Labarai

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH





Musulunci shine miƙa wuya ga Allah Mahaliccin kasantacce kuma Mai jujjuya al'amiransa, da jawuwa gareShi dan so da kuma girmamawa, tushen Musulunci shine imani da Allah, kuma cewa Shine Mahalicci, dukkan wanda baShi ba abin halitta ne, kuma cewa Shi Shine wanda Ya can-canci bauta Shi kaɗai baShi da abokin tarayya, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, yana da sunaye kyawawa, da siffofi maɗaukaka, cika tsantsa ta Sa ce, batare da tawaya ba, Bai haifaba kuma ba'a haifeShi ba, kuma baShi da wani kini ko tamka, baYa sauka baya jikintuwa a cikin wani abu daga halittarsa.





Musulunci shine addinin Allah - Maɗaukakin sarki - wanda baYa karɓar wani addini waninsa daga mutane, shine addinin da dukkanin annabawa - aminci ya tabbata agare su - sukazo da shi.





Yana daga tushen musulunci yin imani da dukkan manzanni, kuma cewa Allah Ya aiko manzanni dan su isar da umarce-umarcensa ga bayinsa, kuma Ya saukar musu da littattafai, na ƙarshensu ya kasance (Annabi) Muhammad ne - aminci ya tabbata agare shi -, Allah Ya aikoshi da shari'ar Allah mai cikewa mai shafe shari'un manzannin da ke gabansa, Allah Ya ƙarfafeshi da Mu'ujizoji masu girma, kuma mafi girmansu al-Kur'ani mai girma, zancen Ubangijin talikai, mafi girman littafin da mutum ya sanshi, mai gijiyarwa a abinda ya ƙunsa da lafazinsa da tsarinsa, a cikinsa akwai shiriyarwa zuwa gaskiya mai sadarwa ga arziƙin duniya da lahira, shi abin kiyayewa ne har zuwa yau din nan  da harshen larabcin da ya sauka da shi, ba  a canza ko jirkita koda harafi ɗaya a cikisa ba.





Yana daga tushen Musulunci, imani da mala’iku, da imani da ranar alƙiyama, a cikinta ne Allah Zai tayar da mutane daga ƙaburburansu a ranar alƙiyama, domin yi musu hisabin ayyukan su, wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhalin shi yana mumini, to  shi yana da tabbatacciyar ni’ima a aljanna, wanda kuma ya kafirta ya aikata ayyuka munana, to yana da azaba mai girma a cikin wuta.Yana daga tushen musulunci cewa kayi imani da abinda Allah Ya ƙaddara shi na alheri ko na sharri.





Musulmai suna imani cewa (Annabi) Isa bawan Allah ne kuma manzonSa ne, kuma shi ba ɗan Allah bane; domin cewa Allah Mai girma bazaiyiwu Ya zama Yana da mata ko da ba, sai dai Allah Ya bamu labari a cikin al-Kur'ani cewa (Annabi) Isa ya kasance annabi ne da Allah Ya ba shi mu'ujizoji masu yawa, kuma Allah Ya aikoshi dan kiran mutanensa zuwa ga bautar Allah Shi kaɗai baShi da abokin tarayya, kuma Ya bamu labari cewa (Annabi) Isa bai nemi mutane su bauta masa ba, a'a ya kasance shine yake bautawa mahaliccinsa.





Musulunci addini ne mai dacewa da ɗabi'a da kuɓutattun hankula, kuma rayuka madaidaita suna karɓarsa, Mahalicci Mai girma Ya shara'antashi ga halittarsa, shine addinin alheri da tsira ga mutane baki ɗaya, baya banbance wani asali akan wani asali, ko launi akan wani launin, mutane a cikinsa madaidaita ne, wani baya banbanta a musulumnci akan waninsa sai da gwargwadan aikinsa na gari.





Yana wajaba akan kowane mutum mai hankali yayi imani da Allah Ubangiji, da musulunci (a mtsayin) addini, da (Annabi) Muhammad (a matsayin) manzo, wannan wani al'amari ne babu wani zaɓi ga mutum acikinsa domin cewa Allah Zai tambayeshi ranar al-Kiyama abisa abin da ya amsawa manzanni da shi; idan ya kasance mumini ne to rabo da tsira mai girma ya tabbata gare shi, idan kuma ya kasance kafiri ne, to taɓewa mabayyaniya ta tabbata gare shi.





Wanda yake son shiga Musulunci to ya wajaba a kansa ya ce: (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne), yana mai sanin ma’anar ta, yana kuma yin imani da ita.To da wannan ne zai zamo musulmi; sannan ya koyi sauran dokokin Musulunci a hankali a hankali, domin ya aiwatar da abinda Allah Ya wajabta shi akansa.





Dan ƙara samun bayanai: byenah.com





 





 





MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH......................................................................................





 



Posts na kwanan nan

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

MUSULUNCI Addini ne n ...

MUSULUNCI Addini ne na ɗabi'a ta asali da hankali da kuma tsira

Az Iszlám [Al-Iszlám] ...

Az Iszlám [Al-Iszlám] A Fitra (a tiszta, romlatlan, veleszületett egyistenhit), az értelem és a boldogulás Vallása