17
gwamnatocin da ‘yan siyasa suka taimaka wajen yaxuwar qungiyar Boko Haram
da qarfafa ta. Wannan cin amanar al’umma ne.
Kuma yaqar Shi’a, da ma sauran nauo’in bidi’a, ba yana nufin afka musu da
xauri da kisa ba. Bidi’a aqida ce, aqida kuwa ba’a yaqarta da qarfi kamar yadda
ba’a yaxa ta da qarfi. Koda yake a baya kaxan mun ce mahukunta su yi amfani da
qarfin ikonsu wajen yaqar Shi’a, amma ba qarfin soja da ‘yan sanda muke nufi ba,
a’a qarfin zartaswa muke nufi. Qarfin sawa a yi, kuma dole a yi. A nan gaba za mu
bayyana hanyoyin yaqar bidi’a, in Allah ya yarda.
Miyagun Malamai Ke Yaxa Bidi’a
Miyagun malamai su ne malamai masu ci da addini waxanda suke sa rigar
addini, su yi da’awar ilmin addini, amma ba addinin ne ya dame su ba, sai dai wasu
bukatu dabam na duniya, imma dukiya ko mulki ko qasaita da tara mutane domin
hore su da cin guminsu bisa qarya. Miyagun malamai yawanci ba sa wuce nau’i
biyu: imma jahili fitik wanda yake da’awar ilmi, yana wasa da hankalin jahilai, ko
mai ilmi wanda yake neman duniya da ilminsa; don haka sai ya voye abinda Allah
ya saukar ko ya karkatar da ma’anarsa, ya bi son zuciyarsa, ya vata kuma ya vatar
a bisa sani.
Irin waxan nan malamai su ne suke vata duniya, su vata addini. Daga cikin
miyagun ayyukansu akwai yaxa bidi’a.
Allah Maxaukaki yana cewa, “Ya waxanda suka yi imani! Lalle ne masu
yawa daga Ahbar (malaman Yahudu) da Ruhbanawa (masu ibada a cikin Nasara),
haqiqa suna cin dukiyar mutane da qarya, kuma suna kangewa daga hanyar Allah.”
(Suratut Tauba: 34). Da yake fassara ayar, Imam Ibnu Kathir ya ce, “Abin nufi da
wannan aya tsorataswa daga miyagun malamai da masu ibada vatattu,1 kamar
yadda Sufyan binu Uyaina ya ce: ‘Wanda ya vaci daga cikin malamanmu yana da
kamanni da Yahudu, kuma wanda ya vaci daga cikin masu ibadarmu to yana da
kamanni da Nasara.’”2
1 Yana nufin masu ibada da bidi’a, kamar wasu Sufaye da ‘yan Shi’a masu kago ibada, su yi ta da ka.
2 Duba Tafsirul Kur’anil Azim na Isma’il binu Umar binu Kathir, bugun Maktabatul Asriyya, Bairut, 1414/1994,
mujalladi na 2 shafi na 319.
18
Wannan aya, tare da fassararta daga bakin magabata, tana nuna cewa an
samu miyagun malamai a cikin al’umman da suka gabata kamar yadda ake samun
su a cikin al’ummarmu a yau. Ga misali, a cikin Banu Isra’ila an samu miyagun
malamai kamar Bal’am binu Ba’ura, wanda Allah yake faxi dangane da shi: “Ka
karanta musu labarin wanda muka kawo masa ayoyinmu, sai ya savule daga gare
su, sai Shaixan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.” (Suratul A’araf: 175),
da Samiri wanda ya sa mutanen Annabi Musa suka bauta wa xan maraqi. Waxan
nan mutane biyu duka malamai ne, amma sun sava wa Allah, suka bi son
zukatansu, sai suka vata kuma suka vatar; don haka suka zama daga miyagun
malamai.1
Kuma kamar yadda Alqur’an ya yi nuni zuwa ga miyagun malamai, hadisai
ma sun yi nuni zuwa gare su. Annabi (SAW) ya ce, “Ba Dujal na fi tsoracewa
al’ummata ba, amma na fi tsorace musu shugabanni masu vatarwa.”2 Abin nufi da
shugabanni a nan su ne malamai.
Ba yau aka fara samun miyagun malamai a qasar nan ba, amma an same su
tun kafin zamanin jihadin Shaihu Xanfodiyo. Wani babban malami da ya ziyarci
qasar Hausa a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Runfa, kuma ya zauna ya koyar
a birnin Kano da Katsina, Muhammad binu Abdil Karim Almagili, ya yi rubutu a
kan miyagun malamai, inda ya bayyana sifofinsu da halayensu, kuma ya kafa hujja
a kansu da ayar da muka kawo a sama ta Suratut Tauba, sa’an nan ya ce, “A cikin
wannan al’umma ma akwai irin waxan nan mutane su ne miyagun malamai.”
Shaihu Usman Xanfodiyo ya naqalto wannan magana tasa kuma ya tabbatar da ita
a cikin littafinsa Wathiqatul Ikhwan.3
A zamanin jihadi, lokacin da Shaihu Usmanu ya zage dantse wajen yaqar
bidi’a da tabbatar da Sunna, miyagun malamai na qasar Hausa sun haxa kai da
azzaluman sarakai wajen yaqar Shaihu da jihadinsa, don tabbatar da cewa jihadin
bai yi nasara ba, kuma tutar Sunna ba ta xaukaka ba.
1 Domin ganin labarinsu, sai a duba Tafsirin Ibnu Kathir, tushen da ya gabata, mujalladi na 2 shafi na 245-246; da
mujalladi na 3 shafi na 156. Haka nan, a duba Hashiyatus Sawi alal Jalalaini na Ahmad Sawi, bugun Mu’assasatu
Daril Ulum, Dimashqa, ba tarihi, mujalladi na 2 shafi na 52.
2 Imam Ahmad ya fitar da hadisin a cikin Musnad nasa. Duba Silsilatul Ahadisis Sahiha na Muhammad Nasiruddin
Albani, bugun Maktabatul Ma’arif, Riyal, 1408/1988, mujalladi na 4 shafi na 646.
3 Duba Wathiqatul Ikhwan na Usmanu Danfodiyo, rubutun hannu, shafi na 17.
19
Wannan ya sa malaman jihadi, Usmanu Xanfodiyo da Abdullahin Gwandu
da Muhammadu Bello, suka xaura xamara wajen xauki-ba-daxi da miyagun
malaman, suka rubuta littafai masu yawa don tona asirinsu da bayyana wa jama’a
halinsu, don su guje su.
A cikin littafinsa, Hisnul Afham, Shaihu Mujaddadi ya yi bayani filla-filla
na irin yaqin da ya kasance tsakanin malaman jihadi da miyagun malamai na
zamaninsu, inda ya zayyana fagagen da aka gwabza wannan yaqin da kuma
matakan da malaman jihadi suka xauka don karya lagon miyagun malaman.1 Har
yau, a cikin littafin Wathiqatul Ikhwan, Shaihun ya bayyana sharrinsu ga addini,
inda ya sifanta su da cewa, “Su ne wakilan Shaixan a bayan qasa.”2 Sa’an nan ya
qara da cewa, “Sun fi shaixanu dubu sharri a kan al’umma.”3
Shaihu Abdullahi Xanfodiyo (Abdullahin Gwandu), a nasa vangaren, ya
ambaci miyagun malamai a cikin littafinsa Diya’u Ahalir Rashad, ya sifanta su da
jahilci da son duniya da yaxa bidi’a da taimakon azzaluman masu mulki wajen
danne haqqin talakawa ta hanyar ba da karkatacciyar fatawa da fassara nassoshin
Shari’a da yi musu tawili yadda za su dace da son zuciyar masu mulkin.4
Shi ma Muhammadu Bello xan Shehu ya bijiro da maganarsu a cikin
littafinsa Algaithul Wablu, inda ya sifanta su da jahilci, musamman na harshen
Larabci da fannonin addini, kuma ya bayyana cewa dangana kansu da addini
da’awa ce kawai, kuma hanya ce ta hore mabiya da tara abin duniya. Sa’an nan
daga bisani ya ce, “Wajibi ne a hana musu koyarwa da ba da fatawa da riqe
muqaman duniya da na addini.”5
A bisa ga wannan ra’ayi na Muhammadu Bello bai kamata a bar miyagun
malamai, masu yaxa bidi’a da taimakon azzaluman shugabanni, su koyar a
makarantu ba, ko su yi wa’azi a radiyo, ko su riqe wani muqami a aikin gwamnati
ko na al’umma.
1 Duba Hisnul Afhami min Juyushil Auhami na Usmanu Danfodiyo, tahaqiqi Dr. Falalur Rahman Siddiqi, shafi na 99-
136.
2 Wathiqatul Ikhwan, shafi na 17.
3 Duba Wathiqatul Ikhwan, shafi na 18.
4 Duba Diya’u Ahalir Rashad na Abdullahi Danfodiyo, rubutun hannu, shafi na
5 Duba Algaithul Wablu na Muhammadu Bello, tahakikin marigayi Dr. Omar Bello, shafi na 37.
20
Irin wannan fatawa ce muka bayar dangane da ‘yan Shi’a, a qarshen littafin
Vacin Tafarkin ‘Yan Shi’a da Aqidojinsu, kuma wasu jahilai masu fakewa da
‘yanci da haqqin bil Adama, suke ganin an zalunce su. Xan bidi’a mai zagon qasa
ne ga addini da al’umma; don haka ba’a ba shi amana kamar ta aikin gwamnati ko
koyar da ‘ya’yan al’umma.
A taqaice, malaman jihadi sun yaqi miyagun malamai, sun yi nasara a
kansu, kuma sun bar mana kayan gado na ilmi wanda zai taimaka mana wajen
fahimtar miyagun malamai na zamaninmu da ci gaba da yaqar su a qoqarin sake
jaddada addini da yaqar bidi’a da tabbatar da Sunna.
Dangane da sifofinsu da manufofinsu, babu abinda ya raba miyagun
malamai na wannan zamani da na lokacin jihadi sai bambancin zamani da ci
gabansa. A farkon wannan gava mun ambata cewa, miyagun malamai ba sa wuce
xayan biyu: imma jahilai fitik wa imma malamai waxanda suke nufin duniya da
ilminsu. Waxan nan kashi biyu su ne muke da su a wannan qasa a yau.
Akwai malaman gargajiya waxanda babban abinda ya dame su shi ne tara
abin duniya da gina gidajensu na gado da tarbiyyar ‘ya’yansu don su ci gaba da
danne almajiransu a bayan ransu. Irin waxan nan malamai yawanci idan ka ji ana
faxa da su to duniyarsu aka tava, ko matsayinsu aka yi wa barazana, ko mabiyansu
za’a janye. Su a wajensu su ne addini; idan aka yi musu hidima to an yi wa addini,
idan kuwa aka qyale su to kome aka yi wa addini ba’a yi ba!
Suna tara mutane ta hanyar fito musu ta inda suke so. Wannan ya sa suke
qarfafa bukukuwa bidi’a masu kama da addini, da kaxe-kaxe da raye-raye da
waqe-waqe, kamar yadda suke fakewa da son Annabi amma babu ruwansu da
Sunnarsa.
Miyagun malamai suna yaqi da ilmi; saboda suna son al’umma ta ci gaba
da zama cikin duhu, su kuwa su ci gaba da hore jahilai suna ci da guminsu. Ba sa
koyar da kowa sai ‘ya’yansu, waxanda suke naxawa halifofi a bayansu, amma
‘ya’yan al’umma to suna yin duk abinda suke iyawa don su hana musu karatu.
Wannan ya sa muka sha ganin ana aiko da guraben karatu daga jami’o’i na gida da
na qasashen waje, amma sai su danne, su hana wa ‘ya’yan mabiyansu amfana da
su.
21
Suna gaba da duk wani malami ko qungiya da suke kira zuwa ga riqo da
Sunna da numan ilmi da dogaro da kai wanda yake tabbatar da karamar xan Adam.
Kuma suna maraba da duk abinda yake kawo ci bayan al’umma, kamar jahilci da
zaman banza da barace-barace waxanda suke raunana zukatan mutane da
qwaqwalensu, kamar yadda suke qawance da azzaluman masu mulki da varayin
‘yan siyasa da vata-garin al’umma.
Bidi’a Baquwa ce, Sunna ce ‘yar Gida
Wasu mutane da zarar an ambaci Sunna, sai tunaninsu ya tafi ga wasu
qungiyoyi da aka san su da kira zuwa ga Sunna kamar qungiyar Jama’atu Izalatil
Bidi’a wa Iqamatis Sunna ko qanuwarta Salafiyya. Kasancewar waxan nan
qungiyoyi sababbi ne sai su xauka cewa ita ma Sunna wani abu ne sabo. Saboda
haka sai su qudure, a bisa rashin sani, cewa Sunna baquwa ce kuma kishiyarta,
watau bidi’a, ita ce ‘yar gida. Alhali kuwa gaskiyar lamarin shi ne, bidi’a ita ce
baquwa, Sunna kuma ‘yar gida.
Kuma a bisa irin wannan layi na tunani ne, wasu suke zaton Sunna da muke
kira zuwa gare ta, kuma muke yaqi da kishiyarta, ta fara ne da Muhammad binu
Abdilwahhab, ko da Ibnu Taimiyya. Don haka suke kiran Ahalus Sunna ‘yan
Wahhabiyya. Wannan duka rashin sani ne, da maimaita abinda wasu ke faxi irin
maimaitawar akun kuturu.
Sunna ta fara ne da mai ita, watau Annabi (SAW), da almajiransa, watau
Sahabbai, Allah ya qara yarda a gare su. A zamanin Sahabbai, dukkan Musulmi
Ahalus Sunna ne, watau masu bin Sunna, sai a zamanin Tabi’ai ne aka fara samun
masu qago bidi’a da masu bin ta. Kuma zamani na qara nisa, masu rungumar
bidi’a suna qara yawa. Wannan ita ce hikima da ta sa Manzon Allah (SAW) ya yi
umarni da riqon Sunna da yaqar bidi’a, kamar yadda muka gani a farkon wannan
littafi.
Savanin yadda wasu da yawa suke zato, Sunna a Nijeriya ba ta fara da
zuwan Izala ba, ba ta ma fara da jihadin Xanfodiyo ba. Tun radda Musulunci ya zo
qasar nan, da ma ya zo ne da Sunna. Don haka, Musulmin qasar nan, malamansu
da sarakansu da talakawansu, ba su san kome ba sai Sunna. Hatta mabiya xariqun
22
Sufaye a qasar nan sun kasance masu riqo ne qwarai da Sunna, kuma masu yaqar
bidi’a. Sai daga baya ne, bidi’a ta watsu a tsakanin jama’a, kuma duk da yaxuwarta
ba’a tava rasa masu yaqar ta ba, tun kafin jihadin Xanfodiyo har zuwa yau, kuma
har abada in Allah ya yarda.
Babban abinda yake tabbatar da wannan shi ne cewa, Shaihu Usmanu
Xanfodiyo wanda ya jagoranci tajdidin da ya kafa durakun Sunna a Afirka ta
Yamma baki xaya, shi da kansa ya samu ilminsa ne da aqidarsa ta Sunna a cikin
qasar nan, tunda bai tava fita daga iyakokin qasar ba. Shaihu Xanfodiyo da sauran
malaman jihadi ba su je aikin Hajji ba, ba su ziyarci wata qasar Larabawa ba, kuma
da xai ba su xauki ilmi daga wajen wani Balarabe ba.
Haka nan a bayan jihadin Shaihu Xanfodiyo, bidi’a ba ta tava miqe qafa ba
a qasar nan, ba ta tava samun karvuwa da yaxuwa ba, ko a tsakanin Sufaye, sai a
shekaru kaxan da suka wuce. Sauyawar rayuwa da tasirin al’adu bare, tare da
zuwan wasu miyagun malamai waxanda suka karve ilmi a hannun mutane, suka
musanya musu da Diwani da waqe-waqe da kaxe-kaxe, shi ya kawo yaxuwar
bidi’a a qasar nan.
Shekaru hamsin kacal da suka wuce, bidi’a a wajen kowa a qasar nan
matsayinta shi ne kishiyar Sunna, kuma kowa yana qyamar ta, yana yaqar ta. Har
‘yan boko da gama-garin mutane suna qyamar bidi’a, kuma suna yaqar ta. Shaida a
kan wannan shi ne abinda uban ‘yan bokon Arewa1 kuma malamin Aminu Kano a
fagen siyasa,2 Malam Sa’adu Zungur, ya rubuta a cikin wata qasida tasa yana
zargin bidi’a. Ga qasidar zan xebo wasu yankuna daga cikinta don amfanin mutane
da suka yasar da adabinsu, suka mance da tarihinsu:
A farkon qasidar yana cewa:
Ka xaura niyya a kan waqa kana adu’a,
A’uzu billahi daga Shaixan a kan bidi’a.
San nan kawo Basmala bisa kan riqon Sunna,
Ka biya da yin Hamdala ita ce uwar sa’a.
1 Shi ne dan Arewa na farko da ya fara zuwa makarantar Yaba College dake Legas. An haife shi a shekarar 1915
kuma ya rasu a shekara ta 1958.
2 Karanta littafin Rayuwar Ahmad Mahmud Sa’adu Zungur na Malam Aminu Kano, bugun NNPC, Zaria, 1973.
23
Daxa kawo salsala don kammalar xa’a,
Ga wanda aikensa rahama ce wajen jama’a.
Ka iyar da kalmar Salatu zuwa ga Alaye,
Da sallama ga Sahabbai masu kyan dara’a.
Da Tabi’ina da Tabi’him, da ihsani,
A kan tafarki na Sunna wanda ba bidi’a.
Da malaman gaskiya fitilu na zamani,
Don haskakawar duhun fitinu na mai bidi’a.
Manzo ya ce, la tazalu tutur akwai jama’a,
Da za ta dage a kan Sunna da qin bidi’a.
Da waxanda kuma za su juya kan dugagensu,
Domin su koma ga Arnanci na son bidi’a.
Allahu ya yi umarni duk ga Al’ummai,
Da sunka sava umarni sunka bar xa’a.
Yau ga shi mun sava juna mun zamo bamban,
Bisa kan hadisi na Manzo Annabin sa’a.
Da ya ce a kwana a tashi sannu za mu rabu,
Saba’in da ukku tafirqa duk mutan bidi’a.
Face guda xaya ita ce za ta san tsira,
Sauran a tura Jahannama don rashin xa’a.
Allah Ta’ala muna roqon ka taufiqi,
Ka fid da mu rundunar jama’a ta ‘yan bidi’a.
Ya xan uwana dake fatawa a kan zancen,
24
Tawakkali da du’a’i wanda ba bidi’a.
Da fassarar qaddara bisa yadda anka faxi,
Cikin Kitabu da Sunna inda ba bidi’a.
A kan juriya wajen riqo da Sunna, Malam Sa’adu Zungur ya ce:
Allah ya shirye mu mu duka mui riqon Sunna,
Mu kama igiya ta taufiqi a kan xa’a.
Idan jawabinmu ya dace da fatawarka,
Kai Hamdala kuma ka zage tattalin jama’a.1
Ka jure suka ta kibiyoyi na jahillai,
Don za su harbe ka, ka zarge su kan bidi’a….
To, xan uwa sai ka jure kuma ka xau haqure,
Bisa gargaxin jama’armu su daina yin bidi’a.
Duba ga nassi ka zam koyi da Manzanni,
A kan jidali da al’adu na ‘yan bidi’a.
Fa’in tawallau, idan suka soma bauxewa,
Suka juya baya ga ma’anar kamilar xa’a.
Su je da niyyarsu mu dai hasbunallalhu,
Wa ni’ima, madalla mai tanyon dukan jama’a.
Iyyaka na’abudu bauta wadda ba shirku,
Iyyaka kuma nasta’inu a kan gudun bidi’a.
Ya Rabbi shirye mu hanya wadda babu kwana,
Hanya ta bayin da suka san kamilar xa’a.
1 Tattalin jama’a, yana nufin riko da tafarkin Sunna wal Jama’a.
25
Hanyar waxan nan da kai ni’ima gare su duka,
Ai ban da hanyar miyagu tarkacen bidi’a.
A kan rantse-rantsen bidi’a kuma, ya ce:
Ga wani jawabi da yai suka ga al’ada,
Ta rantsuwar jahili don qarfafar bidi’a.
Da xai ba ka ji shi ya rantse da Allah ba,
Don qarfafawar batunsa don yana bidi’a.
Sai dai ya rantse da hubbare na kakansa,
Ko ko da tsohon ubansa a Majalisar bidi’a.
Ko ko ya rantse da shehunnai da sunka wuce,
Domin ya qarfafa zance, kaito xan bidi’a.
Kamar ya rantse da Ahmadu Shehu Tijjani,
Ko Shehu Jilani, wai a zatonsa yai xa’a.
Ko ko da aradu kwarankwatsa tabbatar tsafi,
Bisa rantsuwarsu ta Arna zamanin bidi’a.
Kuma Shehu Xan Hodiyonmu da shi da Hubbare,
Suna cikin rantsuwar magana ta ‘yan bidi’a.
Inko abin ya yi zurfi har ya je matuqa,
Domin a qarfafa zancen Majalisar bidi’a.
Sai kuma a rantse da Annabi ko da Alqur’an,
Da Mala’ikun Rahamanu a Majalisar bidi’a.
Kai hasali duk Bahaushe jahili tsintsa,
Da furfurarsa yakan rantse a kan bidi’a.
26
In ka ji ya ce da kai Wallahi qarya ce,
Ya xunguma ta yana tuhumar ka ko da ba’a.
Ko ko yana dariya zance na wargi ne,
Ko kuma ya guntse ta Billahillazi da ba’a.
Daga qarshe, Malamin ya cikashe qasidarsa da faxin:
Allah Ta’ala muna roqo ka shirye su,
Su kama igiya ta Allah duk su bar bidi’a.1
Wannan qasida ta Malam Sa’adu Zungur, uban ‘yan bokon Arewa, malamin
Aminu Kano a fagen siyasa, tana nuna mana matsayin Sunna a qasar nan. Sa’adu
Zungur ba almajirin Abubakar Gumi ba ne (duk abinda na karanta dangane da shi
yana nuna bai tava ganin Gumi ba. Haka shi ma Gumi bai ambace shi a cikin
littafin tarihin rayuwarsa ba: Where I Stand), ba Ustazu ba ne, bai yi karatu a qasar
Larabawa ba, shi xan boko ne, amma ya sha Sunna daga maman wannan al’umma
wacce aka gina ta a kan Sunna. Bai san Izala ba, kasancewarsa ya rasu a shekara ta
1958, shekaru ishirin kafin a kafa Izala, ba xan Salafiyya ba ne (amma dubi
zunzurutun Salafiyyanci a cikin waqarsa) duk da haka mai karatu ya ga yadda yake
kira zuwa ga Sunna, yana yaqar bidi’a. Babu shakka wannan yana nuna matsayin
Sunna cewa, ita ce ‘yar gida, bidi’a kuwa baquwa, mai shigege.
Kuma na tsakuro daga vangarorin wannan qasida masu tsawo saboda in tuna
wa mai karatu da Adabinmu mai gwavi da kayan gado na ilmi wanda iyayenmu
suka bar mana, amma a yanzu mun jefar saboda mun jahilci kanmu.
Bambancin Yaqar Bidi’a da Tsaurin Ra’ayi
Wasu mutane suna kasa bambancewa tsakanin yaqar bidi’a da tsaurin ra’ayi.
Sai su xauka cewa duk mai kira zuwa ga riqo da Sunna ya jefar da bidi’a mai
tsananin ra’ayi ne. Wannan zato tushensa shi ne rashin sani, da sauraron maqiyan
Musulunci, masu sukar mabiyansa da cewa su masu tsananin ra’ayi ne.
1 Duba Wakar Bidi’a a kundin Wakokin Sa’adu Zungur, bugun NNPC, Zaria, 1968, shafi na 1-6.
27
Riqo da Sunna da yaqar bidi’a shi ke tsare Musulunci daga lalacewa, da
canjawa ta hanyar qari ko ragi, kamar yadda tsoffin addinai suka lalace, suka canja.
Addinin Musulunci shi ne addini na qarshe da Allah ya yi nufin ya wanzu kamar
yadda ya saukar da shi ba tare da sauyawa ba har zuwa qarshen zamani. Don haka
Allah ya tanadi wasu matakai na tsare shi da kiyaye shi don kada ya canja ko ya
sauya. Daga cikin waxan nan matakai akwai tsare littafin Musulunci, Alqur’ani,
daga sauyawa kamar yadda aka sauya Attaura da Linjila, da tsare Sunna wacce ita
ce fassarar Alqur’ani a aikace daga gurvacewa.
Allah Maxaukaki ya xauki nauyin tsare Alqur’ani shi da kansa, kamar yadda
ya ce, “Lalle mu ne muka saukar da Ambato (Alqur’ani), kuma lalle mu, haqiqa,
masu kiyayewa ne gare shi.” (Suratul Hijr: 9). Haka nan, ya tsare Sunna ta hanyar
umarni da riqo da Sunna da yaqar bidi’a a bisa harshen Manzonsa, kamar yadda
muka gani a cikin hadisai ingantattu.
Saboda haka, masu yaqar bidi’a suna bin umarnin Manzon Allah ne, ba wani
abu sabo suke qirqira ba. Su masu gadin Musulunci ne, masu tsare shi daga
lalacewa kamar yadda tsoffin addinai suka lalace. Ba don aikin masu yaqar bidi’a
ba da yanzu Musulunci ya zama kamar Kiristanci, babu abinda zai rage a cikinsa
sai sunansa kawai. Shi ya sa yaqar bidi’a ya zama mafi girman ibada, sama da
ibadojin nafila da yaqin jihadi, kamar yadda magabatan al’umma na qwarai suka
tabbatar.1
Bidi’a tana Rusa Duniya da Addini
Ma’anar bidi’a, kamar yadda muka gani a farkon littafin, ita ce, “Qagar wani
abu a cikin addini wanda ya yi kama da addinin, amma ba ya cikin addini.”2
Wannan yana nufin bidi’a algus ce a cikin addini, kamar yadda za’a qara ruwa a
cikin nono don nonon ya qara yawa. Babu shakka qara ruwa a cikin nono vata
nonon ne, kuma ko yaya ruwan ya gauraya da nonon ba zai zama nono ba. Banda
wannan kuma, qara ruwa a nono, koda ya qara wa nonon yawa a ido, a haqiqa rage
masa inganci zai yi.
1 Domin bayani, duba farkon wannan littafi.
2 A duba Ihya’us Sunna wa Ikhmadul Bidi’a na Usmanu Danfodiyo, bugun Darul Fikir, Bairut, 1962, shafi na 22.
28
Da za mu xauki misalin algus a nono mu mayar da shi algus a cikin magani,
da sai munin al’amarin ya qara bayyana. Domin maganin da aka qara masa ruwa,
banda rasa qarfinsa na magance ciwo, yana kuma iya zama sanadin cuta. Wannan
dai-dai wa daida shi ne misalign bidi’a a addini.
Idan muka xauka cewa, addinin Musulunci ga Musulmi shi ne maganin
matsalolin duniya da na lahira, sai mu fahimci cewa yi wa wannan magani algus
babu abinda ya fi shi haxari.
Haxarin bidi’a ga addini a fili yake; saboda ibadar mai bidi’a ba’a karvar
ta. Idan kuwa bidi’ar ta zamo a cikin quduri ne ko aqida, to a wannan lokaci
haxarinta ya fi tsanani, saboda tana iya kai mai ita ga kafirci, wal iyazu billahi!
Amma dangane da haxarin bidi’a ga rayuwar Musulmi, ya ishe mu misali
yadda kixe-kixen bidi’a na yabon Annabi (wai ma!) da waliyyai ya kai mu ga
kixe-kixen finafinan Hausa, da yadda samarin al’umma suka zama ‘yan daudu a
yayin da ‘yan matan Musulmi suka zama kilakai. Bari mu daina yaudarar kanmu.
Duk mace Musulma, baliga, da ta kaxa gabanta, ta kaxa bayanta, aka yi kallo aka
biya, to wannan sunanta KARUWA. Haka nan, duk Musulmin da ya bar ‘yarsa ko
matarsa, ko wata mace da yake da hannu a kanta, tana neman kuxi ta hanyar yin
rawa ana kallo ana biya, to sunansa DUYUTH.
Yawancin mawaqan Hausa da ake kira mawaqan zamani, mazansu da
matansu, sun fara waqa ne daga makarantun Islamiyya na ‘yan bidi’a masu koya
wa yara waqe-waqe da sunan addini da son Annabi. Idan mai karatu yana so ya
tabbatar da wannan, sai ya saurari hira da ake yi da irin waxan nan mawaqa a
gidajen radiyo da sauran kafafen labarai, zai ji daga bakinsu.
A fili take cewa, matasan da suka zama kilakai da ‘yan hamsin ba za su
qulla wani abin ku-zo-ku-gani ba a al’amuran duniya. Banda lalata da zinacezinace
da shaye-shaye da aikata laifi, wani yayi har da kisan kai, ba ka jin kome
daga waxan nan matasa, waxanda bidi’a ta kai su ta baro.
Ba wai sana’ar fim ce ake zargi ba a nan, a’a tarbiyyar da ta vata sana’ar ita
ake zargi. Tarbiyyar ‘ya’yan al’umma a kan kixe-kixe da waqe-waqe da raye-raye,
da nuna musu cewa wannan addini ne, shi ne abin zargi. Idan aka lura, masu finafinan
Hausa da wasan kwaikwayo na zamanin da, waxanda gidajen talabijin na
29
qasar nan masu yawa suka kwashe shekaru suna nunawa, ba’a samu varna ta
bayyana a tsakaninsu ba, kamar yadda ba su yi mummunan tasiri ga masu kallon su
ba, saboda su ba su tarbiyyantu a cikin bidi’a ba. Maimakon haka, sun taso a cikin
al’umma wacce take qyamar bidi’a, saboda haka fina-finansu da wasan
kwaikwayonsu ba su vata tarbiyyar mutane ba.
Kafirai Suna Abota da ‘Yan Bidi’a
Saboda tasirin bidi’a mummuna na rusa addini da duniya, maqiyan
Musulunci suna abota da masu yaxa bidi’a da masu kira zuwa gare ta. Wani dalili
kuma da yake kusanta ‘yan bidi’a da kafirai shi ne cewa wata bidi’ar, kamar bidi’ar
Shi’a, a haqiqa daga cikin kafircin ta fito.1 Don haka dangantaka tsakanin irin
waxan nan bidi’o’i da kafirai ta wuce dangantakar abokai, dangantakar ‘ya’ya da
iyayensu ce.
A littafi na biyu a Jerin Littafan Sufanci, na rubuta kamar haka:
Bidi’a kishiyar Sunna ce kuma ita ce adireshin vata, kamar yadda Salim
Alhilali yake faxi a cikin littafinsa Albid’ah wa Atharuhal Sayyi’ fil Ummah.
Wannan ya sa ake samun karkata ga juna da soyayya da qauna da jivinta tsakanin
‘yan bidi’a da mabiya sauran addinai karkatattu. Kuma gwargwadon kaushin
bidi’a, gwargwadon kusancin masu bin ta da waxan nan mutane. Wannan ya sa
‘Yan Shi’a suka fi sauran ‘yan bidi’a duka kusanci da kafirai da mushirikai a
tsawon tarihinsu, saboda bidi’arsu ta fi ko wacce bidi’a kaushi da muni.
Idan mutum yana neman misali a kan wannan, sai ya dubi auren zobe da ya
kasance tsakanin madugun ‘yan Shi’a na Nijeriya, Malam Ibrahim Ya’aqub
Alzakzaki, da gwamnatin Olusegun Obasanjo. Zakzaki ya shekara ishirin yana
adawa da gwamnatoci dabam-daban, yana kiran su gwamnatocin xagutu.
Gwamnatin Shehu Shagari da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da Sani
Abacha da Abdussalami Abubakar duka a wurin Zakzaki gwamnatocin kafirci ne
da xagutanci; sai gwamnatin Obasanjo ita ce Musulma! Zakzaki ya yi tsundum a
cikin wannan gwamnati, inda ya karvi muqamin mai bai wa shugaban qasa
shawara na musamman, kuma Obasanjo ya yi amfani da shi wajen qara rarraba kan
1 Dangane da tushen Shi’anci, duba Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a, shafi na 7-9.
30
Musulmi da raunana qarfinsu, da nufin cimma manufarsa ta karya Musulmin
Nijeriya da danne su da mayar da su bayi a qasarsu ta haihuwa.
Alaqar ‘yan Shi’a da kafiran Nijeriya ta kai a yau suna fita tare a wajen
bukukuwan addini na ‘yan Shi’a, kamar yadda muke gani a jerin gwanonsu da
suke kira Maulidi, inda Kiristoci suke fitowa su ma a jera tare da su, alhali suna
xauke da Kuros, watau katakon da suke bautawa.
Sufanci shi ma, a matsayinsa na tafarkin bidi’a, yana da kyakkyawar
dangantaka da kafirai tun ba yau ba. Ga misali, tun shekaru aru-aru marubutan nan
kafirai da aka fi sani da sunan Gabasawan-Giri (Orientalists), sun yi ta yin rubucerubuce
suna yabon Sufanci, suna bayyana cewa ya fi ko wace mazhaba ta
Musulunci sassauci da inganci. Mashahuran Gabasawan-Giri kamar su Bayahude
Kenneth Cragg mai littafin The Call from the Minaret da Bayahude Gold Zeher
mai littafin Studies in the Sunnah da Banasare Gibb mai littafin Whether Islam? da
sauransu, duka sun yabi Sufanci a cikin rubuce-rubucensu, inda suka bayyana shi
da cewa shi ne Musulunci mai sassauci, wanda ya san girman sauran addinai kuma
yake zaman lafiya da mabiyansu.
Amma mai karatu ba zai yi mamakin wannan dangantaka ba idan ya dubi
maganganun manyan Sufaye kamar su Muhyiddin binu Arabi, wanda suke yi wa
laqabi da Alshaihul Akbar, wanda yake cewa a cikin wata qasida tasa:
Haqiqa zuciyata ta kasance tana karvar ko wace irin sura (ta ibada),
(Ta zama) wurin kiwon bareyi da wurin ibadar Kiristoci.
(Ta zama) xakin gumaka da Haramin Makka,
(Ta zama) allunan Attaura da gafakar Qur’ani.
Ko kuma kamar yadda wani babban shaihinsu, Aljiyali, yake cewa:
Ina miqa kaina inda duk zuciyata ta ja ni,
31
Ba na jayayya da hukuncin son zuciya.
Wani lokaci ka gan ni cikin masallaci ina sallah,
Wani yayi kuma ka gan ni a coci ina holewa.
Idan yin haka ya zama savo a hukuncin Shari’a,
To lallai a hukuncin Haqiqa biyayya ne da xa’a!
Idan mai karatu ya duba sai ya ga cewa idan Yahudawa da Kirista sun yabi Sufanci
ai ba wani abu suka yi ba, a haqiqa, face ramawa kura aniyarta.
Bayan hare-haren da aka kai a qasar Amurka ranar Talata 11 ga watan
Satumba, 2001, gwamnatin Amurka ta xauki wasu matakai domin tunkarar
qalubalen masu jihadi waxanda take kira ‘yan ta’adda. Daga cikin waxan nan
matakai har da lalubo Musulmi waxanda suke bin Musulunci mai sassauci, irin
Musuluncin da Amurka za ta iya zaman lafiya da shi, da ba su taimako na dukiya
da xaurin gindin siyasa da goyon bayan kafafen yaxa labaru, da sauransu, domin a
yi amfani da su a yaqi Musulmi masu tsaurin ra’ayi (mabiya Sunna da sauran masu
jihadi), a gurvata koyarwar Musulunci, kuma a kashe wutar jihadi. An bai wa
Hukumar Leqen Asiri ta Amurka (C.I.A.) wannan aiki, kuma ba tare da vata lokaci
ba ta riqa zaqulo mabiyan xariqun Sufaye waxanda ke zaune a Amurka da Turai
da sauran qasashe, tana kafa su a manyan biranen duniya domin cimma wannan
manufa.
Sun kafa cibiyoyi da zawiyoyi kuma suna nan suna shagala da kixe-kixe da
raye-raye da koyar da miyagun aqidu da almarori waxanda suke sakwarkwata
qwaqwalen mutane, su yashe zukatansu, su mayar da su fanko, huhun-ma’ahu,
waxanda ba su da tushe, ba alqibla, ba madogara, sai iska tana yawo da su kamar
mai kayan kara. Wannan shi ne yadda Amurka take son Musulmi su zama; domin
ta samu sauqin taushe su, ta hore su, kuma ta cusa kafirci a cikin zukatansu
waxanda suke wayam.
Daga cikin irin waxan nan cibiyoyi akwai babbar zawiya da suka buxe a
birnin New York wacce wata shaihanya mace take shugabanta. Babban aikin
wannan zawiya, wacce take da reshe a birnin San Fransisco, shi ne ‘yantar da mata
32
Musulmi waxanda wai Musulunci yake bautar da su da danne haqqinsu, da kuma
qago wani Fiqihu na zamani wanda yake kulawa da haqqin mata! Daga cikin irin
mabiya wannan zawiya ne aka samu wata mace limamiya mai suna Dr. Amina
Wadud wacce ta jagoranci sallar Jumma’a, inda maza da mata suka tsaya a sahu
xaya. Wannan ya faru a birnin New York ranar 18 ga watan Maris, 2005 kuma
kafafen yaxa labarai na duniyar kafirai sun yayata shi, suna kiran sa “Abin tarihi
mai muhimmanci, kuma aikin tajdidin Musulunci mai nuna ci gaba!”
Akwai kuma wani shaihin xariqar Naqashabandiyya (reshe ne na xariqar
Qadiriyya) wanda suka kafa shi a tsibirin Quburus, ko kuma Cyprus (qasa ce ta
Turai wacce rabin mazaunanta Musulmi ne Turkawa, rabi kuma Kirista Girkawa).
Aikin wannan shaihi shi ne ya sa gaba da qiyayya tsakanin Larabawa da Musulmi
waxanda ba Larabawa ba, kuma ya wargaza tunanin Musulmin qasarsa, ya sa
hayaniya a cikin qwaqwalensu, ya bar su fankan-fayau.
Gidan talabijin na Aljazeera ya watsa wata hira da ya yi da wannan shaihi
ranar Alhamis, xaya ga watan Afrilu, 2004. Daga cikin maganganun da ya faxi a
cikin hirar ya ce wai sai da ya buga wa Annabi (SAW) waya ya nemi izini, sa’an
nan ya yarda ya yi hira da gidan talabijin xin!! Shaihin yana koyar da cewa
Larabawa ba bisa addini suke ba (yana nufin mabiya tafarkin Sunna da waxanda
ake kira ‘yan Wahhabiyya), domin su wai vawon Musulunci suke riqe da shi, shi
kuwa shaihin, da shi da ire-irensa, su ne suke riqe da qwanduwa!
Haka nan Amurka da kafircin duniya suke qoqarin ciccixa launin Musulunci
wanda suke kira mai sassauci, Musuluncin kixe-kixe da raye-raye da baracebarace,
Musuluncin almarori da bautar kusheyi, Musuluncin da idan an ce masa
“kule” ba ya cewa “cas” kuma idan an mare shi a wannan kunci sai ya juyo da
wancan shi ma a mara in ya so a zauna lafiya! Irin Musuluncinmu na Nijeriya daidai
wa daida, wanda idan Kirista suka kashe ‘ya’yansa, suka rushe garuruwansu da
dukiyoyinsu, suka kame matansu a matsayin ganima, sai shugabanni baki xaya su
taru su ce a zauna lafiya!
Wannan aiki na jaddada Musulunci da Amurka take yi tare da taimakon
abokanta masu sassaucin ra’ayi bai riga ya iso qasar nan ba tukuna ga saninmu,
amma ba ma fitar da tsammani cewa zai iso; domin alamomi suna nuna haka.
Shekarun baya kaxan, an yi wani taro na Sufayen duniya a Moroko, wanda qasar
33
Amurka ce ta xauki nauyin taron, kuma wani babban shaihi daga Nijeriya ya
halarta. Bayan gama taron, shaihin ya yi hira da gidan radiyon Muryar Amurka
(VOA) sashen Hausa, inda ya faxa wa duniya cewa, Amurka ba ta faxa da
Musulunci amma tana faxa da ‘yan Wahhabiyya ne waxanda su abokan gabar
Musulmi ne da Kiristoci baki xaya.
Wannan yana nufin shaihin xariqa, kuma xan Nijeriya, ya zama kakakin
gwamnatin Amurka, mai magana da yawunta, kuma mai kare ta. Kuma abinda ya
faxi ya nuna irin abubuwan da aka tauna a wajen taron.
Wannan duka tunatarwa ce da ya zama wajibi mu yi ta, “domin tunatarwa
tana amfanin muminai.” (Suratudh Dhariyat: 55).
Rufewa
A daidai sa’ad da nake rubuta wannan littafi, wani xan shiga shara ba
shanun addini ya yi rubutu a jaridar Daily Trust, yana sukan waxanda ya kira ‘yan
Wahhabiyya kuma yana kare ‘yan Shi’a, inda daga cikin maganganunsa yake
cewa: Musulunci ya yarda da ‘yancin addini don me za’a ce babu ‘yancin yin
mazhaba?1
Wannan ita ce musibar jahilci da muke fama da ita a qasar nan. Shi wannan
xan taliki ya yi amfani da hankalinsa ne, ba da nassin Alqur’ani ko Sunna ba, don
haka ya kai ga fahimtar cewa, tunda Musulunci ya ba da ‘yancin mutum ya yi
kafirci in shi ya zava, don me za’a ce babu ‘yancin yin mazhaba, kamar Shi’a
misali, tunda ai kome munin bidi’a ba ta kai ga kafirci ba. Wannan shi ne inda
hankalinsa ya kai shi.
Sai maikaratu ya dubi yadda gwanayen Turanci suke shaqe wuyan alqalami
suna rubutu a cikin jaridu dangane da Musulunci da hukunce-hukuncensa, suna
hukuntar da hankali da manxiqi, kamar suna jawabin bayan labarai.
Shi wannan xan taliki, wanda Turancinsa ya ruxe shi, yana ganin ya isa ya
faxi a saurara tunda ya qware a harshen Nasara, bai lura ba cewa, mutumin da
Musulunci ya ba ‘yancin yin addinin da ya ga dama shi ne wanda bai riga ya shigo
1 Daily Trust, fitowar Jumma’a 18 ga watan Maris, 2016, shafi na 59.
34
Musulunci ba tun farko. Amma idan ya riga ya shigo to dole ne ya bi Musulunci,
ba Musuluncin ne zai bi tunaninsa da ra’ayinsa ba, kuma bai da ‘yancin da zai fita
tunda ya shigo da zavin kansa.
“Babu tilastawa a cikin addini.” (Suratul Baqara: 256) wannan magana ce da
Alqur’ani yake fuskantar da ita ga wanda bai riga ya shigo Musulunci ba, amma
wanda ya shigo to ga abinda Alqur’ani yake ce da shi: “Kuma ba ya halatta ga
mumini ko mumina, idan Allah da Manzonsa suka hukunta wani al’amari, ya zama
suna da wani zavi daga gare su. Kuma wanda ya sava wa Allah da Manzonsa, to,
haqiqa ya vata vacewa mai bayyana.” (Suratul Ahzab: 36). Hukuncin Allah shi ne
Alqur’ani kuma hukuncin Manzonsa shi ne Sunna.
Wata qila wani ya yi tambaya: To wane ne yake da damar faxin abinda
Allah yake nufi da aya, ko Annabi yake nufi da Hadisi, watau waye yake da damar
fassara nassi da bayanin manufarsa?
Amsa ita ce: Sahabban Annabi (SAW), Allah ya qara yarda a gare su baki
xaya, su ne ke da damar fassara nassi da bayanin manufarsa. Saboda su suka karvo
nassin daga bakin Annabi (SAW), ya laqqana musu shi, ya bayyana musu shi, ya
koya musu shi a aikacr. Kuma Allah ya yarda cewa sun fahimci saqon da ya aiko
Annabinsa da shi, don haka ya kira su muminai, kuma ya yi musu albishir da
sakamakon aljanna tun a duniya. Wannan shi ne abinda Ahalus Sunna wal Jama’a
suke nufi da faxin: Riqo da Kitabu da Sunna a kan fahimtar magabata.
Yaqar bidi’a wajibi ne a kan al’umma, xaixaekunta da qungiyoyinta da
hukumominta. Wannan wajibi Allah ne ya wajabta shi da Manzonsa. Da yaqar
bidi’a ne Musulunci yake ci gaba da zama garai-garai kamar yadda Allah ya saukar
da shi. Ba don yaqar bidi’a ba, da yanzu addini ya Musulunci ya zama kamar
Kiristanci, inda fada-fada a wasu qasashe suke xaura aure tsakanin maza biyu,
watau suke halasta luwaxi, duk da cewa an la’anci wannan mummunan aiki a cikin
Bayibul.
35