Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 2


Aqidar


‘Yan Shi’a


dangane da


Sahabbai


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


‘Yan Shi’a suna qudure gaba da qiyayya mai tsanani da jafa’i da


nunqufurci da mugun alkaba’i ga Sahabban Annabi (SAW), Allah ya yarda


da su baki xaya. Littafansu na da, da na yanzu, suna cike da mummunan


suka da zagi da cin zarafi da shiga irili ga waxannan zavavvun bayin Allah


waxanda Allah ya zave su a matsayin waziran Manzonsa don su taimaka


masa iyar da aikensa.


Sahabbai Sun Yi Ridda!!


‘Yan Shi’a suna qudure cewa Sahabbai baki xayansu sun yi ridda


kuma sun kafirta sai kaxan daga cikinsu. Babban malaminsu a fannin


ruwaya, wanda suke xaukar sa kamar yadda muka xauki Bukhari a fannin


Hadisi, watau Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, ya karvo ruwaya daga


Abu Ja’afar (Imamin Shi’a na biyar) wai ya ce, “Mutane baki xaya sun yi


ridda bayan Annabi (SAW) sai mutum uku kawai. (Mai ruwaya ya ce) sai


na ce: Su waye mutum ukun? Ya ce: Miqdad binul Aswad da Abu Zarrin


Algifari da Salman Alfarisi.”1


Amma mene ne dalilin wannan tsatssauran hukunci a kan zavavvun


halitta bayan Annabawa da Manzanni? Mene ne dalilin da ya sa ‘yan Shi’a


suke kafirta Sahabbai? Dalilan guda biyu ne rak, ba daxi ba ragi. Na xaya


shi ne faxinsu cewa wai Manzon Allah (SAW) ya yi wasiya cewa Ali binu


Abi Xalib(RA) ne zai zama khalifa a bayansa amma sai Sahabbai suka qi


qemadagas su zartar da wannan wasiya. Maimakon haka sai suka naxa


1 A duba Alraudatu minal Kafi na Kulaini, Darul Kutubil Islamiyya, Tehran-Iran, ba tarihi, mujalladi na 8,


shafi na 245-246.


3


Abubakar ya zama khalifa kuma daga bayansa suka naxa Umar da Usman.


Sai a karo na huxu ne aka baiwa Ali(RA) wannan matsayi.


Dalili na biyu, a lokacin da fitina ta taso a tsakanin al’umma


sakamakon kisan gila da aka yi wa Sarkin Musulmi Usman(RA), yaqi ya


auku a tsakanin Sarkin Musulmi Ali(RA) da jama’arsa a hannu guda da


kuma Xalha da Zubair da Aisha, Allah ya yarda da su, tare da magoya


bayansu a xaya hannun. ‘Yan Shi’a suna ganin waxan nan Sahabbai sun


yaqi Ali(RA) a bisa zalunci. To da waxannan dalilai biyu ne ‘yan Shi’a


suke kafirta Sahabbai: hana Ali(RA) khilafa a farkon rasuwar Annabi


(SAW) da kuma yaqi da shi a zamanin khalifancinsa.1


Sahabbai Ne Mafi Sharrin Mutane!!


Aqidar ‘yan Shi’a dangane da Sahabbai ba ta tsaya a kan kafirta su ba


kawai, amma suna ganin cewa su Sahabbai su ne mafiya sharrin halittar


Allah, wall iyazu billah!! Kuma suna qudure cewa imani da Allah da


Manzonsa ba ya tabbata sai an barranta daga gare su, musamman dai manyamanya


daga cikinsu kamar Abubakar da Umar da Usman da Aisha da Hafsa


da sauran ire-irensu. Muhammad Baqir Almajlisi, xaya daga cikin manyan


malaman Shi’a, yana cewa: “Aqidarmu ta barranta ita ce cewa mu muna


barranta daga gumaka huxu: Abubakar da Umar da Usman da Mu’awiya;


da kuma mataye huxu: Aisha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam. Kuma


muna barranta daga dukkan mabiyansu da magoya bayansu; kuma muna


qudure cewa su ne mafiya sharrin halittar Allah a bayan qasa; kuma cewa


1 Duba Awa’ilul Maqalat na Muhammad binu Muhammad binu Nu’uman Almufid, bugun darul Kitabil


Islami, Bairut, 1403/1983, shafi na 45; da Al’anwarun Nu’umaniyya na Ni’imatullahi Aljaza’iri, bugun


Madba’atu Bab, Tibriz-Iran, ba tarihi, mujalladi na 2, shafi na 244.


4


imani da Allah da Manzonsa da Imamai ba ya tabbata sai bayan an barranta


daga maqiyansu (yana nufin Sahabbai).”1


‘Yan Shi’a suna nuna qiyayya ta musamman ga Sarkin Musulmi


Umar binul Khaxxabi(RA). Daga cikin irin ruwayoyin da suka keve masa


shi kaxai akwai abinda wani malaminsu mai suna Ni’imatullahi Aljaza’iri ya


ruwaito. Ya ce, “Abinda yake xaure kai shi ne, yaya Ali (A.S) ya aurawa


Umar binul Khaxxabi (diyarsa) Ummu Kulthum, alhali kuwa miyagun


ayyuka sun bayyana daga gare shi kuma ya yi ridda ga barin addini sama da


riddar duk wani mai ridda. Har ma ruwayoyi sun taho da cewa (ranar


Alqiyama) za’a yiwa Shaixan ququmi da sasari saba’in na baqin qarfen


Jahannama sa’an nan a ja shi zuwa ga taron hisabi. Sai ya duba gabansa, sai


ya ga wani mutum mala’ikun azaba suna kora shi, an ququmce shi da sasari


xari da ishirin na Jahannama. Sai Shaixan ya kusanto shi ya ce: Me mara


rabo ya yi har ya fi ni azaba, alhali ni na vatar da halitta baki xaya, na kai su


ga halaka? Sai Umar ya ce da Shaixan: Ba abinda na yi sai dai na qwace


wa Ali binu Abi Xalib khilafa. Ga alama yana ganin qanqantar abinda ya


aikata; bai sani ba cewa duk abinda ya faru a duniya na kafirci da zalunci, ya


auku ne a dalilin wannan aika-aika tasa.”2


Duba ka gani, xan uwa mai karatu, yadda ‘yan Shi’a suke xaukar


cewa wai Umar(RA) ya fi Shaixan tsananin azaba a Lahira, kuma duk


abinda ya faru a duniya na kafirci da zalunci a dalilinsa ne!!


1 A duba Haqqul Yaqin na Muhammad Baqir Majalisi, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, ba tarihi, shafi na


519.


2 Duba Al’anwarun Nu’umaniyya, mujalladi na 1, shafi na 81-82.


5


Qazafin ‘Yan Shi’a ga Sahabbai


‘Yan Shi’a suna yin qazafi ga manyan Sahabbai da matan Manzon


Allah(SAW) Uwayen Muminai, Allah ya qara yarda a gare su baki xaya.


Kuma wannan yana cikin littafan manyan malamansu waxanda suke izna da


su. Ga xan misali:


1. Qazafinsu ga Umar binul Khaxxabi(RA). Wannan babban Sahabi na


Annabi(SAW) yana cikin mutanen da Rafilawa suka fi qi, saboda haka sun


yi masa qazafi mai yawa. Wanda ya fi shahara daga cikin qazafinsu gare shi,


shi ne abinda malaminsu xan hayaqi, Ni’imatullahi Aljaza’iri, ya ruwaito, ya


ce, “Umar binul Khaxxabi ya kasance yana da wani ciwo a duburarsa (idan


ya motsa) babu abinda yake sanyaya shi sai ruwan maza.”1 Inna lillahi wa


inna ilaihi raji’un! Sai mai karatu ya gafarce mu saboda naqalto wannan


xanyar magana wacce da a ce an dangana ta ga kafiri ne da bai kamata a


faxe ta ba haka gatse-gatse. To sai dai malaman Rafilawa, waxanda a haqiqa


su Majusawa ne, zancen batsa ba wani abu ba ne a wajen su. A taqaice dai,


mai karatu ya ga yadda ‘yan Shi’a suke jifan Sayyidina Umar(RA) da liwaxi


a fili, qarara, tare da amfani da qazaman kalmomi da miyagun lafuzza irin


waxanda ba mai iya amfani da su sai su.


2. Qazafinsu ga Usman binu Affan(RA). Ni’imatullahi Aljaza’iri, har yau,


ya ruwaito, ya ce, “Usman ya kasance yana daudu, kuma ya zama ana wasa


da shi.”2 Wannan shi ma jifa ne da liwaxi ga wannan babban bawan Allah,


tsarkakakke, mai kunya da kamun kai, surukin Annabi, wanda Manzo(SAW)


yake jin kunyar sa, kuma mala’iku ma suke jin kunyar sa.


3. Qazafinsu ga Innar Muminai A’isha(RA). Ummul Muminina, wacce


malamin Shi’a, Ali Al’amili Albayali, yake kiran ta ummul shururi3 (uwar


sharrurruka!) ba ta tsira ba daga qagen Rafilawa da qazafinsu. Har yau har


gobe suna gaskata qazafin da munafikai suka yi mata a zamanin


Annabi(SAW), inda suka jefe ta da alfasha, wanda kuma Allah Maxaukaki


ya barrantar da ita, ya kuvutar da ita daga wannan zargi. Amma ‘yan Shi’a


1 Al’anwarun Nu’umaniyya na Ni’imatullahi Aljaza’iri, mujalladi na 1, shafi n 63.


2 Al’anwarun Nu’umaniyya, mujalladi na 1, shafi na 65.


3 A cikin littafinsa, Assirudul Mustaqim ila Mustahiqqi Attaqdim, bugun Madba’atul Haidari, Bairut, ba


tarihi, mujalladi na 3, shafi na 161.


6


ba su gamsu ba; ba su yarda da ayoyi goma sha takwas da Allah ya saukar a


cikin Suratun Nuri ba domin barrantar da ita. Suna ganin waxannan ayoyi


mahaifinta Abubakar ne ya soka su cikin Alqur’ani don ya wanke sunan


xiyarsa, amma ba Allah ya saukar da su ba. Don haka suke ci gaba da laqa


mata wannan zargi. Har ma suna faxin, idan Mahadinsu ya bayyana a


qarshen zamani zai fito da ita daga kabarinta ya tsayar mata da haddi.1


Kafircin da yake cikin wannan magana ba’a voye yake ba. Domin


kuwa, bayan qaryata Alqur’ani qarara, da qazafi ga wannan babbar baiwar


Allah, matar Annabi a duniya kuma matarsa a aljanna, maganar har yau tana


nuna suka da zargi ga Annabi(SAW) cewa shi bai tsayar mata da haddi ba.


Allah ya kiyashe mu tavewa!


4. Qazafinsu ga Muhammad binu Ali binu Abi Xalib. Qazafin ‘yan Shi’a har


da jinin Ali(RA) bai bari ba domin sun jefi wannan xa nasa, watau


Muhammad binul Hanafiyya, da zina.2


Qiyayyar ‘yan Shi’a ga Sahabban Annabi ta kai matuqa har suka


halasta la’antar su. Sun ma xauki la’antar Sahabbai a matsayin ibada wacce


suke neman kusanci ga Allah da ita!! Kuma ko a cikin Sahabban ma,


qiyayyarsu ta fi tsanani ga shugabanninsu mafifita: Abubakar da Umar.


Duba wannan ruwaya, wacce wani malaminsu mai suna Mulla Kazim ya


naqalto, yana dangana ta BISA QARYA ga Ali Zainul Abidin binu Hussain


binu Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara musu yarda. Ya ce: Abu Hamza


Althumali ya karvo daga Ali Zainul Abidin cewa ya ce, “Wanda ya la’anci


Jibtu da Xagutu (yana nufin Abubakar da Umar) la’ana guda, Allah zai


rubuta masa lada dubu sau dubu, ya kankare masa zunubi dubu sau dubu


kuma ya xaukaka masa daraja dubu sau dubu saba’in. Kuma wanda ya


la’ance su da yammaci la’ana guda, za’a rubuta masa kamar haka. (Mai


1 A duba Tafsirul Qummi na Ali binu Ibrahim Alqummi, bugun Darul Kitab, Kum-Iran, 1387 B.H. mujalladi


na 2, shafi na 377.


2 Duba labarin a cikin Furu’ul Kafi na Kulaini, Kitabul Hudud, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Bairut, 1375


B.H., mujalladi na 7, shafi na 187.


7


ruwaya) ya ce: Sai shugabanmu Ali binu Hussaini ya wuce (bayan ya faxi


wannan magana, ni kuma) sai na shiga wurin shugabanmu Abu Ja’afar


Muhammad Albaqir na ce masa: Ya shugabana, wata magana ce na ji daga


mahaifinka. Sai ya ce: Faxe ta mu ji, ya Thumali. Sai na maimaita masa


maganar. Sai ya ce: Haka take, Thumali! Ko kana so in yi maka qari? Sai


na ce: E, ya shugabana. Sai ya ce: Wanda ya la’ance su la’ana guda a ko


wace safiya ba za’a rubuta masa zunubi ba a wannan wunin har zuwa


yammaci, kuma wanda ya la’ance su la’ana guda da yammaci ba za’a rubuta


masa zunubi ba har ya wayi gari.”1


Banda wannan ma, akwai addu’o’i na musamman waxanda aka


wallafa su, aka tsara su, waxanda kuma suka qunshi la’ana da tsinuwa da


miyagun lafuzza ga waxan nan manyan Sahabbai: Abubakar da Umar, Allah


ya qara musu yarda, waxanda yan Shi’a suke yin wurdi da su, suna maimaita


su safe da yammaci kamar yadda Musulmi yake maimaita Ayatal Kursiyu


da Amanar Rasulu da Laqada Ja’akum!!


Daga cikin addu’o’in akwai wata da suke kira Du’a’u Sanamai


Quraishin, watau Addu’ar Gumakan Quraishawa Biyu, suna nufin Abubakar


da Umar, Allah ya qara musu yarda. Ga yadda addu’ar take a Larabci, kafin


daga baya mu kawo fassararta:


“Allahumma Salli ala Muhammadin wa Ali Muhammadin, wal’an


Sanamai Quraishin wa Jibtaihima wa Xagutaihima wa ifkaihima wa


ibnataihima allazaini khalafa amraka, wa ankara wahyaka, wa jahada


in’amaka, wa asaya Rasulaka, wa qallaba dinaka, wa harrafa kitabaka…..


Allahumma il’anhuma fi maknunis sirri, wa zahiril alaniya, la’anan kathiran


abadan, da’i’man sarmadan, la inqixa’a li amadihi, wa la nafaza li adadihi,


la’anan ya’udu awwaluhu wa la yaruhu akhiruhu, lahum wa li a’awani him,


1 Duba Ajma’ul Fada’ihi na Mullah Kazim, shafi na 513.


8


wa ansari him, wa muhibbi him, wal muqtadina bi kalami him, wal


musaddiqina bi ahkami him…. Allahumma azzib hum azaban yastagithu


minhu ahlun nari, amin ya Rabbal Alamin.”


Ma’anar addu’ar: “Ya Allah ka yi daxin tsira ga Muhammad da


alayen Muhammad. Kuma ka la’anci gumakan Quraishawa biyu, da jibtinsu


da xagutunsu, da qarerayinsu da xiyansu mata biyu. Waxanda suka sava


umarninka, suka yi musun wahayinka, suka butulce ma ni’imarka, suka juya


addininka, suka sauya littafinka…. Ya Allah ka la’ance su a cikin


voyayyen sirri da zahirin dake sarari, la’ana mai yawa ta har abada,


madauwamiya ta dun-dun-dun, wacce babu yankewa ga nisanta kuma babu


qarewa ga adadinta, la’ana wacce farkonta zai riqa komowa kuma qarshenta


bai tafiya, gare su da masu mara musu da mataimakansu da masu qaunarsu


da masu koyi da maganarsu da masu gaskatawa da hukunce –


hukuncensu….. Ya Allah ka yi musu azaba, azabar da ‘yan wuta za su riqa


neman tsari da ita, amin ya Ubangijin Talikai.”1


Har yau, akwai wata addu’ar la’ana mai lugude, wacce ta qunshi


la’antar magabata guda tara, waxanda suka haxa da Sahabbai da Tabi’ai,


tare da maimaita la’ana ga Umar binul Khaxxabi(RA) sau tara. Ga yadda


lafazin addu’ar yake:


Allahumma il’an Umara, thumma Ababakarin wa Umara, thumma


Usmana wa Umara, thumma Mu’awiyya wa Umara, thumma Yazid wa


Umara, thumma Ibna Ziyadin wa Umara, thumma Ibna Sa’adin wa Umara,


thumma Shamran wa Umara, thumma Askara hum wa Umara. Allahumma


1 Domin ganin wannan mugunyar addu’a, sai a duba Miftahul Jinan fil Ad’iyati waz Ziyarati wal Azkar,


ba’a san marubucinsa ba, bugun Maktabatul Mahuri, Bahrain, ba tarihi, shafi na 113-114.


9


il’an A’ishata wa Hafsata wa Hindan wa Ummal Hakam. Wal’an man radiya


bi af’ali him ila yaumil qiyamah.1


Ga ma’anar addu’ar: Ya Allah ka la’anci Umar, sa’an nan Abubakar


da Umar, sa’an nan Usmanu da Umar, sa’an nan Mu’awiyya da Umar, sa’an


nan Yazidu da Umar, sa’an nan Ibnu Ziyad da Umar, sa’an nan Ibnu Sa’ad


da Umar, sa’an nan Shamru da Umar, sa’an nan Askar nasu da Umar. Ya


Allah ka la’anci A’isha da Hafsa da Hindu da Ummul Hakam, kuma ka


la’anci (duk) wanda ya yarda da ayyukansu har ya zuwa ranar Alqiyama.


Wannan babbar addu’a, kuma mugunya, ta ‘yan Shi’a tana bukatar


darasu. Da farko dai bari mu bi sunayen da suka zo a cikinta domin mu san


su waye. Abubakar da Umar da Usmanu da Mu’awiyya, Allah ya qara musu


yarda, ba sa bukatar bayani; kowa ya san su. Haka nan A’isha da Hafsa.


Yazidu kuwa shi ne xan Mu’awiyya wanda ya gaje shi a mulkin daular


Musulunci, kuma wanda a zamaninsa ne aka kashe Hussaini(RA). Ibnu


Ziyad shi ne gwamnan Kufa a zamanin mulkin Yazidu, kuma rundunarsa ce


ta kashe Hussaini(RA). Shi kuwa Ibnu Sa’ad (sunansa Umar binu Sa’ad binu


Abi Waqqas) shi ne kwamandan rundunar da ta kashe Hussaini(RA).2


Shamru ban san shi ba; ban gane wanda suke nufi da shi ba. Ga al’adar


Rafilawa idan suka yi amfani da kalmar Askar to A’isha suke nufi da ita,


saboda raqumin da ta hau a yaqin Jamal sunansa Askar. Kuma da yake an


ambace ta da suna a cikin addu’ar, muna iya xauka cewa ita ma an ninka


mata la’ana ne saboda tsananin qiyayya, kamar yadda aka ninninka wa


Umar(RA). Hindu kuwa ita ce mahaifiyar Mu’awiyya(RA) kuma Ummul


Hakam ita ce kakar Marwan binul Hakam, uban yawancin khalifofin Banu


Umayya, ciki har da Umar binu Abdil’aziz khalifa mai adalci, Allah ya yi


masa rahama.


Dalilin la’antar waxannan manyan bayin Allah a wajen ‘yan Shi’a


abu ne mai sauqi. Su dai Abubakar da Umar da Usmanu, Allah ya qara


musu yarda, laifinsu a wajen Rafilawa shi ne wai sun hana Ali binu Abi


Xalib khilafa, kuma sun hana ma Faxima(RA) gado na gonar da mahaifinta


1 A duba La’ali’ul Akhbari na malaminsu Muhammad Attursirkani, bugun Qum-Iran, ba tarihi, mujalladi na


4, shafi na 92.


2 Domin bayanin hakikanin rawar da Yazidu da Ibnu Ziyad da Ibnu Sa’ad suka taka wajen shahadar


Hussaini(RA) a Karbala, sai a nemi littafinmu Wa Ya Kashe Hussaini? bugun Zomo Press, Kaduna, 2010.


10


Annabi(SAW) ya bari. Ita kuma A’isha(RA) ta yi faxa da Ali a Yaqin Jamal.


Hafsa(RA) ba ta yaqi Ali ba, kuma ba ta yi ma Faxima kome ba. Don haka


muna iya xauka cewa wata qila qiyayyar ubanta, Umar binul Khaxxabi, ce


ta nashe ta, ta ja mata wannan la’ana. Mu’awiyya kuwa, Allah ya qara masa


yarda, shi ne uban masu laifi, a ganin Rafilawa, domin shi ya yaqi Ali kuma


ya tankwave masa khilafa a bayan da ya same ta. Kuma wannan babban laifi


nasa shi ya shafi mahaifiyarsa, Hindu. Ummul Hakam, kakar Marwan binul


Hakam, ‘yan Shi’a suna xauka cewa wai jikanta, Marwan, shi ne ya zuga


Usmanu ya yi gaba da Ali. Kuma ga shi jikokinsa sun yi ta more mulki, suka


hana jikokin Ali xanawa. Su kuwa Yazid da Ibnu Ziyad da Ibnu Sa’ad su


suka kashe Hussaini(RA). Wannan ita ce aqidar Rafilawa da fahimtarsu,


kuma ita ta sa suke la’antar waxannan manyan bayin Allah ba dare ba rana.1


Abinda ya gabata a nan xan misali ne kawai na gabar ‘yan Shi’a da


qiyayyarsu ga zavavvun wannan al’umma, watau Sahabban Annabi (SAW),


Allah ya qara musu yarda baki xaya. Kuma wannan gaba haka take tun ran


da maqiyin Allah, Abdullahi binu Saba’i Bayahude, ya kafa wannan


qungiya ta Shi’a har zuwa yau. Haka nan, a kan wannan aqida ne su ma


‘yan Shi’a na wannan zamani suke. Bari ka ji abinda shugabansu kuma


babban malaminsu na wannan zamani, watau Ayatullahi Khumaini, yake


faxi. Ya zo a cikin littafinsa Kashful Asrar kamar haka: “Mu a nan babu


ruwanmu da tsofaffi biyu (yana nufin Abubakar da Umar) da abinda suka


aikata na savawa Alqur’ani, da wasa da suka yi da hukunce-hukuncen Allah,


da abinda suka halasta ko suka haramta daga qashin kansu, da abinda suka


aikata na zalunci a kan Faxima xiyar Annabi (SAW), da kuma sauran


‘ya’yansa. Sai dai mu a nan, muna nuni ne zuwa ga jahilcinsu da hukuncehukuncen


Allah da addini.”2


1 Domin darasun ra’ayin Ahalus Sunna dangane da wannan aqida da fahimta ta ‘yan Shi’a, sai mai karatu


ya nemi littafinmu, Wa Ya Kashe Hussaini?


2 Kashful Asrar na Ayatullahi Khumaini, bugun Daru Amar, Omman-Urdun, 1408/1987, shafi na 126.


11


Duba ka gani, xan uwa mai karatu, wai Khumaini ne yake dangana


jahilci da zalunci ga Sahabban Annabi(SAW): Abubakar da Umar, Allah ya


qara musu yarda!!


Kuma har yau, Khumaini ya zargi Sayyidina Abubakar da Sayyidina


Umar, Allah ya qara musu yarda, da cewa wai sun sauya Alqur’ani!! Ya ce,


“Lallai Allah ya ambaci nau’in mutane takwas waxanda suka cancanci rabo


a cikin zakka, amma sai Abubakar ya jefar da nau’i guda daga cikin


waxannan nau’o’in mutane bayan da Umar ya zuga shi ya yi haka.”1


Sa’an nan daga bisani, ya jefa wa Sahabbai baki xayansu kalmar


kafirci. Wal iyazu billah!! Ya ce, “Babu shakka su (Sahabbai) sun baiwa


Annabi haqqinsa yadda ya kamata!! (yana yi musu ba’a ne). Annabi wanda


ya wahala, ya sha fama, kuma ya jure dukkan musifu domin shiryar da su,


sa’an nan ya cika (a lokacin rasuwarsa) alhali yana jin kalmomin Xan


Khaxxabi waxanda aka gina a kan kafirci da zindiqanci.”2


Wannan mugunyar aqida a kan ta ne ‘yan Shi’ar Nijeriya suke, kamar


yadda muka sha ji da kunnuwanmu, kuma muka sha gani da idanunmu. Sai


dai sau da yawa su kan voye ta ga mutane saboda Taqiyya, watau munafurci


da yaudara!! Muna roqon Allah Maxaukaki ya shirye su, ya arzuta su da


kyakkyawar tuba kafin zuwan ajalinsu. Mu kuma, Allah ya shiga tsakanin


mu da su, ya tsare mu daga qudure aqidarsu.


Falalar Sahabban Annabi(SAW)


Sahabban Annabi (SAW), Allah ya qara yarda a gare su, ba sa buqatar


mu yi wani bayani domin kuvutar da su da barrantar da su daga abin da ‘yan


Shi’a suka dangana musu na kafirci da ridda da zalunci; saboda babu wani


1 Kashful Asrar na Khumaini, shafi na 131.


2 Duba Kashful Asrar na Khumaini, shafi na 137.


12


mai da’awar Musulunci da yake shakkar imaninsu, da xaukaka, da falalarsu,


sai fa wanda Allah ya makantar da basirarsa, ya vatar da shi.


Amma za mu kawo wasu ayoyi na Alqur’ani waxanda suke nuna


falalar Sahabbai kuma suna tabbatar da cewa qudure aqidar ‘yan Shi’a


dangane da waxan nan manyan bayin Allah qaryatawa ne ga Alqur’ani,


kuma qaryata Alqur’ani, kamar yadda kowa ya sani, kafirci ne.


Allah ya tabbatar da imanin Sahabbai: Ya ce, “Kuma waxanda suka


yi imani kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi a cikin hanyar Allah, kuma


da waxanda suka bayar da masauki kuma suka yi taimako, waxannan su ne


muminai da gaskiya, suna da gafara da wani abinci na karimci. Kuma


waxanda suka yi imani daga baya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihadi


tare da ku, to, waxannan daga gare ku suke.” (Suratul Anfal: 74-75).


A cikin aya ta farko, Ubangiji ya yi bayanin waxanda suka yi imani


kuma suka yi hijira (waxannan su ne Muhajiruna), da kuma waxanda suka


bayar da masauki ga masu hijirar (su ne Ansar), ya tabbatar da cewa su ne


muminai na gaskiya. Waxannan kungiyar mutane biyu, Muhajiruna da


Ansar, su ne Assabiqunal Auwaluna: Sahabbai waxanda suka yi rigaye


wajen shiga Musulunci, imaninsu da rigayensu sun tabbata, kuma wanda


duk ya shiga Musulunci daga bayansu yana biye da su ne.


Allah ya tabbatar da tsarkin zukatan Sahabbai da ihlasinsu: Ya ce,


“Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxannan dake tare da shi masu


tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna


masu ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu da yardarsa.”


(Suratul Fathi: 29). Kuma ya ce, “(Ku yi mamaki) ga matalauta masu hijira


waxanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga


13


Allah da kuma yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzonsa. Waxannan


su ne masu gaskiya.” (Suratul Hashri: 8).


Allah ya tabbatar da fifikonsu: Bayan Ubangiji ya tabbatar da imanin


Sahabbai da tsarkin niyyarsu, kuma ya tabbatar da fifikonsu ba kawai a kan


wannan al’umma ba, a’a har ma da sauran al’ummai. Ya ce, “Kun kasance


mafi alherin al’umma wadda aka fitar ga mutane, kuna umarni da alheri


kuma kuna hani daga abinda ake qi, kuma kuna imani da Allah” (Suratu Ali


Imrana: 110). Imam Ibnu Kathir ya ce, “Wannan aya tana nufin dukkan


al’umma, amma kuma mafifita a cikin wannan al’umma su ne na farkonta.”1


Har yau, Allah Mxaukaki yana cewa, “Kuma kamar wannan, muka sanya ku


al’umma matsakaiciya (mafificiya, adala) domin ku kasance masu bayar da


shaida a kan mutane.” (Suratul Baqara: 143). Wannan aya ita ma ma’anarta


kamar ta farko ce.


Allah ya yi gafara ga Sahabbai tare da Annabi: Ubanjigi Maxaukaki


ya ce, “Lallai ne, haqiqa, Allah ya karvi tubar Annabi da Muhajirina da


Ansar waxanda suka bi shi, a cikin sa’ar tsanani, daga bayan zukatan wani


vangare daga garesu sun yi kusa su karkata, sa’an nan (Allah) ya karvi


tubarsu. Lalle shi ne mai tausayi, mai jin qai gare su.” (Suratut Tauba:


117). Ma’anar ya karvi tubarsu shi ne ya yi musu gafara. To idan Allah ya


yi musu gafara, ya wani zai ce sun kafirta, ko sun yi ridda, ko sun yi


zulunci?!!


Allah ya yarda da Sahabbai: Ubangiji Maxaukaki ya ce, “Kuma


magabata na farko daga Muhajirina da Ansar da waxanda suka bi su da


kyautatawa, Allah ya yarda da su, su kuma sun yarda da shi, kuma ya yi


1 Tafsirin Ibnu Kathir, na Isma’il binu Kathir, bugun Maktabatus Safa, Alqahira, 1423/2002, mujalladi na 1,


shafi na 55.


14


masu tattalin gidajen Aljanna: qoramu suna gudana a qarqashinsu, suna


madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo.” (Suratut


Tauba: 100). To, waxanda Allah ya yarda da su, ya tanadar musu Aljanna,


ta ya za’a ce sun kafirta ko sun yi ridda?!!


Allah ya yarda da su alhali yana sane da abinda yake cikin zukatansu:


Ya ce, “Lalle ne, haqiqa, Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi


maka mubaya’a a qarqashin itaciyar nan domin ya san abinda ke cikin


zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a kansu, kuma ya saka musu da wani


cin nasara makusanci.” (Suratul Fathi: 18). Waxanda suka yi wa Annabi


(SAW) mubaya’a a qarqashin wannan itaciya da Allah ya ambata su dubu


da xari huxu ne (1,400). Allah ya ambata cewa ya yarda da su alhalin yana


sane da abinda yake cikin zukatansu, kuma ya kira su muminai. To ta yaya


‘yan Shi’a za su ce Sahabban Annabi duka sun yi ridda bayan rasuwarsa wai


sai mutum bakwai kawai? Allah wanda yake ganin abinda yake cikin


zukatansu, da ya san za su yi ridda bayan Annabi, ya zai saukar a cikin


littafinsa mai tsarki cewa ya yarda da su?


Babu shakka maganar Allah ba ta tashi. Shi ya ce ya yarda da su; su


kuma ‘yan Shi’a suka ce sun yi ridda? Subhanallah!! Wannan wane irin


xanyen hukunci ne? Babu shakka a cikin wannan akwai jayayya da Allah


da kuma qaryata littafinsa. Allah ya tsare mu da vata.


Haqqoqin Sahabbai a kan Musulmi


Sahabban Annabi(SAW), Allah ya yarda da su baki xaya, suna da


haqqoqi a kan ko wane Musulmi waxanda ya wajaba a kiyaye da su.


Haqqoqin sun haxa da:


1. Son su da qaunar su saboda Allah da Manzonsa suna son su.


15


2. Imani da fifikonsu a kan sauran dukkanin al’umma.


3. Imani da fifikon Abubakar, sa’an nan Umar, sa’an nan Usman, sa’an


nan Ali a bisa wannan jeri. An ruwaito daga Abdullahi binu


Umar(RA) yana cewa, “Mun kasance muna faxi, alhali Annabi yana


raye, Abubakar ne ya fi, sa’an nan Umar, sa’an nan Usmanu, sa’an


nan Ali. Kuma Annabi ya ji hakan amma bai hana mu ba.”1


4. Kamewa ga barin ambaton tuntuvensu da kurakuransu, da nesantar


shiga shara ba shanu dangane da savanin da ya afku a tsakaninsu.


5. Imani da alfarmar matan Manzon Allah(SAW) dukkaninsu, tare da


cewa su Uwayen Muminai ne, kamar yadda Allah Maxaukaki ya


tabbatar a cikin faxinsa, “Annabi ne mafi cancanta ga muminai bisa


ga su kansu, kuma matansa uwayensu ne.” (Suratul Ahzab: 6). Kuma


a qudure cewa mafifitansu su ne Khadija da A’isha, Allah ya qara


yarda a gare su baki xaya.


Xan uwa mai karatu, waxan nan su ne haqqoqin Sahabbai waxanda ya


wajaba dukkan Musulmi su kiyaye da su; amma ‘yan Shi’a sun sarayar da


su. Ba kawai sun sarayar da su ba, amma sun akkasa!


An umarce su da su so su, sai suka qi su!!


An umarce su da su fifita su, sai suka wulaqanta su!!


An ce su kame ga barin ambaton tuntuvensu, sai suka yi musu qazafi,


suka dangana musu abinda ba su ji ba, ba su gani ba!!


Muna roqon Allah da sunayensa kyawawa da sifofinsa maxaukaka ya


shiryar da su, ya arzuta su da tuba karvavviya.


1 Sahihul Bukhari.


16


“Ya Ubangijinmu! Kada ka karkatar da zukatanmu bayan har ka


shiryar da mu, kuma ka ba mu rahama daga gunka. Lalle ne, kai, kai ne mai


yawan kyauta.” (Suratu Ali Imrana: 8).


“Ya Ubangijinmu, ka yi gafara gare mu, kuma ga ‘yan uwanmu


waxanda suka riga mu yin imani, kada ka sanya qulli a cikin zukatanmu ga


waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu, lalle kai mai tausayi ne, mai


jinqai.” (Suratul Hashri: 10).



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA