Labarai

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai.





Shin ka tambayi kanka:





Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda yake cikinsu, na halittu masu girma? Wa ya ƙera wannan ƙwararran tsari nagartacce a cikin su?





Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa'idojin sa, waɗanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta ƙwarewa tsawon waɗannan shekaru?





Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi kawai kwatsam?





Wa ya halicce ka?





Wa ya sanya wannan nagartaccan tsari a gaɓoɓi masu aiki na jikinka da jikunan sauran samammu masu rai?





Babu mutumin da zai yarda a ce da shi: Ai wannan gidan kawai ya samu ne ba tare da wani ne ya gina shi ba! Ko a ce da shi: Ai babu ita ce ta samar da wannan gidan! To ta yaya wasu daga cikin mutane za su yarda da wanda yake cewa wannan duniyar mai girma ta zo ne ba tare da Mahalicci ba?. Ta yaya mai hankali zai yarda ace da shi wannan ginin (na sama da ƙasa) wanda ke cike da ƙwarewa ya samu ne haka kawai?





Tabbas akwai wani abin bauta Mahalicci Mai tsara wannan halittar da abinda yake cikinta, shi ne kuwa: Allah - tsarki ya tabbata a gare shi Ya ɗaukaka -.





Ubangiji - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya aiko mana da manzanni, Ya kuma saukar musu da littattafai na Allah (wahayi), na ƙarshansu shi ne al-Kur'ani, wanda Ya saukar da shi ga (Annabi) Muhammad cikamakin Mmnzannin Allah, ta hanyar littattafanSa da ManzanninSa:





Ya sanar da mu kanSa da siffofinSa, da hakkinSa a kammu, Ya kuma bayyana mana hakkin mu da ya ɗorawa kansa.





Ya kuma nuna mana cewa Shine Ubangiji, wanda Ya halicci halittu, kuma Shi rayayye ne baYa mutuwa, halittu kuma suna damƙarSa ne, kuma ƙarƙashin rinjayarSane da tasarrufinSa.





Ya bamu labarin cewa daga cikin siffofinSa akwai sani, haƙiƙa Ya game ko'ina da saninSa, kuma Shi Mai ji ne Mai gani ne, babu wani abu da yake ɓoyuwa a gareShi a cikin ƙasa ko a sama.





Ubangiji! Shi ne Rayayye, Tsayayye, wanda rayuwar duk wani hallita daga gare Shi ne, Shi kaɗai, tsarki ya tabbata a gare Shi, Shi ne kuma Tsayayye wanda rayuwar kowanne halitta take tabbatuwa da shi, tsarki ya tabbata a gare Shi, Allah - Maɗaukakin sarki Ya ce:﴿اللَّهُ لا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلا نَوْمٌ لَهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ وَلا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾ {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}[Suratul Baƙarah: 255].





Kuma Ya ba mu labarin cewa Shi ne: Ubangiji ! Wanda Ya siffantu da siffofi na cika, kuma Ya azirta mu da hankula da abubuwan ji, da suke riskar abubuwan mamaki na halittarSa da ikonSa, wanda hakan yake nuna mana girmanSa da karfinSa da cikar siffofinSa, kuma Ya dasa mana kyakkyawan tunani da suke nuni akan cikarSa, ta yadda ba zaiyiwu a saffanta Shi da wata siffa ta tawaya ba.





* Ya sanar da mu, cewa Ubangiji Yana saman sammanSa, ba yana cikin halittarSa ba ne, kuma halittarSa bata shiga cikinSa ba.





* Ya bamu labarin cewa, Ya wajaba akanmu mu miƙa wuya gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shine Mahaliccin mu, Mahaliccin kowanne abu kuma Mai jujjuya shi.





Mahalicci Yana da siffofin girma, ba zai yiwu ba Ya siffantu da buƙata ko tawaya. Ubangiji baYa mantuwa baYa bacci, baYa cin abin ci, ba zai yi wu ace Yana da mata ko ɗa ba, duk wasu bayanan da suke saɓawa girman Mahalicci to ba ingantaccen wahayi bane wanda manzannin Allah - aminci ya tabbata agare su - suka zo da shi ba.





Allah - Maɗaukakin sarki - a ckin al-Kur'ani mai girma Ya ce:﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ * {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci *ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ * Allah wanda ake nufin Sa da buƙata *لَمۡ یَلِدۡ وَلَمۡ یُولَدۡ * Bai haifa ba kuma ba'a haife Shi ba *وَلَمۡ یَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ﴾ Kuma babu wani da yake kini gareShi}[al-Ikhlas: 1-4].





Idan ka kasance kana imani da Ubangiji Mahalicci… to shin ka taɓa tambayar kanka wata rana game da manufar da tasa aka halicceka? Kuma me Allah Yake nufi da mu, kuma mecece manufar samuwarmu?





Shin zai yi wu Allah Ya halicce mu sannan Ya bar mu a zube sasakai? Shin zai yi wu a ce Allah Ya halicci waɗannan halittun ba tare da manufa ko dalil ba?





A haƙiƙanin gaskiya Ubangiji Mahalicci Mai girma "ALLAH" Ya bamu labari akan manufar halittarmu, itace bautar Allah Shi kaɗai, me kuma Yake so daga garemu? kuma Ya bamu labarin cewa Shine wanda Ya cancanci a bauta maSa, Ya kuma bayyana mana ta hanyar ManzanninSa - aminci ya tabbata a gare su - ta yaya zamu bauta maSa? Ya zamu nemi kusanci gareShi ta hanyar aikata umarninSa da barin abubuwan da Ya hana ? Yaza mu sami yardarSa ? Mu kuma kiyayi uƙubarSa, kuma Ya ba mu labarin makomarmu bayan mutuwa.





Ya bamu labarin cewa ita wannan rayuwar duniyar kawai jarrabawa ce, kuma cewa tabbatacciyar rayuwa cikakkiya da sannu za ta kasance a lahira bayan mutuwa.





Ya kuma bamu labarin cewa wanda ya bautawa Allah kamar yadda Ya umarce Shi, kuma ya hanu daga abinda Ya hana shi; to yana da daddaɗar rayuwa a duniya, da dawwamar ni'ima a lahira, wanda kuma ya saɓa maSa ya kafirce maSa to taɓewa ta tabbata gareshi a duniya, da kuma dawwamar azaba a lahira.





Kuma saboda cewa mu mun san ba zaiyiwu mu tafi a wannan rayuwar ba ba tare da kowanne mutum ya sami sakamakon abinda ya aikata ba na alheri ko na sharri; (a ce) babu wata uƙuba ga azzalumai, kuma babu wata sakayya ga masu kyautatawa?





Haƙiƙa Ubangijinmu Ya labarta mana cewa rabauta da yardarSa da tsira daga uƙubarSa basa kasancewa sai ta shiga addinin Musulunci, wanda shine miƙa wuya gareShi da bauta maSa Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, da miƙa wuya gareShi ta hanyar yi maSa biyayya, da kamanta shari'arSa ta hanyar yarda da karɓa, haƙiƙa Ya labarta mana cewa baYa karɓar wani addini daga mutane idan ba Musulunci bane, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:(وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ) {Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra}[Aal Imran: 85].





Wanda ya dubi abinda mafi yawan mutane suke bautawa a yau; zai sami wannan yana bautawa mutum, wani kuma yana bautawa gunki, wani tauraro yake bautawa, haka dai, baya kamata ga mutum mai hankali ya bautawa wani sai Ubangijin talikai, Cikakke a siffofinSa, to, tayaya (abin halitta) zai bautawa abin halitta irinsa ko ƙasa da shi, wanda ake bautawa ba ya kasancewa mutum ko gunki ko bishiya ko kuma dabba!





Dukkanin addinan da mutane suke bi a yau - in banda Musulunci - Allah baZai karɓa ba, domin addinai ne da mutum ya ƙirƙira, ko addinan na Allah ne sai hannun mutum ya canja su. Amma Musulunci, shi addinin Ubangijin talikai ne, baya canjawa, littafin wannan addinin shine al-Kur'ani mai girma, shi littafi ne tsararre kamar yadda Allah Ya saukar da shi, kuma bazai gushe ba a hannun musulmai zuwa yau da harshen da aka saukar da shi ga manzo cika makakin manzanni.





Yana daga cikin tushen Musulunci kayi imani da dukkanin Manzannin da Allah Ya aiko su, kuma dukkan su sun kasance ne daga cikin mutane, Allah Ya ƙarfafe su da mu'ujuzozi, Ya aiko su domin kiran mutane zuwa bauta maSa Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya.Karshan manzanni shine (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Allah Ya aiko shi da shari'ar Allah mai cikewa mai shafe shari'o'in manzannin dake gabansa, Ya kuma ƙarfafe shi da mu'ujuzoji masu girma, mafi girman su shine al-Kur'ani zancan Allah ne Ubangijin talikai, mafi girman littafin da aka taɓa samu a tarihin mutum, mai gajiyarwa ne a abinda ya ƙunsa da lafazinsa da zubinsa, da hukunce-hukuncen sa, a cikinsa akwai shiriya ga gaskiya, wacce za ta kai ga rabauta a duniya da lahira, haƙiƙa ya sauka ne da harshan larabci.





Akwai dalilai masu tarin yawa na hankali da kuma na ilimi waɗanda suke tabbatar da abinda babu kokwanto a cikinsa, cewa shi wannan al-Kur'anin zancan Mahalicci ne - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba ace mutum ne ya tsara shi.





Yana daga tushen Musulunci, imani da mala'iku, da imani da ranar alƙiyama, lokacin da Allah Zai tayar da mutane daga ƙaburburansu a ranar alƙiyama, domin yi musu hisabin ayyukan su, wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhalin shi yana mumini, to shi yana da tabbatacciyar ni'ima a aljanna, wanda kuma ya kafirta ya aikata ayyuka munana to yana da azaba mai girma a cikin wuta.Yana daga tushen musulunci cewa kayi imani da abinda Allah Ya ƙaddara shi na alheri ko na sharri.





Addinin Musulunci tsari ne da ya game dukkanin rayuwa, yayi daidai da ɗabi'a na halitta da hankali, kuma madaidaitun rayuka suna karɓarsa, Mahalicci Mai girma ne Ya shar'anta shi ga halittarSa, kuma shine addini na alheri da rabauta ga mutane baki ɗaya a duniya da lahira, ba ya banbance ƙabila da ƙabila, ko nuna wariyar launin fata, mutane a cikinsa daidai suke, wani mutum a Musulunci baya wuce wani sai da gwargwadon aikinsa na gari.





Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:(مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِن فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰة طَيِّبَة وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ) {Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa}[al-Nahl: 97].





Yana daga cikin abinda Allah Yake ƙarfafashi a cikin al-Kur'ani cewa imani da Allah shine Ubangiji kuma abin bauta, kuma Musulunci shine addini, kuma (Annabi) Muhammad shine Manzo, kuma shiga (addinin) Musulunci abune da ya wajaba akan kowa, mutum ba shi da zaɓi, a ranar alƙiyama a kwai hisabi da sakamako; wanda ya kasance mumini mai gaskiya to ya rabauta kuma yana da sakamako mai girma, wanda kuma ya kasance kafiri to taɓewa bayyananniya ta tabbata gareshi.





Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:(... وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰت تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ، {…… Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba.وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُۥ يُدۡخِلۡهُ نَارًا خَٰلِدا فِيهَا وَلَهُۥ عَذَاب مُّهِين) Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa}[al-Nisa'a: 13-14].





Wanda yake son shiga Musulunci to abinda zai faɗa shine: (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne), yana mai sanin ma'anar ta, yana kuma yin imani da ita.To da wannan ne zai zamo musulmi; sannan ya koyi sauran dokokin Musulunci a hankali a hankali, domin ya aiwatar da abinda Allah Ya wajabta shi akansa.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA