DA SUNAN ALLAH MAI MATUKAR RAHAMA DA
MATUKAR JIN KAI
TAKAITACCEN BAYANI GAME DA MUSULUNCI
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin talikai, sannan salati da taslimi ga shugaban
manzanni; Annabinmu MUHAMMADU, hada da gabadayan alayensa da sahabbansa. Bayan
haka.
Shi dai MUSULUNCI, shi ne sakon Allah na karshe - daga jerin sakwanninSa - zuwa
gabadayan al’umma, wanda Ya saukar da shi ga cikamakon annabawanSa; MUHAMMADU
DAN ABDULLAHI, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
MUSULUNCI shi ne addinin gaskiya wanda Allah ba Ya karbar wani addini daga wani mahaluki
in ba shi ba. Kuma, hakika Allah Ya sanya shi addini sassauka da ba wata wahala a cikinsa;
don bai wajabtawa mabiyansa abin da ba za su iya ba, bai kuma dora masu abin da ya fi
karfinsu ba.
Hakanan, MUSULUNCI addini ne da kadaita Allah ne tushensa, rahama ruhinsa, gaskiya
takensa; ya tsaya a kanta tsayin-daka, kamar yadda ya ke cike makil da adalci, zuwa gareshi
yake kira, kuma a kansa yake kaiwa yake komowa.
Harwalau, MUSULUNCI shi ne addinin nan mai girma wanda yake fuskantar da bayin Allah
zuwa ga duk wani abu mai amfani a garesu a addininsu da duniyarsu, yake kuma gargadinsu
daga duk wani abin da yake mai cutarwa ne a garesu a addininsu da rayuwarsu.
Haka zalika, MUSULUNCI shi ne addinin da Allah Ya gyara akidu, da halaye, da rayuwar
duniya da ta lahira da shi. Da kuma shi ne ya gyara tsakanin soye-soyen ran da suke a
rarrabe, da zukatan da suke nesa da juna. Ta haka ne ya tseratar da su daga duffan bata
zuwa hasken shiriya, ya kuma yi masu ja-gaba zuwa hanya madaidaiciya.
Sannan - bayan dukkanin abubuwan da suka gabata - MUSULUNCI shi ne tsayayyen addini,
wanda aka kyautata shi matuka gaya cikin kafatanin labarurrukansa, da daukacin hukuncehukuncensa.
Babu wani labari da ya bayar sai da gaskiya, kuma ba bu wani hukunci da ya yi
sai da alheri da adalci, daga ingantattun akidu, da kyawawan ayyuka, da halaye mafifita da
ladubba madaukaka.
MANUFAR SAKON MUSULUNCI
Manufar sakon musulunci ita ce tabbatar da wadannan abubuwa:
(1) Sanar da mutane Ubangijinsu (mahaliccinsu) ta hanyar ilmantar da su sunayenSa
wadanda suke iyaka ne wajen kyau, da sifofinSa wadanda suke sun kai kololuwa wajen
daukaka, da ayyukanSa cikakku.
(2) Kiran bayin Allah zuwa bautar Allah Shi kadai, ba shi da abokin tarayya (wato su aikata
abubuwan da ya wajabta masu su kuma bar wadanda ya hane su). Kuma wannan bauta ce
kadai za ta gyara masu duniyarsu da lahirarsu.
2
(3) Tunatar da su halinsu, da makomarsu bayan mutuwarsu, da kuma abubuwan da za su
gamu da su a kaburburansu, da kuma lokacin tashinsu daga cikinsu ranar kiyama suna
rayayyu, hada da lokacin yi masu hisabi, da kuma tuna masu makomarsu cewa dayan biyu
ce: ko dai aljanna ko wuta.
GINSHIKAN MUSULUNCI
Ginshikan musulunci da suka fi muhimmanci a takaice su ne:
GINSHIKI NA FARKO: AKIDA
Wato imani da jiga-jigan imani guda shida:
JIGO NA FARKO: IMANI DA ALLAH
Wannan kuma ya kunshi abubuwa masu zuwa:
(1) IMANI DA RUBUBIYYAR ALLAH
Wato imani da cewar ba wani ubangiji, mahalicci, mamallaki, mai gudanarwa da sarrafa
al’amuran bayinsa sai shi.
(2) IMANI DA ULUHIYYAR ALLAH
Wato imani da cewa Shi kadai ne abin bauta na gaskiya; duk wani abin bauta ba shi ba,
karya ne.
(3) IMANI DA SUNAYEN ALLAH DA SIFOFINSA
Wato imani da cewa tabbas Allah Yana da sunaye masu matukar kyau, da cikakkun sifofi
masu matukar daukaka, a tabbatar masa da su kamar yadda suka zo a Al-Kur’aninSa da
sunnar manzonSar.
JIGO NA BIYU: IMANI DA MALA’IKUN ALLAH
Mala’iku manyan bayi ne da Allah Madaukakin Sarki Ya halicce su, Ya kuma dora masu
ayyuka daban-daban, su kuma suka mika wuya gareshi, suna masu yi masa biyayya, kamar
yadda suke bauta masa ba-dare-ba-rana.
Daga cikin wadannan Mala’iku akwai:
1- JIBRILU, wanda aka wakilta wajen sauko da wahayi, yana sauko da shi daga Allah zuwa
wanda Allah din Ya so na daga AnnabawanSa da ManzanninSa.
2- MIKA’ILU; wanda a ka wakilta wajen ruwa da tsirrai.
3- ISRA’FILU; wanda a ka wakilta wajen busa kaho lokacin da komai da kowa zai mutu, da
lokacin tashinsu daga kaburburansu ranar kiyama.
4. MALAKUL MAUTI (MALA’IKAN MUTUWA); wanda a ka wakilta wajen karbar ran duk wanda
zai mutu.
JIGO NA UKU: IMANI DA LITTATTAFAN ALLAH
3
Ba shakka Allah Mai matukar daukaka da buwaya Ya saukar da littattafai ga manzanninSa.
Duk wata shiriya, da alheri, da gyara suna cikinsu.
Wadanda muka sani daga cikin wadannan littattafai su ne:
1. ATTAURAT; Saukakken littafin Allah zuwa Annabi MUSA r kuma shi ne littafin Bani Israa’ila
mafi girma.
2. AL-INJIL; Saukakken littafin Allah zuwa Annabi ISA r
3. AZZABUR; Wanda Allah Ya bai wa Annabi DAWUD r
4. SUHUFU IBRAHIM; Na Annabi IBRAHIM r
5. ALKUR’ANI MAI GIRMA; Littafin da Allah Madaukakin sarki Ya saukar da shi zuwa
Annabinmu MUHAMMADU r, karshen annabawan Allah, sai Allah Ya shafe daukacin littattafan
da suka gabata da wannan Al-Kur’ani, kamar yadda Ya yi alkawarin kare shi; don kuwa zai
wanzu hujja a kan gabadayan halitta har zuwa ranar kiyama
JIGO NA HUDU: IMANI DA MANZANNI
Ba shakka Allah Madaukakin Sarki Ya aika manzanni zuwa bayinSa. Na farkonsu dai shi ne
Annabi NUHU r, na karshensu kuma Annabi MUHAMMADU r.
Gabadayan manzannin Allah mutane ne, ‘yan Adam; halittarsu aka yi; ba su da wani abu
daga cikin abubuwan da Allah Ya kebanta da su (kamar yin arzuki, ko ruwa, rayawa ko
matarwa ... d.ss) domin su bayi ne daga bayin Allah, Allah Ta’ala Ya girmama su da aiko su
da Ya yi da sakonSa.
Allah Madaukakin Sarki Ya rufe aiko da sakwanninSa da sakon da Ya aiko MUHAMMADU r da
shi, Ya kuma aiko shi zuwa daukacin mutane. Babu wani annabi bayansa.
JIGO NA BIYAR: IMANI DA RANAR LAHIRA
Ranar lahira ita ce ranar kiyama da ba wata rana bayanta. Ranar da Allah zai tashi mutane
daga kaburburansu suna rayayyu, don wasu su wanzu a gidan ni’ima (ALJANNA) wasu kuma
a gidan azaba mai matukar radadi (WUTA).
Imani da ranar lahira shi ne: Imani da duk abubuwan da za su kasance bayan mutuwa, daga
tambayar kabari, da ni’imarsa da azabarsa, da kuma duk wani abu da zai kasance bayan
wannan hali, kamar raya matattu da tashinsu daga kaburburansu, da hisabi, har dai a kai ga
shiga Aljanna ko Wuta.
JIGO NA SHIDA: IMANI DA KADDARA
Imani da kaddara shi ne mutum ya yi imani da cewa hakika Allah Ya kaddara duk wasu
abubuwa da za su kasance tun kafin kasancewarsu, ya kuma samar da daukacin halittu
kamar yadda ya rigaya a iliminSa, kuma yake kunshe a cikin hikimarSa.
Dukkanin abubuwa sanannu ne kuma rubutattu a wurin Allah Ta’ala, shi Ya so samuwarsu,
kuma shi Ya samar da su.
GINSHIKI NA BIYU: JIGAJIGAN MUSULUNCI
4
Shi dai musulunci ginannen addini ne daga wasu jigajigai guda biyar, mutum ba zai zama
musulmin gaskiya ba sai ya yi imani da su gabadaya da zuciyarsa, yana mai aikata su da
gabbansa.
WADANNAN JIGAJIGAI SU NE
JIGO NA FARKO: KALMAR SHAHADA
Wato:
شهادة ألا إله إلا الله وأن محمداً رسول الله
“SHAHADATU AN LA ILAHA ILLA ALLAH, WA ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH”. Shahada
ita ce mabudin musulunci, kuma tushensa da a ka a za harsashinsa a kanta.
Abin da a ke nufi da الإله shi ne abin da a ke bautawa.
MA’ANAR: شهادة ألا إله إلا ا لله “LA ILAHA ILLA ALLAH” Babu wanda ya cancanci a bauta masa
sai Allah Shi kadai, Shi ne abin bautawa na gaskiya, kuma duk wani abin bautawa ba shi ba,
karya ne, kuma shirme ne.
MA’ANAR: شهادة أن محمدا رسول ا لله “SHAHADATU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH” Ita
ce: Gaskata MUHAMMADU MANZON ALLAH r cikin duk abin da ya fada, da aikata duk abin da
ya ce a yi, da barin duk abin da ya ce a bari, kar kuma a kuskura a bautawa Allah sai da abin
da ya shar’anta.
JIGO NA BIYU: SALLOLI
Salloli ne guda biyar, kowa ce da lokacinta. Allah Ya yi horo da su don bayi su ba shi
hakkinSa, su kuma gode ni’imominSa. Kamar yadda ta ke wata kullalliyar alaka ce tsakanin
musulmi da ubangijinsa, da ya ke kiransa a cikinta, ya ke kuma ganawa da shi.
Hakanan, Allah Ya shar’anta su don su hana musulmi aikata alfasha da miyagun ayyuka.
Bayan haka, alherin addini da gyaran imani, da ladan Allah na duniya da lahira duk Allah Ya
rataya su da wadannan salloli. Ka ga musulmi ya samu abin da zai ba shi jin dadin duniya da
na lahira; mutane su na cikin damuwa a zukatansu da jikkunansu, shi kuwa garau ba abin da
ya dame shi, kullum ya na cikin walwala da annashuwa.
JIGO NA UKU: ZAKKA
Zakka ita ce sadakar da wanda ta wajaba a kansa ya ke bayar da ita duk shekara ga
wadanda suka cancance ta kamar fakirai da shauran wadanda ya halatta a ba su.
Zakka ba ta wajaba a kan fakiri tun da bai mallaki gwargwadon abin da shari’a ta kayyade za
a fitar masa da zakka ba (wato NISABI). Don haka tana wajaba ne a kan mawadata.
Allah Ya wajabta masu ita don kammala masu musuluncinsu da kyautata yanayi da
halayensu, da kiyaye su, su da dukiyoyinsu daga masifu da bala’ai, da kuma tsarkake su daga
zunubai. Hakannan, don share hawayen fakirai da mabukata, da kula da manyan
masalahohinsu, wadanda rashinsu ya ke ci wa kowannensu tuwo a kwarya.
Tare da duk wadancan abubuwan da a ka ambata za ka ga abin da a ka ce mawadatan su
bayar, bai fi cikin cokali ba in ka kwatanta da dukiya da arzukin da Allah Ya yi masu.
5
JIGO NA HUDU: AZUMI
Wato azumtar watan Ramalana mai albarka; watan tara a jerin watannin shekarar hijira.
A cikinsa musulmi su na haduwa kwansu da kwarkwatarsu, su bar manyan sha’awowinsu da
rana; ba ci, ba sha, ba saduwa da iyali (tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana).
Kuma Allah Madaukakin Sarki, Yana musanya masu wadancan abubuwa da suka bari daga
falalarSa, da ihsaninSa; wato Ya cika masu addininsu, da imaninsu, Ya kuma kankare masu
zunubansu, Ya kuma daga darajojinsu, da dai shauransu na daga manyan alheran duniya da
na lahira da Ya rataya su da azumi.
JIGO NA BIYAR: HAJI
Haji shi ne zuwa dakin Allah Mai girma (da ke Maka), a wani lokaci takamaimai don gudanar
da wasu ayyukan ibadu na musamman. Allah Madaukakin Sarki Ya farlanta haji ga mai iko
sau daya kacal a rayuwarsa gabadaya.
A lokacin aikin haji ne daukacin musulmi su ke yin tururuwa su hadu - daga duk fadin duniya
- a fiyayyaun wurare a bayan kasa, suna masu bautawa ubangiji daya, suna sanye da kaya iri
daya, ba bu bambanci tsakanin shugaba da talaka, babu bambanci tsakanin mawadaci da
mabukaci, babu bambanci tsakanin fari da baki.
Haka, za su yi dafifi gabadaya don gabatar da wasu iyakantattun ibadu, alal misali tsayuwar
arfa, dawafi (wato zagaya Ka’aba madaukakiya alkiblar musulmi), sa’ayi (wato kai-kawo
tsakanin dutsen Safa da dutsen Marwa). Wasu ke nan daga cikin ibadu mafiya girma da a ke
gabatarwa a wadannan wurare masu albarka.
Hakika Allah ne kadai Ya san dumbin alfanu na addini da na duniya da aikin haji ya tattaro;
don ba za su kirgu ba.
GINSHIKI NA UKU
Sannan hakika musulunci ya tsara rayuwar mabiyansa daidaikunsu da jama’unsu da abin da
zai tabbatar masu jin dadin duniya da na lahira.
DON KUWA ya halatta masu aure ya kuma kwadaitar da su yinsa, ya kuma haramta masu
zina da luwadi, da duk sauran ayyukan assha.
SANNAN ya wajabta masu sada zumunta, da tausayin fakirai da musakai da kula da su. Ya
wajabta, ya kuma kwadaitar da su da siffatuwa da duk wani kyakkyawan hali ya kuma
haramta hada da kada akalarsu daga duk wani mummunan hali.
Sannan ya halatta masu neman na-kansu, su nemi halaliyarsu, ta hanyar kasuwanci, ko
kodago, da makamantansu. Ya kuma haramta masu riba, da duk wani haramtaccen ciniki,
kazalika duk wani abin da akwai algus ko garari a ciki.
Hakanan ya kula da bambancin mutane wajen kiyaye tsare-tsare da dokokinsa, da kiyaye
hakkokin wasu, haka ce ma ta sa ya shar’anta wasu ukubobi masu tsawatarwa (wanda duk a
ka zartarwa da daya daga ciki ya bar sha’awar kuma aikata laifin da ya janyo masa ita, kai!
waninsa ma ba zai yi tunanin aikatawa ba).
Wasu ukubobin sun shafi keta hakkokin Allah Madaukaki kamar ridda (yin abin da zai fitar da
mutum daga musulunci), da zina, da shan giya. Wasu kuma sun shafi daukacin nau’oin
ta’adda ga hakkokin mutane, kamar kisan-kai ko sata ko kazafi (zargin kamamme ko
kamammiya da zina ba tare da shedu ba), ko yin ta’adda da duka, ko duk wata cutarwa.
6
Hakika, duk wanda ya yi duba da idon basira zai ga kowace ukuba ta dace da laifin da a ka
shar’antata dominsa, don zai ga hukunci ne tsaka-tsaki (ba sako-sako, ba kuma shige-gonada-
iri).
Bugu-da-kari, musulunci ya tsara ya kuma tantance alakar da ke akwai tsakanin
shuwagabanni da talakawansu, haka ce ma ta sa ya wajabtawa talakawa bin
shuwagabaninsu cikin duk abin da ba sabon Allah ba ne, ya kuma haramta masu tawaye da
fito-na-fito da su, saboda kanana da manyan barnace-barnacen da hakan ke haifarwa.
A karshe, zai yiwu mu ce ba wani shakku ko tababa kan cewar musulunci ya kunshi gini da
samar da sahihiyar alaka hada da ingantaccen aiki tsakanin bawa da ubangijinsa, da tsakanin
mutum da ragowar mutanen da suke kewaye da shi a cikin dukanin al’amura na yau da
kullum. Ba wani alheri na daga halaye da mu’amaloli sai ya nuna wa al’umma ya kuma
kwadaitar da su don su aikata. Hakanan babu wani sharri a cikin halaye da mu’amaloli sai ya
gargadi al’umma ya kuma hana su aikata shi. Hakika wannan yana bayyana mana kuru-kuru
cikar wannan addini da kyawunsa ta kowace fuska.
DUKKANIN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI
FASSARAR : MUHAMMAD NURA ABDULLAHI