Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai.
Musulunci addinin Ubangijin talikai ne.
Wanene Ubangijin ka?
Wannan itace mafi girman tambaya a cikin samammu; kuma shine mafi muhimmancin tambayar da sanin amsarta yake wajaba akan mutum.
Ubangijinmu Shi ne wanda ya halicci sammai da kasa, ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai ya fitar daga wannan ruwan nau’ukan‘ya’yan itatuwa da bishiyoyi abin ci a garemu da dabbobin da muke ci.Shi ne wanda ya haliccemu ya kuma halicci iyayammu, ya halicci kowanne abu, shi ne wanda ya sanya dare da rana, shi kuma ya sanya dare lokacin bacci da hutu, yini kuma lokacin neman abin ci.Shi ne wanda ya sawwake mana rana da wata da taurari da koguna, ya sawwake mana dabbobi muke ci, muke kuma anfanuwa da nononsu da kuma gashintsu.
Menene Siffofin Ubangijin Talikai.
Ubangiji Shi ne wanda ya halicci halitta, shi ne kuma wanda yake shiryar da su ga gaskiya da shiriya, shi ne wanda yake juya lamuran halittu gaba daya, shi ne yake azirtasu, Shi ne yake da mulkin duk abinda yake a Rayuwar duniya da lahira, duk wani abu to nasa ne, abinda ba shi ba to mallakarsa ne.Shi ne Rayayye wanda ba ya mutuwa kuma ba ya bacci, shi ne Tsayayye wanda dukkan rayayye ya tsayu da umarninsa ne, shi ne wanda rahamarsa ta yalwaci kowanne abu, shi ne wanda babu wani abu da yake boyuwa a gare shi, a kasa ko a sama.Babu wani abu da ya yi kama da shi, Shi kuma mai ji ne mai gani, Shi yana saman sammansa, ya wadatu da bayinsa. Halittu masu bukatuwa ne gare shi, ba ya shiga halittarsa, babu wani a halittarsa da yake shiga zatinsa, Tsarki ya tabbata agare shi.Ubangiji shi ne wanda ya halicci wannan halittar da ake gani, da dukkan tsare-tsarensa wacce ba ta canzawa, dai-dai ne tsarin jikin mutum ne ko dabba, ko kuma tsarin halittun da suke gefen mu, da ranarsu da taurarinsu da sauran abubuwan da suke tare da su.
Kuma dukkan abinda ake bautawa da ba Allah ba, to shi ba ya iya mallakawa kansa wani anfani ko (hana) cuta, to tayaya zai mallaki janyo anfani ga wanda ya bauta masa, ko zai kawar masa da cuta.
Menene Hakkin Ubangijinmu Akammu?
Abinda yake hakkin sa a kan mutane baki daya (shi ne) su bauta masa shi kadai kada su hada shi da komai, kada su bautawa wani da ba Shi ba, ko tare da Shi mutum ne ko dutse ko korama ko sandararrun abubuwa ko taurari, kada su bautawa kowanne abu, kawai su sanya ibada ga Shi kadai tsantsa wanda yake Ubangijin talikai.
Menene Hakkin Mutane Da Ubangiji Ya Dorawa Kan Sa.
Lalle hakkin mutane da Allah ya dorawa kansa idan suka bauta masa, ya yi baiwar samun kyakkyawar rayuwa wacce za su sami aminci da kwanciyar hankali da natsuwa da walwala da yarda, a ranar Alkiyama kuma ya shigar da su aljanna a cikinta kuma akwai Ni’ima tabbatacciya da dawwama ta har abada. Idan suka saba umarnin Sa kuma ya sanya rayuwarsu cikin kunci da wahala ko da sun kasance suna zaton suna cikin hutu da walwala. Alahira kuma ya shigar da su wuta wacce ba za su fita daga cikinta ba, kuma suna da azaba har abada a cikinta da dawwama ta dindindin.
Mecece Manufar Halittarmu ? kuma Saboda me Aka Haliccemu ?.
Lalle Ubangiji Mai karamci ya bamu labarin cewa Ya halicce ne don wata kyakkyawar manufa, ita ce mu bauta masa shi kadai, kada mu hada shi da komai, ya halifantar da mu domin raya kasa da kyawawan ayyuka da gyara, duk wanda ya bautawa wani da ba Ubangijin sa ba, ba Mahaliccin Sa ba, to bai san manufar halittarsa ba, kuma bai yi abinda ya kamata ba dan gane da Mahaliccin sa ba, wanda kuma ya yi barna a bayan kasa to wannan bai san aikin da aka dora masa ba.
Tayaya Zamu Bautawa Ubangijinmu ?.
Lalle Ubangiji mai girma da daukaka bai halicce mu ya bar mu haka kawai ba, kuma bai sanya rayuwarmu wasa ba, a’a ya zabi Manzanni daga cikin mutane (ya aika su) zuwa ga mutanan su, Su suka fi mutane cikar dabi’a, mafi tsarkakar su hankali da tsarkin su zuciya, sai Allah ya saukar musu da sakonninsa, ya kunsa duk abinda ya wajaba ga mutane su sani dangane Ubangiji mai girma da daukaka, da kuma tashin mutane a ranar Alkiyama ita ce ranar lissafi da sakamako.Manzanni sun isar wa mutanan su yadda za su bautawa Ubangijin su, suka kuma bayyana musu yadda tsarin ibadar yake da lokutanta da ladanta a duniya da lahira, kuma sun tsoratar da su abinda Ubangijin su ya haramta musu na abin ci da abin sha da aure, kuma suka nuna musu kyawawan dabi’u, suka kuma hana su munanan dabi’u.
Wanne ne Karbabban Addini A Wurin Allah ?
Karbabban addini a wurin Allah, shi ne Musulunci, shi ne addinin da annabawa gaba dayansu suka isar da shi, kuma Allah ba zai karbi a ranar Alkiyama wani addini da ba shi ba. Duk wani addini da mutane suka runguma-banda musulinci- to batacce ne, ba kuma zai anfani mai shi ba, zai ma kasance azaba ne a gare shi duniya da lahira.
Menene Tushen Wannan Addinin (Musulunci) Da Rukunnansa ?.
Wannan addinin Allah ya sawwake shi ga bayinsa, mafi girman rukunansa: su ne, ka yi imani da Allah Ubangiji kuma abin bauta, ka kuma yi imani da mala’ikunsa da Littattafan sa da Manzannin sa da ranar karahe, da kaddara. ka shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah , kuma (annabi) Muhammad Manzan Allah ne, ka kuma tsaida Sallah, ka kuma bada Zakkah idan kana dukiya da Zakkah ta wajaba a ciknta, ka yi azumin watan Ramadan, shi wata guda ne a shekara, ka yi Hajji domin Allah zuwa dakinsa mai alfarma wanda (annabi) Ibrahim ya gina amincin Allah su tabbata a gare shi da umarnin Ubangijin sa idan ka sami iko.Kuma ka nisanci abinda Allah ya haramta maka na shirka da kashe rai da zina da cin dukiyar haram. To idan ka yi imani da Allah ka aikata wadannan Ibadan ka kuma nisanci wadannan haramun din to kai Musulmi ne anan duniya, a lahira kuma Allah zai baka kyautar Ni’ima dawwama da kuma dawwama ta har abada a aljanna.
Shin Musulunci Addinin Wasu Mutane ne Ko Wani Jinsi?.
Musulunci shi ne addinin Allah ga dukkanin mutane, ba Fifiko a cikin shi ga wani saida tsoron Allah da aiki nakwarai, mutane daidai suke a cikin shi.
Tayaya Mutane Zasu san Gaskiyar Manzanni tsira da aminci ya tabbata a gare su ?
Mutane suna sanin gaskiyar Manzanni ta hanyoyi daban-daban, daga ciki:
Abinda suke zuwa da shi na gaskiya da shiriya hankula da kyakkyawan tunani suna karbarsu, hankula suna shaida kyawunsa, kuma wadanda ba Manzanni ba, ba za su iya zuwa da irin shi ba.
Lalle abinda Manzanni suka zo da shi, akwai gyaran addinan mutane a cikinsa, da duniyarsu, da daidaituwar lamuran su, da gina ci gaban su, da tsare addinin su da hankulansu da dukiyoyinsu da kuma mutuncin su.
Lalle Manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su ba sa neman lada a wurin mutane akan nuna alheri da shiriya da suka yi, kawai suna jiran ladansu ne a wurin Ubangijin su.
Lalle abinda Manzanni suka zo da shi gaskiya kuma tabbas ne, kokonto bai haduwa da shi, kuma ba ya warware juna, ba ya rikitarwa. Kowanne Annabi yana gasgata annabawan da suka riga shi, kuma yana kiran (mutane) da irin abinda suka yi kira izuwa gareshi.
Lalle Allah yana karfafar Manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su da ayoyi bayyananu da mu’ujizozi masu karfi wadanda yake tafiyar da su a hannayansu (Manzanni), domin su kasance shaidu na gaskiya akan su Manzanni ne daga wurin Allah, mafi girman mu’ujizozin annabawa ita ce Mu’ujizar wannan Manzon cikamakin (annabawa) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ita ce kuma Alkur’ani.
Mene ne Alkur'ani Mai girma?
Alkur’ani mai girma shi ne Littafin Ubangijin talikai, shi ne zancan Allah da Mala’ika Jibrilu aminci ya tabbata a gare shi, ya saukar da shi ga Manzo (Annabi) Muhammad. Acikinsa akwai duk abinda Allah ya wajabtawa mutane saninsa, dangane da Allah, da Mala’ikunsa da Littattafansa da Manzannin sa da ranar karshe da kaddara alheri ce ko sharri.A cikin sa akwai ibadu na wajibi, akwai abubuwan da aka haramta da ya wajaba a kiyaye su, akwai kyawawan dabi’u da munana, da duk abinda yake da alaka da sha’anin addinin mutane, duniyar su da lahirarsu, shi Littafi ne mai gajiyarwa, Allah ya kalubalanci mutane da su zo da irinshi, Shi littafi ne da aka tsare shi har zuwa ranar Alkiyama, da harshan da ya sauka da shi, ba’a rage wani harafi daga gareshi ba, ba’a kuma canza kalma ba.
Menene Dalilin Tashi Da Lissafi ?
Shin ba ka ganin kasa matacciya (bushasshiya) babu wata rayuwa Tare da ita, idan aka saukar mata da ruwa, sai ta girgiza kuma ta fitar da dukkan tsire mai ban sha’awa, lalle wannan da ya rayata mai iko ne akan ya rayar da matattu.Lalle Wanda ya halicci mutum daga maniyyi na ruwa wulakantacce, mai iko ne akan ya tayar da shi a ranar Alkiyama, sai ya yi masa lissafin (ayyukansa) sai kuma ya sakanka masa cikakken sakamako, idan alheri ne to ya ga alheri, idan kuma sharri ne ya ga sharri.Wanda ya halicci sammai da kasa da taurari mai iko ne akan ya sake halittar mutum, domin sake mayar da halittar mutum Karo na biyu shi ya fi sauki akan halittar sammai da kasa.
Menene Zai Kasance A Ranar Alkiyama.
Ubangiji mai girma da daukaka, zai tashi halittu daga kaburburansu, sannan ya yi musu sakamakon ayyukan su, wanda ya yi imani ya gasgata Manzanni zai shigar da shi aljanna, wacce take da ni’ima dawwamamma da mutum bai taba tunaninta ba, saboda girmanta, wanda ya kafurta zai shigar da shi wuta wacce take azaba ce ta har abada, wacce mutum bai taba tunaninta ba, idan aka shigar da mutum aljanna ko wuta to shi ba zai mutu ba har abada, shi madawwami ne da zai dawwama a cikin ni’ima ko azaba.
Idan mutum yana son shiga Musulunci to ya zai yi ? Shin akwai wani abu ne da ya wajaba ya yi ko wasu mutane da za su ba shi izini?
Idan mutum ya san cewa addinin gaskiya shi ne Musulunci, kuma shi ne addinin Ubangijin talikai, to ya wajaba a gare shi ya yi gaggawar shiga Musulunci, domin mai hankali Idan gaskiya ta bayyana gare shi to ya wajaba a gare shi ya yi gaggawar zuwa gare ta, kada ya jinkirta wannan al’amarin.Wanda yake son shiga Musulunci, babu wani haraji da zai biya, kuma ba’a ce hakan dole sai agaban wani ba, saidai idan ya kasance a gaban wani Musulmi ko a wata cibiyar addinin Musulunci, to ya zama alheri kan alheri, domin ya ishe shi ya ce: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lalle Muhammad manzan Allah ne. yana mai sanin ma’anarta kuma yana mai imani da hakan, to da haka ne zai zamo Musulmi, sannan sai ya koyi sanin sauran dokokin addinin Musulunci, a hankali a hankali domin ya tsayu akan abinda Allah ya wajabta masa.