna fada da bakunan su abinda baya cikin zuciyoyin su……………...……8


-    Ka ce: Shin da Allah da kuma ayoyin Sa da Manzon Sa kuka kasance...….10


-    Kuma hakika sun fadi kalmar kafirci kuma sun……………………...…….10


-    Kuma wanda yabi Allah da takawa, Allah Zai sanya masa mafita………...10


-    Wadancan ne kafirai domin sun fifita son duniya a kan lahira,……...…….11


-    Kuma da dai sun yarda da abinda Allah Ya ba su,……………...………….11


-    To amma wadanda yake a cikin……………………………………………13


-    Kuma anyo wahayin wannan Alkur’ani domin in muku gargadi dashi..…..14


-    Wanda ya kafirta da Allah daga bayan imaninsa face wanda………..…….20


-    face fa domin kuyi tsaro daga gare su da ‘yar kariya………………...…….20


-    Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku riki yahudu da nasara majibinta....21


-    Ba za ka sami mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira………...…21





FIHRISAR HADISAI


-    Wanda ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,……………..……..13


-    To lallai Allah Ya haramta wuta ga dukkan wanda yace:…………...……..13


-    Wanda yace la ilaha illahu kuma ya kafirta da abinda………….………….19


-    To lallai Allah ya haramta wuta ga wanda yace babu………...……………19


-    An umarce ni da in yaki mutane har sai sun ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,……………………………………………………………………19





ABUBUWAN DA KE CIKI


- GABATARWA……………………………………………………………….…4


- Tambaya ta daya: Da me kafirci babba yake kasancewa ko riddah?……..……..4


- Tambaya ta biyu: Hakikanin Imani?…………………..……..…...…….……….6


- Tambaya ta uku: Shin ayyuka rukunai ne a cikin imani ko wani bangere daga shi ko sharadin cika ne gareshi…?………………….…………………………………6


- Tambaya ta hudu: Menene rabe-raben Murji’ah? ……………..………………..7


- Tambaya ta biyar: Shin sabanin ahlus sunnah da murj’iah fukaha’u cikin ayyukan zuciya ne ko gabbai?………………..…………….………………………8 


- Tambaya ta shida: Menene hukuncin wanda yabar gaba daya ayyukan zahiri, sai dai yayi furuci da shahadah kuma ya tabbatar da farillai?………...……………….9


- Tambaya ta bakwai: Game da maganar Imani furuci nr da aiki da kudurcewa yana karuwa yana raguwa…?……………….……………..……………………….9


- Tambaya ta takwas: Game da maganar cewa wanda ya zagi Allah ya zagi Manzo ba kafiri ne a Kankan sa ba…?…………………..………..………………………10


- Tamabaya ta tara: Menene hukuncin wanda yake zagin Allah da manzon Sa da addini…?…..……………………………………………………….……………..10


- Tambaya ta goma: Menene zance a cikin wanda ya kafa gumaka da kabarirrika na alfarma da kabarirrika ya gina masallatai akan su…?.........………...…………11


- Tamabaya ta goma sha daya: Shin sallah tana inganta a bayan limami da yake neman taimako da matattu kuma yake neman madadi daga su ko a’a…?..............12


- Tambaya ta goma sha biyu: Hadisan da wasu sashe suke kafa dalili dasu akan cewa wanda ya bar gaba dayan ayyuka shi mumini ne mai tauyayyen Imani…?……………………..……………………………………………………13


- Tambaya ta goma sha uku: Menene hukuncin wanda yake kiran wanin Allah alhali yana rayuwa cikin Musulmai…?...................................................................14


- Tambaya ta goma sha hudu: Shin an shardanta a cikin tsayar da hujjah fahimtar hujjar fahimta mai fadi budaddiya ko fahimtar ta kawai ya isa…………………..14


- Tambaya ta goma sha biyar: Kafirtawar Sheikhul Islam Ibn Taimiyya ga mutanen da suke hana bayar da ibadar Zakkah?…….…………….....…...………15


- Tambaya ta goma sha shida: Menene hukuncin watsi da shari’ar musulunci da maye ta da dokokin kasa koma baya?……………………………….……………15


- Tambaya ta goma sha bakwai: Barin aiki na dindindin ko barin sashen aiki domin baya ganin sa zai shiga cikin Murji’ah?………………...…………………16


- Tambaya ta goma sha takwas: Kafirtawar magabata ga Jahmiyyah?….………16


- Tambaya ta goma sha tara: Maganganun magabata cikin kafirta ayyanannun ‘yan Jahmiyya?…………………………………………..………………………..17


- Tambaya ta ashirin: Kalmomi cikin littattafan Ahlus Sunnah…?……...………17


- Tambaya ta ashirin da daya: Ma’anar fadin Sheikh Muhammad bn Abdulwahhab “wanda bai kafirta..?………………………..…………..…………18


- Tambaya ta ashirin da biyu: Kafirta yahudu da nasara bai takaita a surar Ma’idah ba…?…………………………………………………………………….18


- Tambaya ta ashirin da uku: Menene dalili akan shari’anta sharuddan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah…?………………..…………………….19


- Tambaya ta ashirin da hudu: Tafsirin fadin Sa Madaukakin Sarki (wanda ya kafirta da Allah daga bayan imaninsa…?…………………….…………………..20


- Tambaya ta ashirin da biyar: Menene hukuncin jubuntar kafirai da mushrikai…?.......................................................................................................…21


- Tambaya ta ashirin da shida: Nasiha ga daliban ilimi ga wanda ke son kiyaye mas’alolin tauhidi da shirka da mas’alolin Imani da kafirci…?…….…………….21


- Fihrisar Ayoyi………………………………………………………..………….23


- Fihrisar Hadisai………………………………………...………………………24


- Abubuwan da ke ciki……………………………………………..………….….25



 



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH