Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 6


Ahalul Baiti


a mahangar


‘Yan Shi’a


da


Ahalus Sunna


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


Gabatarwa


‘Yan Shi’a suna da’awar son Ahalul Baiti, da qaunar su, da jivintar


su, da yin biyayya a gare su, da koyi da su. Suna iqirarin cewa wai suna


karvo addininsu daga shugabannin Ahalul Baiti, musamman Sayyidina


Ali da Hassan da Hussaini, Allah ya qara musu yarda, da kuma


jikokinsu waxanda suke kira Imamai.


A lokaci guda kuma, ‘yan Shi’a suna dangana wa Ahalus Sunna


qin Ahalul Baiti da gaba da su da rashin girmama su. Suna xauko abin


tun daga tushe, inda suke cewa wai Sahabban Annabi(SAW), Allah ya


qara musu yarda, sun nuna matuqar gaba da qiyayya ga Ahalul Baiti,


sun zalunce su, kuma sun hana musu haqqoqinsu, ciki har da haqqinsu


na shugabantar al’umma bayan rasuwar Annabi(SAW). Kuma suna


ganin daga nan ne Ahalus Sunna, a matsayin su na mabiyan Sahabbai,


masu koyi da su, suka gado wannan qiyayya da gaba ga Ahalul Baiti.


Manufar wannan littafi, in Allah ya yarda, ita ce warware wannan


mas’ala a ilmance, kuma a bisa doron adalci.


Littafin zai yi bayanin ma’anar Ahalul Baiti a mahangar ‘yan


Shi’a, da yadda suka xauke su, da yadda suka karkasa su gida-gida,


wasu suna yin burus da su, wasu kuma su xaukaka su, su kambama su


har ya zuwa matsayin bauta da allantarwa.


3


Kuma har ila yau, littafin zai yi bayanin ma’anar Ahalul Baiti a


mahangar Ahalus Sunna, da yadda suke xaukar su, da yadda suke


qaunar su, suna girmama su, suna yin koyi da su kamar yadda suke yin


koyi da Sahabbai, kuma ba sa bambance wa tsakanin su, watau su


rungumi wasu, wasu kuwa su jefa su a kwandon shara kamar yadda ‘yan


Shi’a suke yi.


Sa’an nan daga bisani, littafin zai qyale mai karatu ya yi hukunci


shi da kansa a kan wane tafarki ne ya fi dacewa da Shari’a a wajen


muamalantar iyalin gidan Annabi(SAW), Ahalul Baiti: tafarkin ‘yan


Shi’a ko na Ahalus Sunna?


Kuma a nan, kafin mu rufe wannan gabatarwa, muna tuna wa mai


karatu cewa, kamar yadda muka saba a rubuce-rubucen mu, za mu


dogara kacokan a kan littafan malaman Shi’a wajen bayanin mahangar


su da ra’ayinsu, kamar yadda za mu dogara da littafan malaman Sunna a


wajen bayanin mahangar su da ra’ayinsu. Za mu yi haka domin tabbatar


da adalci wanda Allah ya yi umarni da shi, kuma domin yanke hujja da


bayanin mahajja.


Muna roqon Allah Maxaukaki ya xora mu a kan sawaba, ya sanya


ihilasi a cikin ayyukan mu da maganganun mu, kuma ya amfani


Musulmi da wannan xan qaramin aiki. Allah shi ne abin dogaro.


4


Babi Na Xaya


Ahalul Baiti a mahangar Ahalus Sunna


Da farko, za mu fara gabatar da bayani a kan Ahalul Baiti daga mahangar


Ahalus Sunna, kafin daga bisani mu juya ga mahangar ‘yan Shi’a don mu gwada


mu ga bambanci. Kuma abinda duk za mu qarrara a nan zai fito daga littafan


malaman Sunna sanannu, waxanda suka shahara da cewa su mabiya Sunnar


Annabi(SAW) ne kuma masu qin bidi’a.


Ma’anar Ahalul Baiti A Wajen Ahalus Sunna


Asalin kalmar ahalu tana nufin matar mutum, kuma tana nufin xaya ko da


yawa (watau kalmar tilo ce kuma jama’u a lokaci guda). Ita kuwa kalmar baiti


abinda take nufi gida. Idan aka ce ahalul baiti na mutum to ana nufin mutanen


gidansa wanda ya haxa da matansa da ‘ya’yansa da dukkan waxanda suke gidan na


zuri’a da makusanta.


Akwai kuma xaya kalmar mai kama da wannan kuma mai ma’anarta, watau


alu, ko kuma kamar yadda muke faxi da Hausa: alaye. Waxannan kalmomi biyu


ma’anarsu xaya, ba bambanci. Amma idan aka danganta waxannan kalmomi ga


Annabi(SAW), aka ce Ahalu Baitinsa ko kuma Alayensa, to malamai sun yi savani


dangane da ma’anarsu, ko kuma mu ce dangane da waxanda suka qunsa daga cikin


iyalin Annabi(SAW) da zuri’arsa.


Ra’ayi na farko. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa Ahalul Baiti, ko


kuma Alaye, su ne waxanda sadaka ta haramta a kansu. Dalilin masu wannan


ra’ayi shi ne hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito cewa, “Manzon Allah(SAW)


5


ya kasance ana kawo masa dabino lokacin girbinsa; sai wannan ya kawo dabino,


wancan ya kawo dabino har ya taru ya yi tsibi. Sai Hassan da Hussaini (suna yara)


su riqa yin wasa da dabinon. (Wata rana) xayansu ya xauki dabino guda ya sa a


bakinsa. Sai Manzon Allah(SAW) ya gan shi, sai ya fitar da dabinon daga bakinsa,


sa’an nan ya ce, “Ba ka san cewa Alayen Muhammadu ba sa cin sadaka ba?!”1


Wannan hadisi ya nuna a fili cewa Hassan da Hussaini suna cikin Alayen


Annabi, watau Ahalul Baiti nasa. Amma su ke nan su kaxai su ne Ahalul Baiti ko


kuwa? A’a, akwai wasu bayan su. Bayanin hakan kuwa an same shi a cikin


hadisin da Imam Muslim ya ruwaito cewa, “Abdul Muxxalib xan Rabi’a ya ba da


labari cewa babansa Rabi’a xan Harisa xan Abdul Muxxalib da shi da Abbas xan


Abdul Muxxalib sun faxa wa Abdul Muxxalib xan Rabi’a da Falalu xan Abbas,


Allah ya yarda da su, (suka ce): Ku tafi wurin Manzon Allah(SAW) ku ce masa:


Ka saka mu cikin masu aikin tattara sadaka. Sai ya ce musu: Waxannan sadakokin


dattin mutane ne kawai, kuma lalle ba sa halasta ga Muhammad da Alayen


Muhammad.”2


Wannan hadisi yana nunawa a bayyane cewa ba ‘ya’yan Annabi ne kawai,


ko jikokinsa, su ne Ahalul Baiti ba, a’a har ma da baffanninsa da ‘ya’yayensu.


Domin su waxannan mutane guda biyu da aka ambata a cikin hadisin cewa sun


tambaye shi ya saka su cikin masu aikin tattara zakka, watau Abdul Muxxalib xan


Rabi’a da Falalu xan Abbas ‘ya’yan baffanninsa ne, guda abokin wasansa ne,


gudan kuma xan abokin wasansa ne. Saboda haka, xaya qani ne, xayan kuma xa


ne a wajensa. (Abdul Muxxalib da aka ambata a hadisin an sa masa sunan kakansa


ne na biyu.)


1 A duba Sahihul Bukhari. Muslim ma ya fitar da irinsa.


2A duba Sahihu Muslim.


6


Wannan shi ne ra’ayin malamai kashi na farko, cewa ‘ya’yan Annabi(SAW)


da jikokinsa da baffanninsa da zuri’arsu su ne Ahalul Baiti. Daga cikin masu


wannan ra’ayi akwai Abu Hanifa da Shafi’i da Ahmad binu Hanbal da wasu


malaman mazhabar Malikiyya.1


Ra’ayi na biyu. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa alayen Annabi(SAW)


su ne ‘ya’yansa da jikokinsa da kuma matansa na aure kawai. Sun kafa hujja da


hadisai guda biyu. Na farko hadisin Humaidin Assa’idi cewa Sahabbai sun tambayi


Annabi(SAW) ya za su yi masa salati? Sai ya ce, “Ku ce: Ya Allah ka yi tsira ga


Muhammad da matayensa da zuri’arsa kamar yadda ka yi tsira ga Ibrahim, kuma


ka yi albarka ga Muhammad da matayensa da zuri’arsa kamar yadda ka yi albarka


ga Ibrahim, lalle kai ne abin godewa, mai girma.”2 Na biyu hadisin da yake cewa,


“Ya Allah ka yi tsira ga Muhammad da alayen Muhammad.”3 Suka ce hadisi na


biyu ya fassara na farkon, kuma ya nuna qarara cewa matan Annabi(SAW) da


zuri’arsa su ne alaye, ko kuma Ahalul Baiti nasa. Yawancin malaman Malikiyya


suna cikin masu wannan ra’ayi, kuma shi ne zavin manyan malamai, ciki har da


Ibnu Taimiya, Allah ya rahamshe su baki xaya.4


Wannan ra’ayi yana da qarfi ainun kuma masu shi suna da hujjoji qarfafa da


dalilai masu yawa, bayan waxanda muka ambata a sama. Daga cikinsu akwai


hadisin Innar Muminai A’isha, Allah ya qara mata yarda, ta ce, “Alayen


Muhammad ba su tava qoshi da gurasa tare da abin tsomi (miya ko romo) ba


kwana uku a jere, har ya koma ga Allah mai girma da xaukaka.”5 A wannan hadisi,


Innarmu A’isha, Allah ya qara mata yarda, tana ba mu labarin yanayin rayuwar


1A duba Almuntaqa sharhin Muwadda na Abul Walid Sulaiman binu Khalaf Albaji, bugun Darul Kitabil Islami,


Sa’udiyya, ba tarihi, mujalladi na 2, shafi na 153.


2 Bukhari da Muslim.


3 Bukhari da Muslim.


4 A duba Attamhid sharhin Muwadda na Abu Umar Yusuf binu Abdillah binu Abdil Barri, bugun Wazaratu Umumil


Awqaf, Maroko, 1384, mujalladi na 17, shafi na 303.


5 Sahihul Bukhari.


7


iyalin Annabi(SAW) da irin abincin da ake ci a gidansa. Kuma ta yi amfani da


kalmar alu, ko kuma alaye, wacce babu shakka ta haxa da matansa da ‘ya’yansa.


Har yau, masu wannan ra’ayi sun kafa hujja da aya, faxin Allah Maxaukaki,


“Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa ba daga mata, idan kun yi taqawa,


saboda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa


ya yi xammani, kuma ku faxi magana ta alheri. Kuma ku tabbata a cikin gidajenku,


kuma kada ku yi fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyar farko. Kuma ku


tsaida sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi xa’a ga Allah da Manzonsa.


Allah na nufin ya tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida


(Ahlal Baiti). Kuma ya tsarkake ku tsarkakewa.” (Suratul Ahzab: 32-33). Suka yi


bayani cewa, waxannan ayoyi waxanda suke magana da matan Annabi kai tsaye


sun kira su Ahalul Baiti, saboda haka duk wanda ya shiga qarqashin wannan suna


to bayansu yake bi. Kuma wannan magana haka take idan aka duba ta a hankalce;


domin matan mutum su ne haqiqanin mutanen gidansa, saboda ko ‘ya’yan mutum


wannan sifa ba ta lazimtar su a ko da wane lokaci; domin suna iya ficewa daga


gidan (su zama ba mutanen gidan ba) imma zuwa gidajen aure idan ‘ya’ya mata ne


ko kuma su yi gidan kansu idan maza ne. Matan mutum kuwa su ne mutanen


gidansa na har abada.


Muna qara karfafa wannan ra’ayi, muna bayyana hujjojinsa a fili, saboda


mai da martani ga ‘yan Shi’a waxanda suke ganin cewa matan Annabi(SAW),


Allah ya qara musu yarda, ba sa cikin Ahalul Baiti, kamar yadda za mu gani a nan


gaba kaxan in Allah ya yarda.1


Ra’ayi na uku. Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa, alayen Annabi(SAW),


watau Ahalul Baiti, su ne mabiyansa dukkaninsu baki xaya har zuwa ranar


1 Domin karin bayani, sai a duba Aljami’u li Ahkamil Qur’an na Imam Qurdubi, bugun Darush Sha’ab, Alqahira,


1372, mujalladi na 2, shafi na 290.


8


Alqiyama. A wajen masu wannan ra’ayi duk Musulmi Ahalul Baiti ne domin


ma’anar alu, ko kuma alaye, a wajensu shi ne mabiya. Daga cikin dalilansu sun


kafa hujja da waxannan ayoyi: faxin Allah Maxaukaki, “Wuta ana gitta su a kanta,


safe da maraice, kuma a ranar da Sa’a take tsayawa, ana cewa: Ku shigar da


mutanen Fir’auna (alu Fir’auna) a mafi tsananin azaba.” (Suratu Gafir: 46). Da


faxinsa Maxaukaki, “Lalle mun aika iskar tsakuwa a kansu, face mabiyan Luxu


(alu Luxin), mun tserar da su a lokacin asuba.” (Suratul Qamar: 34). Suka ce a


cikin waxannan ayoyi biyu an yi amfani da lafazin alu Fir’auna da alu Luxin ana


nufin mabiyan Fir’auna da mabiyan Annabi Luxu(AS), wanda yake nuna ma’anar


alu shi ne mabiya. Daga cikin masu wannan ra’ayi akwai wasu ‘yan mazhabar


Shafi’iyya, ciki har da mashahurin malamin nan, Imam Annawawi mai littafin


Arba’una Hadisan.


Akwai wasu ra’ayoyi dangane da ma’anar Ahalul Baiti banda waxanda


muka zana, amma ba za mu tsawaita da ambatonsu ba. Za mu taqaita a kan uku da


muka rattaba saboda qarfin hujjojinsu, musamman ma ra’ayi na tsakiya wanda shi


ne zavin manyan malamai. Saboda haka, ma’anar Ahalul Baiti a wajen Ahalus


Sunna su ne matan Annabi(SAW) da zuri’arsa, watau ‘ya’yansa da jikokinsa, haka


zalika baffanninsa da zuri’o’insu waxanda suka karvi Musulunci. Duk wata falala


da baiwa da daraja wacce ta kevanci alaye to ta game waxannan duka, kuma duk


sa’ad da Musulmi ya yi salati ga alaye tare da Annabi(SAW) to a gare su duka


salatin yake faxawa.


Matsayin Ahalul Baiti A Wajen Ahalus Sunna


Ahalus Sunna suna xaukar Ahalul Baiti a matsayin Musulmi na gari, masu


baiwa da xaukaka, waxanda Allah ya zave su, ya kevance su da falala da baiwa


9


saboda kusancinsu da Annabi(SAW). Saboda haka suna girmama su irin girman da


ya cancance su a Shari’a, ba tare da azarvavi ko wuce gona da iri ba, kuma suna


qaunar su saboda sonsu son Annabi ne, kuma son Annabi son Allah ne.


Waxanda suke a cikinsu Sahabbai ne, kamar Ali da Faxima da Hassan da


Hussaini da Aisha da Hafsa da Abbas da xansa Abdullahi, da Ja’afar da Aqilu da


sauransu, to waxannan suna ba su daraja biyu: kasancewarsu Sahabbai kuma


kasancewarsu Ahalul Baiti. Waxanda kuma ba Sahabbai ba ne, ba su rayu tare da


Annabi ba, kamar sauran ‘ya’yan Faxima qanana Ruqayya da Ummu Kulthum, da


sauran ‘ya’yan Ali waxanda ya haifa da wasu matan nasa dabam, irin su


Muhammad binul Hanafiyya da ‘yan uwansa, da sauran zuri’o’in baffanin


Annabi(SAW) da ‘yan uwansa: zuri’ar Abbas, zuri’ar Hamza, zuri’ar Aqilu,


zuri’ar Ja’afar, da sauransu, to waxannan ana ba su darajarsu da Allah ya ba su ta


kusanci ga Annabi(SAW) da haxa dangantakar jini da shi. Haka nan kuma, Ahalus


Sunna suna yin salati ga Ahalul Baiti tare da Annabi(SAW) a duk sa’ad da suka yi


masa salati.


Ahalus Sunna suna son Ahalul Baiti so irin na Musulunci, so na Shari’a, ba


so na jahiliyya ba. Saboda haka, ba sa wuce makaxi da rawa a wajen qaunar su da


girmama su. Ba sa dangana musu almarori, ko su qudure cewa suna da wani kayan


gado na annabta wanda suka kevanta da shi koma bayan sauran Musulmi, ko su ce


sun san gaibu, ko kuma su kaxai suka cancanci khilafa, da sauran irin waxannan


qudure-qudure na masu addini da jahilci ko son zuciya. A wajen mu’amala da


Ahalul Baiti, Ahalus Sunna suna tsayawa a kan koyarwar Alqur’ani da Sunna, ba


sa wucewa ko taqi xaya.


10


Haqqoqin Ahalul Baiti a kan Musulmi


Ahalus Sunna suna qudure cewa, Ahalul Baiti Allah ya qara musu yarda


baki xaya, suna da haqqoqi a kan ko wane Musulmi waxanda yake wajibi ne a


kiyaye da su, kuma a bayar da su ta fuskar da ta kamata. Waxan nan haqqoqi sun


haxa da:


1. Qaunar su da jivintar su da ba su girma, saboda faxin Allah Maxaukaki, “Ka


ce (ya Muhammad): Ba na tambayar ku wata ijara a kansa (iyar da aike),


face dai soyayya ta cikin zumunta.” (Suratush Shura: 23) Ibnu Kathir ya


bayyana cewa, daga cikin ma’anonin ayar tana nufin, “Ku so ni ta hanyar


son makusantana. Watau ku kyautata musu.” Kuma ya dangana ruwayar


haka ga Imam Bukhari.1


2. Yin salati a gare su tare da Annabi(SAW), watau haxawa da su a salati duk


sa’ad da aka yi masa. Kuma ana iya yin salati ga xayansu yayin da aka


ambace shi shi kaxai.


3. Ba su kaso daga khumusi (watau kashi xaya bisa biyar) na ganima, saboda


faxin Allah Maxaukaki, “Kuma ku sani cewa, abin da kuka sami ganima


daga wani abu, to, lalle ne Allah yana da humusinsa kuma don Manzo, kuma


saboda masu zumunta.” (Suratul Anfali: 41) Ibnu Kathir ya ce malamai


masu yawa suna ganin kason masu zumunta ana ba da shi ga Banu Hashim


da Banul Muxxalib.2


4. Quduri mai qarfi da cewa nasabar Annabi(SAW) ita ce mafi xaukakar


nasaba, kuma danginsa su ne mafi darajar dangi.


5. Kare su da tsare mutuncinsu da kuvutar da su daga qarerayin da aka laqa


musu a bisa jahilci ko son zuciya. Misali irin qarerayin da malaman Shi’a


1 Duba Tafsiru Ibni Kathir na Abul Fida Isma’il binu Kathir, bugun Maktabatus Safa, Alqahira, 1423/2002, mujalladi


na 7, shafi na 123.


2 Duba Tafsiru Ibni Kathir, mujalladi na 4, shafi na 37.


11


suke laqa musu na abubuwan da suka sava da abinda kakansu, Manzon


Allah(SAW), ya zo da shi na haske da shiriya dake cikin Qur’ani da Sunnah.


Muhimmyar Faxakarwa: Waxan nan haqqoqi da aka ambata suna tabbata da


sharuxxa biyu: Musulunci da tabbatar nasaba. Watau mutum sai nasabarsa ta


tabbata cewa ya haxa jini da Annabi(SAW), kuma ya karvi Musulunci sa’an nan


yake cancantar waxan nan haqqoqi.


12


Babi Na Biyu


Ahalul Baiti a mahangar ‘Yan Shi’a


Bayan mun ga ma’anar Ahalul Baiti da matsayinsu a wajen Ahalus Sunna,


bari a yanzu mu karkata akalar alqalami zuwa ga ra’ayin ‘yan Shi’a da qudurinsu


dangane da waxan nan zavavvun bayi da yadda suka xauke su. Kuma, kamar


yadda muka faxi a gabatarwa, za mu dogara kacokan wajen rubuta wannan babin a


kan littafan malaman Shi’a waxanda suka shahara kuma Rafilawa a ko ina a


duniya suke izna da ilminsu da maganganunsu.


Ma’anar Ahalul Baiti A Wajen ‘Yan Shi’a


A wajen ‘yan Shi’a, Faxima da Ali da ‘ya’yansu Hassan da Hussaini, Allah


ya qara musu yarda baki xaya, da zuri’o’insu su kaxai su ne Ahalul Baiti. Sun


gina wannan ra’ayi nasu a kan wani hadisi da suke ruwaitowa cewa, Innar


Muminai Ummu Salmah, Allah ya qara mata yarda, ta ce, “Ayar ‘Allah na nufin ya


tafiyar da qazanta kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida, kuma ya tsarkake


ku tsarkakewa’ ta sauka a xakina ina zaune kusa da qofa, sai na ce: Ya Ma’aikin


Allah, ni ba na cikin mutanen Babban Gida? Sai ya ce: ‘Ke kina bisa alheri, ke


kina cikin matan Annabi(SAW).’ Ta ce: A cikin xakin Manzon Allah da Ali da


Faxima da Hassan da Hussaini suna zaune, sai (Annabi) ya lulluve su da wani


tufafi, sa’an nan ya ce, ‘Ya Ubangiji, waxannan su ne iyalin gidana, ka tafiyar da


qazanta daga gare su kuma ka tsarkake su tsarkakewa.”


Wannan hadisi malaman Ahalus Sunna sun ruwaito irinsa amma banda qarin


da aka ce wai Innar Muminai Ummu Salmah, Allah ya qara mata yarda, ta tambayi


13


Annabi(SAW) ko ita ba ta cikin Ahalul Baiti, ya ce e. Wannan qarin bai inganta


ba.1


Amma su ‘yan Shi’a sun yarda da wannan qarin, kuma a dalilinsa ne suka


kore matan Annabi(SAW) daga cikin Ahalul Baiti. Sai dai ba Uwayen Muminai


kawai suka kore ba, sun ma kore har da wasu ‘ya’yan Faxima xin. Faxima ta


haifawa Ali ‘ya’ya huxu. Su ne Hassan da Hussaini da Ruqayya da Ummu


Kulthum. Ruqayya ta rasu tana qarama, amma Ummu Kulthum ta girma kuma


ubanta ya aura wa Sarkin Musulmi Umar ita, har ta haifa masa xa mai suna Zaidu,


kuma tana cikin matansa da suka yi masa takaba. Shi wannan xan Zaidu ya girma


amma bai haihu ba.


Sa’an nan ‘yan Shi’a sun kore sauran xiyan Annabi duka, maza da mata, da


zuri’o’insu daga jimillar Ahalul Baiti. Kamar yadda suka kore dukkan baffanin


Annabi da zuri’o’insu.


Kai a cikin malaman Shi’a ma akwai waxanda suka ce Annabi(SAW) ba shi


da xiya mace sai Faxima kawai. Suka ce wai Zainab da Ruqayya da Ummu


Kulthum duka agololinsa ne; ‘ya’yan Nana Hadiza ne da ta haifa da mijinta na


farko.2 Wasu malaman nasu ma sun wuce nan, suka ce wai Hadiza ma ba


haihuwarsu ta yi ba, riqa su tayi!3 Kuma duka wannan sun yi haka ne don su kore


wa Sayyidina Usman(RA) auren ‘ya’yan Manzo biyu, watau Ruqayya da Ummu


Kulthum, Allah ya qara musu yarda, wanda hakan ya tabbata a tarihi kuma a


dalilinsa ne ya samu laqabin Zun Nuraini. Amma ina rowan ‘yan Shi’a da tarihi,


kuma ina ruwansu da ilmi?! Su kawai son zuciyarsu suka sani. Allah ya shirye su.


1 Imam Ahmad da Tirmizi sun ruwaito hadisin daga Ummu Salmah(RA) kuma Imam Muslim ya ruwaito shi daga


A’isha(RA). Duba bayani kan hadisin a cikin Tafsiru Ibni Kathir, mujalladi na 6, shafi na 193-195.


2 Domin wannan karyar ta rashin albarka, duba littafin Da’iratul Ma’arifish Shi’iyya na babban malaminsu, Hassan


Amin, bugun Darut Ta’aruf, Bairut, ba tarihi, 1/50.


3 Domin wannan karyar ta rashin kunya, duba littafin Al’istigatha fi Bida’is Thalatha na babban malaminsu Abul


Qasim Ali binu Ahmad Alkufi, bugun Darul Kutubil Ilmiyya, Qum-Iran, ba tarihi, shafi na 108.


14


Babu shakka akwai abin ta’ajibi dangane da ma’anar Ahalul Baiti a wajen


‘yan Shi’a. Su a wajensu Ali da Faxima da ‘ya’yansu guda biyu kawai, banda


sauran, su ne Ahalul Baiti. To me ya sa ba sa maganar Ummu Kulthum, ba sa


lasafta ta a cikin Ahalul Baiti alhali kuwa ita ma xiyar Faxima da Ali ce kamar


Hassan da Hussaini ba bambanci? Kuma ta ya za’a yi maganar mutanen gidan


mutum amma a ce matansa ba sa ciki? Wane irin gida ne za’a ce matan gidan ba


mutanen gidan ba ne, sai ‘ya’ya ne kawai mutanen gidan? Wannan hukunci ya


sava wa hankali da al’ada kamar yadda ya sava wa nassoshin Shari’a. Abu guda


kawai wannan hukunci ya dace da shi, shi ne son zuciya wanda ‘yan Shi’a suka


gina yawancin addininsu a kai.


Wani abin mamakin kuma shi ne, ko a cikin ‘ya’yan Faxima xin, su ‘yan


gaban goshin, banda Ummu Kulthum wacce suka jefar a juji, ko su ‘yan gaban


goshin a cikinsu akwai wasu zavavvu fiye da wasu. ‘Ya’yan Hussaini sun fi


‘ya’yan Hassan qima, kuma a cikinsu ne ake da imamai tara tsaba, ko kuma goma


in mun haxa har da ubansu Hussaini. Shi kuwa Hassan shi kaxai shi ne imami,


amma a cikin zuri’arsa babu imami ko xaya. Don me ya sa aka samu wannan


bambanci? Babu dalili, ba hujja sai son zuciyar ‘yan Shi’a kawai wanda, kamar


yadda muka faxi a baya kaxan, shi ne tushe da suka gina addininsu a kai.


Duba ka gani, mai karatu, yadda Shaixan yake wasa da hankalin ‘yan Shi’a.


Xiyan Faxima, Allah ya qara mata yarda, su kaxai su ne Ahalul Baiti. Kuma a


cikinsu banda Ummu Kulthum. Kuma, har yau, a cikin zavavvun, watau Hassan da


Hussaini, zuri’ar Hussaini suke da imamai, duk da cewa shi ne qani, amma zuri’ar


Hassan ba imami ko xaya a cikinsu.


Mutane masu aiki da hankali suna tambaya: Da wane dalili ‘ya’yan Hussaini


suka fi ‘ya’yan Hassan? Babu amsa mai gamsarwa sai ko hasashen tasirin


15


Majusanci na mutanen Iran. Tarihi ya tabbatar da cewa, a zamanin Sarkin Musulmi


Umar binul Khaxxabi, bayan an ci daular Majusawa ta Farisa (Iran) da yaqi,


Musulmi sun ci ganimar dukiyoyi da mataye. Daga cikin wannan ganima, Umar ya


baiwa Hussaini(RA) kyautar ‘yar Sarkin Farisa mai suna Shaharbano wacce


Hussaini xin ya mayar da ita sa-xaka. Wannan gimbiya kuma kwarkwara ita ce ta


Haifa wa Hussaini xansa Ali wanda ake wa laqabi da Zainul Abidin, wanda kuma


ta hanyarsa ne zuri’ar Hussaini ta xore.1 To da yake yawancin ‘yan Shi’a mutanen


Farisa ne, sai suka laqe wa zuri’ar Hussaini saboda ‘ya’yan xiyarsu ne. Dalili ke


nan da ya sa suka fifita su a kan zuri’ar Hassan.


Kamar yadda mai karatu yake iya gani, wannan abu (watau fifita ‘ya’yan


Hussaini a kan na Hassan) ba’a gina shi a kan wata hujja ko dalili ba, sai dai son


zuciya kawai. To ta qaqa son zuciya zai zama addini?


Matsayin Ahalul Baiti A Wajen ‘Yan Shi’a


A wajen ‘yan Shi’a, Ahalul Baiti, kamar yadda suka fahimce su, su kaxai su


ne Musulmi kuma babu mai zama Musulmi sai wanda yake son su kuma yake


jivintar su, jivinta da so waxanda suka dace da fahimtar Rafilawa. A kan wannan


ne suka gina aqidarsu cewa Sahabbai duka sun yi ridda bayan rasuwar


Annabi(SAW) sai mutum bakwai kawai. Waxannan mutane su ne Miqdad binul


Aswad, Abu Zarrin Algifari, Salman Alfarisi, Ammar binu Yasir, Abu Sasan


Al’ansari, Huzaifa binul Yaman da Abu Amra, Allah ya qara musu yarda.2


Waxannan Sahabbai bakwai da ‘yan Shi’a suka yarda da Musuluncinsu, babu


abinda ya raba su da sauran Sahabbai ‘yan uwansu sai kawai cewa sun yi qaurin


1 Babban malamin Nasaba dan Shi’a, Ibnu Anbata, ya tabbatar da wannan a cikin littafinsa, Umdatud Dalib fi


Ansabi Aali Abi Dalib, 192.


2 A duba babin Akidar ‘Yan Shi’a dangane da Sahabbai a cikin littafinmu Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a da Akidojinsu.


16


suna da kasancewa su masoyan Ali binu Abi Xalib ne kuma sun goyi bayansa a


rikicin da ya faru tsakaninsa da Mu’awiyya binu Abi Sufyan. Wannan yana nuna


cewa, a ganin ‘yan Shi’a, ba Musulmi sai Ahalul Baiti, sai kuma waxanda suka bi


su, suka jivince su. Don haka ne suka sanya imani da imamai a matsayin xaya daga


shika-shikan Musulunci. Babban malamin Hadisi a wajen ‘yan Shi’a, Muhammad


binu Ya’aqub Alkulaini, ya ruwaito Abu Ja’afar, imamin Rafilawa na shida, yana


cewa: “An gina Musulunci a kan abubuwa guda biyar: sallah da zakka da hajji da


azumi da wilaya (watau imama).”1 Idan mai karatu ya kula zai ga cewa, a cikin


wannan ruwaya ta ‘yan Shi’a imama ta maye makwafin Kalmar Shahada wacce


ba’a ambace ta ba. To imama, a wajen ‘yan Shi’a, ita ce Kalmar Shahada kuma sun


kawo ambatonta a qarshe domin vad da bami.


Don haka, matsayin Ahalul Baiti a wajen Rafilawa ya wuce a ce wai su


zavavvu ne, ko masu girma, ko masu falala a addini. A’a, sun wuce nan! Ahalul


Baiti a wajen ‘yan Shi’a su ne addinin kansa. Don su aka halicci duniya da lahira,


suna sama da annabawa da manzanni da mala’iku makusanta, don haka ya wajaba


a bauta musu. Wannan zai bayyana a fili idan muka yi darasun matsayin imamai a


wajen Rafilawa.


Matsayin Imamai A Wajen ‘Yan Shi’a


Matsayin imamai a wajen ‘yan Shi’a babu sama da shi, domin suna aza su a


bisa da annabawa da manzanni, kuma a wani yayi su ba su sifofin allantaka.


‘Yan Shi’a suna xaukar imamai a matsayin ma’asumai, waxanda ba sa


kuskure kuma ba sa aikata zunubai qanana ko manya, kamar annabawa da


manzanni ba bambanci. Saboda haka, ba sa mantuwa, ba sa tuntuve, ba sa sha’afa,


1 Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Teheran-Iran, ba tarihi,


mujalladi na 2, shafi na 18.


17


ba sa rafkanuwa. Dangane da wannan, wani babban malaminsu da ake kira


Muhammad binu Nu’uman Almufid, yana faxin, “Lalle imamai waxanda suke


tsaye matsayin annabawa wajen zartar da hukunce-hukunce da tsai da haddoji da


tsare shari’o’i da ladabtar da talikai ma’asumai ne kamar ismar annabawa, kuma


bai yiwuwa su yi rafkanuwa a cikin wani lamari na addini, kuma ba sa mance wani


abu na hukunce-hukunce.”1 Wani malamin nasu mai suna Abu Ja’afar Muhammad


binu Ali binu Hussain binu Musa binu Babawaihi Alqummi (wanda aka fi sani da


laqabin Assaduq) yana cewa, “Qudurinmu dangane da annabawa da manzanni da


imamai shi ne cewa su ma’asumai ne, tsarkaka ne daga dukkan wani datti. Kuma


cewa su ba sa aikata zunubi qarami ko babba, kuma ba sa savawa Allah abinda ya


umarce su kuma suna aikata abinda aka umarce su. Wanda ya kore musu isma


dangane da wani abu na lamarinsu to haqiqa ya jahilce su, kuma wanda ya jahilce


su to shi kafiri ne.”2


‘Yan Shi’a Rafilawa suna qudure cewa imamansu sun san gaibu, kuma suna


da sanin abinda ya faru tun farkon halitta da abinda zai faru har zuwa ranar


Alqiyama. Malaminsu Kulaini ya ruwaito daga imaminsu na shida, Abu Abdillahi,


ya ce, “Na rantse da Ubangijin Ka’aba, na rantse da Ubangijin wannan ginin


(Ka’aba) -ya maimaita sau uku- da na kasance tare da (Annabi) Musa da Haliru da


na faxa musu cewa ni na fi su sani, da na ba su labarin abinda ba su sani ba; domin


Musa da Haliru(AS) an ba su sanin abinda ya kasance ne (kawai) amma ba’a ba su


sanin abinda zai zo da abinda zai kasance ba har zuwa ranar Alqiyama. Mu kuwa


(watau imamai) mun gaji wannan ilmi daga Manzon Allah gado na haqiqa.”3


Malaminsu, Muhammad binu Nu’uman Almufid, ya tabbatar da wannan aqida


1 A duba Awa’ilul Makalat na Muhammad binu Nu’uman Almufid, bugun Darul Kitabil Islami, Bairut, 1403/1983,


shafi na 71-72.


2 A duba Aka’idul Ithnai Ashariyya na Ibrahim Almusawi Alzanjani, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, ba tarihi,


mujalladi na 2, shafi na 157.


3 Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, mujalladi na 1, shafi na 261.


18


tasu. Ya ce, “Imamai daga zuri’ar (Annabi) Muhammad (SAW) sun kasance suna


sanin abinda yake voye cikin zukatan wasu bayi, kuma sun san abinda zai kasance


kafin kasancewarsa.”1


‘Yan Shi’a suna qudure cewa wahayi yana sauka ga imamansu. Domin


tabbatar da haka, sun ruwaito daga imaminsu Abu Abdillahi, ya ce, “Mu ana ba mu


guzuri (na ilmi) dare da rana, kuma ba don ana ba mu guzuri ba da abinda yake


gare mu (na ilmi) ya qare. (Mai ruwaya) Abu Basir ya ce: Allah ya sanya ni fansar


ka, wane ne yake zuwa muku? Ya ce: Daga cikinmu akwai wanda yake gani da ido


quru-quru; daga cikinmu akwai wanda yake ji da kunnensa amo kamar amon sarqa


a cikin tasa. (Mai ruwaya) ya ce: Na ce: Allah ya sanya ni fansarka, waye yake


zuwa muku da wannan? Ya ce: Wani halitta ne wanda ya fi Jibirilu girma.”2 Mai


karatu yana iya gani cewa wannan ruwaya ba ta bar wani yanayi na saukar wahayi


ga annabawa da manzanni ba face ta tabbatar da shi ga imamai.


Har ila yau, ‘yan Shi’a suna wuce gona da iri wajen son imamansu da


girmama su da kambama su har su fifita su a kan annabawa da manzanni da


mala’iku makusanta ga Ubangiji. Ya zo a cikin irin ruwayoyin da suke danganawa


ga Annabi(SAW) cewa wai ya ce da Ali(RA): “Lallai Allah mai girma da xaukaka


ya fifita annabawansa manzanni a bisa mala’iku makusanta, kuma ya fifita ni a


kan dukkanin annabawa da manzanni. Ya kai Ali, fifiko a bayana ya tabbata a gare


ka da imamai masu zuwa a bayanka.”3 A cikin wani littafin nasu mai suna Haqqul


Yaqin fi Usulid Din, mai littafin, Abdullahi binu Shabbar, yana cewa, “Ya wajaba


a yi imani cewa Annabinmu da alayensa ma’asumai suna da fifiko a kan annabawa


1 Awa’ilul Makalat na Muhammad binu Nu’uman Almufid, shafi na 75.


2 Biharul Anwar na Muhammad Baqir Almajalisi, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, ba tarihi, mujallaadi na 26, shafi


na 53.


3 A duba Ilalush Shara’i’i na Muhammad binu Babawaihi Alqummi Assaduk, bugun Almaktabatul Haidariyya, Najaf-


Iraq, shafi na 5.


19


da manzanni da mala’iku makusanta saboda hujjoji masu yawan gaske da suka zo


da haka.”1


Banda wannan duka, Rafilawa suna tabbatar wa da imamansu sifofin


allantaka. Daga cikin irin abubuwan da suke danganta wa Ali binu Abi Xalib(RA)


akwai wannan ruwaya cewa wai ya ce, “Ni ne idanun Allah; ni ne hannun Allah; ni


ne qofar Allah.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Ni ne ilmin Allah; ni ne zuciyar


Allah mai kiyayewa; ni ne harshen Allah mai furuci; ni ne idanun Allah masu gani;


ni ne haqarqarin Allah; ni ne hannun Allah.”2


Dangana irin waxannan ruwaroyi na qarya bai tsaya kan Ali ba kawai, a’a


har ma ga Annabi(SAW) suna danganawa. Sulaim binu Qais ya ruwaito cewa


Manzon Allah(SAW) ya faxi ga Ali kamr haka: “Ya Ali, kai kana daga gare ni, ni


ina daga gare ka. An gauraya namanka da namana, da jininka da jinina…. Wanda


ya yi musun wilayarka ya yi musun allantakar Allah. Ya Ali, kai ne tutar Allah


mafi girma a bayan qasa bayana, kuma kai ne bango mai girma a ranar Alqiyama.


Wanda ya shiga inuwarka ya rabanta domin hisabin talikai duka yana hannunka


kuma makomarsu na gare ka. Mizani naka ne; siraxi naka ne; taron Alqiyama naka


ne; hisabi naka ne. Wanda ya fake da kai ya tsira kuma wanda ya sava maka ya


halaka. Allah ka shaida, Allah ka shaida.”3


Kamar yadda mai karatu yake iya gani, a wajen ‘yan Shi’a imamai su ne


komai. Suna gaba da annabawa da manzanni kuma suna tarayya da Ubangiji a


allantakarsa. Wannan ya sa aka samu wasu daga cikinsu waxanda suke bauta musu


kuma suna bayyana wannan a fili ta wajen irin sunayen da suke saka wa ‘ya’yansu,


kamar Abdul Hussain, Abdul Amir (Amir suna nufin Ali), da sauransu.


1 A duba Hakkul Yakin fi Usulid Din na Abdullahi Shubbar, bugun Darul Kitabil Islami, Bairut, ba tarihi, mujalladi na


1, shafi na 209.


2 A duba Basa’irud Darajat na Muhammad binu Hassan Alsaffar, bugun Manshuratul A’alami, Teheran-Iran, 1362,


shafi na 81.


3 Kitab Sulaim binu Qais na Sulaim binun Qais Alkufi, bugun Manshuratul A’alami, Teheran-Iran, ba tarihi, shafi na


244-245.


20


Wannan ita ce aqidar ‘yan Shi’a dangane da imamai, kuma wannan shi ne


yadda suka xauke su. Babu shakka wannan aqida ta sava da Alqur’ani mai girma


da hadisan Annabi(SAW) ingantattu. Kai ta ma sava da hankali lafiyayye. Haka


nan kuma ta sava da aqidar imaman su da kansu, saboda imaman Shi’a


dukkaninsu, tun daga kan Ali binu Abi Xalib har ya zuwa na qarshensu, mabiya


Sunnar Annabi ne, sai dai malaman Shi’a sun laqa musu qarerayi don su fake da


su, su samu dammar vatar da al’umma.


Wannan shi ne qudurin Ahalus Sunna dangane da imaman Shi’a, Allah ya


qara musu yarda, cewa duk abinda aka dangana musu wanda ya sava da Alqur’ani


da Sunna, to qarye ce ake yi musu. Muna roqon Allah ya isr musu wannan qarya


da qazafi da Yahudawa da Majusdawa suka laqa musu.


A nan gaba, za mu ware imamai da ambato, mu yi bayanin matsayinsu a


wajen Ahalus Sunna a wani littafi na musamman, in Allah ya yarda.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA