Labarai

ABUBUWAN DAKE KARYA


ALWALA





ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA


Shinfida: Lalle wannan babi yana da matukar


muhimmanci, domin bayan da kasan alwala to


ya kamata kasan abin da ke warwareta, akan


haka ya ka yiwa kanka hukunci idan zaka yi


sallah ko abinda dole sai da alwala ake yinsa,


saboda haka yana da matukar kyau mu kula da


wadannan hukunce-hukunce. Allah ya yi mana


jagora.


Abubuwan da suke bata alwala sunkasu


kashi biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi anan


shine, akwai abinda shi karankan sa yake bata


alwala to wannan shi ake kira Hadasi


(Al'ahdaas). Akwai kuma wanda shi karankan sa


bai warware alwala amma zai kai ka ga abinda


yake warware alwalar to wannan shi ake kira,


Sabuban Hadasi (Asbabul Ahdas).


To shi hadasin wato abinda yake karya


alwala da karankansa, abubuwane guda


shidane, hudu daga cikinsu suna fitane ta gaba,


sune kuma; Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi da kuma


Maniyyi. Wadannan idan suka faru ko dayansu


ya faru to tsarki kawai za'a yi a sake alwala in


banda maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya


bata alwala sai kuma anyi wanka.


4


Sai kuma guda biyu da suke fita daga


dubura, sune kuma; Bayangida da kuma tusa.


Amma shi bayan-gida tsarki za'a yi sai a sake


alwala, sabanin tusa wacce take ita ba'a yi mata


tsarki alwala kawai za'a sake.


Sai kuma abubuwan da suke sabubbane na


hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai,


amma su wadancan da zarar ya diga komai


kankantarsa to ya karya alwala inbanda mai


fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa


sune;


(1) Bacci: Shi bacci a nan ya kasu kashi


hudu;


(a) Dogon bacci mai nauyi, kai tsaye wannan


ya karya alwala.


(b) Takaitaccan bacci mai nauyi, shi ma ya


karya alwala.


(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai


karya alwala ba.


(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala


amma anfi so a sake ta.


Ma'aunin da ake auna bacci da shi domin a


gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shine;


Idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to


baccinka bai yi nauyi ba, amma idan baka san


wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to baccin


ya yi nauyi. Kenan idan kuna fira sai amma


5


kana gyangyadi sai da ka farka sai kace; ina


wane? Ko; wane yaushe ka zo? To kasan


baccinka ya yi nauyi, Allah ya sa mu dace.


(2) Gushewar Hankali: Idan hankalin mutun


ya gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma


ko maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan


idan mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko


kuma suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a


asbiti ko kuma ya sha ta yi Marisa-ta sha kafso


to alwalar ko wannensu ta karye.


(3) Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi


al'aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba


al'aurarsa bawai ta samani riga ko wandoba ko


kuma wani kyalleba to malamai sun karawa


juna sani kan makomar al'walarsa, wadansu


suke ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma


suka ce idan ya tabane domin ya ji dadi to ta


karye amma idan ba wai ya yi hakanne domin


ya ji dadi ba alwalarsa nanan, wannan maganar


kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai


sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al'aurarsa


ba kai tsayeba ko dai ta saman wando ko


saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa


nanan daram.


(4) Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji ba alwalarsa ta karye, haka kuma al'amari yake idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta ji


6


dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye, malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu; (a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji dadin to alwalar ta karye. (b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma ya ji dadin to ta karye. ( c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji da din ba to alwalar ta karye. (d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma bai ji dadinba to alwalarshi tanan daram. Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya kawosu. Mu sani wadannan bayanai sun shafi macema idan ita ta yi. Akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akan suna karya alwala ko basa karyawa?, wadannan kuma sune: (5) Shakka Akan Hadasi: Idan mutum ya tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokwanto ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan bashi da tabbas? Wasu malamai sukace; Ai da ya yi kokwanto alwalarsa ta karye domin ba'a sallah da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma suke: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai daga bayane yake shakka to ai shakka bata ture abinda yake dahir, saboda haka sukace alwalar nanan, Allah shine masani.


7


(6) Ridda: Shine mutum musulmi ya kafirta (Allah Ya tsaremu). Wadansu malamai sukace da zarar ya bar musulunci to da zarar alwalar ta karye, wasu malaman kuma sukace; A'a, ai ayyukansa da ya yi ba za su baciba sai in ya mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi yafi. Alwala bata baci idan mutum ya yanke farce (Kunba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko anyi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko kuma tuntube har jini ya fita duk alwala bat abaci saboda wadannan, ko mace ta shafi gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu sunce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin fitsari ko tusa ko bayan gida abinda musulunci ya karantar shine mutum ya je ya biya wannan bukatar ta shi tukunna, maimakon ya matse.


Kammalawa: Alwala tana da muhimmanci matuka saboda haka a kiyayeta a san kuma abinda yake warwareta, kuma wannan yake nuna mana cewa tunda har alwala za'a ce akwai abubuwan da suke warwareta dudda ga laima a jikin mutum amma ace alwalarsa ta warware to lalle yana da kyau musan kuma abubuwan da suke warware musulunci domin kullun mutum


8


ya dinga ba addininsa kariya ta yadda kada ya


warware, Allah yak are mana addinimmu, amin.


Rbutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA