HUKUNCIN JININ HAIHUWA
( JININ BIKI)
Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai,
tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin
tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya.
Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jerin
hukunce hukuncen jinin biki wanda ake kira jinin haihua wanda yake
da izinin Allah bayanshi za mu kawo a wannan karon bayan da
abayanan da suka gabata muka kawo bayanai akan jinin al'ada.
Menene Jinni Biki: Jinine da yake fitowa daga mahaiffa ta
sanadiyyar haihuwa. Kenan shi jinin biki jinine da yake da alaka da
haihuwa, idan mace taga jini kwana daya ko biyu kafin haihuwa to
shima malamai suna lissafashi cikin jinin haihuwa.
Mafiyawan Kwanakinsa: Mafi yawan kwanakin da macan data
haihu zata ga jinin haihuwa malamai sun karawa juna sani, wadansu
sukace kwanaki ar'bainne (40), wadansu kuma sukace kwanaki
sittinne (60) kamar yadda mai Akhdari ya bayyana. Sabanin na al'ada
shi kwanaki goma sha-biyarne.
Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to zata jira kwanaki
arba'in, ko sittin, idan ya dauke a kwanakin shikenan sai ta yi
wankan tsarki na daukewar jinin haihuwa ta ci gaba da sallah da kuma
sauran ayyuka na ibada, idan kuma bai daukeba to sai a nemi magani
ya zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da ibada, idan
kuma jinin ya dauke kafin kwanakin kamar ya dauke ranar da aka yi
haihuwar to annan ma zata yi wankana ta ci gaba da sallah, laifine
maigirman gaske mace jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin
sallah wai sai ta yi arba'in wannan ba tsari bane na addinin musulunci,
domin tsarin musulunci dazarar jinin yananan kafin kwanaki arba'in to
dazarar ba za'a yi sallah ba, amma dazarar jini ya dauke ko kafin
sunane to dazarar za'a ci gaba da sallah, sai a kiyaye.
Imam Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi ijima'i tun daga
Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan
cewa lalle mace mai haihuwa zata bar salla tsawon kwanaki arba'in sai
dai idan ta ga tsarki kafin hakan (kafin kwanaki arba'in din) sai ta yi
wanka ta kuma yi sallah.
Idan mace ta yi bari sai ya zamana halittar mutum ta bayyana a
barin kamar ace ga tsarin halittar ba wai gudan jini bane ya zamana
4
kuma akwai jini day a zuba to anan tana da hukuncin jinin biki jinin
haihuwa, gwar gwadon kwanakin da asune ahalittar take bayyana a
ciki sune watanni ukune galibi ammadai mafi karanci sune kwanaki
tamanin (80).
Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta yadda halittar
mutum bata bayyanaba to ba'a la'akari da wannan jinin da ya zubo,
saboda haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar azumiba saboda
jinin domin bata da hukuncin jinin biki.
Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan kwanakin da aka yi
bayaninsu to zata yi wankane ta kuma yi sallah ko da jinin ya daukene
a ranar da aka yi haihuwar, to idan jinin ya dauke kafin wadancan
kwanakin sai kuma ya dawo to sai mu tsaya mu gani idan tsakani
daukewar da dawowar ya kai kwanaki goma sha-biyar zuwa abinda ya
yi sama to wanda ya dawodin jinin al'adane bana biki bane, amma
idan tazarar batakai kwanaki goma shabiyarba to jinin da ya dawo
cikon jinin haihuwane.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai Jinin Bikiba: Mu sani
dukkan abuwan da jinin al'ada yake hanawa ayiwa mai al'ada to jinin
haihuwama yana hanawa a yi wa mai biki, haka namma abinda jinin
al'ada yake hanawa mai al'adar ta yi to jinin haihuwama yana hanawa
ta yi, kamar: Saki, saduwa, taba Alkur'ani, zama a masallaci dadai
sauransu kamar yadda bayani ya gabata a jinin al'ada.
Haka namma kamar yadda ya halatta mai al'ada ta yi kunzugu
megidanta ya shasshafata ya taba ko ina a jikinta in banda daga
cikibiya zuwa gwiwa to haka namma ya halatta ga mai jinin haihuwa.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai da suka gabata
ya bayyana a fili cewa al'amarin jinin haihuwa ba abune da za'a yi
wasa akansaba, watakila hankali ya tafi kan bukukuwa suna maijego
kuma bata sallah kuma ga shi jinni ya dauke, kuma mun fahimci
munin tsohuwar al'adar nan na cewa maijego sai ta yi arba'in kafin ta
fara sallah ashe al'amari da bashi da alaka da addinin.
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu